← Book details Bakar Shuka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 56

Sashe 44

Bakar Shuka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Babah ya fad'a yana kallan Abbi daya kasa magana, magana take san yi amma kuka yaci k'arfinta ta yadda ta kasa furta koda kalma d'aya, illa kallansu da take yi da jajayen idanuwanta da suka rine, " ni fa na kasa fahimtar komai ko kai ka fahimci wani abu?

Abbi ya tambayi Babah idonshi kansu, "yi shiru ki nutsu sai kiyi mana bayani yadda zamu gane, Deen bayyi magana ba ya mik'e ya nufi fridge ya bud'e ya d'auko mata robar ruwan Faro ya dawo ya zauna kusa da ita ya zauna ya bar 'yar tazara kad'an a tsakanin su, ya bud'e rofar ya mik'a mata, hannunta na rawa ta amsa tasha sosai, so take ta tsaida kukanta amma ta kasa, tana ta k'ok'arin yin shiru amma kukan yak'i tsayawa, tana shashsheka ta kalli Abbi tace " kada ku zargi Deen wallahi babu ruwanshi shima yayi iya bakin k'ok'arin shi akaina, kuyi hak'uri karku raba mu dan Allah muna san junan mu, tayi maganar muryarta na shak'ewa.

"To munji babu ruwanshi, fad'a mana meke damunki daya haddasa miki wannan mummunan ciwon?

"Babu komai Abbi ta fad'a tana girgiza kanta, babu irin tambayar da ba'ayi mata ba amma amsarta d'aya babu komai, dole tasa Abbi ya sallame su badan ya yarda ba, sai dan kar ya matsa mata, har sun kai bakin k'ofa zasu fita Babah ya kira sunanta cikin sanyin murya, "Deeyanah!.

Jikinta a sanyaye ta juya ta kalle shi had'i da amsawa.

"Deeyanah yaye wata babbar garkuwa ce ga mutum duk girmanshi, iyaye sune katangar da mutum yake jingina da ita a kowanne irin yanayi wala farin ciki ko sab'anin haka, iyaye ginshik'i ne na kowanne mutum, zaki ga ko dabba tana k'ok'arin bayar da kariya ga d'anta, duk wani bala'i ko masifar daya tasowa d'a iyaye sukan shiga gaba dansu tarewa d'an wannan masifar data tunkaro shi koda hakan yana nufin mutuwarsu, koda ace bamu da k'arfin tare miki bala'in daya tunkaro ki, koda ace bamu da ikon yaye miki damuwarki ai zamu raba damuwar tare, kuma koba komai zamu tayaki da addu'a, kuma addu'ar iyaye tana da matuk'ar tasiri ga rayuwar d'a, ko kin sanar damu ko baki sanar damu ba zamu tayaki addu'a da duka k'arfin mu, murmushi kawai tayi mishi batare data ce komai ba, deep down tana jin sanyin dad'in dace da sa'ar iyaye nagari da tayi da ahali masu matuk'ar son ta.

Har cikin d'aki ya raka ta, ta zauna saman gado, ya jawo dorowar gefen gado, ya ciro ledar magungunan ta ya b'allar mata ya mik'a mata had'e da ruwa ba musu ta amsa had'i da runtse idonta da k'arfi saboda bata san shan magani, ta afa maganin ta kora da ruwa, " ki kwanta ki huta, ya fad'a tare da ja mata bargo, bai sake magana ba ya fice, tabi bayanshi da kallo tana tuno a baya idan bata da lafiya yadda yake lallab'a ta yana tarairayarta kamar kwai, musamman idan akazo fannin shan magani daya san bata so, sai ansha daga da gwagwarmaya ta zuba sangarta da shagwab'a san ranta kafin tasha maganin, amma yau ita dashi tamkar bak'in da basu tab'a ganin juna ba.

"Ubangiji kayi min sassauci, kayi min afuwa ka yafe min ka dai-daita tsakani na da mijina ya Rabbi, tayi addu'ar tana zubar da kwalla har lokacin idaonta na kan k'ofar.

A hankali bacci ya soma fisgarta, tana lumshe ido tana bud'ewa bacci na d'aukarta ta ganshi tsaye kanta, da fari ta d'auka gizo yake yi mata ko kuma idonta ne, sai da ta bud'e idon ta ganshi tarrr a gabanta, a firgice ta mik'e zaune tana k'ok'arin sake bud'e idanuwanta da sukayi mata nauyi saboda cikin magungunan akwai me sa bacci, ta zuba su akanshi gami da cewa " me.....me...ya...kawo...ka?

Ta fad'a bakinta na rawa, " me kazo yi gidan aure na Ajlaal?

"Ka dai rantse saika k'arasa wargaza min rayuwata ka lalata duniya ta meyasa Ajlaal?

"Meyasa baka jin rok'o da magiya?

"Yanzu bazaka barni na rayu cikin salama da guntun farin cikin da nake k'ok'arin samarwa kaina ba?

"Wai me yayi saura Ajlaal bayan komai ya k'are ka riga ka gama tarwatsa komai?

Hannunta ta had'e waje d'aya kukan bak'in ciki na kufce mata tace " dan Allah, dan girman Allah ka barni Ajlaal, ka barni haka, dan zatin Allah, ta fad'a cikin rikitaccen kuka.

Bisa mamakinta sai taga ya zube gabanta gami da rusa kuka wiwi shima ya kifa kanshi kan k'afafuwanta, yadda kasan wuta ya zuba mata kan cinyoyinta tayi saurin zame su kanshi ya bugi katakon gado, duk da haka bai damu ba, ya tallafe kanshi da duka hannayenshi yana rusa kuka wiwi kamar mahaukacin daya gudo daga gidan mahaukata, a tsorace take binshi da kallo kamar kace mata arrrrr ta ruga.

"Ina sanki Deeyanah, bazan rayuwa babu ke ba, dan Allah ki taimaka min ki dawo gare ni idan ba haka ba mutuwa zanyi, tunda kika barni rayuwata ta shiga tangard'a, mutuwa zanyi muddin kika barni Deeyanah, dan Allah ki taimaki rayuwata karki barni, karki barni ina sanki, kece duniya ta, kece hasken rayuwata please...!

"Ni kuma bana sanka Ajlaal idan dakai a cikin rayuwata komai nawa lalacewa zayyi dan Allah ka barni.

"A'a Deeyanah ba haka bane, kizo muyi aure mu haifi 'ya'yanmu mu rayu cikin salama da farin ciki, zan baki dukkan farin ciki da jin dad'in duniya da kowacce mace ke burin samu a wajen d'a namiji, zan mayar dake macen tafi kowacce mace a fad'in duniya, zan mantar dake kowa da komai babu abinda zaki rink'a tunawa sai ni da yaranmu da zamu haifa, nayi miki alk'awarin zan shinfid'a miki rayuwata a k'asan k'afarki, nayi miki alk'awarin zan yi miki biyayya bazan tab'a sab'a umarnin ki ba har izuwa fitar da numfashi na k'arshe, nidai fata na kada ki barni, ki zauna tare da ni please, yayi maganar yana durk'ushe gabanta while yana rusa kuka.

"Kai tamkar wani gajimare ne daya wanzu a rayuwata kuma ya washe, kai ba komai bane face mummunan mafarki dana tab'ayi dakai da babu duk d'aya ne a ryuwata, danni a waje na babun ma ta fiye min dan baka da amfanin komai a wajena sai tarin rashin amfani.

" Deeyanah an halicce mu ne dan junan mu, nine mijinki, nine wanda zaki rayu dashi.

"A'a ya isa dan Allah ya isa haka, bani da wani miji a duniya da lahira bayan Deen, shine mijina duniya da lahira, ina fata ya zama mijina har a aljanna, shine uban ya'yana dashi ne zan haihu, shi kad'ai zan haifawa 'ya'ya, danshi aka halicce ni, danni aka halicce shi, bana sanka Ajlal, Deen nake so, danshi zuciyata ke dokawa, shine zab'in rai na, kuma shine zab'in iyaye na, dashi kad'ai zan rayu nayi farin ciki.

" Yanwa anzo wajen dama nasan shi d'in ba zab'in ki bane, kina tare dashi ne saboda shine zab'in iyayenki amma a bad'iri nine zab'inki, dan Allah kada ki azabatar da zuciyoyin mu ta hanyar nesanta mu da juna hakan kan haifar da rugujewar rayuwar mu.

" Ya isa! Ta fad'a cikin tsawa, zayyi magana ta nuna mishi k'ofa tace " fice min daga gani daga yau kada ka sake nuna min wannan bak'ar fuskar taka, me mugun nufi, bak'in azzalumi, shaid'an mai san raba sunnar Ma'aiki, ka fice min bana fatan sake ganinka a rayuwata.

" Dan Allah Deeyanah kada kiyi min haka please, mik'ewa tayi had'i da fincikar gaban rigarshi ta hankad'a shi waje, ta karkad'a mishi yatsa a fuska tace " karka sake zuwar min gidan aure in ba haka ba.... ta cije leb'enta na k'asa da k'arfi.

Hawayenshi yasa d'an yatsa ya goge yana murmushi ya kalli cikin kwayar idonta yace " kisa a ranki ke tawa ce ni kad'ai kuma zan tabbatar miki da hakan, nayi miki alk'awarin babu wani d'a namiji daya isa ya rab'eki a fad'in duniya duk wanda ya kuskura yayi gangancin rab'arki ya cije leb'enshi na k'asa yana murmushi ya juya yabar wajen.

Bata damu ta furucin da yayi ba ta koma cikin d'akinta ta fad'a saman gado had'i da sakin rikitaccen kuka me cin rai tana fad'in " na cuce kaina na jefa rayuwata cikin masifar da bazan iya fitar da kaina ba, wayyo Allah kaico na kaicon rayuwata.

Yana kwance d'akinshi ya jiyo sautin kukanta kad'an-kad'an d'an sararawa yayi danya tabbatar, tabbas kunnenshi bayyi mishi k'arya ba da gaske kukan nata ne, " wai me yake damun yarinyar nan ne?

Ya fad'a yana mik'ewa silifas d'in dake gefen gadonshi ya sanya ya fita yana d'aure igiyar rigar baccin jikinshi, zaune ya iske ta gefen gado tana rusgar kuka, har ya shigo ya tsaya kanta bata sani ba, ya d'an dad'e tsaye kanta yana kallanta, sai da ya sauke ajiyar zuciya kana ya zauna kusa da ita ya dafa k'afarta had'i da kiran sunanta " Deeyanah!

Firgigit tayi a tsorace dan bata san shigowar shi ba, murmushi yayi mata da suka had'a ido cikin dakewa yace " komai yayi tsanani maganinshi Allah, Ubangiji ya dank'a mana maganin damuwar mu a tafin hannunmu tunda yayi mu a musulmai masu imani, ya bamu Alkur'ani da addu'o'i, koma wacce irin matsala kike ciki idan kika dage da addu'a kina kaiwa Allah kukanki da sannu zai yaye miki dukkan matsalarki, kiyi hak'uri ki dangana ki mik'awa Allah komai, kiyi imani akan zayyi miki maganin dukkan damuwa da matsalarki.

Hawayen ta goge ta d'aga idonta ta kalleshi cike da girmamawa tace " bazaka tambaye ni komai ba Yaya?

Kyakkyawan murmushi yayi yace " bazan matsa miki kamar wancan karon ba, idan kin so kinga na cancanci nasan damuwarki, keda kanki zaki sanar dani komai, bana san sake haifar miki da wata damuwar bayan wacce kike ciki.
Chapter 44 · 0% Book details