Sashe 9
Bakar Shuka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
" Kai dawa?
Cike da kunya kanshi k'asa yace " dama na dawo ne ayi auren sai mu koma tare, " wai kai da wa?
D'an shiru yayi yana sosa k'eyarshi, " wai da wa?
Abbi ya fad'a yana kallanshi, cikin in ina yace " Dee....ya...nah yana k'ara duk'ar da kanshi k'asa, " Deeyanah?
"To kun dai-daita kanku ne koyaya?
"Eh! Abbi, mun gama magana, da so muke a d'aura auren yau, sai mu tafi gobe ko jibi, " kasan me kake cewa kuwa Deen?
"An fad'a maka maganar aure maganar yanzu-yanza ce?
" Ko an fad'a maka ana yiwa aure gaggawa?
" Sabo.....! shigowar Deeyanah yasa Abbi yin shiru, da kallo duk suka bita, ko ince kallan tuhuma dan kallo d'aya zakayi mata ka fuskanci taci kuka,
ga jikinta dake rawa hakan yasa suka fahimci akwai wani abu a k'asa kuma akwai rashin gaskiya a tattare da ita,
yadda kowa ke jifanta da kallan tuhuma yasa tayi saurin kallan Deen tsoronta na bayyana a saman fuskarta tsammaninta ko Deen ya fad'a musu abinda ya faru tsakaninta da Ajlaal,
a d'arare ta raba kusa da Deen ta zauna had'i da b'oyewa a bayanshi, " hakan da kikayi kina ganin ya fiye miki?
Abbi ya fad'a yana samun tabbacin akwai abinda ke faruwa, kuka ta saka tana fad'in " dan Allah Abbi kuyi hak'uri wallahi sharrin shaid'a.....,
saurin d'ora hannunshi yayi saman nata tare zare mata ido yana girgiza mata kai, alamar bai fad'a musu abinda take tunani ba,
ajiyar zuciya ta sauke da k'arfi, duk abinda ya faru akan idon iyayensu, Babah ya kalli Abbi da iyayensu wato kakaninsu Deen,
kowa yasan akwai wani abu, akwai abinda ya faru, musamman da Deeyanah tace " sharrin shaid'an ne, Abbi zayyi magana suka jiyo kamar hayaniya a harabar gidan,
da sauri duk suka mik'e suka fita, a harabar gidan suka iske ana kokowa haik'an da Ajlaal da ma'aikatan gidan, wani irin mugun tsoro da rikici ne suka shigeta sauran kad'an fitsari ya kwace mata,
" lafiya?
Babah ya buk'ata yana bin Ajlaal da kallo, gashi dai tsaf bashi da wata alama ta hauka ko motsuwar kai, " k'aramin me gida ne yace karmu bari kowa ya shigo muddin ba d'an family bane,
da wannan abokin Deeyanah yazo na hanashi shine yasa mun k'arfi ya shigo, ina k'ok'arin rik'eshi, yana kwacewa zai shiga cikin gidan,
a fili Abbi yace " abokin Deeyanah kuma?
Idon Ajlaal na sauka akan Deeyanah yayiyo kanta gadan-gadan zai rungume ta, fitsarin datake iyakar k'ok'arin wajen ta matse shi ya kwace mata saboda rud'ewa da tashin hankali,
yana gaf da isa gareta Deen ya shiga tsakiyarsu, kallan kallo suka fara yi a tsakaninsu kafin Ajlaal ya cukumi wuyan rigar Deen, cikin matsanancin zafin zuciya Abbi ya kifawa Ajlaal lafiyayyan mari, ya d'ora da fad'in,
" kana da hankali kuwa?
"Kazo har cikin gidanmu zaka rungume 'ya ta akan idona saboda fitsara, da rashin tarbiyya, rikitaccen kuka Ajlaal ya saka had'i da durk'usawa gaban Abbi yana fad'in,
" nayi kuskure, dan Allah kuyi min hak'uri, karku rabani da ita, itace rayuwata, itace farin ciki na da duniyata,
dan girman Allah karku rabani da ita please yayi maganar yana rik'e k'afafuwan Abbi, " wallahi aurenta nake san yi, nayi muku alk'awarin zan bata duk wani farin cikin dake cikin duniya,
" fice daga gidan nan, cewar Abbi a hasale yana nuna mishi get, ko motsawa Ajlaal bayyi ba, ya had'e hannuwanshi yana rok'onsu kan su taimaka karsu rabashi da Deeyanah,
ihunnn da Deeyanah ta saka ya jawo hankalin sauran mutanen gidan mata duk suka fito, wani irin mugun duka Babah keyi mata da iya k'arfinshi,
take duk ilahirin jikinshi ya d'auki kerrrrma idanuwanshi suka rufe ruf baya ganin komai sai duhu, a haukace Ajlaal yayi kan Babah ya rik'e kwalarshi ya d'aga hannu zai nausheshi, jini nabin bakinta ta d'aga murya da k'arfi tace " Baba na ne mahaifi Ajlaal,
hannunshi ya dunk'ule had'i da dukan iskan bayan ya saki Babah, Babah da sauran jama'ar dake wajen suman tsaye sukayi cike da mamaki,
gaba d'aya 'ya'ya mazan Family d'in sukayi kan Ajlaal suna dukanshi kamar zasu kashe shi,
Babah da har lokacin yana tsaye kamar an dasa shi yayi k'arfin halin cewa " ku daina dukanshi, ba laifinshi bane laifin 'yar mu, ku kyale shi bashi da laifin komai,
Abbi yace " ku fitar mana shi daga gidanmu, cali-cali sukayi da Ajlaal suka fitar dashi waje,
bai damu da yadda jikinshi yayi jina-jina ba ya mik'e da sauri ya shiga mota, ikon Allah ne yakaishi gidansu, daga yadda yayi parking iyayenshi suka san ba lafiya,
a tare Hajiya Halimatu da Alhaji Basaan suka fito, ganinshi haka a birkice kamar wanda ya kwato daga bakin kura yayi masifar d'aga musu hankali dan duk duniya babu abinda suke so sama da Ajlaal,
" Abba nace kaje tunda wuri ka nemar min auren Deeyanah kak'i, idan na rasata mutuwa zanyi Abbah, wallahi mutuwa zanyi, yayi maganar yana dafe saitin zuciyarshi,
jikinsu na rawa suka tallafeshi suna tambayarshi " lafiya Ajlaal?
"Meke faruwa ne?
"Ba lokacin doguwar magana Abbah inba haka ba lokaci zai k'ure zan rasata rasawa ta har abada, kazo muje gidansu Deeyanah yanzu ka nema min aurenta dan Allah Abbah,
Alhaji Basaan zayyi magana Hajiya Halimatu ta daka mishi tsawar datasashi rud'ewa " dalla Malam karka tsaya b'ata lokaci d'ana ya mutu,
wallahi idan Ajlaal ya mutu kaima saika bishi lusari kawai ka tsaya kana shirme rayuwar d'anka na neman salwanta kan ya rasa abinda yake so,
a dururuce Alhaji Basaan ya mik'e yana fad'in" to to tashi muje Ajlaal , " kai kad'ai zan bari kaje neman auren kaje kayi hauka ka lalata komai?
"Tsaya nazo muje tare, tayi maganar tana komawa cikin gida.
Abbi da Deen suka tallafe Babah suka shigar dashi babban parlour'n gidan, duk akabi bayansu har matan, parlour'n yayi shiru ba mai magana, babu abinda ke tashi sai sautin kukan Deeyanah,
tsawa Azan ya daka mata yana fad'in " dalla yiwa mutane shiru mutuniyar banza kawai,
Hannu Babah yasa a aljihu ya ciro kud'in da baisan adadinsu ba, ya mik'awa Abb muryarshi na rawa can k'asa yace " ga sadakin d'ana Deen nan ina nemar mishi auren 'yarka Deeyanah.........!Duk da halin da take ciki bai hana ta shiga mummunan tashin hankali ba, gabanta yayi mummunar fad'uwa,
a razane ta d'ago kanta ta kalli Deen suka had'a ido, in banda hawaye babu abinda ke rige-rigen sauka saman kuncinta,
kanshi ya langwab'ar gefe yana kallan kwayar idonta, Abbi ya kalli Babah cike da neman tabbacin abinda ya fad'a,
gane irin kallan da Abbin keyi masa yasa Babah gyad'a kanshi tare dayin murmushin k'arfin hali, dan bazai iya fad'ar koda kalma d'aya bace,
" me kake san ce min Abduljalal?
"Karka yanke hukunci cikin fushi da b'acin rai, kar muyi abinda daga baya zai raba kanmu, ya kawo rugujewar zumuncinmu, farin cikinmu da kwanciyar hankalinmu,
kar muyi abinda zai tarwatsa kanmu ya kawo lalacewar komai, dakyar Babah ya iya bud'e baki da fad'in " babu komai sai Alkhairi in sha Allah,
Abbi ya bud'e baki zayyi magana cikin sanyi yana danne abinda ke taso mishi ya katse shi da fad'in " dan Allah Yaya....!
ni dai alfarma nake nema a wajenka ta aurawa d'ana 'yarka in kuma....! shiru Babah yayi ya kasa k'arasa abinda yayi niyyar fad'a,
Abbi ya mayar da kallanshi ga Deeyanah da Deen, kan Deen duk'e, fuskarshi fayau cike da annuri, while Deeyanah nata faman kuka kamar ranta zai fita,
" dan Allah Yaya please! Babah ya kuma fad'i har zuwa lokacin yana mik'a mishi sadakin, jikin Abbi a sanyaye ya karb'a, anan take a gaban kowa, aka d'aura auran Deen da Deeyanah,
ana shafa fatiha Babah ya sauke numfashin da bai san yana rik'e dashi ba, yace " Allah ya sani dai-dai nayi, Ubangiji yasa hakan ya zama Alkhairi,
Na yafe muku duniya da lahira, Allah ya baku zaman lafiya da zuri'a ta gari, ya d'ora da " yaushe zaku tafi?
Yayi maganar yana kallan Deen, kanshi ya k'ara duk'arwa k'asa cike da matsananciyar kunyar Babah data saukar mishi a lokaci d'aya yace " cikin satin nan in sha Allah,
" Allah ya kaimu, Babah ya fad'a yana mik'ewa ya fice, Abbi ya kalli Deeyanah cike da tausayawa dan yaga kamar bata san Deen d'in,
bayasan yak'i yarda da hukuncin da Babah ya zartar ne dankar ya zargi wani abu musamman da Deen ya kasance d'anshi,
" Allah baku zaman lafiya, Abbi ya fad'a yana mik'ewa, gaba d'aya suka mik'e suka fice daga parlour'n, a harabar gidan suka iske Babah da Alhaji Basaan da Hajiya Halimatu tsaye,
mamaki shinfid'e a saman fuskar Abbi ya k'arasa wajen tare da mik'awa Alhaji Basaan hannu suka gaisa, Deen da Deeyanah da sauran 'yan gidan sunyi tsaye suna kallansu,
"Mu shiga daga ciki, muyi magana, ba musu suka koma parlour'n gaba d'ayansu har su Deeyanah, bayan kowa ya zauna Abbi ya tsaida kallanshi akan Alhaji Basaan cike da san jin meke tafe dasu,
sai da Alhaji Basaan yayi gyaran murya had'i da satar kallan Hajiya Halimatu kana ya soma magana,
" munji abinda Ajlaal yayi tabbas bai kyauta ba, muna baku hak'uri a bisa abinda yayi, ya d'anyi shiru kafin ya d'ora da " tun a kwanakin baya ya sameni da maganar inzo na nemar mishi auren Deeyanah a wajenku to sai aka samu d'an akasi Allah yasa ban zo ba,
murmushi Babah yayi yana fad'in " ayya sai dai kun makara dan yanzu-yanza aka d'aurawa Deeyanah aure da d'an uwanta Deen,
cikin kid'ima Ajlaal ya mik'e tsaye kanshi ya shiga sarawa, ya kalli Deeyanah da Deen, murmushin da Deen ya sakar mishi ya bashi tabbaci akan maganar Babah,
" kaga sadakinta a hannuna, cewar Abbi yana nuna musu sanadin Deeyanah...... ihunnnn da Ajlaal ya saki yasa Abbi yin shiru,
" nooo! A'a hakan bazata tab'a faruwa ba, Deeyanah tawa ce ni kad'ai, danni kad'ai aka halicceta, yayi maganar kamar zararre,
Gabanta yaje ya durk'usa ya k'ura mata ido, " kina so na Deeyanah na sani, ina sanki kin sani, karki bari a rabamu please yayi maganar yana k'ok'arin rik'o hannunta,
cikin zafin rai Deen ya had'ashi baya, " are you mad?
" Kasan me kake k'ok'arin yi kuwa?