← Book details Billy Pinky Durlin Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 49

Sashe 1

Billy Pinky Durlin Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

[9/22, 5:36 PM] ‪+234 810 038 8117‬: [7/26/2016]
*👛BILLY PINKY DURLING*👛

*Na*
*Billy giro😊*

*Page*
*👛1 & 2 👛*
*I* hate u!
*I* hate u!! *I* am absolutely hate u *Bobby!!*bagidaje kawai wanda bai san abinda yake ba!....ke! ni kike gaya ma haka! Eh na fad'a kai baqauye ne,kana ikirarin ka waye amma kana abubuwan qauyawa,bari in gaya ma kai baqauye ne ko baqauye kuwa na qarshen qarshe domin duk wayeyyen mutum bazai ta6a sa ido akan abinda wani keyi ba wlh!da har zaka zo kana takura ni akan ra'ayi na!hakan yasa naji na tsane ka a rayuwa ta!
Gabadaya gayen yaji duk ta halaka shi domin da ka kira shi baqauyen mutum gara ka same shi ka masa dukan tsiye har ma ka had'a da zagin iyayen sa da kaf danginsa hakan ya fi masa da kace mishi baqauyen mutum.
Wani irin 6ari jikin sa keyi idanuwan sa sukayi jajir sbd tsananin 6acin rai yace"ke ni kike kira baqauyen mutum.... qarya nayi dube ka fa! Ta fad'i haka ne yayinda take kallon shi sama da qasa a wulaqance,
wanda ni Billy giro a iya gani na gayen ya bala'in waye wa kuma ya had'u ta ko ina baya da makusa domin da waye wa da kyau kesa a shiga Aljannah sae dae nace yayi sa'a.

Amma ita kallon shi take cike da tsana qarara a idonta yayinda take qara ganin shi baqauye bidib.
Tace lemmi tell u one thing, wlh bobby da saman ka har qasa kallo daya za'ayi maka a gane cewa kai baqauye ne na qarshe na fad'a!.....wani irin wawan mari ya kife ta dashi ta saki ihu sosai duk gidan ya kar6a, da sauri wata mata ta fito tace"me nake shirin gani Hakeem ba dai qanwar taka ka mara ba,yanxu har fadanku ya fara kai ka da dukan qanwar ka,,gwaggo wlh idan ta sake kira min wannan kalmar da take fad'a min sae na mata dukan tsiya... Kai Hakeem qanwar kace fa ka daina biye mata yarinya ce.......Ki bashshi gwaggo ba dukan tsiya zai min ba ya kashe ni idan zai iya,amma ni bazan ta6a daina ce masa baqauye ba!
Nace kai baqauye ne na qarshe,na fad'a ka kashe ni!.....rufe bakin ta keda wuya taji saukar mari,ihu ta saki mai had'e da kuka tace wlh bazan daina ba sae dae ka kashe ni,nace kai baqau......wacce suka kira da gwaggo ce ta rufe mata baki,wanda yayi dai dai da isowar wata mata, cikin 6acin rai matar tace"Hakeem ban hana ka ba,wai me ya
sa baka jin magana!nasha gaya ma ka fita harkar 'yata!ran Hakeem ne yayi mugun 6aci domin ya tsani ayi masa fad'a a gaban mutane!yace "umma kinji me take ce min kuwa,a commonn Stupid girl irin ta zata kira min wannan kalmar.....ka fara kira ma kanka stupid kafin ka kira ma wani!...wai baza kiyi shiru bane billy,keda ma ba kya tanka masa meyasa yau kika tanka masa? Wlh mama ya ban haushi ne kullum ya cika takura ni wai me kala d'aya, mai kala d'aya me ye ruwan sa da ra'ayi na, ni naji ina ra'ayin pink colour ba wanda ya sani, shine wai yau don nasa an canza min mota ta to pink colour ya hana a shigo da ita gidan nan kuma yasa aka qona min ita..... What! motar taki da aka siya jiya jiya? Eh mama tayi" maganar ne cikin muryar kuka.

Mamar ta kalli Hakeem da mamaki tace"Hakeem lafiyar ka kuwa!kallon mamar yayi ya d'an kauda kansa gefe yace"mama wai ba ku ganin dabbacin da takeyi ne komai nata pink colour har ma ace duk garin nan ba wanda bai sani ba,wannan wace irin jaraba ce da hauka! Kuma ko cikin kaloli bata ga colour din da take so ba sae pink,bagidajiyar kala.... To Hakeem ina ruwanka! ra'ayin ta ne... Hm mama ki barshi tukun yaje ya kalli madubi idan yaga kansa da kyau sannan ya iya dawo wa yaci gaba da inda ya d'ora,cike da tsana Hakeem ya kalle ta ya buga tsaki tare da "fad'in er iska kawai mai kala d'aya" yana gama fad'a ya fita,Billy ta ya mutse fuska zuwa kuka sbd kiran ta da yayi er iska.
Fadawa tayi jikin mamar tana kuka cike da shagwa6a ta d'ago idanun ta da suka cika tap da hawaye tace"mama kin ji shi ko"yi haquri zo muje daki shi da Abban shi ne yau ba mai raba su.

Hakeem kuwa yana shiga d'aki ya cire kayan sa gabadaya komai bai bari a jikin sa ba, yayi musu kallon d'ai d'ai,bai ga ko dot d'in pink a tare da kayan shi ba,
tsaki kawai ya buga ya wuce toilet ya watso ruwa ya fito yayi zaune kan mirror yana qarewa kansa kallo domin yaga shin ina ne pink yake a jikin sa domin ya hanzar ta cire shi, haka ya qarewa kansa kallo baiga pink ba,nan ma tsaki ya buga yana mai jin haushin kansa yace"meyasa zan 6ata lokaci na,na yarda da maganar wannan dabbar,tashin da zai yi ne sae ya tsaya cak yana qarewa fuskar shi kallo har dai lips d'in sa, a hankali yakai hannu ya murza lips din shi, da sae yau ya ta6a fahimtar pink ne,wani irin tsanar kansa yaji,cikin d'aga murya yace"No!!!!nan yayi watsi da duk turakkan da ke kan mirror, na fashewa suka fashe wad'an da basa fashewa suka shiga yawo a tsakiyar tiles.

Nan ya shirya a gaggauce ya figi motar sa ya fita bai zarce ko ina ba sae *HAKEEM SPECIAL HOSPITAL*
Da shigar shi mutane sae bashi hanya suke sbd gudun kar ya bangaje su.
Office d'in wani doctor ya nufa ko sallama bai yi ba yace"Amjad kasan me ya kawo ni!?ya nuna lips din sa yace "pink lips d'in nan nake so ka canza min su koma irin na kowa,da mamaki Amjad yace"Hakeem wannan fa halitar kace ba yanda za'a canza ta... Kai dai ne baka san yanda zakayi ba ko kuma nace baza a iya yin hakan a qasar nan ba,gobe ya zama dole na bar qasar nan zuwa New delhi domin amin plastic surgery a canza min wanan pink lips,,,
me yake damun ka ne Hakeem,Amjad idan ba a canza min pink lips d'in nan ba bana jin zan sake son kai na,Amjad zan iya kashe kaina idan har nayi sati da wannan abun,bai jira me amjad zai ce ba ya fita yabar Amjad cikin tsananin mamaki.

A 6angaren Billy kuwa Abban yana dawo wa ya shiga lallashin ta kan ta kwantar da hankalin ta indai mota ce, yau d'in nan zata yi sabuwar mota dal domin yanzu haka motocin da Hakeem yasa aka yo masa order sun iso ciki taje ta za6i d'aya son ranta,ya fadi haka ne yayinda ya bata keys.
Nan Billy ta qanqame baban tace"thank u dad!

Hakeem kuwa yana fitowa asibiti ya zo gida, koda ya shigo harabar gidan sae kallon sabbin motocin sa yake guda biyu black & white sae dai kamar yafi son baqar domin yafi kallon ta.

Yana shiga falon yayi dai dai da billy ta tashi zata je ta za6i d'aya daga cikin motocin da aka ce ta za6a.

Abba yace "yayi kyau Hakeem! naji duk irin izgilancin da kayi don haka kasani izgilancin da kayi zai koma kanka,domin mamana zata za6i d'aya daga cikin motocin da suka iso yanzu... Pls Abba wlh ina son mota ta,kasan cewa dayar ta Amjad ce,kuma Abba kasan irin yanda aka wahala kafin a sami dayar, Hakeem wannan karon bazan lamunta maka abin da kake yiwa mamana ba,,,ni gasky Abba sae dae na biya ta kudin motar ta amma baza ta dauki tawa ba.

Billy najin haka ta sace jiki ta fita sae da ta qare ma motocin kallo sannan ta nufi dakin mai gadi ta dauko galan ta nufi baqar mota wacce iya haduwa ta hadu har ma takai qarshen had'uwa,
Billy na zuwa ta shiga motar ta maida ta dai dai tsakiyar gida,ta fito riqe da galan wanda nake tsammanin fetur ne a ciki, tabi koina na motar ta zuba.

Sae ga Hakeem ya fito ya same ta tana aikin,ta kalle shi fuska ya mutse tace "dama kuwa a gaban ka nake so na aiwatar da abin da nake shirin yi yanzun,idan kai ka kasa yi a gabana ko kuma ince kasa wasu sukayi sbd tsoro to ni da kaina zanyi kuma a gaban ka!

Hakeem bai ce mata komai ba sae kallon ta yake a wacce ta zautu don ganin yake ko giyar wake tasha bazata qona masa mota ba asali ma ya dauka ruwan banza ne ta sakawa motar.

Taci gaba da cewa"Bobby na yaba sosai da yanda Abba yamin,wato hukuncin da ya yanke, amma sanin kan ka ne duk wani abu da ya fito daga hannun ka ko ya fito da sunan ka na tsane shi bare har na iya zama da shi a matsayin nawa, shiyasa zan yanke hukuncin da nake ganin shine dai dai a gurina, tana gama fadar haka ta qesta ashana ta cinnawa motar wuta, sannan ta jefa masa key tace"go and save ur motor if u can"ta wuce ta bar shi tsaye sororo yana kallon motar sa naci da wuta wanda ji yake tamkar zuciyar sa ce ke ci da wuta.

*Billy giro😊truncated by WhatsApp]
[9/22, 5:39 PM] ‪+234 810 038 8117‬: [ 7/27/2016] Billy giro😊:

*```👛BILLY PINKY DURLING👛```*

*Na*
*Billy giro*😊
Chapter 1 · 0% Book details