← Book details Billy Pinky Durlin Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 49

Sashe 13

Billy Pinky Durlin Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Nan ya gama zancen zucin sa ya fice Billy tayi murmushi had'e da girgiza kanta tace"za dai ka gano ne nan gaba.

Bayan ta fito daga wanka ta d'auko Vaseline tana shafawa,Mimi tace"didi kar ki shafa mai kan qafar ki mai ciwo bcs akwai wani magani da naga uncle ya shafa miki kina bacci"
Billy tayi fari da ido tace
_"a ranta amazing yanzu har hakan ta fara faruwa tsakani na da Bobby"_
Sannan tace da Mimi a u sure? Allah kuwa didi, kingan shi ma,
ta bude ledar magungunan da Hakeem ya ajiye a dazu ta dauko mata maganin,
tube ne d'an qarami da shi,ta dubi instruction nashi sau uku ake shafa shi a rana ta matsa maganin ta fara shafawa yayinda fuskar ta ke d'auke da murmushin da ita kadai ta baiwa kanta sani.

Bayan ta gama shiri ne ta bud'e ledar abincin ta,
snacks ne a ciki da gasasshiyar kaza.

Ta tashi da d'an d'ingishin ta taje ta bud'e fridge ta dauko freshmilk tayi sanyi har ta gaji taje ta zauna taci abinci tasha magani.

Bayan kwana biyu da faruwar haka qafar Billy tayi sauqi sosai domin har girki ta ci gaba da dora musu.

Hakeem,Naini,Mimi sune zaune kan dining Billy na zuba musu abincin dare.
Fried rice ce wacce taji spices taji komai yanda ya kamata sae qododi dake yawo cikin ta.

Hakeem ya kalli abincin sau d'aya ya kauda kai"yace wai ke meyasa long time kin daina min favourite food d'ina?da mamaki ta kalle shi domin tasan ko wannan favourite food d'insa ne tace"kamarya?i mean tuwon shinkafa da miyar ganye... oh yes naga baka son ayi maka tuwo da wata shinkafa face er gote kuma dama er goten da kaga ina yi maka tuwo da ita a kwanaki wacce su umma suka ta6a bari ce wani zuwan da mukayi kafin wannan,
kuma ba wani yawa ne da ita ba bcs kasan its just bcs of u ake zowa da ita.
Ajiyar zuciya yayi cike da damuwa Yace olryt.
Nan yaja plate suka fara cin abinci shida Mimi.
Naini kuwa shi kadai yake cin abinsa haka ita ma Billy amma farfesun kaji ne take sha.

Haka rayuwar su taci gaba yayinda yanzu Hakeem komai yaga Billy tayi sae yaga hakan ya bashi sha'awa amma yaqi yarda da abin da zuciyar sa ke son raya masa na cewa he is in love wit her,,, just ya d'auki abun a zaman da suke guri d'aya ne ya kawo hakan.
Sbd yanzu duk inda Hakeem yake,sae Billy tayi qoqarin ganin tana gurin,sbd qarawa plan d'in ta qarfi wanda
ko school Hakeem zai kai Mimi sae Billy tayi ta begging d'in sa cike da shagwa6a kan zata yiwa Mimi rakiya.
Shi kuwa Hakeem shagwa6ar da Billy keyi mishi kesa ko yayi niyar dizgata se ya sami kansa da kasawa hakan yasa yake zuwa da ita wanda har suje su dawo ba mai ce ma wani qala sae idan Billy ce tayi magana.

Kwance yake a falo kan sofa sanye da singlet da three quarter da alama bashi da lafiya domin alamu sun nuna hakan.

Billy ce ta sauko downstairs sanye da riga pink handless wacce tsayin ta bata qarasa kai mata a guiwa ba,
tazo ta zauna qasa kusa da kujerar da Hakeem ke kwance idanun sa a lumshe suke amma Billy na zama ya bude su a hankali,ta sakar mai sexy eyes d'inta tace"zakaci wani abu kafin doctor yazo?um um bana jin yunwa ruwa kawai nake son sha.
Nan ta tashi ta kawo mishi ruwa bai kar6i ruwan ba sae da ya tashi zaune yayinda Billy ta bashi ruwan,sai da yasha sannan ya koma ya kwanta.
Billy ta wani nuna damuwa sosai a fuskar ta tana mishi sannu kamar da gaske.
Kallon ta kawai yayi bai ce da ita komai ba Yace"ki tashi kije daga ciki doctor na kan hanya kuma kinsan bai kamata yazo ya ganki da kayan da ke jikin ki ba"
Ba musu ta miqe yayinda Hakeem ya shiga tsananin mamakin kansa da furta hakan, meye damuwar shi koda a tsirara doctor zai ganta,wata zuciyar tace ka furta haka ne kawai sbd ita musulmace haramun ne wani wanda ba muharramin ta ba ya ganta haka.

Billy kuwa cike da sh'umin murmushi ta shiga d'aki sbd ta fahimci yanda Hakeem ya shiga mamakin kansa sosai.

Zuge zip din rigarta tayi ta cire rigar ya zamo daga ita sae pant ta jawo towel ta daura sbd wanka take so tayi amma bata shiga wankan ba ta tsaya gyaran d'aki.

A 6angaren Hakeem kuwa Billy na tashi sae ga doctor.
Sai da suka d'an gaisa
yace da Hakeem me kake jin yana maka ciwo a jikin ka? Kawai ka duba ni doctor bcs bansan ainihin abinda ke damuna ba.
Nan ya shiga dube duben shi a jikin Hakeem inda yake mishi wasu tambayoyi yana bashi amsa.
Bayan dube duben shi da jin amsoshin Hakeem,
sae yayi shiru kamar mai mamaki har yana d'an jinjina kan sa,
can dai ya dafi kafad'ar Hakeem ya fara magana cike da natsuwa yace"Hakeem ba wani abu ne ke damunka ba face tsantsar sh'awa!

da mamaki Hakeem yace as how doctor? I mean kana buqatar kasancewa da mace!

Hakeem ya qara jin
zancen wani iri yayi murmushin yaqe yace"doctor bancin matar da nake da,
sae na nemo wata macen? Hakeem kenan kar ka manta kana tare da doctor ne,domin a binciken da nayi na fahimci sha'awar da ke dauke da kai ba alamar ka kusanci mace nan kusa ma'ana ka jima sosai baka kusanci matar ka ba!

kan Hakeem ne ya kunce domin shi a iya sanin sa bai ta6a jin yana buqatar mace ba, bare shi da ke tare da Billy ta ya zai sakawa kansa buqatar mace bcs Billy fanko ce ba abin sha'awa bace,kawai dai yasan idan ya shaqi qamshin turaren ta yakan ji wani yanayi a jikin sa har dai idan tana kusa da shi, haka idan tana mishi shagwa6a ji yake kamar ya rungomo ta yana lallashin ta...doctor ya katse shi da cewa Hakeem ya kamata ka ajiye wata qiyayya da girman kai,ka kar6i abinda kake buqata a gurin matar ka,idan ba haka ba sha'awar nan zata kai ga illata ka..... Pls doctor ka daina wannan zance bcs even yesterday night I slept with my wife ta ya zaka ce wani sha'awa ce ke damuna!

D'an guntun
murmushi doctor yayi yace a ransa.
_nayi boko kayi boko baza mu nuna wa junan mu wani abu ba,but zan nuna ma nafika yawan shekaru na kuma nuna ma ba abu d'aya muka karanta ba_

Yace "shikenan kayi haquri da nayi ma rashin fahimta amma ina zuwa,
nan ya tashi ya fita bai wani jima sosai ba ya dawo,
yace da Hakeem ga wannan magani kasha,
magani ne wanda idan an kasa gane ainihin matsalar mutum idan ya sha shi inshaAllah zai ji sauqi,
Ba musu Hakeem ya kar6i tablet d'in yasha.
Yayi minti d'aya da shan maganin,
yace doctor maganin nan jiri yake sawa ne?
sorry ba jimawa zaka daina jin haka but idan ba damuwa ko zaka kira min pinky nayi mata en wasu tambayoyi a game da ciwon ka?

Da qyar Hakeem ya iya ce mishi ba damuwa" sbd wani yanayi da ya fara jin kanshi,
nan ya tashi ya tafi sae tangad'i yake kamar wani mashayin da yasha ya fara buguwa a haka har ya shiga d'akin Billy.

Doctor ya girgiza kansa yace a ransa"lallai Hakeem da pinky duk da had'a ku auren da aka yi bai sa kun haqura kun shirya kanku ba,
amma ba komai na kusa kawo qarahen abun,domin wannan maganin da kasha ba zai ta6a baka damar fitowa a dakin pinky ba har sae ka kusance ta!
Yana gama fad'ar haka ya fita daga gidan.

Hakeem kuwa yana shiga d'akin Billy....

*Billy giro😊*
👛👛👛👛👛👛👛👛👛👛
[9/22, 6:47 PM] ‪+234 810 038 8117‬: [ 8/15/2016] Billy giro😊:
*👛BILLY PINKY DURLING👛*

*Na*

*Billy giro😊*

*page*
*👛33&34👛*
Hannun ta ya ajiye a hankali hade da fitar da ajiyar zuciya, ya d'an kauda kansa gefe ya kuma sake kallon Billy wacce har yanzu idon ta yana kanshi.
Idanun ta ne suka ciko tap da qwallah sbd rad'ad'in bala'in da take ji a qasan ta, ta shiga kallon yananyin d'akin cike da mamaki yayinda hawaye ke qoqarin gangarowa kan kumatun ta,cike da damuwa Hakeem ya d'an matsa kusa da ita tare da riqo hannun ta kamar mai son cewa wani abu.
Billy kuwa cikin muryar kuka tace"Bobby me yake faruwa da ni ne?
Shiru Hakeem yayi ya rasa me zai ce da ita, domin ko kad'an baya son tasan dalilin faruwar hakan.
Hannun ta da yake riqe da shi ya ke faman murzawa a hankali cike da tunanin me zai ce mata.

Sautin kukanta ne ya dawo dashi,
yayi saurin kallon ta hade da girgiza mata kai alamar ta daina kuka.
Cike da shagwa6a ta fizge hannunta da yake faman murza tace"to ni ka sanar dani me ya faru dani har ka kawo ni asibiti?
cikin muryar lallashi abinda bai ta6a yi mata ba yace"shi kenan kukan ya isa haka kiyi shiru idan kina son na sanar da ke kinji, nan ta share hawayen ta kamar wata er baby tace"to fad'amin ina jinka, um um ni bazan gaya miki ba sae kinci abinci tukun, yayi maganar ne tamkar da qaramar yarinya yake magana kuma yana sane yayi hakan just bcs ya samu ya lalla6a ta.
Bata ce da shi komai ba har ya tashi ya fita daga d'akin.
Chapter 13 · 0% Book details