← Book details Billy Pinky Durlin Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 49

Sashe 32

Billy Pinky Durlin Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Ya jima a zaune bcs har 11 tayi nan yaji qarar bud'e qofa sannu sannu.
D'aga kanshi yayi ya hango pinky ce ta fito cikin shiri mai kyau English waers riga da skirt wad'an da basu nuna tsiraici kuma sukayi matuqar d'aukar ta.

Tana had'a ido dashi tayi saurin duqar da kanta cikin jin kunya ta kuma yi tsaye har sae da yazo ya d'auke ta,sae kallon ta yake cike da so long time har sae da taji kunya ta 6oye fuskar ta a qirjin sa domin ba abinda take tunawa kamar abinda ya faru tsakanin su a daren jiya.

Shidai Hakeem murmushi kawai yayi sannan ya sauka da ita downstairs suka zauna kan seater,ya kalle ta da kulawa yace"Billyta hope da sauqi gurin ya daina miki zafi sosai ko?shiru kawai tayi ta riqo hannuñ shi tana wasa da yatsun sa,can ta d'ago ta kalle shi kamar wacce ke son yin kuka.

*Billy giro😊*
👛👛👛👛👛👛👛👛👛👛
[9/22, 8:08 PM] ‪+234 810 038 8117‬: [7:45AM, 8/31/2016]

*👛BILLY PINKY DURLING👛*

*Na Billy giro😊*

*Page*

*👛61👛*
Tace"Bobby wai har yanzu su Feenah basu shigo bane? Pinky ke nake jira sae kin tashi daga bacci tukun ko zan bud'e 6angaren,amma yanzu tunda kin tashi bari naje na bud'e,,,
Bobby zan bika,,,ok muje,,, ya fad'i haka ne tare da riqo hannun ta suka fita.
Suna isa qofa suka ji knocking koda Hakeem ya bud'e Baraka ce mai aikin pinky riqe da basket na abinci sae da ta gaida su sannan tace"umma tace a kawo wanda tun d'azu aka kammala break fast d'in sae aka sami 6angaren ku a rufe kuma tayi kiran number ka a kashe,,, mtsw haka ne fa na manta da wayar na a kashe since yesterday but yanzu je ki jera mana abincin kan dining.

Suna dawowa Hakeem yaje ya d'auko wayar shi ya kira umma da suka gaisa take cewa"wane irin bacci ne kuke tayi haka Hakeem, bayan kasan mafi yawa har dai abokanan ka yau suke son komawa kuma ya kamata su kanga kafin su tafi amma kaje ka shantaqe kana ta bacci,,, umma yi haquri Allah tun d'azu na tashi but na manta cewa ban kunna waya ta ba,,,to shi kenan yanzu kuyi ku gama break fast abokanan Billy da mutanen Maiduguri suna son shigowa kafin su fice,,, ok umma nan ya ajiye wayar, ya jawo pinky suka fara break fast.

Basu jima da kammalawa ba mutanen Maiduguri suka shigo tare da su Feenah,shi kuma Hakeem ya tafi old 6angaren shi inda ya bawa abokanan shi masauki ya samu tuni umma tasa an kai musu break fast sunci.

Billy cike da fara'a ta gaisa da en uwansu na maidugiri tana wasa da en qananan 'ya'yansu.

Sun jima suna fira a falon yayinda Billy tasa Baraka ta kawo musu abubuwan motsa baki.

Feenah taja Billy suka je d'aki tace
"ke wannan tafiyar fa sumui sumui kamar wacce bata son motsa jiki,,,da wasa ta dalla wa Feenah harara tace"dama ya nake tafiya? a hankali kike tafiya amma hankalin tafiyar yau yayi yawa,,, au shi hankali har yawa yake?eh gashi na gani a gunki yau... kingan ki Feenah Allah sa idon ki yayi yawa but zan miki ubanshi ne idan kika yi aure, gwara ma ni na jure har ina game cinyoyi na ina tafiya,ke nasan a yanda kike son jiki sae dae na same ki a kwance ba kya ma iya motsin kirki...cab ai wlh kin fini son jiki...naji nidai meyasa kika taso ni ina zaman zama na ko don kawai kiga tafiya ta ne?a'a wlh kayan jikin ki zaki canza kin wani sanya mana English wears sae kace ba Amarya ba,,, oh oh Feenah ta kura ni kawai kike so kiyi, wlh ni ban cika son sa hausawan kayan nan ba fa kin sani nauyi suke min...kar ki damu akwai wani material da na gani mai bala'in kyau a cikin akwatinan lefen ki Allah baya da nauyi ko kad'an gashi ya sami d'inki mai kyau ba wani rigima a d'inkin,nan Feenah ta d'auko kayan.

Ba a son rai Billy ta saka kayan ba amma tayi matuqar kyau fiye da kayan da ta cire.
Feenah tayi tsaye tana qare mata kallo tace"wlh Allah kinyi kyau sosai har dai d'aurin d'ankwalin nan har mamaki ki ban wai kece kika d'aura shi bayan ba kya saka iren iren kayan nan,,, ah ah kaji ki don bana saka kayan sae na kasa sarrafa kaina yanda naso ko kuma da nike ganin kuna d'aurawa fa....oh sorry na manta cewa ke gifted ce kallo d'aya zaki yiwa abu ki riqe bare ma kin sha ganin munayi,,,,
dalla mata harara tayi tace "Feenah bana son zolaya fa".... Hmm ba wani ai kin san gaskiya na fad'a....mtsw kinga zo muje don Allah kin san na bar mutane a falo kuma sunce suna so zamuyi photo kafin su tafi,,,nan suka fita.

Da zuhur mutanen maiduguri suka wuce,su Feenah da sauran abokanan Billy kuwa suka shiga kiciniyar had'awa abokan Hakeem abinci sbd sun fasa komawa sae gobe da safe.

Da dare kowa ya watse Hakeem yaje 6angaren su umma ya tafi d'akin umma yana fad'in wai umma ina pinky ta shiga ne tun lokacin da mukayi break fast ban sake sata a idona ba sae qawayen ta nake ta gani suna zirga zirga kuma yanzu kowa ya watse bata 6angaren mu,,,,,Ayyah ai Billy tunda en Maiduguri suka wuce wani irin zazza6i ya taso mata tun sannan tana kwance sae idan anyi sallah take tashi tayi,,,cike da damuwa ya kai duban shi gun Billy wacce sai yanzu ya ganta qundundune cikin blanket sae rawar d'ari take,,,ta6a jikin ta yayi yaji yayi mugun zafi shiru yayi cike da damuwa komai ya kasa cewa sae zama yayi tare da yaye hular kanshi had'e da yin guntun tsaki,,, umma tace"lafiya? umma inaga tun ciwon kai da zazza6in da ta fara a Germany ne yake bin ta har yanzu,sbd taqi bari ayi mata allura bare zazzabin ya tafi gabad'aya,,,,,ai yau da kukan ta da komai nasa aka mata allura kuma na tasa ta gaba taci abinci tasha magunguna shine ta d'an samu bacci ya d'auke ta amma kuma sae rawar d'ari take,,, to umma ko zan bar ta nan ne taci gaba da baccin ta har safe?a kan me ka dai tashe ta ku tafi 6angaren ku,,, ko kad'an bai so hakan ba sbd baya son ya tashe ta daga bacci kuma yana jin kunyar daukar ta a gaban umma,haka ya tashe ta ba a son ransa ba yaja hannun ta suka wuce.

Tana shiga d'aki ta cire skirt d'in jikinta sannan ta zuge zip d'in rigarta bata iya cire rigar ba ta fad'a ruf da ciki kan bed sbd taji tsayuwa na son gagarar ta shiyasa ma ta kasa jiran Hakeem da ya tsaya rufe musu 6angaren su,,,,Hakeem ne ya shigo bai zarce koina ba sai gurin ta ya zauna ita ma ya zaunar da ita tare da jingina ta a jikin sa yana qarasa cire mata rigar,ya zamo inner wears ne a jikin ta,a hankali yakai hannun sa kan ma6allar bz bai cire mata ba sae da ya d'auko towel,,,yace"muje na miki wanka bata iya ce mishi komai ba sae towel ta kar6a ta kare qirjin ta tare da qara lafewa a jikin sa,shafo gefen fuskar ta yayi cike da damuwa yace"pinky wai kodai zafin abun ne ya sa ki zazza6i? murya qasa qasa tace"um um its headache kuma allurar da aka min har yanzu gurin na min zafi,,ta qarasa maganar cikin muryar kuka yayinda take share hawaye tace"kuma sae da nace ma umma bana son allura amma tasa aka min,,, yi haquri ya isa daina kuka kinji, bari na murza miki gun,nan ya kai hannun sa a bayan ta yana murxa mata gurin da aka mata allura sannu sannu,
tun tana fad'in wash wash tana riqe mishi hannu har ta daina tayi shiru daga haka tayi bacci.
A hankali Hakeem ya d'ago fuskarta yana kallo yaga alamar baccin na mata dad'i,ganin ta fara zufa kuma zafin jikin ya fara sauka.

Ya kwantar da ita ya samo qaramin towel da ruwa yana daddanna mata fuskar ta har zuwa qirjinta wanda hakan yasa ta sauke ajiyar zuciya a hankali,bai barta haka ba sae da ya nemo riga ya saka mata suka shiga bacci.

Da safe guraren 8 Hakeem ne ya fito daga wanka riqe da d'an qaramin towel yana goge ruwan jikin sa,Billy ya samu tana shafa jikin teddy a hankali yace"Billyta har kin tashi? d'ago idon ta tayi, tayi saurin rufe su sbd komai babu a jikin sa,hakan yasa ya koma toilet corner ya d'auro towel ya dawo,damuwa ce fal ta bayyana a fuskar shi sbd fuskar ta ya shafo yaji zafin jikin ba sauqi,riqo hannun shi tayi ta bud'e idon ta a hankali tana kallon shi.

*Billy giro😊*
👛👛👛👛👛👛👛👛👛👛👛
[9/22, 8:15 PM] ‪+234 810 038 8117‬: [3/9/2016]

*👛BILLY PINKY DURLING 👛*

*Na Billy giro😊*

*page*
Chapter 32 · 0% Book details