← Book details Billy Pinky Durlin Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 49

Sashe 34

Billy Pinky Durlin Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

*👛67&68👛*
Wayar sa ce tayi qara bai qaraso ba ya fita dakin nan tayi saurin shan maganin tana gama sha sae gashi ya sake shigowa ba shiri tasa qafa ta take pills din da bata riga ta tsince ba ta kuma yi surin 6oye kwalbar da ke hannun ta.
Hakeem ya qaraso yayi tsaye yana kallon ta ita kuma sae faman tura qafar ta take a hankali tana tura pills under bed yayinda take kallon fuskar shi dauke da guntun murmushi yace "meyasa kika baro daki ko a nan kike so muyi bacci yau? um um
To lafiya me yake damun qafar ki naga kin kasa tsaidata guri d'aya ko wani abu ya cije ki? ba komai
bai kula ta ba sae zaunar da ita yayi kan bed wanda hakan yasa ta tura kwalbar under pillow shi kuma ya durqusa ya dora qafar ta kan jikin sa yana duba qafar kafin yace wani abu ya hango pills qwara d'aya sae dai duk ya rarratse kan takin da pinky ta mishi.
Dauko pills din yayi yana kallon ta yace "Billyta wannan maganin fa na mene ne?shiru ta mishi, ya tsure maganin da kallo ko zai gane wani abu,
cikin kakkausar murya yace" am asking u! uhm uhm...... ba kuka na tambaye ki ba so nake naji wane irin magani ne bcs bana so na miki rashin fahimta kallon shi kawai take
idanun ta har sun cika da qwalla kauda fuskar shi yayi yayinda idanun shi suka kai gun jakarta da ke kan drawer wani irin kallo ya mata sbd kwalin maganin da ya zaro cikin jakarta,
da mamaki yace"pinky me kike yi da wannan magani? girgiza kanta ta shiga yi ba tare da tace komai ba yace "say something pinky stop doing dis talk to me" Bobby ba nawa bane.... na waye kuma ina kwalbar maganin take? nima ban sani ba.... kinga gaya min ina kwalbar take bana son qarya fa ! shiru ta mishi yayi2 da ita tayi magana taqi sae kuka take mishi, ransa ne yayi mugun 6aci ya daka mata uwar tsawa har sai da ta miqe a tsorace nan ya fizgi hannun ta suka tafi d'akin shi suna shiga dakin ya saki hannun ta yaje ya kwanta zuwa tayi ta kwanta kan jikin shi tana mishi kuka tana bashi haquri tsawa ya daka mata kan ta sauka kan jikin sa qanqame shi tayi ta cusa fuskar ta a qirjin shi duk ta rikice tana bashi haquri sbd ta dauka ko dukan ta zai yi, komai bai sake ce mata ba sae kukan ta yake saurare mai qona mishi rai tsaki yayi yace "wai baza ki sauka kan jikina bane ,
Jiki sanyaye ta sauka ta tafi nesa dashi ta kwanta sae ci gaba take da kuka.
Rigar jikin sa ya kalla yaga duk ta jiqa gaban rigar da hawaye canza rigar yayi ya kwanta tare da juya mata baya.

Dare yayi sosai amma kowanen su ya kasa bacci kan 6acin rai da kuma sabon da sukayi wa juna na bacci manne da juna,
can Billy ta kwatanci Hakeem yayi bacci ta lalla6o a hankali ta kwanta bayan shi tare da rungumo shi.
Hakeem da bai riga yayi bacci ba ya bude idonshi a hankali yana kallon hannayen ta da ta saqado kan qirjin sa shiru yayi abinshi har sae da yaji tayi bacci nan ya juyo yana kallon fuskar ta ya kai hannun sa a hankali yana share mata en hawayen da ya gani kan fuskar ta sannan ya qara rungume ta hade da sauke ajiyar zuciya yana shafa bayan ta a hankali daga nan bacci ya d'auke shi.

Washe gari ta riga shi farkawa ta zare jikinta a hankali tana kallon shi nan ya bude idon shi yana kallon ta tayi saurin kauda fuskar ta kamar mai jin kunya ta tashi ta bar d'akin.

Guraren qarfe goma yaje dakin ta ya samu tana toilet zama yayi kan bed ya dauki kwalin magani yana juya shi a hankali yana cikin haka ne yaji fitowar pinky a natse ya dago yana kallonta sanye da towel iya cinya kanta qasa yace"pinky zo ki zauna "a sanyaye taje ta zauna nesa da shi yace matso kusa zamuyi magana ne, ba musu ta matsa kusa da shi yace"pinky me yasa kike shan maganin nan kuma yaushe kika fara shan sa? 3days a go,
a wane dalili kika fara shan sa ko wata matsala na gaya miki kina d'auke da ita ko kika ga alamar hakan ? ko daya... to meyasa kike shan sa, shiru tayi yace" kar ki sake min shiru idan ina tambayar ki abu bana so, yi haquri, naji amma bani kwalbar maganin sbd bana so ki sake shan sa bcs Allah yayi min ke mai cikakkiyara ni'ma na kuma yi alfahari da hakan sosai don haka bana buqatar kina shan wani magani kinji, kayi haquri nima bani shi akayi ba wai ra'ayi na bane....dama nayi tunanin hakan but waya baki maganin? kayi haquri bazan iya sanar da kai ba, olryt bani maganin,
ba musu ta dauko maganin ta bashi ya kalle ta yace "pinky ina so kimin alqawari baza ki sake shan maganin nan ba" nayi ma alqawari bazan sake shan sa ba, maimata min naji, Bobby nayi ma alqawari bazan sake shan wannan maganin ba,promise? yes i promise to u, but idan kika sake wane irin hukunci zan miki?kamin komai ma, yauwa Billyta ai nasan ma baza ki sake sha ba ko? gyada mishi kai tayi yace "aha to mu tafa,da murmushi ta bashi hannu suka tafa yace" then give me a kiss"
ya fadi haka ne yayinda ya nuna kumatun shi Billy taje a hankali ta mishi kiss kan kowane kunce, murmushi ne ya bayyana a fuskar shi shima ya dora mata kiss a ko wane kunce ya kuma dora mata kan goshin ta sannan ya je kan lips dinta ya dora mata, murmushi tayi cike da jin dadi ya jawo ta ya rungume yace " Billyta kiyi haquri da fushin da nayi da ke dama haka rayuwar aure take sae da haquri kinji" nima kayi haquri Bobby bazan so na sake 6ata maka rai ba "olryt tashi ki shirya muje muyi breakfast bcs yunwa nake ji,
tace" to " kafin yake tashi ya fita daga dakin ita kuma ta tashi ta shirya taje sukayi breakfast cike da nishad'i.

Bayan sun gama su kaje 6angaren su umma sun jima sosai a can sae fira suke da umma,
Billy kam biye kawai take da su yayinda take faman jure ciwon da marar ta ke mata wanda tun jiya take jin tana mintsila mata amma ta basar.
Hakeem ya lura da ita nan yaja ta suka koma 6angaren su, suna isa ta fashe mai da kuka yace " mene ne pinky? marata ke min ciyo sosai, dama kina ciwon mara ne? um um ban ta6a ba, to ya isa yi shiru zata daina ne may be canjin yanayi ne nan ya shiga rarrashin ta tun tana jurewa har ta fara mishi ihu tana fad'in wayyo Allah Bobby na shiga uku zan mutu don Allah ka taimaka min! gabad'aya ya shiga damuwa sae shafa qasan cikin ta yake yana fadin "tayi shiru ta daina kuka zai daina amma ina kamar qara mata ake sae kuka take yayinda ko yatsan ta bata son motsawa kan bala'in ciwon da take ji nan ta riqe mai hannun da yake shafa mata gun sae kuka take ba wasa hawaye sha6e2 duk tayi zufa ta jigata cikin qanqanin lokaci .
Tashi yake sonyi amma ta rirriqe shi tana fad'in "Bobby in ka tafi zan mutu don Allah ka tsaya " komai kasa cewa yayi duk jikin sa yayi sanyi ganin irin yanda take kuka cike da tausayi, nan ya samu da qyar ta saki hannun shi ya tashi zai je 6angaren su umma, wani irin
ihu ta saki ta fara juyi tana kiran sunan shi da saurin sa ya dawo yaga rigar jikin ta tayi staining da jini.
Durqusawa yayi tare da tallabota jikin sa cikin muryar rarrashi yace "pinky yi haquri daina kuka kinji kinga ashe ma menstruation preod dinki ne yazo yana baki wahala, yarfi take da hannu tace" Bobby bai ta6a min haka ba don Allah muje asibiti ka duba kaga wlh Bleeding nakeyi sosai kamar fanfo a rikice Hakeem ya duba hankalin sa ne yayi mugun tashi ganin yanda take bleeding.....sallamar Amjad yaji yayi saurin amsa sallamar,
Amjad na shigowa yace "subhanallah Bobby me yake faruwa da pinky? ba wannan ba Amjad nidai muje asibiti nan suka fita hankali tashe sae asibiti.
Da qyar aka samu ta rage Bleeding inda har yanzu tana fama da ciwon mara sae dai ya rage ba Kamar farko ba hakan yasa akayi admitting din ta a aminity.

Jingine take a qirjin Hakeem shi kuma yana zaune yayinda hannunsa ke cikin rigarta yana shafa qasan cikin ta a hankali yana mata sannu hannunta ta d'ora kan na Hakeem tare da 'qara lafewa kan qirjin sa sbd baccin da ta soma ji kan allurar bacci da aka mata nan Hakeem ya zaro wayar shi zai kira umma sae ga Amjad ya shigo yace dashi kaxo zamuyi magana.
Cikin kulawa Hakeem ya kwantar da pinky wacce har yanzu bata iya motsin kirki.
Chapter 34 · 0% Book details