← Book details Billy Pinky Durlin Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 49

Sashe 11

Billy Pinky Durlin Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Sae da ta wuce ya kalli Naini wanda ransa bai masa dad'i ba kan ganin ran Billy ya 6aci.

Hakeem kuwa duk haushin naini yake ji amma haka ya da ke yace"sorry Naini i dnt mean to hurt you kasan halin ta bata san me take yi ba.

*```Billy giro😊```*
👛👛👛👛👛👛👛👛👛👛
[9/22, 6:41 PM] ‪+234 810 038 8117‬: [8/9/2016] Billy giro😊:
*```👛BILLY PINKY DURLING ```*👛

*```Na Billy giro😊```*

*```page```*
*```👛22&23👛```*
Washe gari da safe Billy ce da Mimi suka sauko downstairs suka sami Hakeem da ke jiran fitowar Mimi domin ya kai ta school.

Kallon Billy yake wacce yaga idanun ta sun kumbura da alama kuka tayi kan game d'in da ya hana ta qarasa.

Girgiza kanshi yayi yace a ransa"wai ko dai yarinyar nan ta manta cewa tare da Hakeem take ba umma ba.

Mimi ce ta kula da kallon da yake ma Billy tace"yaya kai ma ka fahimci didi bata da lafiya ko?
ta6a jikin ta ma kaji yanda yayi zafi.
Ta fadi haka ne yayinda ta riqo hannun Hakeem zata kai jikin Billy.
Cikin hikima ya hana faruwar hakan bai yarda ya ta6a jikin Billy ba sae break fast din Mimi ya kar6a a hannunta da ke cikin lunch box.
Yaja hannun Mimi suka fita.
Yayinda Billy ta bi bayan su taje ta bude musu gate sannan ta dawo cikin gida ta fada toilet zuwa wanka.
Ta fito ta shirya cikin doguwar riga mai dogon hannu zubin ta kamar arabian gown.

Saukowa tayi downstairs wanda yayi dai dai da shigowar Hakeem shida Naini suka nufi dining.
Ta same su a can ta d'an saki fuska suka gaisa da Naini.
Sannan ta zuba musu abinci.

Ta zauna kusa da kujerar Hakeem zata fara ciyadda shi ya kar6i spoon din yace jeki yau bana buqatar hakan.
Kallon sa tayi tace a ranta"ai dama don ka wulaqanta ni ne kace na riqa baka abinci ammà baya daga cikin aikin gidan nan...
Me kika ce?
Da mamaki Billy ta kalle shi domin tasan maganar ta bata fito ba bare ace yaji me tace, tace"ai banyi magana ba... Kinyi magana man a cikin ranki domin yanayin fuskar ki ya nuna hakan, sanin kanki ne tun farko ke kika fara dorawa kanki lalurar gidan nan ba wani yace kiyi ba, wanda kinyi haka ne don wata banzar manufar ki.
Bobby ka fahimce ni mana har ga Allah manufar da kake tunani ba ita bace.
Abinda na gaya ma d'in dai ne....
naji da Allàh kar ki cika mu da surutu.
Nan Billy ta d'ibi quaker oats ta zuba madara da sugar ta wuce.
Naini ya bi ta da kallo har ta shige daki bai janye idon shi ba.
Hakeem da ke kallon shi yace"ya dai Naini ko wani abu kake buqatar ta kawo ma ne?
Ajiyar zuciya ya sauke yace"no ba komai"

Daga haka sukayi shiru basu sake cewa komai ba,Hakeem sai kallon naini yake kamar wanda ke son ya fahimci wani abu.

Suna kammala cin abinci naini ya wuce school.

Guraren qarfe biyar Naini da Billy ne ke volleyball cike da nishadi yayinda kowannen su ke sanye da games wears sbd dama haka suke da sun had'u guri d'aya basu da aike sae volleyball.

Suna cikin wasar ne suka ji oda Billy ta tafi cikin jogging ta bud'e gate da suka shigo ta rufe,ta koma kan wasar su.
Naini yace ina gate man dinku da kika bude gate?
Baya nan,
tayi maganar ne a taqaice taja hankalin sa suka ci gaba da volleyball.
Mimi wacce Hakeem ya dauko daga school taxo da gudu billy na ganin ta ta tarbe ta tana mata wlcm.
Nan suka ajiye wasar suka shiga daga ciki akasin Naini da ya wuce 6angaren shi.
Bayan Billy tayi ma Mimi wanka ta bata abinci taci kuma bata fito ba sae da ta tabbatar bata buqatar komai.

Tana fitowa ta sami Hakeem zaune a falo yana waya,
ta fita haka yace ina zuwa?
Ta d'an yi mamaki amma ta basar otace"zanje mu qarasa Volleyball nida Naini.....so kike ki bar Mimi ita kad'ai bayan yanzu ne dawowar ta. Game take bata buqatar fitowa.
Ki dai koma daga ciki ba inda zakije.
Ba musu ta koma bcs bata son ranta ya 6aci irin na jiya.

Sae dae wani abun yau kusan kwana uku Hakeem na mata abu d'aya wato yana hana ta fita suyi volleyball ita da Naini wanda ta kasa gane dalilin hakan,gashi tasan cewa ba yau ya saba ganin tana wasa da Naini ba duk zuwan da suke da su umma shine abokin wasan ta hakan yasa ta shiga dogon tunani can tace"kodai plan d'ina ya kama shi ta 6angaren da na fison ya kama shi, wata zuciyar ta ce da wuri haka?
haka ne but ba mamaki amma yanzu xan gawada wani abu naga idan haka ne.

Nan ta fad'a toilet tayi wanka ta fito ta shirya cikin wasu en iksan tufafi, sae dai tayi matuqar kyau.
Ta fito tana tauna chewing gum cike da natsuwa.
Qamshin turaren ta ya bawa Hakeem damar kallon ta inda ya shiga qarewa suturar jikin ta kallo.
Riga ce iya guiwa mai dogon hannu sae dae gabadayan ta net ce tsaf ake hango er fincikar rigar ciki wacce iya mammanta ta tsaya bata da mara ba da bz sae dan guntun wandon da ya tsaya mata iya cinya yayi mata d'as a jikin ta.
Wani hair style ne tayi ma gashin ta mai kyau kamar wacce taje saloon.
Tana sanye da takalma masu tsini.

Bai yi mamakin ganin dressing din ta ba sbd haka ko gida haka take abin ta idan bata fita,ma'ana iyakar ta ta zauna da shi a cikin gida domin shaqatawa.

Tana saukowa ta nufi gun center table ta dauki key zata fita Hakeem yace"ajiye min makullin mota.
Ba musu ta ajiya ta nufi hanyar fita yace"ina zaki je bayan kinsan Mimi awa daya ta rage naje d'auko ta daga school,
wa kika ajiye wanda zai kula da ita?
Ai bazan jima ba tana gama fada ta sa qafa ya sake dakatar da ita Yace"ina zaki je da en iskan kayan nan sae kace wata arniya!

Wani irin farin ciki taji amma ta nuna 6acin rai a fili.
Ta shagwa6e fuskar ta sosai tace"Oh Bobby city beach fa zan tafi idan bansa kayan nan ba wanne kake so na sa, domin kasan ko rigar nan ta sama idan naje cire ta zanyi domin naji dadin shiga ruwa, please ka bar ni naje nan da 30mnt zan dawo.
Wani mugun kallo Hakeem ya sakar mata wanda yasa ta bar gurin cike da shagwa6a tana kuka.
Hakeem bai daina kallon ta ba sae da ta shige daki ya tashi ya rufe qofa hade da zare key ya tafi da shi dakin sa.

Billy na shiga daki ta fada kan gado cike da murna tace"tabbas gayen nan ya fara sona bai sani ba that's my plan yanzu abinda ya rage na fara nuna maka so kamar da gaske but not now zan dai ci gaba da shagwa6e ma sannan daga bisani na fara nuna ma so sannu sannu kamar yadda nawa son ke shigar ka.
Bazan qarasa plan d'ina ba har sae ka fahimci kana sona ka kuma zurfafa a ciki ta yanda rashi na zaiyi iya illata ka, ni kuma a lokacin zan zille ma na nuna ma sam ba sonka a cikin zuciya ta basaja ne kawai, na kuma had'a ma sharrin da su Abba zasu raba auren mu kai tsaye bcs abinda zan fad'a da kuma shaidar da zan bayar qwaqqarar shaida ce wacce da a raba auren da kar a raba ba aure a tsakanin mu.

Bayan kwana biyu kwance take kan bed sae juyi ta ke duk taji ba dadi tana son tayi volleyball amma tasan Hakeem zai iya hana ta tunda yana gida gashi yanzu take son suyi kafin Naini yaje lectures bcs yàu evening lectures ne da shi.

Tana nan kwance taji oda tsaki ta buga sae kuma taji dad'i Hakeem zai fita ta samu suyi wasar kafin ya dawo.

Nan ta tashi taje tana zuwa ta same shi har ya cika fam yana jiranta cikin hanzari ta bud'e mishi gate ya fita ta rufe ta tafi 6angaren naini bata jima ba suka fito.

Suka fara volleyball.

Sun jima sosai suna yi sae taji odar Hakeem ya dawo nan taje ta bud'e mai gate ta dawo suka d'ora inda suka tsaya.

Hakeem ya fito daga cikin mota ya kalle su sau d'aya ya wuce daga ciki.

Billy ta bishi da ido domin tayi tunanin zai ce mata wani Abu.

Falo yaje ya zauna yana hutawa sae yaji yana son fitowa waje ya sha iska.

Da jaridar shi ya fito yaje kan resting chair ya zauna iska mai dad'i na buso masa.
Chapter 11 · 0% Book details