← Book details Billy Pinky Durlin Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 49

Sashe 44

Billy Pinky Durlin Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shiru ya mata yayinda murmushin fuskar shi ya 6ace,
ya Kalle ta sau d'aya ya kauda kai,
nan wayar shi tayi qara yace " d'auko min waya ta " wanda kafin yace hakan tayi niyar d'auko mishi wayar sbd tana tunanin Abban ta ne ya kira bcs tana cikin waya da shi ne cajin wayar ta ya qare sea tayo d'akin Hakeem.
Da hanzari ta tafi d'auko wayar tana fad'in "yeah Allah yasa Abbana ne" .......qara ta saki sbd fad'uwar da tayi kan wani jiri da ya d'ebe ta.
Ba shiri Hakeem ya jefar da d'an qaramin towel d'in da ke hannun shi yana isa ya tayar da ita ta fada kan qirjin sa da qarfi duk tabi ta qanqame shi tana kuka kamar wacce ta tsorata
hakan yasa Hakeem ya d'ago fuskar ta tare da fad"in "Billyta mene ne, me ya kayar da ke?tace" wani irin jiri ne ya d'ebe ni har naga d'akin yana juya min kamar zai fad'o min" oh no sorry but a u ok? "am ok" nan ya kwantar da kanta a qirjin shi yana mata sannu shafo cikin ta yaji tayi yayi saurin kallon ta tare da shafo cikin yace " wani abu ya sami babyn mu ne? girgiza kanta tayi tace" um um ba komai.....no tashi muje asibiti a duba bcs hankali na yafi kwanciya da hakan nan suka shirya sae asibiti bayan an gama duba ta Amjad yace "fad'uwar da tayi bai illata babyn ba amma ta rage dogon motsi sosai sbd hakan kesa taji jiri ya d'ebe ta kai tsaye kuma dama ba a cika son mai ciki na fizgar jikin ta ba, har dai ga mai sabon ciki then ga wasu magunguna da zan rubuta ma sea ka siya mata su ta riqa sha nan Hakeem ya kar6i takarda tare da sauke ajiyar zuciya yayi ma Amjad godiya kafin yake riqo hannun Billy yace "muje"

Har suna batun fita Hakeem ya juyo ya kalli Amjad da ba'a yace " doctor ko har da tafiya kar na sake bari tayi na riqa d'aukar ta..... Amjad yayi dariya yace" Baban soyayya to ko haka ne ai baza ka iya ba.... wa ya gaya ma Billyta ce fa,i know amma zai maka wahala..... to wane aikin wahala ne banyi ba nida nayi soja..... hehe ai ba zancen soja bane maza ne basu da tabbas sae kun fara d'and'anawa mutum dad'i kai tsaye ku daina koda hakan baya wahal da ku kuwa, Hakeem ya kalli matar Amjad wacce shigowar ta kenan tayi magana.

yace " wasu mazan dai don ni bana d'aya daga cikin su ko Billyta? hm Bobby kenan a bar zancen kawai....gara da kika ce haka domin yanzu baza ki gane halin d'a namiji ba sae rayuwa taci gaba inda ke zakiyi ta haquri kina danne zuciyar ki ki samu ku zauna lafiya tare da fatar kar hawan jini ya kama ki.......a'a fa kar ki tsora ta min Billyta,wlh Allah ina sonta bazan so na nuna mata halin d'a namiji ba.....dariya sukayi gabad'aya sbd yanda yayi maganar.

Matar Amjad tace "kenan ka yarda Kuna da hali?eh amma *wasu mazan*.... ba wani komai haqurin d'a namiji sae an sami wani hali nasa da yake 6atawa matar sa rai bare zaman tare ai sa6ani yayi yawa a cikin sa sae anata haquri ne ake cin ma riba domin yau ba don haquri ba Allah bazan kawo ma abincin nan ba, Amjad take gaya ma hakan yayinda take dariya tace "nifa na d'aukawa kaina kawo ma abinci ba kai kasa ni ba amma duk ranar da uzuri ya kama ni nayi lettin kawo ma sae ka cika ni da masifa......naji amin afuwa dan Allah kin san matsalata duk yanda naji yunwa nan take ne ulcer ta ke tashi kuma kinsan yanda ulcer kemin kamar na mutu,no ba komai my dear ai kasan na fi kowa tsorata idan ulcer ka ta tashi bcs ko mutuwa kayi ni aka bari da takaba ba kowa ba,
shiyasa kullum roqona na mutu kafin kai.......no no gaskiya ni ya kamata na mutu kafin ke bcs idan kika mutu ai shikenan na tashi da aiki bazan qara yiwa kowa amfani ba.... hm zo zo muje Billyta kar zumar da suke nunawa junan su tasa su haifo 'ya' yan zuma yanzu abin al'ajabi ko ya same mu,,, kaji ka wai kwando kece wa rariya na yoyo, cewar Amjad kafin yake cewa
"kinga dear zo mubi sahun su bcs yau banda wani aiki da zai kaini dare da na sani ma baza kiyi wahalar kawo min abinci ba".
Nan suka fita tare inda kowa ya shiga mota suka nufi hanyar gidajen su.

Suna isa pinky ta cire kayan jikin ta ta zamo daga ita sae vest da d'an guntun wando Hakeem ya shigo sanye da singlet and boxer ya same ta ruf da ciki tana chat zuwa yayi close to her ya kwanta rairan yayinda ya d'ora qafa kan qafa yana mai kallon fuskar ta.
ajiye wayar tayi tare da kwanciya kan qirjin sa ta kai hannu kan sajen fuskar shi da ya soma taruwa tana d'an jan sirarin sumar a hankali ta yanda ba zai ji zafi ba,
hannun sa taji tsundum cikin vest in ta yana abinda ya saba yi a qirjin ta turo baki tayi tana kallon shi taja sumar sajen shi da qarfi har sae dai yayi qara inda hakan yasa ya fitar da hannun shi cikin vest in ta ba shiri yana murza sajen shi,
jaye hannun shi tayi tana ci gaba da murza mishi a hankali da wasa ya buge mata hannu yace ki daina min bana so,tukuna ma me namiki? ba kai bane ko yaushe idan ina tare da kai sae kayi ta takura ni kan abokanan wasan ka, oh yayi kyau a kanshi ne kawai sae kace ba kaya na ba.....a'a gaskiya bana la6i ni kad'ai nake da abuna kar ka sake ta6a min, haka kika ce?eh, shi kenan da ga yau nima kar ki qara kwanciya kan jikina sbd na fahimci jikin nan nawa yana miki dad'in kwanciya ko yaushe kina maqale da ni,cikin ko in kula tace"ai wannan ba matsala bane amma dai bara nayi na qarshe,
nan ta rungumo shi sae kuma tayi saurin jaye wa tana dariya sae kare qirjin ta take kar ya ta6o, murmushi yayi ya tallebeta cak tare da fad'in ai da kin daina kare qirjin ki sbd ba abinda zan miki bacci ma nake so muje muyi " um um fa nasan halin ka Bobby kullum idan zamuyi bacci sae kayi ta takura ni kan abokanan wasan ka har bacci ya d'auke ni baka daina ba,
hancin ta ya lakato tare da fad'in" banda yau zan barki ki hutu har safe.
Kaji shi kaman zai iya, dariya yayi Yace"Billyta kenan to zan miki qarya ne "
rufan asiri ni bance qarya kamin ba.

Ta fad'i haka ne yayinda suka iso d'aki ya dire ta kan bed yaje ya rufe d'aki sannan ya rage hasken d'akin yaje ya kwanta yayinda Billy ta mirgino kan qirjin sa da ko yaushe take jin dad'in kwanciya akai sbd fad'in qirjin, shiru sukayi inda suke jiran bacci ya d'auke su,
Hakeem sae shafa bayan Billy yake a hankali kamar yanda Billy ke yawo da hannun ta kan qirjin shi.
Da haka har tayi bacci nan Hakeem ya zare hannun ta a hankali da ke cikin vest in shi ya gyara mata kwanciya shima ya shiga bacci.

*******
Sannu sannu lokaci ke ta tafiya inda yanzu cikin pinky yakai har wata shida.

Shiri take cikin sauri yayinda Hakeem ke tsaye yana jiran ta kan bikin su Feenah da Naini da zasu je.
Yace"Billyta kinga mutane sae kira na ake tayi kuma ke gashi har yanzu shirin naki bai gadi qarewa ba, yi haquri Bobby yanzu zan qarasa shirin,
numfashi ya sauke ya duqa a hankali kan cikin ta da ya fara fitowa ya d'ora kiss akai yace " sorry my child ni zan tafi ku same ni a mota "nan ya tashi ya d'ora mata kiss kan kumatu yace"zan jiraki a mota" gyada mishi kai tayi yayinda take ci gaba da shiri.
Tana gamawa ta tafi sauri sauri ta same shi a mota suka tafi.

Sun jima sosai da zuwa sae ga Billy ta dawo ita da Hajiya seema sae dai bata jira Hajiya seema ba,
ta shiga 6angaren su umma kan ta shiga wata ta tsaida ta tace "da Allah pinky fa? nice pinky da wani abu ne, sae da ta kalli cikin Billy tace" no ba komai kawai ni qawar feenah ce ina so zanje event in da ake yi yau amma ban gane guri ba,, Eyyah wato ke qawar Feenah ce but ya akayi ba mu san juna ba,,, baza ki sanni ba bcs a kasuwa kawai abotar tamu ta had'u, ok haka ne bazan sanki ba gsky but muje daga ciki idan zan koma sae mu tafi tare.
Nan suka shiga baquwar ta zauna Billy ta haura sama zuwa d'akin umma ta sami umma tana waya ta zauna tare da kwantar da kanta kan kafad'ar umma, umma na gama waya tace "umma yunwa nakeji ko da fresh milk a nan 6angaren sbd mu a namu 6angaren jiya da dare na qarasa shanye ta? Cabd'i sae dai kije ki bincika idan zaki samu sbd jiya da su Feenah suka kwana a nan ita suka bawa qarfi,
cikin shagwa6a ta tashi tace" Allah yasa zan samu "
Nan ta nufi fridge d'in dakin.
Chapter 44 · 0% Book details