← Book details Billy Pinky Durlin Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 49

Sashe 28

Billy Pinky Durlin Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sae gashi har aka yi sati biyu ba wani bayani har umma tazo min da zancen ansa lokacin aure hakan yasa na firgita sosai har ina qoqarin sanar da umma akwai auren Bobby akai na amma na fasa,
nan na kira Feenah ta shiga kwantar min da hankali,wanda haka take min kullum har yau da Allah yasa suka ga Bobby kuma ina tunanin matsalar da ya samu ta kau a bisa furucin da ya min lokacin da ya bud'e idon shi.
Amma don Allah Abba kuyi haquri Ku yafe min wlh bada niya na aikata hakan ba,na tsorata ne da abin da Bobby zai sanar da ku domin na dauka cewa wani sharri zai min,amma don Allah kuyi haquri.

Ba wanda yace komai cikin su domin sun cika da mamaki sae ajiyar zuciya suka sauke.
Abban Hakeem kuwa damuwa ce fal ta bayyana a fuskar sa ya nisa yace"mamanah kema ina mai baki haquri sbd ya zama dole ki haqura da auren Hakeem sbd accident d'inda Hakeem yayi doctor ya sanar dani Hakeem ya sami matsala wacce ba zai ta6a iya biyan buqatar sa da mace ba bare zancen haifuwa.

Zumbur pinky ta miqe tana ji kamar ta kurma ihu,me yasa ta zamo silar jawa Hakeem wannan babbar matsala,kuka ta fashe da shi tana kallon Abban ta da umma wad'an da suma da alama sae yanzu suka ji matsalar domin sun shiga tashin hankali sosai.
Taje cikin kuka gurin Abban Hakeem ta durqusa kan guiwoyin ta tace"Abba don Allah kayi haquri kar a raba auren mu,wlh Allah zan iya zama da abuna haka koda kuwa ace bani ce sila ba bare nice sila.... Mamanah ai qaddara ce Allah ya riga ya rubutu hakan zai faru da Hakeem sae dai kiyi haquri domin ko a addinan ce baza a had'a mai lafiya da marar lafiya guri d'aya ba, shiyasa kika ji nace dole za a raba auren ku,
kuma barin ki dashi cutuwa ce a gare ki.... wlh Abba zan iya zama da shi a haka,Abba yayi shiru cike da damuwa kuma da alama pinky ta bashi tausayi ganin yanda ta shiga rud'u,cikin muryar rarrashi yace "mamanah kiyi haquri kinji ba yanda zanyi duk da na fahimci kuna son junan ku amma dole Ku haqura da juna a bisa qaddarar da ta same ku"
Kuka ta shiga yi sosai taje gurin Abban ta tana roqon shi kan yasa bakin shi ita zata iya zama da Bobby a haka.
Kasa ce mata komai yayi domin ya cika da jin takaicin ta nan ta garzaya gurin umma tana roqon ta,
umma kam kuka ke qoqarin zo mata shiyasa ta kasa cewa komai duk ta cika da tausayin d'an ta Hakeem,
ganin haka yasa pinky ta garzaya gurin Hakeem wanda idanuwan sa sun cika tap da qwalla magana take mishi amma ya kasa ce mata komai ya kafe guri daya sae kallon ta yake cike da tsananin so inda ya shiga tunanin yanda zai iya rayuwa ba ita.....cikin kuka ta girgiza shi tace Bobby kayi magana mana ka sanar da su ni mai iya rayuwa da kaine a ko wane hali kake ciki....pinky ni bazan so ki cutu ba dole muyi haquri da son da muke yiwa junan mu, nan ya fashe da kuka mai tsanani ya rungume ta a qirjinsa tace"don Allah Bobby kace ka amince zamu iya rayuwar mu a haka please kaji Bobby,,,d'agowa yayi yana mai share mata hawaye yace"i'm really sorry pinky,I'm really sorry sbd abinda kike so ba zai yiyu ba kuma ni mai son ki ne bazan so na tauye miki jin dad'in rayuwar ki ba,sae dai nace muyi haquri da junan mu kinji,,,,komai kasa ce mishi tayi sae kallon shi take hawaye na fita a idon ta kamar yadda shima Hakeem ke fitar da hawaye yayinda yake jin kamar ace mafarki yake ba gaske ba.

*Billy giro😊*
👛👛👛👛👛👛👛👛👛
[9/22, 7:51 PM] ‪+234 810 038 8117‬: [8/27/2016]

*👛BILLY PINKY DURLING👛*

*Na*
*Billy giro😊*

*page*

*👛55👛*
A qirjin sa ta shiga kai mai duka mai kama da dukan shagaw6a tace"meyasa zaka ce haka Bobby bayan kasan baza mu iya rayuwa ba a tare ba,why Bobby?.
Abban ta ne ya daka mata tsawa yace"kina da hankali meye haka! a tsorace ta tashi ta fad'a jikin Abban Hakeem wanda yazo domin hana Abbanta ya dake ta.
Zama yayi da ita kan seater sae kuka take kan jikin sa shi kuma yana rarrashin ta.
Hakeem kuwa duqar da kansa yayi yana mai kallon center carpet hawayen sa na d'iga akai.

Cike da tausayi Abban Billy ke kallon shi ya kalli Abban Hakeem Yace"yaya inaga wannan matsala abu ce da za'a iya magan ce ta,domin bai kamata abar Hakeem haka kawai ba,,, haka ne amma da kamar wuya har dai a yanda doctor yayi min bayani,gaskiya na karaya sosai da jin bayanin shiyasa na jima ina tunanin yanda zan sanar da ku wannan matsalar,,, yaya sanin kan ka ne ina da wani aboki a Germany qwararren likita ne a fanni wannan matsalar kuma inshaAllah zai iya magance ta,,,haka ne idan ance Allah ba a rashi amma yanzu ya kake ganin za'ayi? zan so nima kamin bayanin yanda doctor yayi ma bayanin matsalar in yaso na kira abokin nawa na sanar da shi idan yace Hakeem yaje sae yaje,to shiken nan zan sanar da kai bayan mun sallame su.
Mamanah kukan ya isa haka tashi kije daga ciki kinji,to Abba amma ina so naji idan abokin Abba yace Bobby yaje, to shikenan jeki umman ku zata sanar da ke.
Ba musu ta tashi haka Naini da Feenah suka tashi cike da tausayin Hakeem,yayinda kowanen su yaja motar shi suka fice.

Pinky kuwa daki ta nufa,tayi kwance lamo ba abinda take karantowa a zuciyar ta face addu'oin samun nasara har kusan 30 mnt tana abu d'aya,umma ce ta shigo d'akin ta zauna gab da pinky, yayinda
Pinky ta tashi tana mai share hawayen ta hade da duqar da kanta qasa domin yanzu cike take da jin nauyin umma,
umma ta dafa kafad'ar ta tace"Billy ki kwantar da hankalin ki domin abokin abbanki ya bawa Hakeem damar zuwa Germany ya same shi domin ya duba matsalar ko Allah zai sa ya magan ce ta,sae dai abbanku yace a tare zaku je sbd wani dalili, yanzu ba abinda ya dace face ki ajiye kuka gefe ki rungumin addu'a domin ita ce magani,yanzu kije Hakeem baya jin dad'in jikin sa kuma da alama yana buqatar abinci sae ki samar masa wani abun da zai ci.
Nan umma taja hannun ta suka zo downstairs inda suka sami Amjad yana duba Hakeem,bayan ya gama en binciken sa ne ya kalli Abba yace"Abba Maganin bacci Hakeem yasha wanda yafi qarfin sa ma'ana yayi over dose shiyasa kwata kwata baya iya tsayin kirki har jiri na dibar sa.
Hakeem ya duqar da kanshi ganin Abba nayi mishi kallon tuhuma kafin Abba yace komai Hakeem yace Abba kayi haquri ban sha don komai ba sae don rashin lafiyar da na kamu da ita sosai da ke hana min bacci.
Ajiyar zuciya Abba ya sauke wandà har ya soma nadamar korar Hakeem daga gida sbd ya d'auka shaye shaye ya fara.

Duk da haka dai don Allah iyaye ku kula Ku riqa haquri kan duk abinda 'ya'yan ku suka muku kar kuce zaku Kore su daga gida,ku bisu da addu'a da kuma fatan shiriya domin korar su daga gida zai iya haifar da wata matsala wacce tafi matsalar da yasa kuka kore su.
Allah dai ya bamu ikon kiyaye wa ya kuma bamu ikon haquri da 'ya'yan mu.
Ya kuma sa 'ya'yan mu su kasance masu mana tarbiya da tausayin mu.
Ameen.

Abba bai ce komai ba sae allura da amjad ya yi ma Hakeem ya kuma bashi magunguna.
Ya fita tare da yi mishi Allah sauwaqe.

Bayan Amjad ya fita umma tace da Billy ki taimaka mishi yaje 6angaren shi sannan kizo ki samar masa abinda zai ci.
Nan ta taimaka mishi suka je 6angaren shi.
Ta dawo ta nemi ruwan tea sbd shi Hakeem yace zai sha.

Da ta koma ne ta same shi yana son ya tashi tsaye amma jiri bai bar shi ba da sauri ta ajiye flask d'in hannun ta taje ta kama shi suka zauna tace"Bobby me kake so?wanka nake son nayi pinky help me please,,,ok Bobby.
Nan ta jawo towel ta zauna tana cire mai buttons din rigar shi bayan ta cire mai rigar ne ta taimaka mishi ya tashi tsaye,
a hankali take zare mai belt d'in wadon shi inda tana aikin ne cike da jin kunya,ganin haka ya zare wandon da kanshi,ya zamo daga shi sae d'an guntun wando.

Har toilet ta kai shi ta had'a mishi ruwan wanka ta fito.
Ta d'auke tufafin da ya cire ta kai su inda ya dace.

Ya d'an jima kafin yake fitowa tayi saurin tarbo shi gudun kar ya fadi.

Sae da yayi shirin kwanciya sannan ya nemi ta had'a mishi tea.

Rungume yake a qirjin ta tana bashi tea cike da kulawa.
Da ya gama ya kwanta ta rufa mishi blanket.
Tayi mishi sae da safe kafin take fita daga d'akin.
A hankali Bobby ya tashi ya biyo bayan ta ba tare da ta sani ba,har tazo 6angaren su umma inda taji qofar gam,
tsaye tayi tana tunanin danna door bell....no ki bar su kawai muje a nawa 6angaren kiyi bacci, a tsorace ta juya ganin hakeem yasa ta sauke ajiyar zuciya tace"Bobby Allah har kasa naji tsoro"
Am sorry na rakoki ne sbd gidan nan yana da fad'in da yasa bazan iya barin ki kizo ke kad'ai ba.
Thank u Bobby amma bai kamata ace ka taso ba a halin da kake ciki, ai na daina jin jiri qarfin jiki ya rage.
Zo muje ki kwanta naga kamar bacci kike ji sosai,
bai jira me zata ce ba yaja hannun ta suka je 6angaren shi.

Rungume yake da ita wacce tuni tayi bacci shi kuwa sae kallon ta yake ganin yanda take motsi,motsin da ya kasa gane dalilin yinsa.
Chapter 28 · 0% Book details