← Book details Billy Pinky Durlin Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 49

Sashe 5

Billy Pinky Durlin Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Nan umma ta fitar da turarukka kusan kala goma,kuma kowanne da kusurwar da ake shafa shi.
Da yake dama Billy ba kunyar umma take ji ba, nan umma ta shiga shafa mata turarukkan kowane lungu da saqo na jikinta, amma banda na qirji da kuma private part,
Billy taje toilet ta shafo ta dawo, wanda ita dai biye kawai take da umma,kuma dama ita ma'abociyar turare ce sosai wacce ko kusa da ita ka tsaya zaka iya kwasar qamshin turaren jikin ta ba tare da ka ko ta6a ta ba.

Umma bata bar dakin ba sae da ta shirya Billy tsaf ta kuma tsare ta sae da tasa ma cikin ta wani abu.
Sannan ne aka bawa en uwa da abokan arziqi damar shigowa.

Guraren 11 gidan kamar ya tsage sbd mutane sun cika maqil kyace an jima ana zancen auren.

Haka shima Hakeem a 6angaren sa duk cike yake da abokanan sa,wanda a bakin su ne yake jin amjad ne yakai musu IV bcs Abba na ganin Hakeem yaqi daukar invitations ya kira Amjad ya bashi,haka ita ma Billy Feenah aka ba domin ansan Billy jibge su kawai zatayi.

Da aka daura aure ne abokanan Hakeem sae tsula masa tsiya suke suna barkwanci shidai jin su kawai yake, ko ba qiyayya me zai yi da Billy wacce ta riga ta bada kanta wa maza,gashi sam qirar Billy bata daya daga cikin tsarin matar da yake so ya aura acewar billy tayi mishi sililiya sosai,
don haka bai ga abin tsinta a jikin ta ba.

Haka ita ma Billy abokanan ta keta mata tsiya yayinda wata er uwarsu ta Maiduguri ta tsare ta tana zana mata lalle ba don taso ba,acewar lalata mata jiki kawai za ayi sbd dama Billy bata son taga digon komai a fatar ta,
ra'ayin ta kamar wata baturiya, bata son lalle ko kadan qyamar sa ma take ji,hakan yasa a rayuwar ta bata ta6a lalle ba sae yau.

Sae gashi yayi matuqar kyau har dai yanda take da hasken fata,duk wanda ya gani sae ya yaba lallen.

Kwana uku akayi ana bukukuwa, en uwa da abokan arziqi kowa yayi farin ciki da auren domin kallo d'aya zakayi wa ango da amarya kasan sunyi bala'in dacewa da juna,kowa naji da nashi kyau ba wanda zai nuna ma wani.
Amma su a gurin su basu ga ta inda suka dace ba suna dai jin mutane na fad'a kawai,wanda har ma haushi abin ke basu.
Haka aka qare bikin da murna yayinda Ango da amarya suke cike da baqin ciki.

Da dare umma ce tayi ma Billy packing din zuwa new Delhi ta saka mata abubuwan gyaran jiki sosai hade da turarukka inda take mata bayanin amfanin su d'aya bayan d'aya, Billy sae kallon umma take ba eem ba um um.

Washe gari har air pot en uwa da abokan arziqi suka raka su sae da jirgi ya tashi sannan suka fice cike da kewar juna.

Billy da Hakeem ba abinda suke tunani a cikin jirgi face sharrin da zasu qullawa juna domin ku6uta daga auren.

Har suka isa ba wanda ya kalli wani bare zancen magana,idan baka sansu ba baza ma kace sun san juna ba.

Da yake dama new Delhi gurin zuwan su ne, wato sun saba zuwa dasu umma.
Jirgin su na sauka kowa ya kira drivan shi yazo ya d'auke shi.

Masaukin su d'aya ne amma yau kwanan su biyu ba wanda yasa wani a ido, wanda hakan yayi ma Billy dadi sosai har ma tana roqon Allah yasa wani masauki Hakeem ya nema.

Kusan kullum sai ta fito tana zagayawa a cikin gidan sae yau taji bari ta shiga room by room.

Sanye take da er riga mai hade da wando iya cinya rigar handless ce dai dai ita,gashin kanta a sake yake sae cat eye sunglasses da tayi qawa dashi saman kanta,riqe take da glass cup mai dauke da fresh milk a ciki,
da yake dama ma'bociyar shan ta ce.
Haka take tafiyar ta cike da natsuwa har taje room d'in da daga shi sae d'akin ta.
Tana bude dakin ta shiga dai dai Hakeem ya fito daga wanka, ba shiri ta kauda idon ta,ta juya cikin sauri zata bar dakin,Hakeem ya jawo ta da qarfin tsiya ya manna ta a jikin gina,sae duk fresh milk din da ke hannun ta ta watso masa a qirji, wanda yayi dai dai da faduwar eyeglass din da ke saman kanta,kar6e cup din yayi, ya kama hannyen ta duka biyu da da'yan hannun sa, ya mayar a baya ya jimqe gam,har yana qoqarin jefar da glass cup sae kuma ya fasa, ya kalli Billy wacce ta kauda kai ta rumtse idonta gam, ta qara qanqame jikin ta da jikin gina bata son ta ta6a jikin Hakeem da yayi mata rumfa, qirjin ta sae kai komo yake, har ana jin sautin fitar numfashin ta sauri sauri sbd ta tsora ta sosai da ganin Hakeem ba komai a jikin sa,bcs bata ta6a ganin namiji haka ba sae yau ko lokacin da ta ganshi da jennifer bata ga tsiraicin sa ba sbd Jennifer ta masa rumfa.

Bai damu da ta tsora ta ba,
sae ma wata uwar tsawa da ya daga mata yace"uban me kika zo yi a daki na kuma dai dai lokacin da nake fitowa daga wanka!?bud'e idon ki kiga yanda kika 6ata min jiki!ki bud'e idon ki nace!!cike da tsiwa Billy ta bude idon ta ta tsayyadda duban ta a iya qirjin sa, ta buga uban tsaki ta kauda kai,sae mutsu mutsun qwatar hannun ta take,tace "dallah malam ka sake min hannu na fita!ran Hakeem ne yayi mugun 6aci yace"ba inda zaki je sae kin lashe kaf abun da kika watsa min a qirji, ko kuma wlh na tu6e ki na shafa miki ita a naki qirjin!

*```Billy giro😊```*

®NWA✍truncated by WhatsApp]
[9/22, 6:02 PM] ‪+234 810 038 8117‬: [8/2/2016] Billy giro😊:
*👛 BILLY PINKY DURLING👛*

*Na*
*Billy giro😊*

*Page*
*👛12👛*
A wulaqance Billy ta kalle shi sama da qasa tace"u have gone mad!
dallah ni ka sake min hannu na wuce ko kuma wlh duk abin da na maka kai kaja!

Da mamaki Hakeem ke kallonta ya rasa me yasa Billy ta raina shi da yawa,amma yau zai yi maganin ranin domin sae ya tu6e ta kaf ba zai barta da komai na jikin ta ba.
Nan yakai hannun yaja rigar ta da qarfi har sae da rigar tayi qara.
Cike da masifa cikin daga murya Billy tace wlh kar ka yaga min riga! Hakeem bai saurare ta ba sae qoqarin yaga rigar yake ta qarfin tsiya, nan Billy ta rikice ganin da gaske yake, gashi tayi iya qoqarin ta na ganin ta qwace kanta amma ta kasa.

Inda Allah ya taimake ta high heel ta saka, bata tsaya wata wata ba ta daka masa tsinin takalmin a qafa ta kuma fizge kanta da qarfi ta ture shi ya fada kan bed yayi saurin jawo bedsheet ya rufe jikin sa.

Ita kuwa Billy tayi saurin zare makullin qofa ta fita da shi, ta rufe Hakeem ta waje tana jin sa yana dukan qofa yana fadin"kizo ki bude min qofa ko kuma duk na fito ki gane kuren ki!
Nan ta gudu ta bar key a jikin qofa.
Tana shiga daki ta fada ruf da ciki kan bed tana sauke numfashi.

Bata yarda ta fito daga dakin ba sae da safe.

Ta fito sanye da doguwar rigar er simple amma ta mata kyau sosai sbd Billy mace ce wacce komai munin sutura idan ta saka suna mata kyau.

Ko wannan karon riqe take da fresh milk, yayinda take
saukowa kan staircase ta hango Hakeem zaune a falo yana waya rai 6ace ya dora qafa kan centre table qafar ta qabe sul sae sheqi ta ke.
Yana hada ido da ita ya sakar mata mugun kallo.
Duk da ta tsorata haka ta dake tabi ta gaban shi ta wuce zuwa garden.
Inda ta zauna kan resting chair tana kur6a fresh milk a hankali cikin natsuwa.

Hakeem kuwa ya matsu bai gama wayar da yake ba yazo ya sami Billy.

Tana tsaka da hutawar ta sae ga Hakeem cikin yanayin 6acin rai wanda bata ta6a ganin sa ba kamar wanda allurar sa ta soja ta motsa,shiyasa ta tsorata sosai amma bata yarda ya fahimci hakan ba sae ma kauda fuskar ta tayi gefe tana ci gaba da shan fresh milk.

Bata ankara ba taji ya kar6e kofin ya jefar da shi, ya damqi gashin kanta tare da dora qafar sa kan qafar ta yana mutsutsuka qafar,wani zafin bala'i taji wanda yasa ta shiga yin ihu yayinda Hakeem ke fadin"wa ya sanar dake abinda nazo yi garin nan da har zaki sanar da Abba, wanda dalilin haka ya hana min na aikata abin da nazo yi,ki gaya min munafurci me yasa kika sanar da Abba!

Billy kam bata iya ce mishi komai ba sae qoqarin qwatar gashin ta take, kuma bata ma fahimci zancen da yake ba, gashi kuwa ya zage sae fad'a yake, yayinda yake ci gaba da mutstsukar qafar ta,ita kuwa tana faman ihu,
Wayar sa ce tayi qara ya jefar da Billy ta fada sae kan resting chair ta riqe qafar ta da tayi jajir,Hakeem kuwa ya fita tare da rufe Billy a cikin garden.

Nan Billy ta shiga kuka domin ta fahimci hadarin da ya gani ne yasa ya mata qeta.

Ba 6ata lokaci ruwa suka fara sauka sosai, Hakeem kuwa yana jin yanda ruwan ke sauka da qarfi amma yayi kamar ya manta da Billy da ya rufe a garden, da qarshe ma baccin sa yayi.
Chapter 5 · 0% Book details