← Book details Billy Pinky Durlin Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 49

Sashe 10

Billy Pinky Durlin Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

2 days latter .
zaune take kan bed daure da towel tana waya.
Hakeem ne ya shigo dakin ba ko sallama tayi saurin gyara daurin towel dinta sbd yanda ta daura shi da farko ana ganin rabin mamman ta.
Fuskar ta daure ta kalle shi bcs bata son ana shigo mata daki kai tsaye bai damu da yanayin fuskar ta ba yace"kije na fitar da kayan datti ki wanke ki goge.
Ya fita ba tare da ya jira amsar ta ba haka ita ma bata bashi amsa ba sae ma wayar ta da taci gaba dayi.

Bayan ta gama ta saka tufafi ta dauki waya ta nemo numbar gate man ta kira shi domin yazo ya wanke mata kayan in yaso ta biya shi.
Domin bata jin zata iya duk da kuwa suna da washing machine.

Bai jima ba yazo ta miqa mishi kayan dattin tace yayi sauri ya wanke ya goge kafin Hakeem ya dawo.

*Billy gir[truncated by WhatsApp]
[9/22, 6:38 PM] ‪+234 810 038 8117‬: [ 8/8/2016] Billy giro😊:
*```👛BILLY PINKY DURLING```*👛

*```Na Billy giro😊```*

*```Page```*
*```👛20&21👛```*
Gate man ya wuce ita kuma ta koma ta kwanta a nan falo daga nan sae bacci.

Tana cikin bacci ne gate man ya kawo mata kayan har ya kammala,ta kar6i kayan ta bashi kud'i ya qi kar6a!tayi tayi yaqi kar6a,
bata yi mamaki ba sbd tasan sabon da sukayi ne yasa yaqi kar6ar kud'in bcs duk xuwan da suke dasu umma shine gate man d'in su.
Nan taje daki ta dauko wata had'addiyar sarqar indiyawa sabuwa dal wacce da gani zata yi tsada ta hado mishi da set din en hannu ta kawo mishi tace"ya kar6i ko wannan ya kai ma matar sa, ba musu kuwa ya kar6i kayan yana ta godiya cikin harshen turanci kamar yadda ita ma take masa magana a harshen turanci.

Da ya wuce ta wuce kitchen ta duba store duk kayan abinci sun qare indomie kawai ta rage.
Tsaki kawai tayi taje tayi kwanciyar ta domin bata jin zata iya fita ta siyo, ta maga kayan sun jima basu qare ba bcs ta siyo su ne a iya sati biyu,domin ta zaci two weeks zasuyi su koma sae taga har yanzu basu koma ba,inda ta rasa dalilin da yasa Hakeem ya wani zauna a garin kamar wani ma'akacin garin.

Daga haka ta koma bacci abinta.

Hakeem ne ya shigo riqe da hannun wata yarinya er 6 yrs,da gudu yarinyar taje kan jikin Billy tana fadin"didi"
Hakan yasa Billy ta farka tana ganin yarinyar ta sake mata murmushi tace"mimi keda waye? nuna mata Hakeem tayi dake qoqarin haurawa upstairs,sannan tace"da kuma yaya Naini ya tsaya a boys quarters zai saka kayan sa,ni kuma ga nawa a bakin qofa.
Billy da bata san makari ba ta kalli mimi a rashin fahimta tace"tare da ku zamu koma Nigeria?no didi zamu dai zauna a nan ne har su Abba su dawo... Ina suka je, cewar Billy wacce tayi maganar ne yayinda wani d'an saurayi ya shigo ta sakar mai murmushi tace"su Naini manya ba a ganin ku duk da muna gari d'aya, ba haka bane pinky kinsan karatu muke kuma lokacin exam ya matso ko yanzu karatun ne yaja mana baza a je da mu Nigeria ba...lah su Abba Nigeria sukayi? sosai kuwa....cike da shagwa6a tace"oh no ina ma za'a je dani,wlh Allah na matsu naje naga umma,,,
sosai shagwa6ar Billy ta bawa Naini shawa har ya jima yana kallon ta,
haka shima Hakeem dake saukowa ya kalle ta sau daya ya kauda kai tare da komawa upstairs.

Billy tace"zasu jima sosai kenan naga har akwati mimi tazo dashi kaima kuma ka shigar da kayan ka a boys quarters?eh to baza su jima a Nigeria ba daga can sae su wuce umrah, domin tun a last month suka so suje se wani aiki ya tsaida Abba,wanda shine ya kawo muku tsaiko kan komawar ku nigeria da wuri,
bcs baku jima da zowa ba Hakeem yaje gida yaji Abba na magana kan yana son suyi tafiya kuma baya son su bar mu,
mu kad'ai a gida nida Mimi to anan Hakeem yace da Abba ba matsala zaku jira har su Abba suje su dawo in yaso mu kuma mu dawo gurin ku da zama.
kenan can ne Hakeem ke zuwa kullum domin naga kamar kusan kullum sae ya fita?eh gaskiya kullum yakan je sbd wani aiki da yake taya Abba,, ok inace dai umma bata ga laifin rashin zuwa na ba?eh to bata ga laifin ki ba, sbd cewa tayi wai ke amarya ce baki isa fitowa ba...uhm umma kenan, Allah na dai ji kunya bcs tun zuwan mu fa sau daya na kira ta a waya,ta fadi haka ne yayinda ta haura sama naini kuwa ya bi ta da ido cike da so.

Zan muku d'an taqaitaccen bayani game da Mimi da Naini.

Wato sun kasance 'ya'yan aminin Abban Hakeem,asalin su en kaduna ne,suna zama new Delhi ne sbd nan mahaifin su ke aiki,suna jimawa sosai kafin su je Nigeria sbd karatun su da kuma aikin mahaifinsu wato Babban likita na fannin zuciya.
Naini abokin wasan Billy ne sosai,amma shi ba abokiyar wasa kadai ya dauki Billy ba,soyayya mai tsanani yake mata, sae gashi kwatsam yaji tayi aure duk da yaji hakan bai daina jin sonta ba.
ita kuwa Billy bata ma san yanayi ba,domin har yanzu a matsayin abokin wasa take daukar shi.

Wannan kenan.

Tana haurawa sama ta nufi dakin Hakeem tare da danna door bell sae da ya jima sannan ya bud'e,
tabi ta gefen sa ta shiga tare da rufe dakin,
Hakeem sae kallon ikon Allah yake kai tsaye ta shigo mai daki har da wani rufewa,
ta fahimci hakan amma ta basar tace"ba wani abu bane dama ba kayan abinci gashi anyi baqi,,,to me yasa da kika ga ba kayan abinci bakije kin siyo ba? koda naga hakan lokaci ya qure,indomie kadai tayi saura kuma kasan Naini baya cin indomie....sae kisan yanda zakiyi da shi,
ni kije ki hado min indomie nida Mimi,bafa komai a gidan nan da zan bashi kamata yayi kaje ka siyo kayan abinci....wani banzan kallo ya mata yace nayi miki kama da d'an aike....oops sorry zanje d'in da kaina but kudin hannu na sun kusa qare min,bai ce mata komai ba yaje ya zaro kudi ya jefo mata, nan ta duqa ta dauka, tana dagowa suka had'a ido inda ta dawo mishi Billyn da,
wato shaye da toka tana masa kallon kafa raina ni da yawa, a nan take kuma ta dawo Billyn yanzu tace"to yanzu zan dafa ma indomie kafin na tafi ko? Da a tunanin ki zaki bar gidan nan baki dafa min ba!...... Mtsw! ya buga tsakin ne yayinda Billy ta fita daga d'akin yace"oh God! meyasa su Abba suka had'a ni da ke,
bayan baki dace da rayuwa cikin mutane ba face cikin dabbobi domin kullum daqiqancin ki sea abinda ya qaru!

Sak Billy taji abinda ya fada sbd bata riga ta rufe qofar ba tace a ranta
_"ni da kai za a ga wanda zai qare a daqiqi marar fahimta fatana kawai Allah ya kaimu lokacin da plan dina zai gama had'uwa_
nan ta qarasa rufe qofar ta wuce.

Taje ta had'a mishi indomie shida Mimi.

Naini kuma ta kai masa abin motsa baki kafin su sayo kayan abinci a dafa mishi.

Bayan sun gama ne Billy taja Mimi da Naini suka je shopping inda suka bar Hakeem shi kadai a gida ya fito balcony yana karatun jarida.

Sun jima sosai kafin su dawo.
Suna isowa ta fada wanka tayi shirin shiga kitchen.

White rice ta had'a da stew wacce taji naman kaji,koda ta kammala anyi magrib.

Sae da akayi isha'i sannan suka zauna ma cin abincin,
Billy ce ta zuba musu abinci wanda kallo d'aya Hakeem ya masa yaji ransa yayi mugun 6aci,ta gefen ido Billy ke kallon shi inda take dariyar mugunta cikin ranta sbd tasan ya tsani white rice da stew, wanda tayi hakan ne da gayya sbd qin zuwan da yayi na siyo kayan abinci.
Komai ya kasa cewa ya tashi ya bar gurin.
Nan naini ya shiga tambayar lafiya?Billy tace"no kar ka damu may be lalura ce ta kama shi,,"ok" cewar naini daga nan yaci gaba da cin abincin sa.

Bayan sun gama cin abinci sun huta,Naini yaje 6angaren sa domin ya watsa ruwa haka Billy da mimi suka tashi domin zuwa shirin kwanciya.

Hakeem kuwa yana shiga d'aki ya dauki makullin mota ya fita.

Koda ya dawo ya sami Billy da Naini kowannen su da shirin bacci, ya kalli tufafin da ke jikin Billy riga ce handless iya guiwa sae ihu take cike da murna sbd wata game din tserar mota da suke ita da naini,
Nainin da sam hankalin sa baya kan game sae Billy yake kallo wacce keyin komai cike da sha'awa.

Nan Hakeem yaje ya kashe TV Billy tayi saurin kallon shi yace"ki tashi ki koma daki kin bar Mimi ita kadai,
tashi tsaye tayi hade da bubbuga qafafun ta a qasa cike da shagwa6a tace"uhm uhm oh Bobby why!? ya zaka zo ka kashe mana tv bayan kaga yanda hankalin mu ya karkata a can, indai akan Mimi ne fa bacci ma take,but please Bobby kaga yanzu 9:30 tayi idan 10:00 tayi Allah zan koma daga ciki please Bobby kar kace a'a.

Hakeem kam shiru yayi yana kallon yanda take zuba mai shagwa6a tamkar umma ce a gabanta har da wani buga qafa a qasa.
Kauda idon sa yayi cike da ganin yarintar Billy ya kalli Naini wanda ya mato gun kallon Billy har ma wani murmushi ke bayyana a fuskar shi.
Nan ma ya kauda idon shi ya kalli Billy wacce har yanzu begging dinsa take.
Cikin kakkausar murya ya daka mata tsawa yace"ki wuce daga ciki bana son ganin ki a nan!
Tap idanun ta suka cika da qwallah domin ba qaramin takura ta Hakeem yayi ba, wanda duk shagwa6ar nan da ta masa tayi ne don ta samu ya barta ta qarasa game d'in ba wai don plan d'inta ba bcs at all 6acin rai ya mantar da ita kan plan d'in da take had'awa bare har ta fahimci wani abu a ga me da Bobby kan abun da ya mata yanzu.
Chapter 10 · 0% Book details