← Book details Billy Pinky Durlin Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 49

Sashe 37

Billy Pinky Durlin Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*Page*
*👛 71&72👛*
A 6angaren umma kuwa tana shiga gidan Abban Billy take d'an jin wasu suruttai a cikin falo hakan yasa ta d'an dakata bata qarasa shiga ba sbd yanda take jin sunan Billy na fitowa a zancen su kan pills d'in sa suka bata sae murna suke domin Hajiya seema ta gansu a lokacin da su Hakeem suka kai Billy asibiti yayinda taje dubiya.
Ran umma ne ya qara 6aci da kuma mamakin mugun nufin su na gaba akan Billy.
Da hanzarin ta zata shiga falo domin ci musu mutunci Abban Billy ya dakatar da ita wanda tun dazu yake gefen ta bata sani ba kuma duk yaji abinda Hajiya seema ke fad'i ita da qawar ta.
A tare suka shiga falon shida umma suka same su sae ci gaba da kekkewa suke suna tafawa qawar Hajiya seema ce ta fara hango su tayi saurin yiwa Hajiya seema nuni da ido a rikice Hajiya seema ta miqe tsaye tana kallon su ba wata wata Abban Billy ya kife ta da mari tare da furta kalmar saki a kanta, umma tace "subhananlillahi ya zaka furta kalmar saki kai tsaye a cikin fushi..... Saki ya zama dole a tsakani na da ita domin duk matar da ke qoqarin ganin ruguza rayuwar 'yata ba matar zama bace kuma bata dubi irin adalcin da na mata ba naqi qaro aure bayan nasan ta sami matsalar da baza ta sake haifuwa ba duk da ina cike da son 'ya' ya amma na haqura shine bata ga abinda zata saka min da shi ba sae lalata min rayuwar 'yata kwaya d'aya tal sbd kawai ta zamo ita ce silar samun matsalar ta.... cikin kuka Hajiya seema ta durqusa kan guiwoyin ta tace "don
Alhj kayi haquri wlh sharrin shaid'an ne..... hannun sa yasa ya buge hannun ta da riqe mishi babbar riga ya juya zasu bar gidan shida umma tayi saurin cin gaban su tana roqon umma kan ta roqa mata shi ta san yana jin maganar ta.... wani mugun kallo umma ta sakar mata tace "azzaluma kawai macuciya! taya kike tunanin kinyi matsayin da zan roqa miki alfarma! bayan kina neman illata rayuwar er mu! sae dai ma nace Allah ya isa tsakanin mu da ke..... na shiga uku don Allah Halima (cewa da qawar ta) kiyi musu bayani wlh ko d'aya bana da nufin cutar da Billy kece kika bani shawar yin hakan...... Da Allah malama ni sake ni don na baki shawara sae akace dole sae kin bi! soro soro Hajiya seema tayi tana kallon Halima inda ta tuna lokacin da take kwance kan gadon asibiti Halima ta same ta tana mata ya jiki hade da jajanta mata har tana cewa wai garin ya hakan ta faru? wlh qaddara ce Halima Billy ce ke ball ni kuma ina zaune ina shan iska tashin da zanyi kawai naji qwallo a cikin qafafu na hakan yasa na fadi kan tsofon ciki na, nan na buga ihun da tun daga lokacin bansan inda kaina yake ba shine koda na farfad'o na ganni a asibiti bana tare da tsofon ciki na koda na tambayi Abban Billy ina abin da na haifa,
ya shiga gaya min sae dai nayi haquri abinda ke cikin cikina d'a namiji ne kuma ya fito ba rai sanadiyar far masa da nayi..... innalillahi wa Inna ilaihi raji'un! seema yanzu duk irin wahalar da kika sha kan laulayin cikin nan ace abinda ke ciki ya fito ba rai.... Halima da ace shi kad'ai ne da da sauqi yanzu fa shike nan bazan qara haifuwa ba sbd likitawa sunce mahaifata ta sami matsala..... What! keda haifuwa har abada kuma har kike kiran abin da qaddara.... me zan Kira abun idan ba qaddara ba Halima? Hmm! Lallai ke kidahuma ce mara tunani to ai da gayya aka miki haka domin na tabbatar baqar matar nan ce umman Hakeem ta turo Billy ta miki haka don kawai ki sami matsala da ke har abinda ke cikin cikin ki sbd kar ki sami qaruwa kizo nan gaba ki fita da y'a'ya ganin Hakeem ne kad'ai d'anta kuma har yanzu shiru ba alamun zata sake haifo wani don haka kar ma ki yadda da hakan ba qaddara bace.... Hm Halima ai kin fi kowa sanin nida umman Hakeem ba ma wannan kishin da matan sauri keyi ni mutunci ne tsakanin mu don haka ki ajiye wannan zancen kawai..... Kin yarda da qaddara ce kenan kuma a haka zaki zauna har abada ba ke ba haifuwa sae dai ki gani a gun wasu matan se kace kin rako mata duniya.... Halima don Allah ki ajiye wannan zancen bana so,
na yarda da qaddara kuma zanci gaba da haquri kan yanda Allah ya tsaro min rayuwata.

Duk wannan tunanin yana faruwa ne yayinda take gaya musu komai cikin kuka sannan taci gaba da cewa haka tayi ta bani muguwar shawara har nazo na fara jin haushin Billy da umman Hakeem shine kuma yanzu ta bani shawara kan cewa na lalata mahaifar Billy amma shine Halima baki ga abinda zaki saka min dashi ba sae haka bayan kece kika bani shawara....... Mtsw har wa yau ke kidahuma ce kuma marar tunani in banda rashin tunani baki san shawara mai kyau da mara kyau ba ko kuwa idan nace ki fad'a wuta zaki fad'a wuta ne to bari kiji in gaya miki abinda baki sani ba, ba Billy ce ta jefo qwallor ba nice sbd na jima ina baqin cikin ganin ci gaban rayuwar ki kinyi aure kin barni har yanzu banyi auren ba sae faman yawo nake kan titi shiyasa na shiga baki baqaqen shawarwari don kawai naga cewa naki auren ya mutu inda sae yau Allah ya cika min burina sae dai nace miki sannu da abinda ya faru da ke, ni kinga tafiya ta,
nan ta d'auki jakar ta tana mata kallon wulaqanci ta fita.
wani irin kukan nadama ne yazo mata taji komai ya cakud'e mata.
Nan su umma suka barta suka wuce zuwa asibiti.

Sae zuwa dare suka dawo ko shi Billy ce ta matsa bata son kwana asibiti amma ba'ayi niyyar sallamar ta ba.

Hakeem ne ke mata shirin bacci bayan ya gama ya had'a mata tea mai kauri ya bata tasha sannan ya bata magunguna tasha yasa tissue ya share mata bakin ta ya kwantar da ita kan qirjin sa yana mata sannu yayinda yake shafar bayan ta a hankali, qara shigewa tayi a qirjin sa tana share hawaye cike da son kar ya ganta, Hakeem da duk wani motsi nata yana kule dashi yace "Billyta me kike ma kuka ko har yanzu sosai marar ki ke ciwo? girgiza mai kai tayi yayinda ya shafo qasan cikin ta a hankali yace to mene ne? akan Abba ne da mama banji dadin yanda ta biye wa shawarar qawar ta ba har tazo ta kai ta ga haka n.... Billyta ki ajiye wannan zancen domin haushi yake bani na rasa me yake damun wasu mata da suke biye wa shawarar qawaye daga qarshe suzo suna yin nadama .
Ni yanzu ba abinda yake damu na irin na samu ki daina bleeding ko zamu qara samun tabbacin lafiyar ki duk da cewa bincike ya nuna mahaifar ki lafiya lau take bata da wata matsala.

Har kusan two weeks pinky na faman bleeding hakan yasa ko yaushe suna kan yawon asibiti duk Hakeem ya rame sbd yanda ya shiga damuwa haka ita ma Billy duk tabi ta rame kan zirzirga da yawan shan allurai wanda duk za'ayi allura sae tayi ta faman kuka.

Zaune take gaban madubi d'aure da towel tana shafa turarukka duk d'akin ya qamsashe .

Tana gama shafe shafen ta ta tashi sae ga Hakeem ya shigo d'akin sanye da uniform din sa na sojawa ya lumshe idon shi tare da sauke ajiyar zuciya sbd jin dad'in yanayin d'akin luf luf ga sanyin Ac da qamshi.
Billy wacce ta zaro rigar da zata saka ta saki rigar ta tafi cikin murna ta tarbi Hakeem haka shima Hakeem da murnar shi ya tallebeta yaje kan bed ya zauna tare da zaunar da ita kan cinyar shi yace "Billyta ya ake ciki ne naga sae murna kike ko kin daina bleeding ne ? gyada mishi kai tayi yayinda take wasa da buttons d'in rigar shi,
fuskar ta na d'auke da murmushi,
yace" Alhmdlh ina ce komai normal kike ji a jikin ki ba wata matsala ko ?ta lumshe idon tare da fad'in "eh"
zuruf taji hannun sa cikin towel yana lalubar qirjin ta yana matsa su a hankali yace"abokanan wasa ta fa na jima ban tambayi lafiyar su..... kunya taji tasa tafukan hannyen ta ta rufe fuskar ta,
Hakeem yayi murmushi yana kallon ta sbd sosai yake son ganin yanayin pinky idan taji kunya hakan yasa wani lokaci da gangan yake mata wani abun don kawai yaga yanayin jin kunyar ta.
Jaye hannyen ta yayi yaje a hankali kan lips d'in ta ya bata kiss yace "pinky wai har yanzu kunya ta kike ji" murmushi kawai ta mishi tare da kwantar da kanta a kafad'ar shi sae yawo take da yatsan ta kan qirjin sa kamar mai zana wani abu yace "muje ki taya ni wanka na samu nazo naci abinci nan ta taya shi ya cire kayan jikin sa ta d'auko towel ta d'aura mishi suka je toilet.
Chapter 37 · 0% Book details