← Book details Billy Pinky Durlin Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 49

Sashe 41

Billy Pinky Durlin Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Hava Hakeem ya tana jin yunwa zaka ce sae kun dawo bayan yunwar ce ta maida ta gida....amma umma shine zata ajiye min kuka bata min bayani ba bayan tasan bana son kukan nan da takeyi kuma yunwa sae kace ba abinci a can duk ina kalolin abincin da kika baro? Bobby bana ra'ayin ko d'aya a cikin su kuma ba fresh milk a gurin....Mtsw ya buga guntun tsaki yaja hannun ta yace"zo muje kya sha ta a cikin mota, qunquni ta shiga yi ita baza ma ta sha ba ko yunwa zata kashe ta kuwa, Hakeem yaji sak me take fad'a yayi shiru kamar bai ji ta ba.
Da suka shiga mota ya bata fresh milk taqi kar6a nan ya ajiye mata ita kan jikin ta yaja motar cikin 6acin rai.
Suna isa ta fita tun mota bata qarasa tsayi ba ta kuma jefar da fresh milk kan seat ta wuce kallon ta kawai Hakeem yayi shima ya fito motar ba tare da ya d'auko mata fresh milk in ba.

Tun six sae guraren qarfe tara na dare suka dawo inda har yanzu fishi Billy keyi.
Sun d'an jima da dawowa ne Hakeem yaje d'akin Billy ya samu har tayi wanka tana shirin kwanciya zama yayi kusa da ita yana rarrashin ta har ya samu ta haqura suka je d'akin shi.
Suna shiga d'aki ya bud'e fridge ya d'auko fresh milk da cup yaje ya zauna kusa da ita ya tsiyaya mata a cup yace "ungo kisha tunda muka shigo na sanya miki ita a fridge shine har ta d'an soma yin sanyi,
ba musu ta kar6a takai kan lips kenan taji bata yi sanyi a yanda take so ba cikin fushi ta ajiye cup tace" tun d'azu da ace ka barni nasha da zan fi jin dad'in ta amma sae da ta rage sanyi zaka wani ce nasha,
Tissue ya zaro ya goge mata lips in ta dake dauke da d'igon fresh milk yace "yi haquri bari na sanya miki qanqara tayi sanyi sae kisha kinji" ba ta ce komai ba sae kwanciya tayi kan gadon tana kuka mai cike da shagwa6a,,
Nan Hakeem yaje ya fashe qanqara ya saka mata sae da ya kwatan ci tayi sanyi yace " kukan ya isa haka tashi kisha yanzu tayi dai dai yanda kike so kinji "
nan ta tashi da mazarin ta sbd yunwa take ji sosai,
babyn cikin ta duk ya hana ta saqat sae motsi yake,
"jawota yayi jikin shi zai fara bata yace" bari dai nasha tukun naji idan tayi sanyi yanda kike so kar kiji ba dai dai ba ki ajiye min wani sabon kuka,
nan ya kai cup a bakin sa ya kur6a yace "wow tayi sanyi yanda kike so" oya bud'e bakin ki kisha " nan ta bud'e bakin ta bai riga ya bata ba wani irin tari yazo mishi ba shiri ya ajiye cup ya fara tari har da su zamewa kan gado duk Billy ta rikice ta durqusa kusa da shi tana murza mishi bayan shi sae sannu take mishi.
Ganin tana qoqarin mishi kuka ya samu da qyar ya tsaida tarin yace " is ok ta d'an sarqe ni ne kar kiyi kuka kinji, ungo sha kar yunwa ta miki yawa but take care kema kar ta sarqe ki kinji, gyada mishi kai tayi ya tashi ya nufi toilet cikin sauri sbd tarin da ke qoqarin sake zo mishi,
da shigar shi ya kunna famfo don kar taji sautin tarin da yake wanda kan tsananin wahala har wani kalar amai ya fara yi mara kyan gani.
Billy kuwa sae da ta qara qanqara tayi zaune tare da kai cup a bakin ta.

*Billy giro 😊*
👛👛👛👛👛👛👛👛👛👛
[9/22, 8:40 PM] ‪+234 810 038 8117‬: [9/9/2016]

*👛BILLY PINKY DURLING 👛*

*Na Billy giro 😊*

*Page*

*👛75&76👛*
Bata daina aman ba sae da ta amaye abinda taci kaf nan wani irin jiri ya d'ebeta ta tafi suuuu zata fad'i kwance a gurin.
Hakeem yayi hanzarin jawo ta ta fad'a jikin shi,sae kallon ta yake kamar wanda zai mata kuka duk ta bashi tausayi haka ma Naini da Feenah da ke gurin duk ta basu tausayi.
Hakeem ya kalle su cikin matsananciyar damuwa yace "pls Naini kira min Amjad a waya yazo ya duba min ita,
nd u Feenah pls je kira min umma, ba musu Feenah ta tashi ta fita Naini kuma ya shiga dialing number d'in Amjad shi kuma Hakeem ya d'auki Billy cak ya haura da ita sama nan Baraka taxo zata gyra gurin.

Hakeem na shiga da ita d'aki ya cire mata rigar jikin ta ya tafi da ita toilet ya watsa mata ruwa ya mata brush suka fita, suka sami umma tana jiran fitowar su ajiye Billy yayi kan bed wacce taje kan jikin umma tana wani galaibataccen kuka kan cikin ta da har yanzu masifar ciwo yake mata.
Umma ta kalli Hakeem wanda ke kallon Billy yana ji kamar ya maida ciwon kan jikin shi,
tace "Hakeem tun yaushe ne Billy take fama da rashin lafiya har tazo ta galabaita haka baka sanar da ni ba? 2 days but abin bai yi yawa ba sae yau,
Amma gsky umma na tsorata idan ba farfesun kifin da taci bane yake d'auke da wani abu, kamar ya?bcs tana kan cin farfesun kifi kawai ta tashi tana amai..... kar ka damu indai wannan ne, yanzu sanya mata riga Amjad zai shigo ya duba ta.
Nan ya nemo riga ya saka mata aka bawa Amjad damar shigowa yayi en gwaje gwajen sa kan pinky ya kammala yace "MashaAllah Hakeem sae ka kwantar da hankalin ka domin wannan abin farin ciki ne ya samu sae dai nace congratulation u are going to be a father....... bakin sa ya bud'e dariya ko murmushi ya rasa wanda zai yi ya nuna Amjad tare da fad'in tsakanin ka da Allah!?eh tabbas kuwa juna biyu ne da Billy.

Kai a bar zancen kawai domin murnar da Hakeem ya shiga ta wuce a bar misali kan tsananin murna bai san lokacin da ya jawo pinky yana kai mata hot! hot! kiss ta koina sae tambayar ta yake da gaske Billyta,
da gaske na kusa zama Abba da gaske I'm going to be a father at year of 2017!
"ya Rahman! "
ya fad'i hakane yayinda ya zame jikin sa ya durqusa kan guiwoyin sa ya d'aga hannyen sa sama yana godewa mai duka mai komai.

Hm! a yanda ya shiga gode masa kyace shekara ashirin yayi yana neman haifuwa bai samu ba sae yanzu.

Cikin farin ciki da dariya umma tace" Hakeem ya isa haka mana .... "no umma ai godiya bata yawa ko Billyta?
Ya fad'i haka ne yayinda ya riqo hannyen Billy yana murmushi ita ma murmushin ta mishi wanda yayi dai dai da shigowar Naini da Feenah wad'an da jin sautin yanda Hakeem ke zabgawa ubangiji godiya yasa suka kamo jiki suka shigo,
nan aka sanar da su farin cikin da ake ciki inda sukayi matuqar farin ciki da jin zancen har Naini ya bawa Hakeem hannu yana mishi congratulation Feenah kuma zama tayi kusa da Billy tare da riqo hannyen ta tana taya ta murna da haka suka qaraci farin cikin su inda Amjad ya rubuta irin magungunan da zata riqa sha da kuma irin abincin da zata riqa ci masu qara jini da kuma qara lafiya.
Wannan kenan.
Chapter 41 · 0% Book details