← Book details Billy Pinky Durlin Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 49

Sashe 19

Billy Pinky Durlin Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yana kawo nan police suka jashi, Da gudu Billy ke binsu cikin kuka sae kuma ta tsaya cak"inda ta
shiga magana a cikin ranta
_"meyasa zan damu da yawa haka bayan ba son Bobby ko d'as a cikin zuciya ta da har zanji tausayin shi,kuma hakan da yayi tamkar ya samar min wata dama ce da zan ku6uta da auren sa har abada....._
No ba haka naso ya faru da kai ba Bobby ko don hallacin da kamin a yanzu,,ni dai kawai fatana na rabu da qaddararren auren ka shi kawai nake buqata a rayuwa ba mutuwar ka ba.
Tayi maganar ne a fili kuma cikin kuka kafin take durqushewa gurin tana ci gaba da kuka tana kallon su Bobby da sukayi nisa har suka 6ace mata shima kallon ta yake.
Mimi ce tazo ta fada jikin ta ita ma kukan take sosai.
Cike da tausayi doctor yazo yana lallashin su,tace doctor don Allah ka fitar da Bobby wlh Allah bana so ya mutu.
Doctor bai ce da ita komai ba,domin ya shiga mamakin zancenta da yaji yanzu ace duk hallacin nan da Bobby yayi mata tana kan bakar ta na ganin auren su ya rabu,nan dai ya basar da zancen ya ci gaba da lallashin su.

Wanda da qyar ya samu ya lallashe ta ya maida su gida.

Haka suka kwana cikin kuka,
Mimi ce kadai ta samu bacci ya d'auke ta Billy kuwa tunda suka dawo take faman kiran number umma da Abba amma ta kowannen su taqi shiga.
Tashi tayi ta d'oro arwala,tayi ta nafilfili tana roqon Allah kan ya taimake ta yayi gaggawar fitar da Hakeem.
Daga qarshe ta hade kai da guiwa tana ta rusar kuka inda ta sami kanta da jin wannan hallaci da Hakeem yayi mata,da ace Allah zai ku6utar da shi da kuwa tayi rayuwar zaman aure da shi har abada duk da kuwa ko kadan bata jin son Hakeem a cikin ranta.

Washe gari tunda safe taji door bell da sauri ta fito har tana had'awa da gudu ta bud'e qofar tare da fad'in "Bobby".
Tana ganin doctor ne kuka kawai ta fashe da shi,cikin dasasshiyar muryar ta da tasha kuka tace"doctor tun jiya bana samun wayar su Abba don Allah ka fitar da Bobby,nasan zasu baka shi tunda ba d'an qasar su ya kashe ba, pinky ko ba d'an qasar su ya kashe ba zasu hukunta shi a bisa kisan kai da yayi cikin qasar su kafin suke miqa shi ga hukumar qasar mu.... Haba doctor don Allah ka taimaka mana, nidai ko yaya ne ka fitar da shi please doctor,
ta fadi haka ne yayinda ta durqusa kan guiwoyin ta tana kuka mai ban tausayi.
Da sauri doctor ya bar gurin yaje cikin motar sa ya zauna hade da jinginawa cike da damuwa,yace "sae dai kiyi haquri pinky domin ba yanzu ne ya dace na bayyana cewa Naini yana raye ba,bare har na fito dà Hakeem har sae na fahimci ra'ayin ki ya canza gabad'aya kema kin fara son Hakeem kamar yadda ya fara sonki.

𦰊 D'agowar da zai yi ne ya hango pinky ta jikin mirror ta wuce cikin sauri nan ya fahimci tabbas pinky taji zancen sa, idan kuwa haka ne ta 6ata mai tsari.

Cikin rashin jin dadi ya fito mota ya shiga cikin gidan rai 6ace Billy ta kalle shi taja hannun mimi suka haura sama,tana tunanin lallai doctor nan ya akayi har yasan ba da gaske take son Hakeem ba.

Shi kuma doctor ba yanda ya iya domin ya fahimci ta ji sak me yace.
Nan ya fita bai dawo ba sae tare da Hakeem,wanda tun cikin mota yake tambayar doctor ya akayi ne.
Bai ce da shi komai ba sae tunanin abinda zai ce da shi yake bcs baya son yasan tun farko Naini bai mutu ba,sbd shi kad'ai yake tsarin shi na ganin ya daidaita tsakanin su kafin su koma Nigeria.

Sae da suka fito cikin mota sannan yace"ina taya ka murna sosai Hakeem bcs doguwar suma ce Naini yayi yau da safe ya farfado wanda hakan yasa nayi matuqar farin ciki marar misaltuwa.
Cike da tsananin murna Hakeem ke kallon doctor yace to ai doctor gurin shi ya kama ta ka fara kaini tukun, a'a gabadayan ku nake son muje don haka kaje ka fito da su pinky.

Duk maganar nan da suke pinky na hango su ta jikin window sae duk ta d'auka da hadin bakin Hakeem ciki,inda ta shiga tunanin kenan Hakeem ba soyayyar gaskiya yake mata ba ko hallacin da yayi mata don kawai ta so shi ne yayi, wato kenan shine ya gano plan d'inta ya sanar da doctor shine suke son plan d'in ya koma kanta,to me ya kamata nayi yanzu?
Tana cikin haka ne taji alamar zai shigo da sauri ta haura sama ta shiga d'aki.

Cike da murna Hakeem ya shiga d'akin ta ya same ta ruf da ciki kamar mai bacci"yace bacci kike pinky ki tashi gani na dawo bcs naini is alive, shiru tayi tana sauraren shi da mamaki wato doctor bai fahimci taji ba kenan lallai zata nuna bata ji ba,in yaso taci gaba da bin su har taga iya gudun ruwan su.

Tashi tayi tana kallon Hakeem cike da murna tace"da gaske Bobby da gaske Naini yana raye!?cike da murmushi ya gyad'a mata kai yace "ashe ba mutuwa yayi ba doguwar suma ce.... ihu ta saki ta qanqame shi sae kuma ta fashe da kuka tace"inace basu ma komai ba ko?ba abinda suka min,nan ta share hawayen ta yace ina Mimi? wanka take,kefa kinyi wanka domin yanzu asibiti xa muje gurin Naini, Bobby ta ya zan ji qarfin wanka bayan kana cikin wani hali,olryt ba gani na dawo ba ai sae kije kiyi wanka yanzu, maqale kafada tayi tare da qara mannewa a qirjin sa tace"ni sae na gama ganin ka tukun,cike da jin dadi yake kallon ta sae ga Mimi ta fito daga wanka, yace"kinga Mimi ta fito je kiyi wanka nima zanje nayi amma kiyi sauri domin doctor yana jiran mu fa.
Nan ta tashi ta fad'a toilet shi kuma ya fita.
Mimi cike da murna take shiri domin kafin Hakeem ya fita ya sanar da ita komai.

Tsaye yake jikin mirror ya fito daga wanka har ya saka tufafi yana sanya buttons d'in rigar shi sae ga Billy ta shigo cikin shiri,
taje a hankali ta rungumo shi ta baya inda suke hango juna ta jikin mirror, a hankali ya sauke ajiyar zuciya domin qamshin turaren Billy da ya shiga hancin sa tace"nayi ma wayo na riga ka fitowa har na shirya kai sae yanzu kake shiri,,uhm ai don ba kya kwalliya ne kika riga ni,,au to kai kana yin kwalliyar ne? eh mana baki ga kullum se kyau nake qarawa kamar mace,murmushi tayi yayinda take qarewa fuskar shi kallo ta jikin mirror tace"haka ne fa amma ba wata kwalliya a fuskar ka,kuma fuskar ka ba kyau sae muni kamar tawa,
saurin kallon ta yayi ya girgiza kansa kawai domin shidai yanzu baya ganin munin ta ta koina da ne kawai. yace"ke muni ne dake?eh mana ji hanci na kamar zai ta6o bakina, ga d'an qaramin baki kamar wacce aka emma, idanu kamar wata mai jin bacci,yace"kenan baki gode Allah ba, ya fadi haka ne yayinda ya juyo yana kallon ta,tace"a'a wlh na gode Allah fiye ma da yanda kake tunani,to meyasa kika ce haka? Sbd kawai naji dad'in bakina amma da wasa nake.

Nan yaja hannun ta suka zauna kan bed yace"ina so naji shin me ya had'a ki da Naini har hakan ta faru"shiru tayi tana kallon shi kafin take sanar da shi yanda abin ya faru.
Kansa ne ya d'aure sosai yace"pinky ko dai akwai wani abu tsakanin ki da naini kike 6oye min?a'a wlh,to Ko kun sami sa6ani ne? ko d'aya, ok zo muje nama ji kamar Mimi na kiran ki.
Nan suka fita suka tarar da doctor cikin mota.

Tafiya suke yayinda doctor ke hango Billy ta jikin mirror ta wani narke a jikin Hakeem sae labari suke bawa junan su suna dariya,hakan yasa ya d'anyi mamaki yaushe hakan ta fara faruwa tsakanin Bobby da Billy domin duk a tunanin sa ko kusa da Hakeem bata zama bare zancen had'a jiki,nan ya kawad da zancen sbd sun iso asibiti.

Koda suka shiga sun sami Naini idanuwan sa a lumshe sallamar su ne yasa shi bude ido inda ya sauke su kan Billy wacce ke riqe da hannun Mimi.

Doctor ne ya taimaka mishi ya tashi zaune wanda har yanzu idon shi na kan pinky kafin yake kallon Hakeem yace"am sorry to say Bobby and u pinky i am really sorry, i dnt mean to hurt u, ni kaina ban san meyasa nayi yunqurin aikata abinda nayi niyya ba kawai dai na tsinci kaina da tashi aikata hakan sbd son da nake miki.... saurin kallon shi tayi yace"of course ina sonki pinky ina sonki sosai, tun muna yara bani da burin kasancewa da kowa face ke, ban ta6a tunanin zan rasaki ba pinky, shiyasa ban furta soyayya ta a gare ki ba,
wanda nayi hakan ne har sae idan mun kammala school nida ke ko zan sanar da ke sae gashi kai tsaye naji auren ki wanda ya ritikita min tunani gabad'aya amma idan na tuna wanda aka had'a ki aure da shi sae naji kamar nan kusa zan same ki matsayin mata sbd sanin cewa ba kwa son junan ku ko kad'an,
sae dai zaman da nayi daku ya fahimtar dani wani abu wanda na fara cire ran zan same ki a matsayin mata, shine zuciya ta tayi ta ingiza ni kan na d'auke ki naje dake can inda zamuyi rayuwar mu mu kad'ai gurin da ba wani d'a namji da zai kalle ki bare har naji zafi a raina,amma kiyi haquri da kuskuren da nayi sharrin so ne da kuma sharrin shaid'an.
Chapter 19 · 0% Book details