← Book details Billy Pinky Durlin Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 49

Sashe 2

Billy Pinky Durlin Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*Page*
*👛3 to 4👛*
Billy na shiga falo ta fad'a jikin Abba cikin kuka,Abba yace "mamana lafiya kuma me yake faruwa ko ya kar6e makullan ne? dagowa tayi cikin kuka hawaye sha6e sha6e a kumatun ta har suna diga kan rigar ta,tace"ba makullan ya kar6e ba Abba motar da na za6a ce yaje ya saka mata wuta ina ciki domin ganin lafiyar motar ban ankara ba kawai naga motar ta fara ci da wuta wanda da yanzu dani ciki ba don nayi saurin fitowa ba,"innalillahi wa inna ilaihi raji'un! cewar umma, Abba kuwa cikin tsananin 6acin rai ya tashi ya nufi hanyar fita sae ga Habib ya shigo rai 6ace ya nuna Billy yana qoqarin yace wani abu Abba ya kife shi da mari biyu masu kyau wanda duk tsananin girman falon sae da ya kar6a "abinda ba'a ta6a yiwa Hakeem a rayuwa ba wato mari, hakan yasa ya shiga mamaki muryar shi na rawa yace"Ab..ba me kuma nayi?..... "ba Kaine ka qona motar da na za6a har ma kana qoqarin hadawa dani" cewar Billy wacce ke jikin umma tana kuka kamar da gaske, Hakeem kam kasa cewa komai yayi sbd imani ne ya masa yawa, zafi uku uku a lokaci d'aya wanda nan take idanuwan shi sukayi jajir suka ciko da qwalla,sbd wasu maganganu da yaji umma na fadi"Hakeem sae yau na tabbatar da cewa na haifi d'a ban haifi halin sa ba wanda har fargaba nake idan ba canje aka min a asibiti ba!
Abba yace" tabbas Hakeem na kusan kawo qarshen qiyayyar da ke tsakanin ka da mamana....Abba.. Ka 6ace min da gani shàshan yaro kawai!bai fita ba sai da yayi ma Billy wani irin mugun kallo, yayinda ita ma ta watsa masa shu'umin kallo.

Nan su ka fito domin ganin motar, hayaqi ne baqiqirin har bakin qofar falon duk da irin nisan da ke tsakanin su da motar sbd gidan mai fad'i ne sosai.
Nan take Abba ya kira motar kashe wuta suka zo suka kashe tare da fitar da motar,nan aka sa masu aiki suka gyare harabar gidan tsaf kamar ba abinda ya faru.

Sannan Abba ya samu natsuwar lallashin Billy har ta daina kuka ta tashi taje d'aki tana mai jin farin ciki fal a ranta.

Hakeem kam baqin ciki ne ya masa yawa domin tun lokacin da yaje 6angaren sa ko fitowa bai sake yi ba har safe.

Da safe Billy ce ke saukowa a hankali kan staircase yayinda take dauke da pink dress riga da wando dai dai jikin ta rigar dogon hannu ne da ita a qasan gefen wandon kuma akwai wata er pink flower da ke dauke da duwatsu biyu dake reto a hankali, flat shoes ne sanye a qafar ta kasancewar billy yarinya ce mai tsayi shiyasa high heel basu dame ta sosai ba.
Fuskar ta na dauke da er simple makeup,tana sanye da glass kanta kuwa d'an qaramin gyale ne tayi rolling dashi yayinda jelar gashin ta ke reto a baya,gabadaya jikin ta ba abinda zaka nema ka ganshi a wata kala face pink domin kuwa ko phone din da ke hannun ta pink ce,key holder motar ta ma haka,bcs riqe take da makullin mota da alama fita zata yi.

Murmushi ne ya bayyànà a fuskar ta ganin mutanen da ke zauñe a falo, Abba ne zaune shida wani,cike da murna ta qarasa gurin wannan mutumin ta rungumo shi a hankali tare da d'ora mishi peck a kumatu tace"Abbana yanzun kazo"cike da murmushin dattijan taka yace"yanzu nazo mamanah,ya akayi ina zuwa haka?a shagwa6e ta kalle shi tace"Abba gurin ka zanje mana sae gashi kazo,,to yi haquri mamanah,nazo ne domin magana zamuyi dake da yayanki Hakeem zauna ki jira fitowar shi.
Nan ta zame jiki ta zauna qasa ta jingina a jikinsa ta dora kanta a qafafun sa tana tambayar sa ya hanya da mutanen da ya baro, amsa yake bata yayinda yake shafar gashin kanta.

Ba jimawa Hakeem ya shigo sae da ya gaishe su sannan ya nemi guri ya zauna ba tare da ya kalli gefen da Billy ke zaune ba haka ita ma kamar ma bata san da shigowar shi ba.

Abba ya gyara muryar sa zai fara magana wayar shi ta shiga ruri,ya dauki wayar bayan ya gama ne yace da su"ina zuwa"

Nan ya fita ni Billy giro nace to bari na d'an baku taqaitaccen labarin yanda familyn yake.

Alhj Qasim da Alhj Mansur en uwan juna ne na jini domin kuwa ciki d'aya suka fito,asalin su en shuwa Arab ne, Alhj qasim shine Babba sannan Alhj mansur,kowanen su na da wadata domin ba wanda zai nuna ma wani dukiya a cikin su.

Alhj qasim yana da mata d'aya wato Hajiya Aisha suna da d'ansu d'aya wato Hakeem.

Alhj mansur shima matar sa d'aya hjy maryam wacce garin haifuwa ne ta rasu bayan ta haifo santaleliyar 'ya jawur da ita mai kyaun gaske,wacce taci sunan kakar ta wato Bilkeesu shiyasa suke kiran ta da "Mamana"
Ganin mahaifiyar Bilkeesu ta rasu ne yasa Alhj qasim ya d'auki Bilkeesu ya maida ta gidan shi inda Hajiya Aisha ta d'auke ta tamkar er ta, madara Billy ke sha kasancewar Hajiya Aisha bata da ruwan nono bcs ta jima sosai da yaye Hakeem domin a lokacin kusan shekarun sa 7 kuma basu yi tunanin tasha wani magani ba ko zatà sami ruwan nono sbd Bilkeesu tana shan madarar ba wasa .
Duk da Alhj mansur ya sake aure baisa ya dauki er sa Bilkeesu ba.
Gashi Hakeem baya qaunar ganin umman sa riqe da Bilkeesu,kasancewar sa yaro ne mai kishin ganin mahaifiyar sa riqe da wani yaro ba shi ba,
shine fa tun daga lokacin tsanar Bilkeesu yake,ba Bilkeesu ba ma komai indai nata ne to ya tsane shi,idan kuwa yaga Bilkeesu da irin kayan shi ya rabu dashi har abada ba zai qara waiwayar sa ba, wanda hakan tsanar taci gaba da qaruwa har zuwa girman su haka yasa ita ma Bilkeesu ganin tsanar da yake nuna mata taji duk duniya ba wanda ta tsana kamar shi,da duk wani abu nashi.
Akan tsanar da suke yiwa juna har en aiki suka raba,wato kowa da wanda ke masa aiki,
gwaggo ita ce mai aikin Hakeem,Billy kuma wata yarinya ce mai suna Baraka.

Iyayen su basu ta6a tsammanin haka qiyayyar zata ci gaba ba, sun d'auka cewa a iya yarinta zata tsaya,sae gashi har girman su, shiyasa yanzu abin yake matuqar damun su sosai,har dai da suka kasance su kad'ai ne 'ya'ya a gurin su.

Kuma Hakeem ya qara tsanar Bilkeesu ne bcs of kala d'aya wato pink colour da take mutuwar so tun tana yarinya, iyayen kuwa suka biye mata duk abin da zasu saya mata pink colour suke saya mata,tufafin ta pink,takalman ta pink,underwears pink, haka ma dakin ta har zuwa toilet duk da pink akayi mata qawa,to fa akan haka ne Hakeem ya tsani pink colour kasancewar ta choice d'in Bilkeesu, shiyasa ko cikin gari ya shiga ba yason gani wulgawar pink colour ta koina.

Hakeem yayi karatun soja ne a qasar turawa,inda en mata ke son shi sosai sbd kyaun sa bai ta6a kula kowa ba sae mace d'aya,da ake kira Jennifer rayuwa da Jennifer ne yasa Hakeem bai d'auki ta6a jikin mace a komai ba,hug da kiss kuma ya d'auke su tamkar gaisuwa,wanda har akwai wani lokaci da ya dawo daga karatu, Jennifer ta kasa haquri ta biyo shi har Nigeria agaban su Abba, Hakeem yaje ya rungume ta ya mata kiss.

Akwai kuma wani lokaci da Jennifer taje 6angaren Hakeem ta same shi ya fito daga wanka, ga Hakeem mutum ne wanda tun a toilet corner yake goge ruwan jikin sa hakan yasa ba ya fitowa da towel sae dae ya fito hakan nan ba komai a jikin sa.
Nan Jennifer ta qarewa hallitar sa kallo wacce ta rikitar da qwaqwalwar ta,sae gabadaya sha'awar shi ta taso mata, da yake dama ta jima tana sha'awar Hakeem amma bata ta6a samun damar sa ba.
Kallon sa take tayi Hakeem bai san tanayi ba bcs bai ko lura da mutum a d'akin ba sae jin yayi an rungumoshi tana masa wasu irin rikitattun abubuwan da ya kasa fizgar kansa da sauri,sae ga Billy ta shigo d'akin tana qwala ma jennifer kira,nan Hakeem ya ture Jennifer da qarfi ya nemi abu ya rufa jikin sa, Billy kam tuni ta bar dakin yayinda tsanar Hakeem ta qara ruruwa a cikin ranta.

Hakeem kuwa dukan tsiya yayi ma Jennifer ya kuma kore ta daga gidan.
Wannan kenan a 6angaren Hakeem.

A 6angaren Billy kuma
*Billy pinky durling*shine sunan da qawayen Billy ke kira mata a school,kuma wasu kan kira ta da"Billy pinky ko pinky durling,ko pinky wasu kuma Billy suke kiran ta kamar yadda ake kiran ta a gida.
Billy ta kasance yarinya,wacce kwata kwata bata da girman kai shiyasa maza da mata en school d'in su duk shiri suke da ita, har ma suna kai mata ziyara a gida akai akai sae dae maza sunfi zuwa sosai, wanda ko ba kowa a gidan takan kai su main falo ta kawo musu abin motsa baki,su zauna suyi ta fira suna nishad'i,hakan yasa Hakeem ke kiranta er iska domin ganin yake shigar da takeyi da maza a main falo kuma ba kowa a gida, ba komai sukeyi ba face lalata har ganin yake kaf samarin garin sun santa a matsayin "ya mace.

Wannan kenan.

Ci gaban labari.

Sosai Abba ya jima kafin yake dawo wa da alama baqo yayi,
Zaman sa keda wuya ya fara da cewa"Hakeem,mamana ina so ku bani hankalin ku domin kuji abinda zan fad'a da kyau, a gaskiya qiyayar da kuke nunawa junan ku bata mana dad'i ko kad'an har ma mutanen waje na tunanin kodai ku ba en uwan juna ba ne, jin hakan yana qara qona min rai sosai,wanda a kullum addu'a ta ita ce Allah ya nuna min ranar da kuka daina nuna qiyayya wa junan ku,najima sosai ina wannan addu'ar kuma ina ji a jikina Allah zai amshi roqo na.
Hakan yasa muka kira ku domin sanar da ku hukuncin da muka yanke wanda ba mun yanke shi bane don mun kasa haqurin jiran hukun cin unbangiji, munyi haka ne don kawo karshen qiyayyar da ke tsakanin ku.
Chapter 2 · 0% Book details