Sashe 23
Billy Pinky Durlin Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Suna cikin cin abincin ne Abba sae kallon Hakeem yake wanda bakin sa yaqi rufuwa duk ya qagu su kammala cin abincin ya sanar da su albishir d'in da yake d'auke da shi.
Abban Hakeem yace"wai Hakeem
wannan wane irin albishir ne da kake son sanar da mu, naga tun kuna Abuja ka kira ni ka sanar dani akwai albishir,kuma naga da alama ka qagu ka fada, eh wlh Abba amma dai nafi son mu kammala cin abincin tukun....gaban Billy ne ya bada ras _me Hakeem ke shirin sanar da su da yake farin ciki haka shine har da gaya musu kafin ya iso,koma mene ne ya kamata na riga shi,_
Nan ta ajiye farfesun kifin da take ci sbd ta daina jin dad'in abincin gabad'aya har wani d'aci take ji a cikin bakin ta kamar wacce tayi zazza6i .
Abban Hakeem yace mamanah ya akayi kar dai kice kin qoshi?eh na qoshi....oh wai ke har yanzu kina nan da rashin cin abinci"
umma ce ta fad'i hakan.
Billy dai bata ce komai ba sae qoqarin tashi take domin ta matsu ta bar gurin.
nan ta wuce Hakeem sae kallon ta yake yana murmushi yayinda Feenah ke kallon shi sae duk taji soyayyar su ta fara bata sha'awa domin ta fahimci akwai so a tare da su.
Billy na shiga d'aki cikin sauri ta nemo takarda da biro hannun ta na rawa take rubutu yayinda hawaye ke ta faman zarya a fuskar ta d'agowar da zata yi taga mutum tsaye a kanta har sae da taji faduwar gaba
da sauri ta share hawayen da ke kan fukar ta tace"haba Feenah ya zaki shigo min daki ba sallama ni har kin tsorata ni wlh ... Hmmm lallai pinky me kike shirin yi ne haka naga kin wani rubutu saki kuma har uku...ba ruwan ki! ido ne kawai naki idan baza ki iya ba sae kisa kai, kuma wlh duk kika sanar da su Abba ni na rubuta shi kin san sauran... Meye sauran? Oho miki amma wlh se kinyi nadamar sanar da su da zakayi.
Tana gama fad'a ta nad'e takardar zata fita Feenah ta jayo ta tace"pinky ya kamata ki tsaya kiyi tunani kafin ki aikata komai domin zakiyi babbar nadama idan kikayi hakan,meye matsalar ki da Hakeem bayan kallo d'aya za a yi muku a san kuna son juna.... Hm baki san komai ba Feenah don haka ki barni kawai nan tasa kai zata fice Feenah ta fizgo ta da qarfi tace"pinky kar kiyi haka fa!cikin tsawa tace"Feenah!wai so kike sae ya riga ni aiwatarwa kafin ni!da Allah sake ni na wuce!
nan ta fizge hannun ta wanda yayi dai dai da shigowar umma tace"meye haka pinky me yake faruwa? Pinky tayi saurin 6oye takardar hannun ta tace"it's just about banci abinci ba take takura ni"to ya isa kizo Abbanku yana kira,
nan umma taja ta aka bar Feenah tace"tabbas pinky idan kikayi kuskuren bada takardar nan sae na nuna miki kuskuren ki domin zan aure Hakeem kina ji kina gani dama abinda najima ina nema ne.
Billy kuwa tafiya suke kan staircase gaban ta sae dukan uku2 yake zuciyar ta nata hana ta.
suna isa falo pinky ta sami guri ta zauña Abban Hakeem ya kalle ta yace"mamàna da alama kema akwai magana fal a bakin ki?eh Abba,,,to bari muji abinda yasa Hakeem ya tara mu a nan sannan kema ki fad'i taki ko,nan ta kalli Abba cike da damuwa,Hakeem ya lura da hakan yace"Abba ta fad'a muna jin ta,a'a kafa riga ta"Abban Billy ne yayi maganar,
Hakeem yace"ba komai ta fad'a kawai Abba, yayi maganar ne yayinda yake kallon Billy cike da murmushi yace"talk pinky kinji muna sauraren ki,kalloñ sa take sosai tace a ranta
_"kamar alamu sun nuna da gaske Hakeem ke sona har dai da na kalli qwayar idon shi but zan aiwatar da plan d'in naga bcs idan gaske ne yana sona to kuwa tabbas zai qaryata ni_
Da qyar ta samu ta sai sai ta kanta ta fara magana cikin natsuwa tace"Abba dama ba komai bane face abinda ya zama dole na sanar da ku, wanda nasan zakuyi baqin ciki da jin sa sae dai nace kuyi haquri domin nima ban so hakan ta faru ba,don ba yanda zan yi ne kawai.
Ba mu jima da zuwa new delhi ba, naso ace Hakeem ya bani dama mu kasance tamkar yadda kuke so ma'ana mu ajiye qiyayyar da muke yiwa junan mu, amma sae bai bani damar hakan ba ya nuna sam ba hakan a ransa kuma baya buqatar hakan, a nan ne yake sanar dani cewa na ma ajiye wannan zancen domin tun ranar da aka d'aura auren mu ya rubuta ya ajiye ni ba matar sa bace sam ba aure tsakani na da shi,da farko na d'auka ya fad'a ne kawài se na basar da zancen inda nake ta qoqarin ganin mun dai daita tsakanin mu amma yana zille min.
To da haka ne wata rana ina gyara mishi d'aki ,
a cikin drawers din sa ina tsara mishi wasu takardu se na had'u da wannan takardar wacce ta nuna min tabbas ba aure tsakani na da Hakeem wato da gaske yake tun ranar da aka d'aura auren mu ya raba wannan auren domin har date ya saka........ Innalillahi wa inna ilaihi raji'un! Abba ne ya fad'i zancen yayinda ya zare hular kanshi yana kallon takardar wacce ke rubuce da saki d'ai d'ai har uku.
Hakeem kuwa zumbur ya miqe cikin tsananin mamaki hannun sa na rawa ya kar6i takardar da ke hannun Abba yaga sak rubutun shi ne, kallon Billy ya shiga yi wacce ta tashi tsaye tana kallon shi sae fatar take ya qaryata zancen ta, shi kuma mamaki ya cika shi inda ya fahimci kenan dalilin da yasa pinky ta yaudare shi tasa ya koya mata rubutun shi,kenan soyayyar da take nuna mishi bada gaske bane,
_no!no!no pinky!_
Yayi maganar ne a cikin ranshi yayinda yake kallon pinky idanun sa sunyi jajir duk jijiyoyin kansa sun tashi,kansa ne yayi mugun sara mishi yayinda rayuwar shi da pinky ta new delhi keyi mishi yawo cikin kai,
nan ya dafe kansa yana ja baya yana magana a ranshi cewa _"if yes i can't life any more with out u pinky!d only thing i will just go n kill my self!i will kill my self ryt now!_
nan ya fita gidan kamar wani mahaukaci su Abba suka bishi suna kiran shi, pinky kuwa kuka ke qoqarin zo mata ta tafi da sauri zata haura sama gabadaya idon ta ya rufe bata ganin komai tafiya kawai take kan staircase wanda har ta kai matakalar qarshe sae kawai jiri ya debe ta ta zube, nan ta shiga gangarowa kan staircase.
Hakeem kuwa yana fita ya fad'a mota ya fige ta a haukace inda ya buge gate d'in gidan da qarfin tsiya ya fita.
Umma wacce bata riga ta fita ba tayi saurin zuwa gun Billy tana taslima duk hankalin ta ya tashi domin koda ta gama gangarowa ta some goshin ta sae fitar da jini yake.
Feenah ce ta fito da gudu jin yanda umma ke qwala mata kira.
Hakeem kuwa a bar zancen kawai domin yana fita ba ruwan sa da komai da ke kan hanya duk inda ya samu kad'a motar sa yake nan ya had'u da katuwar mota tayi cilli da motar shi wacce sae da tayi juyi uku kafin take tsayi.
A rikice su Abba dake biye dashi cikin mota suka tsaida motar su suka fito.
Tuni gurin ya cika da mutane akayi gaggawar fitar da Hakeem cikin mota ,nan aka tafi dashi *Hakeem Specialist hospital*
wanda koda suka je Amjad yana kan Billy wacce su umma suka kai hakan yasa wani likitan ya kar6i Hakeem.
Nan aka had'u su umma da Abba kowanen su cikin damuwa.
d'aki d'aya aka aje Billy da Hakeem d'aki ne na mutum biyu kacal sae dai kowanen su bacci yake.
Su Abba na zaune a d'akin ba mai cewa komai sae jiran farfad'owar su ake,kuma Alhmdlh ba wani jin ciwo Hakeem yayi ba.
Har akayi sallar zuhur ba wanda ya farfad'o a cikin su,nan su Abba suka tashi zasu je masallaci ita ma umma tace bari taje gida ta had'o musu abinci kafin su farfado,nan suka fita ya zamo Feenah kad'ai aka bari cikin d'akin.
Tana nan zaune ta fara ganin Hakeem na motsi cikin sauri taje ta kira doctor koda suka shigo Hakeem sae faman dannar kansa yake da ke mishi ciwo nan ya duba shi jiki sanyaye ya kalli Feenah wacce ya zaci er uwar hakeem ce yace"ki same ni office akwai wani abu da zan gaya miki a game da Hakeem.
Ba musu ta bishi ta samu guri ta zauna, nan ya cire gilashin da ke idon sa tare da furzadda iskan bakin shi yace"am sorry to say sae dai kuyi haquri da tsarin ubangiji domin a binciken da nayi kafin Hakeem ya farfado na same shi da matsala guda biyu da ya samu a sanadiyar buguwa, amma ban fad'a ba sbd ina so na qara tantancewa idan ya farfado,koda ya farfado naga haka d'in ne a bisa wasu tambayoyi da na masa.
Matsalar farko ita ce Hakeem ya manta komai wanda ya faru wata biyu da suka wuce ma'ana duk abinda ya faru a wata biyu da suka wuce bazai tuna su ba.
Cike da damuwa Feenah ke kallon shi inda ta shiga wani lissafi cikin qwaqwalwar ta, tace doctor don Allah ina so kar ka sanar da kowa wannan matsalar,sbd zaka d'aga hankalin iyayen mu don Allah doctor,,,gsky wannan matsala ba abin 6oye wa bace dole a sanar da iyayenku ko yanzu don ina sauri zan fita yasa nace kizo na sanar da ke amma mahaifin ku ne ya dace nayi wa wannan bayanin ba ke ba..but doctor na fi so na musu bayanin da kaina Allah bana so hankalin su ya tashi, tayi maganar ne cikin marairaiwa,yace to shike nan nayi miki alqawari bazan sanar da kowa ba, nan ta mishi godiya ta fita cike da jin dad'i a ranta kan ta sami wata damar da ta barwa kanta sani.