← Book details Billy Pinky Durlin Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 49

Sashe 35

Billy Pinky Durlin Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Yana shiga office din Amjad ya samu guri ya zauna yana mai kallon Amjad wanda yayi baqiqirin da rai, Hakeem yace "lafiya Amjad? Mtsw wai kai Hakeem yaushe ne zaka san ka girma ka daina biye wa son zuciyar ka kan baqar aqidar turawa gashi yanzu kaje ka jawa pinky matsala tana Bleeding wanda har ma fargaba nake idan bata sami matsala ba ...... Amjad bangane ba me kake nufi ..... Ina fa zaka gane kaje ka durawa er mutane pills tana sha......zumbur Hakeem ya miqe tare da ture kujerar da yake zaune ta tafi sae shillo take tana juyi yace "pills! ita pinky? Sosai kuwa shine yayi causing din komai ba wai period time din ta bane but kar ka ce min baka san tana shan shi ba?wlh ban sani ba Amjad kawai dai wani magani nasan na kar6e a hannun ta wanda yake min kama da pills but ganin kwalin shi yasa na cire zargin pills ne yanzu haka yana a mota ta bara ma na dauko maka shi kaga,
nan ya tafi cikin sauri ya dauko ya kawo mishi koda Amjad ya duba yace "ya salam pills ne a ciki ba asalin maganin ba fa kuma ko pills had'ararren pills wanda kan had'ararrin sa ne aka daina aiki dashi gabadaya at all ma an daina bugoshi,
Innalillahi na shiga uku wlh matsala yake kawo wa mahaifa a nan take a ina ta same shi Bobby ? bar ni kawai Amjad ina zuwa nan ya kar6i pills d'in ya fita rai 6ace yaje ya sami pinky wacce bata riga tayi bacci ba sae fama take da ciwon mara.
Tana ganin yanayin Hakeem ta yunqura da qyar ta tashi zaune kafin yake zama,
cikin damuwa ta d'ora hannayen ta kan kumatun shi tana kallon qwayar idon sa da ta cika tap da qwallah nan kawai taji nata idanun sun ciko tace "what's wrong Bobby? sauke hannyen ta yayi ya zuba mata pills a tafin hannun ta yace" cin amanar da zaki min kenan ki hana 'ya' ya na zowa a lokacin da ya kamata,,as how Bobby nida ba Allah ba ta yaya zan hana 'ya' yan mu zowa a lokacin da ya kamata ........wane irin magani ne na zuba miki tukun ? Maganin da ka hana ni sha kuma wlh ban sake sha ba..... ban saki rantsuwa ba kawai ina son naji confirm shine kike sha kafin na hana ki ? Eh.....kina sane kenan da cewa pills ne kike sha!shiyasa kika canza kwalba acewar wani magani ne ba pills ba!
saurin kallon pills din tayi dake xube cikin tafin hannun ta tace "pills kuma ya haka?..... tsaki ya buga ya kalle ta cike da tsana yayinda hawaye suka gangaro kan kumatun shi yayi saurin share hawayen zai fita tace"Bobby don Allah ka tsaya wlh bansan pills bane trust me .....never! tace" never trust me? ta fadi hakane yayinda take kallon shi da mamaki a hankali ta taso a daddafe tazo har inda yake tace "please Bobby muje mu zauna na maka bayani kasan na gaya ma bani shi aka yi kuma ba kowa bace face...... Shiiii ban nemi jin wane bayani daga gare ba don haka bazan 6ata lokaci na na saurari wani bayani a bakin ki ba!matsalar da kika ja mana kawai ta ishe ni!don haka ki barni naji da ita!
nan ya sauke yatsan sa da ya d'ora kan lips d'in ta ya fita daga d'akin.

Cikin kuka pinky ta tsure pills din da kallo hawaye na d'iga akai.

*Billy giro 😊*
👛👛👛👛👛👛👛👛👛👛
[9/22, 8:19 PM] ‪+234 810 038 8117‬: [9/6, 10:24 PM] Billy Giro: [06/9/2016] Billy giro😊

*👛BILLY PINKY DURLING 👛*

*Na Billy giro 😊*

*Page*
*👛69&70👛*
Nan ta durqushe a hankali tana ci gaba da kuka.
Amjad ne ya shigo ya same ta tace "Amjad wlh Allah ban san pills bane na gaya ma Bobby bai yarda da hakan ba"
Ajiyar zuciya ya sauke yace "pinky to ya akayi hakan ta kasance ? nima bansani ba bcs ba siya nayi ba bani aka yi shine nake so na yiwa Bobby bayani yaqi ya surare ni please ka kaini gurin shi na samu ko zai saurare ni, pinky Hakeem ya fita daga asibitin nan,eh
nasan ba zai je koina ba face gida please muje ka kaini..... no pinky barin asibitin nan ba naki bane har sae anyi bincike kan mahaifar ki idan ba wata matsala sannan ko zaki iya tafiya..... no ni bazan iya ba Bobby yana fushi dani bana jin zan iya samun natsuwar komai har sai na shawo kanshi please Amjad kar ka ce a'a don Allah ka taimaka min... shike nan naji tashi muje,
nan ta lalla6a ta tashi suka tafi yana ajiye ta gida yace
"don Allah pinky ki qoqarta kiga kun dawo asibiti da wuri Allah bana so aje a sami matsala yanzu ina sauri ne kan wani patient da aka ce an kawo emergency"
InshaAllah Amjad.

Nan yaja motar sa ya tafi ita kuma ta shiga daga ciki koda ta murd'a qofar d'akin Hakeem ya rufe da key nan tayi ta danna door bell har ta gaji bai bud'e ba sbd yaga lokacin da Amjad ya sauke ta.
Falo ta dawo ta kwanta bacci ke son fizgar ta amma taqi yarda da hakan sae jiran fitowar Hakeem take.
Ta jima a kwance amma ba alamar fitowar Hakeem.

umma ce ta shigo gidan da sallama pinky ta amsa sallamar cikin muryar kuka.
Cikin damuwa tace "lafiya me yake faruwa da ku ne Hakeem ya kirani kuma daji shima kuka yake yace naje asibiti na same ki naje ban same ki ba yanzu gashi nazo na same ki sae faman kuka kike ina Hakeem d'in yake ne ? umma yana daga ciki yaqi ya bud'e qofa.
Chapter 35 · 0% Book details