← Book details Billy Pinky Durlin Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 49

Sashe 20

Billy Pinky Durlin Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Pinky a yanzu bani da wani buri a rayuwa da ya wuce na sami mace mai irin hallayar ki da ma komai naki domin idan ban sami haka ba bana jin zan ji dad'in rayuwar duniya har na koma ga mahallici na.....kar ka ce haka Naini ka tuna fa Allahn da yayi ka shiya d'ora maka sona kuma kai tsaye zai iya yaye maka sona ya kuma baka mace wacce ta fini da komai kuma ka daina cire ran ka rasa ni ba mamaki watarana zan zamo taka.
Tayi maganar ne cikin muryar kuka sbd sosai Naini ya bata tausayi domin duk a cikin kuka yayi zancen shi.
Hakeem kam duk kishi ya rufe mishi ido shiyasa ko kad'an bai ji tausayin Naini ba sae ma haushin sa da ya ji.

Da dare bayan sun koma gida pinky ta fito daga wanka tayi shirin kwanciya cikin rigar ta pink iya guiwa.
D'akin Hakeem ta nufa sbd tun a asibiti ta fahimci fishi yake da ita.

Tana shiga ta same shi riqe da glass cup zai sha ruwa yana ganin ta ya fasa shan ruwan.
kafin ta qaraso ya isa gurin ta fuskar shi a daure Yace"lafiya me ya kawo ki d'aki na?kallon shi tayi sau d'aya ta kauda kai ta rasa meyasa take jin ba dad'i sbd fishin da Hakeem keyi da ita,duk da kuwa tana ganin kamar plan ne bada gaske yake kishin ta ba.

Magana nake miki kin min shiru!idanuwan ta ne suka ciko tap da qwallah tace"Bobby meyasa kake fushi dani?in dai akan Naini ne sanin kanka ne mutum baya d'orawa kanshi so.... Naji mutum baya d'orawa kanshi so domin naga hakan a tattare dani amma meyasa kika kama mishi kuna ta kuka har kina ce mishi kar ya cire ran wata ran zaki zamo tashi...ai gaskiya na fada Bobby sbd ba wanda yasan gobe....nasan da hakan ba sae kin sanar da ni ba, amma ke ba don haka kika gaya masa cewa wata ran zai same ki ba ki gaya min meyasa kika ce masa haka?.....sbd na fahimci yana sona sosai shiyasa nake son kwantar mai da hank....kafin ta qarasa zancen ta se kawai taji qarar fashewar glass cup d'in da ke hannun shi, ya kuma jefo shi kusa da ita har sae da tayi saurin matsawa.

A tsorace ta
fashe da kuka tana kallon hannun shi da ke fitar da jini, shima Hakeem kallon ta yake cike da nadamar jefo mata cup,cikin muryar lallashi yace"pinky na same ki ne?girgiza mai kai tayi yayinda ya ware hannyensa alamar tazo,
da sauri taje ta shige jikin sa tana kuka sosai sae haquri take bashi,,,is ok pinky amma don Allah kar ki sake furta cewa wani yana sonki a gabana kinji.
gyada mishi kai tayi hade da share hawayen ta taje ta dauko first aid kit taja hannun shi ta zaunar da shi kan bed,a hankali take cire mishi glass d'in da ya soke mishi hannu wanda har ta gama treatment din shi kallon ta yake,d'ayan hannun sa ya kai yana share mata hawaye domin har lokacin kuka take.
Nan ya matsa gab da ita ya lumshe idon shi yayinda ya kai lips dinsa a hankali kan nata ya zira harshen sa wanda yayi 3mnt kafin yake zarewa, ba yabo ba fallasa pinky ke kallon shi ta kwanta a hankali kan qirjin sa tare da sauke ajiyar zuciya,shiru sukayi na d'an wani lokaci d'akin yayi tsit kamar ba kowa Hakeem sae shafar sumar kanta yake, can ya katse shirun da cewa ki fara shiri domin gobe ne kad'ai muke cikin qasar nan.

*Billy giro😊*
👛👛👛👛👛👛👛👛👛👛
[9/22, 7:18 PM] ‪+234 810 038 8117‬: [8/20/2016] Billy giro😊:
*👛BILLY PINKY DURLING👛*

*Na Billy giro😊*

*Page*
*👛42 to 44👛*
Ba tare da ta d'ago ba tace"su umma zasu dawo ne gobe? tana nufin iyayen su Naini.
Yace "inshaAllah"
tace "Allah ya kawo su lafiya yace"Amin"
Daga haka sukayi shiru.
Yayinda Billy ta qara narkewa a jikin sa kamar mai jin bacci,ba wai don tana jin baccin ba sae don yau taji dad'in kwanciya a jikin shi sosai fiye da kullum,
koda yake kullum duk ta6a jikin sa da take bata ta6a jin wani abu makamancin haka ba sae yau wanda har ma ji take tamkar su tabbata maqale da juna don kar ta daina jin dad'in da take ji a yanzu.

Shi kuwa Hakeem a matse yake gurin domin har zufa ya fara sae Allah Allah yake ta tashi domin shi kad'ai yasan azabtuwar da yake dama kullum ta6a ta da yake yana yi ne sbd idan bai ta6a jikin ta ba har wani zazza6i yake ji idan kuma suka jima a maqale shi kad'ai yasan azabtuwar da yake amma hakan yake jurewa kullum.
Duk da kuwa ba ita ce macen farko da ya fara ta6i ba amma a kanta kad'ai ya fara jin hakan.
A hankali yake d'aga ta kan qirjin sa, ta kalli yanda ya matse qafafun sa kamar mai jin fitsari tace"Bobby zaka je toilet ne?da qyar yace"no pinky tashi kije daki kiyi bacci kinji, bcs bacci nake ji sosai, ba musu ta tashi kan jikin sa ba don taso ba domin da bai ce komai ba sae dai ta lafe kan jikin sa har safe.

A daren ranar kowannen su sae juyi yake da qyar suka samu bacci ya d'auke su.

Washe gari ta fito daga wanka kenan tayi kici6is da Hakeem ya shigo d'akin,
saurin kauda idon shi yayi domin daurin towel d'in ta kamar wanda ke shirin sa6ulewa a qirjin ta ba wani daurin kirki take yiwa towel ba sae duk tabar rabin mama a waje kamar d'aurin en boarding school,sae duk yaji sh'awar ta sosai har dai yanda yaga d'igo d'igon ruwa a jikin ta.
Sae da ta gyara d'aurin towel d'in sannan ya iya kallon ta yace"yau da wuri zaki had'a break fast sbd da wuri su umma zasu dawo.
Yana gama fad'a yasa qafa zai fita tace"Bobby"ya juyo a hankali yana kallon ta, tazo gab da shi ta riqo hannun sa da ya jiwa ciwo jiya,cike da damuwa har tana ji kamar tayi kuka sbd ganin yanda hannun ya kumbura sosai,nan taja shi suka zauna kan bed, sannu a hankali take walwale mishi bandage har ta cire taje ta d'auko first aid kit,a hankali take wanke mishi gurin da kad'a da sprit.
bayan ta gama ta sa mishi wani sabon bandage.
A natse ta d'ago tana kallon shi taga ashe ita yake kallo tace"sannu ko?ya lumshe idon shi tare da fad'in kema sannu,ba tace da shi komai ba domin ganin take taci ya mata sannun sbd ita kad'ai tasan zafin da taji a lokacin da take wanke mishi gurin sae taji abun har cikin ranta tamkar ita ke dauke da jin ciwon.
Nan ya tashi ya fita ita kuma taje ta shirya sannan ta fito zuwa kitchen ta sami Mimi da Hakeem zaune a falo mimi na biya karatun qur'ani.

Sae da ta gama had'a break fast ta jera abun da duk za'a buqata kan dining.

Suka ji oda da gudu pinky taje ta bude gate cikin murna.
Koda suka fito cikin mota har su Hakeem sun fito,
Mimi taje da gudu ta fad'a jikin umman ta kafin take zuwa gurin Abban ta.
Haka Billy da Hakeem suka je suka tarbe su sannan suka shiga daga ciki.
Bayan sun gama cin abinci ne suka je asibiti domin Hakeem ya sanar da su tun kafin su dawo.

Da dare guraren qarfe goma da rabi Hakeem ne kwance sai juyi yake kan bed baya da muradi irin yaji pinky kwance a qirjin sa har ma jin yake kamar ya kira ta a waya tazo ta taya shi bacci tunda Mimi bata nan.

Yana cikin haka ne yaji knocking da hanzarin sa ya tashi ya bude dakin.
pinky ya gani rungume da qatuwar teddyn ta,ajiyar zuciya ya sauke a hankali sannan ya bata hanya a natse ta shiga daga ciki,tayi tsaye ba tare da ta nemi guri ta zauna ba,yaje gab da ita har suna jin qamshin turaren juna yace"ya baki zauna ba ko wani abu kike so? shiru tayi tana kallon shi domin ita kanta bata san me ya kawo ta dakin ba, kuma gashi a daki ta kasa bacci sae faman juyi take wanda duk ta juya ba abin da ke fad'o mata a rai sae Hakeem.... Ki min magana kinji pinky,
still kallon shi take yayinda hawaye suka ciko tap a idon ta har suna qoqarin zubowa, da sauri Hakeem ya dafa kafàdar ta yace"pinky mene ne gaya min kinji"sautin kukan ta ne ya fara fitowa yayinda ya kar6i teddy ya ajiye.
A hankali ta fad'a kan jikinsa yayinda sautin kukan ta ke qara fitowa,duk Hakeem yabi ya damu sosai sae tambayar ta yake lafiya?cikin kuka ta d'ago tana kallon shi tace"uhm uhm nima ban sani ba"no pinky kodai wani abu aka miki, gaya min waya ta6a ki? ya nuna kanshi da yatsa yace "nine?girgiza mai kai tayi yace"ko Abba? umma fa?abokannan ki? duk girgiza mai kai tayi tare da fad'in nifa ba abinda aka min,
bai ce da ita komai ba sae jan hannun ta yayi suka zauna kan bed yakai hannu ya shafo cikin ta da ya lafe sosai yace"kina jin yunwa?gyad'a mishi kai tayi,ya tashi ya dauko fresh milk da cup ya tsiyaye yaje yana bata har sae da tace ya ishe ta sannan ya bata ruwa tasha ya zaro tissue ya goge mata d'an qaramin bakin ta yace"ki daina zama da yunwa kinji bcs bana so"gyada mishi kai tayi sae kawai ya dauke ta cak ya kwantar da ita ya rufa mata blanket yaje ya kwanta tare da rage hasken d'akin.
Chapter 20 · 0% Book details