← Book details Billy Pinky Durlin Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 49

Sashe 47

Billy Pinky Durlin Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*👛83&84👛*
Ya akayi kika san hakan? umma na tambaya meyasa qirjin na keta cikowa haka ko qiba ce, tace min cikin da nake d'auke da shine, but Bobby yanzu kana nufin baka ta6a fahimtar cewa qirjina ya ciko ba sae yau? Ni ma abinda ya d'aure min kai kenan da ban fahimta ba sae a yau,,, well ba mamaki sbd yawan tafiye tafiye bai barka ba, haka ne kuma.
Daga haka sukayi shiru Hakeem ya katse shirun da cewa "pls Billyta d'an samar min sweet na sa a baki na bcs bana jin dad'in bakin nawa, kamar nawa za'a d'auko? qwara d'aya kawai,
Nan ta tashi ta d'auko mishi ta yaye ledar sweet d'in ta saka mishi a baki.
sha yake yayinda yake kwance kan cinyoyin ta qamshin sweet sae bugun hancin ta yake,
a shagwa6e ta kalle shi tace "Bobby en min sweet d'inka,, je ki d'auko mana, maqale kafad'a tayi sbd kasalar tashi take ji hakan yasa ta kai bakin ta a hankali kan nashi tana qoqarin saka harshen ta a ciki, cikin hanzari Hakeem ya hana faruwar hakan ta kalle shi da mamaki tace "Bobby lafiya? Am sorry Billyta ta ya zaki had'a baki na da naki bayan bana da lafiya ba a kuma san ainihin abinda ke damuna ba if ciwon yana transferring ta through slaver fa,
ranta ne yayi mugun 6aci ita har akwai wani ciwo da komai muninsa ace zata guji Hakeem,
tace"ka kyauta Bobby u mean nima idan ina d'auke da ciwo zaka guji yin wani abu dani don kawai kar ka kwashi ciwon, saurin rufe mata baki yayi bcs ji yayi kamar tayi sa6o yace"pinky shin har kina tunanin akwai wani abu a duniyar nan da zai sa na guje miki..... Eh mana gashi ka nuna min, tayi maganar ne yayinda ta kai hannu kan fuskar ta izuwa kuka, cikin rarrashi Hakeem ya riqo hannun yace "I dn mean to hurt u pls kar kiyi kuka dan Allah" Billy kam sae da ta zubo en hawayen ta sbd sunzo gab,
Yace "Billyta pls kar ki min asarar wasu hawaye ya isa haka kinji, gyd'a mishi kai tayi yace" yauwa to zo na share miki hawayen, ba musu ta fad'a kan qirjin shi ta wani lafe kamar wacce zata sha mamma shi kuma ya shiga share mata hawaye yana fad'in "I'm really sorry banyi haka ba sae don gudun kar ke da Babyn mu ku sami ciwon mu zo mu duka uku ba lafiya, bugo qirjin sa tayi a shagwa6e tace" nifa ka daina zancen nan kawai ka ba ni sweet d'in nasha koma mene ne mu d'auka d'in ba komai, ba musu ya ciro sweet d'in bakin sa ya saka mata murmushi tayi tare da d'ora mishi kiss tace"yi haquri bari na d'auko maka wani, girgiza kanshi yayi yace"Billyta kenan wai dama ba qiwuyar tashi kike ji bane? Eh but wa kaina nake ji ma qiwuya amma in don kaine ba komai ko misira ne zanje"
ta fad'i haka ne yayinda ta d'auko sweet ta 6are leda ta saka mishi a baki wanda yayi dai dai da jin knocking, zuwa tayi ta bud'e qofa ta sami Baraka a tsaye, Baraka tace "gashi wayar nan da kika jefar tun d'azu sae faman kira ake" Billy ta kar6i waya ta rufe qofa kan tayi receiving wayar ta tsinke taje ta zauna Hakeem ya kar6i wayar yana dubawa yace "wayar waye? wai wata qawar feenah ce taxo jiya tana so zata je event d'in da ake yi shine ta manta wayar,, ok yauwa ungo an sake kira,
nan Billy ta kar6i wayar inda taga Anti Halima na yawo kan sikirin d'aga wayar tayi kafin tace komai" Halima ta fara cewa amma ke ba er iska irin ki kin san baza ki iya aikin ba shine kika sa na baki,
gashi kinsan boka yace a wannan ranar ake so Billy tasha wannan magani idan ranar ta wuce ko tasha yaron cikin ta ba zai mutu ba domint maganin ba zai yi aiki ba bare har buri na ya cika na ganin na lalata auren seema gashi kin shantaqe tun jiya ba ke ba labarin ki bare naji bayani, kuma sae faman kiran ki nake ba kya d'aga waya lafiya me yake faruwa ne!ina ce dai kinyi nasarar saka wannan garin maganin a fresh milk?
mtsw ya kimin shiru kimin magana mana!
Billy kam saurin rufe bakin ta tayi sbd kukan da ke qoqarin kufce mata sae kallon cikin ta take kafin take kallon Hakeem da ke qoqarin yi mata magana Yace"Billyta... Saurin rufe mai baki tayi ta d'ora mishi wayar a kunne, inda Halima sae fad'a take tana cewa "ke ni kimin magana nasan sak kina ji na gara ma ki daina wani pretending so nake kawai naji idan kin kasa aikin ki gaya min yau na koma gurin boka na sami wata mafitar kar lokaci ya qure min!..... nan Hakeem ya kashe wayar ya kalli Billy wacce ta fara fitar da sautin kuka,
ya rungume ta ya na lallashi yace "bangane me yake faruwa ba but kamar nasan voice d'in matar nan wace ce ita?
cikin kuka tace" Anti Halima ce qawar mama wai......ta qarasa gaya mishi duk abinda taji a waya inda hankalin Hakeem ya tashi sosai ya shiga tambayar ta idan jiya bata sha fresh milk d'in ba bayan tafiyar sa toilet tace"um um ban sha ba"ajiyar zuciya ya sauke yayinda wayar baquwa ta shiga ruri, rai 6ace ya d'auki wayar har yana niyar cika ta da masifa sae kuma ya fasa ya canza amon muryar shi tare da "fad'in kiyi haquri mai wayar bacci take ta d'aga wayar ne a bisa rashin sani
but me za a ce mata idan ta farka..... kai waye? ni boy friend d'in ta ne.... Mtsw kaji matsalar wato baqar jarabar ta ce ta motsa shine har ta kasa zowa ta min bayani to idan ta farka ka gaya mata ta same ni a gida not family house gida na da nake zama ni kad'ai, to shike nan yanzun nan zan tashe ta kuwa na sanar da ita.....da yafi domin idan naga ta jima zan iya zuwa na same ku koma a wane hotel ne!
nan ta katse wayar ya kalli Billy yace " hurry up! shirya muje wlh yau kashin ta ya bushe sae naga bayan ta kafin maganin nan ya qarasa illata ni, Billy kam duk ta rud'e ta kasa yin komai sae Hakeem ne ya shirya ta ya dauki bindiga suka kama hanyar zuwa gidan Halima inda suka kira umma da Hajiya seema da kuma Abban Billy da na Hakeem a cewar su same su a can akwai magana.

Ba qaramin tashin hankali Halima ta shiga ba da jin abinda ya kawo su hakeem amma haka ta dake kan cewa ba ita ce yayi waya da ita ba yaje can ya nemi koma wace ce kar ya tayar mata hayaniya a gida, cikin tsananin 6acin rai Hakeem ya d'ora mata bindiga a goshi yace sae tayi bayanin abinda take shirin aiwatar wa ko kuma ya harbe ta yanzu! ai kuwa nan jikin ta ya d'auki rawa duk ta rud'e tana mishi bayani bayan ta gama yace "Alhmdlh Allah ya kare Billyta domin ni nasha maganin ba ita ba don haka kafin na mutu sae na kashe ki tukun.......don Allah kar ka kashe ni wlh ba maganin mutuwa bane yaron ciki kawai yake kashewa kuma banyi hakan ba sae don na raba auren seema amma don Allah kuyi haquri nan ta shiga basu haquri har tana qoqarin kama qafafun Billy ,
Nan Hakeem ya shiga shuri da ita yana "fad'in wa zaki roqa gafara da kike tunanin zai yafe miki"
Haka ya bita sae buga mata kan bindiga yake a ka inda nan take kan ta ya fashe sae jini yake fitarwa,bai damu da ganin jinin ba sae dukan ta yake ci gaba da yi domin har ga Allah kashe ta yake da niyar yi sbd zuciya ta riga ta kawo masa iya wuya.
Billy sai kallon ikon Allah take domin bata ta6a ganin Hakeem ya hasala irin yau ba duk tabi ta tsorace tana gudun kar yayi kisa hakan yasa taje ta riqe bindigar inda a zuciye Hakeem ya kar6e bindigar wanda by mistake ya harba bindigar ta sami ginar d'akin, yayinda Billy ta saki wani irin razanannen ihu ta qanqame Hakeem kamar wacce zata shige cikin jikin shi sae kuka take a tsorace duk jikin ta ya d'auki rawa gabad'aya.

Su Abba ne suka shigo suna tambayar lafiya me yake faruwa haka da har muke jin qarar bindiga kafin mu shigo? Wani mugun kallo Hakeem ya yi wa Halima yace "ai sae ki musu bayanin muguntar da kika tashi aiwatarwa la'ananniyar mata kawai!
ba musu ta shiga yi musu bayanin komai har tana roqon su gafara inda gabad'ayan su suka yi tir da abinda suka ji, yayinda Hakeem yake ta faman rarrashin Billy ,a kafaice yakai hannu kan cikin ta sbd wani irin juyi da yaji babyn nayi nan yaji baya da wata natsuwa sae sunje asibiti sbd motsin ya wuce yanda Babyn ke motsawa ko yaushe hakan yasa ya kira police a gaggauce suka zo suka tafi da Halima domin a bata azabar da ko kare baza qara tunanin illatawa ba.

Gabad'ayan su suka dunguma zuwa asibiti
aka duba ta ba wata matsala inda Amjad ya sanar da su razanace kawai,,,
Nan suka kama hanyar komawa gida cike da tu'ajjabi da kuma jin dadin nasarar Billy bata sha fresh milk d'in ba.

Har suka isa gida jikin Billy qyarma yake.

Fitowa sukayi cikin mota yayinda Hakeem yake riqe da hannun Billy,
ya d'auko bindiga zai shiga da ita cikin gida ,
Billy tayi saurin shigewa jikin shi kan bata son bindigar ta ta6a ta hakan yasa ko moving Hakeem ya kasa yi sbd yanda ta shige jikin shi yace"is ok Billyta bindigar baza ta ta6a ki ba kinga na ma mayarda ita a cikin mota " nan ya samu ta sassauta riqon da ta mishi suka shiga cikin gida.
Chapter 47 · 0% Book details