← Book details Billy Pinky Durlin Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 49

Sashe 42

Billy Pinky Durlin Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Abincin masu ciki ne kala kala da 'ya' yan fruits ba adadi jere a kan dining table wanda ya cika maqil tamkar mutane goma ne zasu ci abincin, yayinda Billy keta zubawa Hakeem kukan shagwa6a ita baza ta ci ko d'aya ba sbd tsoron kar taci taje tayi amai dmn ko kad'an bata son tuna wahalar aman da tayi a d'azu shiyasa take gudun sake cin wani abu.
Ba irin rarrashin da Hakeem bai yi ba amma taqi ci yace "Billyta kalle ni nan" a hankali ta d'ago kan qirjin sa tana kallon cikin idonshi inda ta hango damuwa fall a cikin su.
Nan ya had'e tafukan hannayen sa yace "don Allah Billyta kici wani abu kinji" le6ace bakin ta tayi xuwa kuka tace "Bobby um um" kina so nayi fishi da ke? saurin girgiza kanta tayi d'auke da hawaye tap a idon ta yace "to idan baki ci ba zanyi fushi da ke kuma bazan qara miki magana ba" ta nuna kanta da yatsa tace "ni d'in ? yace" eh man ba kinqi kici abinci ba kin bar min Baby da yunwa "um um ni bana so kayi fishi da ni ina gudun kar nayi amai ne shiyasa bana so naci,baza kiyi amai ba inshaAllah, nan ya shafo cikin ta yace"ai nasan kina so babyn mu yayi qiba baza kiso ki haifo mana shi a ramamme ba ko? gyad'a mai kai tayi tare da fad'in" eh " yauwa tawan to share hawayen ki kici abinci, ba musu ta share hawayen ta yasa handkerchief ya qara share mata yace" to nuna min me kike so a nan, nan ta shiga rarraba ido kan ko wane abinci nan faten wake ne wanda yaji ganyen ogun da kifi nan kuma ganyen zogale ne da aka soya da qwai mai d'auke da kayan lambun da aka soya sama sama sae qamshi ke tashi,
nan kuma farfesun kaji nan kuma na en ciki nan kuma spaghetti ce wacce akayi ta ruwa ruwa taji ganyen alanyahu da wake da hantar rago sae kuma sakwara tayi laud'i da taushi har ta gaji da miyar stew wacce taji naman rago, nan ta koma kan fruits shammal, gwanda, Apple, grapes, Banana, orange, pineapple, guava,watermelon,whatever haka ta qaraci kallon su har zuwa drinks ta juyo ta kalli Hakeem fuska a shagwa6e tace "Bobby idan naci bazan yi amai ba? lumshe idon shi yayi tare da fad'in "inshaAllah then nuna min za6in ki"
nan ta nuna mishi kankana ya d'auko slice d'aya zai kai a bakin ta sae fargaba take kar tayi amai ta riqo hannu shi tare da bud'e bakin ta a hankali suka saka kankanar a tare kallon shi take tana shan kankanar tana gama shan slice d'in tayi saurin rufe bakin ta ta sauka kan jikin sa tana yunqurin amai se duk Hakeem ya shiga damuwa yayi saurin zamewa kan kujera ya durqusa tare da dafa ta yace "pls Billyta kar kiyi amai dan Allah"
Yunqurin aman kuwa sae zo mata yake amma ta kasa yin amai jinginawa tayi a jikin sa tana sauke numfashi, Hakeem ya dauko ruwa zai bata ta dakatar da shi had'e da girgiza kanta ta samu da qyar tace "Bobby cikina yana min ciwo sosai" sannu ya shiga yi mata ba adadi sannan ya kama ta suka koma kan dining ya zuba mata fresh milk ya samu da qyar ta kar6a ta kur6a kad'an ta kauda kai ganin bata yi amai ba ya qara lalla6a ta yaci gaba da bata,
bata wani sha da yawa ba tace ta ishe ta.
Kallon abincin kan dining yayi yace "to me kike son ci cikin abinci?kukan shagwa6a ta shiga yi mishi tana yarfi da hannu tace" Bobby cikina ke min ciwo dan Allah ka daina zancen abinci "kiyi haquri kici ko kad'an ne sae kisha magani kiyi bacci kinji" uhm uhm Bobby kayi haquri bazan iya cin komai ba,
cikin damuwa yake kallon ta ya rasa me zai ce mata ya dai samu taci ko kad'an ne.
Ita ma Billy kallon fuskar shi take sae duk taji ba dad'i ganin yanda ya shiga damuwa ta share hawayen ta tace"am sorry Bobby zanci abincin "da murnar sa yace to me kike so? faten wake nake so,
nan ya zuba mata ya shiga bata sae dad'i yake ji ganin yanda take cin abinci ita kuma tana cin abincin ne don kawai ta faranta mishi rai sae da tace ya ishe ta sannan ya daina bata ya d'auko ruwa da magani ya bata tasha sannan suka koma d'aki ta kwanta ya rufa mata blanket sae kallon shi take yana gyara mata sumar kanta tace "thank u" yayi murmushi hade da bata kiss kan goshin ta yace " welcome"

Sae da tayi bacci yaje downstairs ya d'obo sakwara da miyar stew ya zauna kan sofa inda yake facing d'inta yana ci wanda komai qanqantar motsin da tayi sae ya d'ago ya kalle ta da haka har ya kammala cin abinci .

*Billy giro 😊*
👛👛👛👛👛👛👛👛👛👛
[9/22, 8:41 PM] ‪+234 810 038 8117‬: [9/10, 10:29 AM] Billy giro😊:
*👛BILLY PINKY DURLING 👛*

*Na Billy giro 😊*

*page*
*👛77&78👛*
Ta jima sosai tana bacci yayinda Hakeem yake kwance kan gadon yana kula da duk wani motsi nata.
A hankali ta shiga motsawa tana juyi tare da dafe cikinta ta fara fitar da sautin kuka kad'an kad'an,
nan Hakeem ya matso kusa da ita yana tambayar abinda ke damun ta bata iya ce mishi komai ba sbd yawun da ya cika mata baki inda duk cikin ta ya mirda ne kesa yawun ya taru,
zare jikin ta tayi ta tafi toilet da sauri tana isa ta shiga kwara amai ta samu da qyar ya tsaya mata , Hakeem da ke riqe da ita ya wanke mata baki ya kuma wanke gurin,
da qyar take iya takawa bata iya miqewa da kyau kan ciwon ciki,
sae kuka take mai cike da wahala,
Hakeem sae faman rarrashin ta yake ya zaro waya ya kira Amjad wanda bai wani jima ba yazo.
cikin damuwa Hakeem yake sanar da shi yanda ciwon cikin ke wahalar da ita, Amjad yace "kayi haquri Hakeem kalar laulayin ta ne yazo da hakan kuma ba a iya magance shi sae idan Allah ne ya yaye mata but zan mata wata allura na kuma rubuta mata wasu magunguna inshaAllah abin zai d'an rage mata har ta samu ta kai lokacin da laulayin zai rage mata.
Nan Amjad ya shirya allura Billy sae kuka take tana roqon kar a mata inda ta shiga qoqarin qwatar kanta ta samu ta guje ma allurar,
ba a son ransa ba ya matse ta aka mata allura kuka take sosai yana murza mata bayan ta,
kai tsaye ta shiga kwara mishi wani irin amai duk tabi ta 6ata jikin su tana qoqarin somewa inda ko qaqa Hakeem yaso yayi kuka ko zai ji sauqin damuwar da ya shiga akan halin da yake ganin pinky ciki amma haka ya dake yana ta hana kanshi domin kukan sae qoqarin zo mishi yake wanda duk da haka sae da idanun sa suka cika tap da qwallah,
ya kalli Billy dake kan jikin shi yaga kwata kwata bata motsi duk ya rud'ewa Amjad yana fad'in Amjad na shiga uku! bata motsi fa dan Allah duba min Billyta kar ta mutu.....calm down suma ne tayi nan suka watsa mata ruwa taja numfashi da qarfi ta kuma ci gaba da kwara amai sae kace wacce zata amaye en hajin ta duk Hakeem ya qara rikicewa yana qoqarin yiwa Amjad kuka, Amjad yace "kayi haquri Hakeem allurar ce ke suffering d'in ta haka but daga haka inshaAllah wahalar zata rage mata,
nan ya rubuta mishi magunguna tare da fad'in tunda yanzu aman ya tsaya mata kayi sauri ka bata wani abu taci kafin tayi bacci sbd allurar tana sa bacci sosai ya fad'i haka ne sannan ya fita tare da fad'in Allah sauwaqe.
Nan Hakeem ya tashi yaje toilet ya wanke musu jikin su sannan ya gyara gurin da tayi amai tsaf,
ya dawo kan Billy wacce ke kwance d'aure da towel,
zare towel d'in yayi ya barta da pant ya d'auko half vest da guntun wando iya cinya ya saka mata sae kallon cikin ta yake da yayi mugun lafewa,
en guntayen hawayen shi ya share yayinda ya kalli Billy wacce ko qaramin yatsan ta bata da qarfin motsawa.
Fresh milk ya debo wanda ko kur6i d'aya da qyar ya samu ta hadi'ye shi yayi 2 ta bud'e bakin ta domin ta qara sha amma taqi har bacci yayi awon gaba da ita.

Tun bayan la'asar da tayi bacci sae goman dare ta farka ta bud'e idon ta inda ta had'a ido da Hakeem wanda ke rungume da ita , wanka ta buqaci tayi yaje ya mata da kanshi ya samu ya bata wani abu taci ta samu ta ranka sallolin da ake binta amma duk da zaune tayi su sbd ba qarfin jiki.

Har ukkun dare basuyi bacci ba,
ba don komai sae don Billy bata jin bacci shi kuma Hakeem sosai yake jinsa amma haka ya dake ya hana kanshi sbd baya so yayi bacci Billy ta buqaci wani abu.
Billy ta lura da irin yanda yake jin bacci hakan yasa ta qara lafewa jikin sa ta tsiri baccin qarya nan Hakeem ya samu yayi bacci ita ma daga baccin qarya na gasken ya zo mata.

Washe gari sae da aka yi mata qarin ruwa har gora biyu sbd bata da qarfin jiki ko kad'an da ta tashi tsaye jiri ne ke d'ibar ta ta fad'i amma tunda aka sa mata gora biyu taji jikin ta yayi dama.
Chapter 42 · 0% Book details