Sashe 4
Billy Pinky Durlin Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Feenah ta lumshe ido hade da sauke ajiyar zuciya tace a ranta
_"ina ma ce nice za'a had'a aure na da Bobby yanda nake mutuwar son sa, oh Allah!meyasa ka bawa Billy wannan dama wacce kwata kwata bata da buqatar hakan"_
A hankali ta bude idon ta ta dafa Billy tace"wlh pinky kinyi babbar sa'a zaki zamo matar Bobby.... Ba shiri billy ta buge hannun ta taja baya kamar wacce taga abin tsoro ta nuna Feenah da yatsa yayinda mamaki qarara ya bayyana a fuskar ta tace"Feenah ashe dama ba kya sona ban sani ba sae yau!
Idan haka ne pinky me kike son cewa da su Abba da ke qoqarin hada auren ku? Feenah su Abba sun yi haka ne sbd kiyayyar da muke yiwa juna nida Bobby tana matuqar damun su,shiyasa suke son hada auren mu domin kamar ganin suke hakan zai sa mu daina nuna wa junan mu qiyayya,, amma ke cewa fa kika yi wai nayi babbar sa'a zan zamo matar Bobby, haba Feenah! kina magana kamar wacce bata san abinda take yi ba.....nasan abinda nake yi pinky, Bobby baya da matsala ta koina matsalar sa d'aya ita ce qiyayyar da yake nuna miki......U have gone mad! Feenah ko ba qiyayya me zanyi da wannan gardin mai qirar samudawa! kece ke ganin haka pinky, amma Hakeem kyakkyawa ne giant man wanda duk mace mai aji ta kalle shi sau d'aya zata so ya kasance mijinta, Bobby sam baya kama da samudawa shi dai kawai cikakken namiji ne wanda ya had'u ta koina baya da makusa...... Feenah!! Wlh idan har maganar bobby zaki tamin fitar min daga d'aki!
Feenah tayi shiru tana kallon Billy da ta fita hayyacin ta a lokaci d'aya,
Sae ta sami kanta da qara jin ina ma ace ita ce zata auri Hakeem.
*```°°°°°```*
Hakeem kuwa yana tashi ya nufi 6angaren sa ya hadu da Amjad yana qoqarin kiran sa a waya.
Bai cema Amjad komai ba ya shige daki.
Amjad ya bishi, yayi tsaye yana kallon Hakeem da yayi baqiqirin da rai"Yace haba Bobby sae ka ce nine na dora ma pink lips.....mtsw Amjad ba ma wannan ba, baka san matsalar da ke faruwa ba, wai ace ni su Abba zasu hada aure da wannan dabbar,
kalar en yunwa wacce ko iskan qwarai ya busa zata iya karye wa, gata da fuska kamar ta aljannu..... Thank God!wlh naji dadi da Allah ya kar6i roqo na!domin na jima ina roqon Allah yasa su Abba su muku haka inga qarshen qiyayya......kukan kura Hakeem yayi ya cakumi kwalar Amjad ya nuna shi da yatsa yayinda idanuwan sa sukayi jajir jijiyoyin kansa duk suka tashi, yace"wato kai ne ka roqi Allah! to bari kaji wlh addu'ar ka bata kar6u ba idan ma har tunani kake ka daina, domin idan har dani za'a d'aura auren to za'a gani!nan ya iza Amjad waje ya kulle qofar dakin da qarfi ya kuma saka key, amjad ya tashi da murmushi ya kakka6e jikin sa ya tafi yana mai mamakin wannan qiyayyah tasu Hakeem wai kuma en uwan juna ne.
*```Billy giro😊```[truncated by WhatsApp]
[9/22, 5:52 PM] +234 810 038 8117: [7/31/2016]
*```👛BILLY PINKY DURLING```*👛
*```Na```*
*```Billy giro😊```*
*```Page```*
*```👛8-9👛```*
Da yamma Abban Billy ne da Abban Hakeem da kuma Billy zaune a main parlor suna jiran fitowar Hakeem.
Abban Hakeem yace wai shi Hakeem ajiye mu yayi da zai bar mu muna zaman jiran shi.
Abban Billy yace da billy"me yace da ke da kika je kiran shi? nifa Abba nayi ta knocking yaqi ya bud'e ni kuma nazo abu na"amma shine kika bar mu muna ta faman jiran shi,wata qil ma baya nan,kira mana shi a waya muji,,Abba nifa banda number shi,girgiza kanshi yayi yana mai kallon ta kafin yake bata numbar Hakeem ya kuma ce sae tayi saving kafin take kiran shi, *village man* shine abinda tasa ma numbar sannan tayi dialling.
Hakeem da ke d'akin shi yana kankanta komai na dakin kamàr su frames da pictures duk ya tattara su ya saka a wardrobe haka shoes da duk wani abu da yake buqa ta ya zuba su ya rufe wardrobe sbd shi a bakin rai yake baza a daura auren da shi ba, da zarar yaje new Delhi sae wanda ya ganshi domin daga can zai cira wata qasa.
Yana cikin haka ne wayar shi ta shiga ruri har ya dauki wayar sae kuma ya jefar kan bed sbd baya receiving call d'in new number,wayar na gab da tsinkewa ya danyi guntun tsaki hade da daga wayar ba tare da yace komai ba.
Billy kuwa Hakeem na d'aga wayar,
murya ciki ciki tace kazo Abba na kiran ka, daga haka ta kashe wayar bata jira jin shin yaji ko bai ji ba.
Ba 6ata lokaci kuwa sae ga Hakeem.
Ya gaida su Abba ya nemi guri nesa da Billy ya zauna.
Abban Hakeem ne ya shiga magana inda yake cewa"kafin nace komai idan na fadi abinda ya tara mu anan,Hakeem da mamana bana son jin komai daga bakin ku har sae na baku damar hakan.
Zancen dai daya ne kan auren ku wanda mun gama yanke hukunci gobe da qarfe goma sha daya na safe za a d'aura aure!
Sunji zancen tamkar dirar mikiya,
sae dae dole sukayi shiru,domin bin umarnin,sae dae kallo daya zakayi musu kasan ba qaramin tension suka shiga ba.
Sosai Hakeem yaso yayi magana amma Abba bai bashi dama ba.
Abba ya fitar da invitations masu yawa dake hade guri daya cikin envelope ya bawa Hakeem yace"sae ka fara gayyatar abokan ka kafin gobe,,Hakeem ya kauda kansa domin ko invitations din baya son gani yace "don Allah Abba ina da magana,
idan kasan ta zancen auren ku ce kar ma kayi domin ba abinda zamu canza!
Ba ita bace Abba,
yau nake so na fara hanya zuwa new Delhi,,, ana zancen auren ku kake zancen new Delhi da ba komai zai kai ka ba in banda hutu,, asibiti zanje Abba shine nake son na isa abuja a yau domin na bi jirgin safe, wane irin ciwo ne kake dauke da shi da baza ka jira har a daura aure ba?
shiru yayi domin idan ya fad'a a shirme Abba zai dauki abin ba kuma zai barshi yaje ba,can yace"Abba ina da matsala a jiki na ne wacce bana so nayi sati d'auke da ita,,,Hakeem wannan ba uzuri bane da zaka ce baza ka jira a daura aure da kai ba, asali ban ga alamar wani ciwo a tare da kai ba da har zai kai ka new Delhi!
Don haka ban baka umarnin kaje ko ina ba!
Can yayi shiru yana tunani irin nasu na manya yayinda ya tsure Hakeem da kallo yace"sae dae kuma kasancewar ban san me ke damunka ba wanda baka so ka fad'a, zan barka kaje amma har sai an d'aura aure, amma kasani tare zakaje da mamana!wani irin abu Hakeem yaji yayinda ya dago yana kallon Billy cike da takaici haka ita ma take masa mugun kallo,suna cikin kallon juna suka shiga magana da zukatan su,kamar haka:
Hakeem yace
_"akanki bazan ta6a bijirewa mahaifina ba tabbas zan bi umarnin sa amma sae kinyi babbar nadamar bi na a new Delhi domin abin da zan miki zai sa ki gudu da qafafun ki kuma ko kinzo gida zan miki qazafin da idan su Abba suka ji baza su ta6a yarda su maida auren mu ba_
Billy tace"
_Tabbas cike nake da baqinci na kasancewa matar ka,sae kuma na hadu da wani baqin ciki wato na biyar ka zuwa new Delhi amma zan jure domin na fahimci wata dama ce ta same ni wacce zan nemi hanyar ku6uta daga aurenka,ku6uta ta har abada, domin zaman da zanyi da kai a new Delhi qalilan ne,na gudo tare da maka sharrin da idan su Abba sukaji baza su ta6a fatar na sake zama matar ka ba har abada!_
*```Billy giro ``[truncated by WhatsApp]
[9/22, 5:58 PM] +234 810 038 8117: [8/1/2016]
*👛BILLY PINKY DURLING👛*
*Na*
*Billy giro😊*
*Page*
*👛10-11👛*
Nan Abba yace"kuna iya Ku tashi ku fice.
Amma mamana ki jira kad'an yanzu naki invitations na kan hanya ki samu ki rabawa abokanan ki kafin safe.
Nan Hakeem ya fice bai damu da daukar invitations din da Abba ya bashi ba.
Billy kuwa ta d'ago kanta ta kalli Abbanta da shima ita yake kallo.
Yace "zo mamana"
cike da son tayi kuka ta tashi taje,ya kalli yanda hawaye ke qoqarin fitowa a idanun ta, yace"mamanah yanzu ashe ba muyi matsayin da zamu yanke hukunci akan ku kuyi haquri da shi ba sae kunyi ta sa damuwa a ranku,hawaye ne suka zubo mata yayinda take kallon Abbanta, ta kwanta kan jikin sa tare da fadin"kayi haquri ba haka bane amma Abba hukuncin da kuka yanke ne yayi tsauri.
Abba bai ce mata komai ba sae lallashin ta da ya shiga yi.
Sosai Abban Billy ya shiga damuwa yayinda yake ci gaba da lallashin ta sbd ko kadan baya son ganin ta cikin damuwa, amma kuma dole tayi haquri da hukunci su domin sun gaji da qiyayyar da suke yiwa juna ita da Hakeem.
Washe gari tun da safe umma ce ta shiga d'akin Billy da sallama ta same ta kwance duk tunanin duniya ya dame ta.
Tace"Billy tashi kiyi wanka ki shirya ki sami abinda kika ci, sbd yanzu nan Abbanku ya gama waya da mutanen Maiduguri suna gab da isowa (cewa da familyn su dake zama a garin maiduguri)
kuma kar ki saka qananin kayan da kike sawa iya cinya,ki sami doguwar riga ki saka.
Tana gama fadar haka ta fita,kafin take cewa kiyi sauri fa.
Nan Billy ta tashi da qyar ta fad'a toilet, ta jima sosai kafin take fitowa sbd haka take jimawa gurin wanka kamar wacce ke shirin canza fata.
Koda ta fito ta sami umma ta shigo dauke da wata leda, ta bude ledar duk turarukka ne a ciki masu qamshi domin kafin ta bude ledar ma kamshi har ya cika daki.
Umma tace "kinga har sun iso ga turarukkan da na bada saqo da kuma wadan da suka zo miki da su, sae ki fara aiki da su tun yanzu.