Sashe 27
Billy Pinky Durlin Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*page*
*👛53&54👛*
D'ago kanta tayi tana mai qara godewa Feenah.
Feenah tace"bani kad'ai zakiyi wa godiya ba,ta nuna Naini tace"kin ganshi a tare mukayi komai"
Da mamaki pinky ta kalli Feenah kafin take kallon Naini wanda yayi murmushi tare da duqar da kanshi qasa sbd hawayen da yaji suna qoqarin zo mishi
Feenah tace"tabbas dashi mukayi komai kar kiyi mamaki domin shi masoyin ki ne na gaske wanda baya son ganin kin shiga qunci.
A ranar bayan na gama yi miki bayani a d'aki na fito cike da tunanin yanda zan fara aikin ni kad'ai haka nake ta faman magana zan shiga mota sae kawai naji magana kamar daga sama yace"ba wanda ya dace kiyi aikin nan dashi face ni, nayi masa kallon mamaki, yace"kar kiyi mamaki akan komai indai game da soyayyar da nake yiwa pinky ce zan iya yin komai na ganin farin cikin ta ya dawo koda ni a gurina ba farin ciki bane, bare tun a new delhi na haqura da komai domin na fahimci ba wanda ya dace da pinky face Hakeem shiyasa naji baqin cikin rabuwar su, amma yanzu bani da wani baqinci sae na rashin sanin inda Hakeem yake domin naji duk maganar da kuke ta waya,
bcs na kira pinky ta ta d'aga wayar a cikin rashin sani shiyasa naji komai da kuke fad'a,don haka a shirya nake muje mu nemo Bobby duk inda yake kafin ranar d'aurin aure yayi.
Daga ranar ne muka shiga neman Hakeem ta koina inda sae yau Allah ya nuna muna shi zai shiga wani Hotel.
Kinji abinda ya kasance pinky ba a riga an d'aura aure ba kuwa mun kawo miki Hakeem har gida kuma fasa auren da akayi a yau duk Naini ne ya sami dabara na ganin iyayen sa kar su iso yau, ko yanzu fitar nan da kika ga za'ayi abokanan sa ne wad'an da sukayi karatu tare a new Delhi suka matsa sae anyi Indian night, ba irin zillewar da bai yi musu ba amma suka nace shiyasa kika ji abun kai tsaye.
Wani irin farin ciki pinky ta qara tsintar kanta a ciki yayinda Feenah ta kawo qarshen zancen ta,billy ta kalli Naini inda ta shiga yi mishi godiya tare da nuna farin ciki kan namijin qoqarin da yayi.
Nan yaji sauqi a ransa domin kalaman da ta mishi masu tausasa rai ne.
Sai yaji gabad'aya ya haqura ba abinda yake fata irin ya sami mace irin ta wacce har ya fara tunanin ya same ta.
A hankali Billy ta miqar da Hakeem tsaye yayinda Hakeem ya jingina a jikin ta tare da rungumo ta ya dora kan sa a kafada'ar ta sbd ko tsayuwa baya iya yi da kyau.
D'ago kanta da zata yi ne taga ashe kaf mutane na zagaye dasu har su Abba,
duqar da kanta tayi ba tare da tayi mamakin ganin su ba sbd ba wata tafiya mai nisa suka yi ba tasan wani ne yaje ya sanar da su abinda ake ciki.
a hankali ta d'ago fuskarta ta kalli Abban Hakeem tace"Abba don Allah kayi haquri kar kace zaka hana Hakeem shiga gida wlh ko kad'an baya da laifi nice silar komai abisa bahagiyar fahimta da na mishi.
Abba yace ba komai mamanah sbd ke zan bawa Hakeem damar shiga gida kuma zamu so muji wannan shiri naku wanda ba mu riga mun fahimta ba.
Na gode Abba amma zan so kayi haquri har muje gida inyaso acan sae nayi bayanin komai.
Ba komai mamanah dama a can ya dace ayi bayanin ba a nan ba don haka ku shiga mota muje gida ,nan suka shiga mota suna isa gida suka zarce main falo,
feenah ce taje ta kira umma,ya kasance Abban Billy, Abban Hakeem,umma ,Hakeem,Billy,Naini,and Feenah sune zaune a falon yayinda gurin yayi tsit ana sauraren abinda pinky zata ce.
Duqar da kanta tayi qasa idanun ta suka ciko tap da qwallah muryar ta na rawa tace"Abba zan so kuyi haquri kan abinda zai fito daga bakina duk da cewa nasan dole zaku ji haushi na,a gaskiya wannan takardar sakin ba Hakeem ne ya rubuta ta ba nice na rubuta ta da hannun na kasancewar yaudarar Hakeem da nayi ya koya min rubutun sa sbd tun kafin muje new delhi nake tsara ganin na rabu da auren shi,bayan munje ne bamu jima sosai ba na shiga nuna mai a zahiri komai ya wuce a gurina amma a bad'ini sam ba haka bane nayi haka ne don na samu na shawo kanshi domin ya fara sona sbd a ganina na idan muka rabu ba soyayyata a tare dashi sam ba zai ji zafin rabuwar mu ba, shiyasa na shiga yi mishi komai kamar da gaske wanda nasan sannu sannu abuwawan da nake mishi zasu sa ya fara sona.
Da haka ne har ya fara sona kuwa wanda kan sona ne ya tashi sadaukar da ranshi da duk wani farin ciki nashi sbd wani al'amari da ya faru tsakani na da Naini,nan ta shiga yi musu bayani dalla dalla sannan ta ci gaba da cewa duk a tunani na plan ne suke shida doctor na ganin plan d'ina ya koma kaina ashe sam ba haka bane da gaske dai Hakeem ke sona.
Kuma dalilin da yasa Hakeem yace shi ya rubuta saki ashe accident d'in da yayi yasa ya manta duk wasu abubuwañ da suka faru wata biyu da suka wuce, wanda naji haka ne a bakiñ Feenah lokacin da na shiga daki ina kuka kan auren da naji zaka hada ni da Naini.
Da na shiga d'aki ina kuka nake sanar da ita nan ta share min hawaye inda ta kulle koina na d'akin bayan tace zata bani wata shawara wacce bata son kowa yaji.
A maimakon naji tace wani abu sae kawai naga ta fashe da kuka tace"pinky wlh naso na cutar da ke amma na sami kaina da kasawa duk da cewa cike nake da jin haushin ki kan na hanaki bada takardar saki amma kika qi,hakan yasa nace zan aure Hakeem domin na nuna miki kuskuren ki ba wai don ina son shi kad'ai ba,amma kuma sae na shiga tunanin a yanda na fahimci Hakeem yana sonki da kamar wuya ya kula wata 'ya mace,
sae gashi bayan Hakeem yayi accident doctor ya sanar dani irin matsalar da Hakeem ya samu na ya manta komai da ya faru na wata biyu da suka wuce, wanda doctor ya fada min ne sbd ya dauka cewa ni er uwar Hakeem ce,
da farko na shiga damuwa sae kuma nayi farin ciki da na tuna kenan Hakeem ya manta duk wata soyayya da yake yi miki,
yanzu zan iya samun damar fara nuna mishi tawa soyayyar.
Hakan yasa na roqi doctor kar ya sanar da kowa halin da ake ciki.
Inda duk wani fad'a da Abba keyi kan sai Hakeem ya bar gida duk ina ji kamar na fadi gaskiya amma kuma wani 6angaren zuciya ta ya hana ni, kuma da ace Abba ya bawa Hakeem damar magana a wannan lokaci da tabbas zai fahimci matsalar da Hakeem ya samu.
Da dare naje asibiti domin na sami Hakeem na sanar da shi cewa yazo gidan mu ni zan bashi masauki,
yayinda ni kuma zan sami damar fara nuna mai soyayya har mukai ga yin aure,
sae gashi ban tarar da shi ba,
nayi baqin ciki sosai har dai da na karanta takardar da ya bari sae dai jin cewa yana mai sauraren afuwar Abba a ko yaushe nan na fahimci cewa kenan bazai yi nisa ba ma'ana zai tsayà a cikin garin nan,
Nan na qudura a raina zanje neman sa koma a ina ne domin na maida shi gidan mu da zama.
Amma kuma a duk lokacin na fito zanje neman shi sae naji rashin kyautatawa ta sbd ba a kanki zan nemo shi ba a tawa buqatar ne,
duk da nasan irin damuwar da kika shiga sosai akan rashin sa,
Ba abinda ke fad'o min irin nifa qawar ki ce wacce muka taso tun muna yara da qaunar juna sam cutuwa bata dace nida ke ba,bana jin zan iya cutar da ke ko kad'an.
Wlh pinky zuwan da nayi a yau banzo da niyar komai ba sae don na sanar da ke komai na kuma roqe ki gafara.
Nan muka ci kuka tamkar wad'an da akayi wa mutuwa na kuma yafewa Feenah domin bana jin zan iya riqe ta da komai, amma kuma na qara shiga nadama sbd na lalata duk wata soyayya da Hakeem keyi min ta gaskiya yanzu ni kad'ai ke fama da son shi ya manta tawa soyayyar.
Feenah ce ta katse ni da cewa"pinky dama shawar da zan baki ita ce idan Abba ya kira ki kan zancen auren Naini ki nuna amincewar ki.... a rikice na kalle ta domin na firgita da jin zancen ta bcs ta ya zan amince a matsayi na na musulma nayi aure kan aure,tace"pinky akwai dalilin da yasa nace hakan na tabbatar idan kika sanar da su Abba qarya kika tsara musu Hakeem bai sake ki ba,
to kuwa kai tsaye ciwon Abban ki zai iya tashi sbd baqin ciki,
kin ga na d'aya kece silar accident d'in Bobby har ya sami matsala,
na biyu kece silar da yasa Abba yayi fushi dashi ya kore shi wanda har yanzu Abba yaqi haqura.
Haka ne Feenah nima abinda nake tunani kenan sae dai gaskiya wannan tunanin naki kamar bai yi ba domin ina gudun amincewa auren Naini yaje yaja min matsala.... kar ki damu inshaAllah zan nemo Bobby kafin ma a fara zancen auren,,, haka kike gani feenah?haka nake gani domin yafi ace sae Bobby ya dawo ko zaki sanar da su Abba komai bcs ransu ba zai 6aci sosai ba,irin ace Bobby baya nan.
Shike nan Feenah naji kuma Allah yasa ayi sa'a amma ya kike ganin Naini zai ji bayan an sanar da Naini auren mu daga baya yaji akwai auren Bobby a kaina?wannan ba matsala bane sbd shi musulmi ne duk kuwa cikakken musulmi yana da tawakkali kuma zai fahimci cewa dama ke ba rabon sa bace ,,, to Feenah Allah yasa ya fahimci haka,,,Amin ni zanje domin na fara aikin neman Hakeem daga yanzu.
Nan na mata godiya ta fita.