← Book details Bakar Shuka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 56

Sashe 17

Bakar Shuka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bakinshi ya sake mayarwa cikin nata tare da surarta cak wutsil-wutsil ta soma yi zata kwace amma Ina wane ita, saman sofa 3 sitter ya direta ya bita ya danne cikin salo ya cire mata gaba d'aya kayan jikinta silky naked body d'inta ya bayya hannayenta ta sanya ta kare jikinta while tana cigaba da kukan had'i da rok'onshi.

K'ok'arin tashi daga kan kujerar ta soma yi amma wane ita maza bisa kanta Ajlaal dake cin k'arfe, gaba d'aya nauyinshi ya sakar mata ya danne ta, ya soma rikita mata jikinta, babu inda baya shafawa a jikinta, musamman hips da breast d'inta, jikinshi ya d'auki wata irin muguwar rawa da kerrrma ya rikice ya fita daga hayyacinshi a haukace ya rink'a romancing d'inta, duk ihuu da rok'on da Deeyanah keyi mishi akan ya kyaleta bai sarara mata ba sai da hak'onshi ya cimma ruwa.

Sakwaf jikinshi ya saki ya zube kanta yana mayar da numfashi deep down kuma yana jin wata irin nutsuwa na lullub'eshi, murginashi tayi k'asa ya zube kan Turkish Carpet dake malale a tsakiyar falon, tayi saurin mik'ewa jikinta na rawa ta mayar da kayan jikinta saboda rud'ewa ma nan tabar hand bag d'inta da mukullin motar zube a k'asa tana gaf da ficewa daga falon ta jiyo muryarshi na cewa " dad'in ne ya saki manta jakarki da mukullin motar?

" Da alama nafi Deen iya hak'on rijiya.

Yayi maganar cike da shak'iyanci, dawowa tayi ta d'auka, tana k'ok'arin sake ficewa tajiyo shi yana fad'in " na baki nan da 24hrs kuje kiyi tunani ki zab'i d'aya cikin zab'in dana baki in ba haka ba, ya cije lips d'inshi na k'asa had'i da lumshe idonshi.

Bata tsaya bashi amsa ba ta fice saboda tsabar yadda jikinta ke rawa saura kad'an ta kifa a steps d'in bene, da d'an gudu ta fice daga gidan tana shiga motar ta kifa kanta kan sitiyarin motar ta saki kuka me k'una, ta dad'e tana kukan, taji shigowar text cikin wayarta tasan shine, kamar bazata duba ba sai kuma ta d'ago kanta had'i da goge hawayenta ta bud'a text d'in.

"Idan kin gama zaman kukan ki dawo ki k'ara bani mara ban k'oshi ba! a fili taja tsaki kafin tayiwa motar key ta fige ta tabar wajen.

Bata zame ko'ina ba sai gidansu, tana yin parking ta fito ko d'an mukullin motar bata tsaya cirewa ba, tun a falo tayi cilli ta hand bag da hijabinta ta fad'a bedroom, directly ta wuce bathroom, a k'asan ban d'akin ta cire kayan jikinta ta zubar, duk da muku-mukun sanyin da ake bai hanata sakarwa kanta ruwan sanyi ba, ita bama ta jin sanyin wani irin zafi take ji a duk wata k'ofar gashi dake jikinta.

Da iya k'arfinta take dirzar fatar jikinta tamkar zata b'are ta daga jikinta, sai da ta gaji dan kanta kana tayi zaman dirshen a k'asan tiles d'in ban d'akin ta saki rikitaccen kuka tana fad'in " innalillahi wa'inna ilaihir raji'un yau ni Deeyanah ke yin zina da aure na?

" Na shiga uku! Na cuci kaina da rayuwata! na lalata duniyata da lahira ta, Allah na tuba ka yafe min, ta k'arashe maganar tana k'ara sautin kukanta.

" Deeyanah afiyarki kuwa!?

Deen ya fad'a yana daga bakin k'ofar bathroom d'in had'i da d'an kwankwasawa kad'an, firgigit tayi a razane ta mik'e tana goge hawayenta tace " lafiya lau wanka nake yi, tayi maganar tana k'ok'arin saita kanta.

" kuma shine kike kuka?

"Kuka kuma Abban Deedee?

"Babu wani kuka wanka nake yi fa.

"Ok, bari na shigo muyi tare, kafin tayi magana ya shigo, kallanta ya tsaya yi, tayi muguwar rama tayi fayau da ita, hasken ta ya k'ara fitowa, ga idonta yayi ja sosai ya kumbura da alama ta dad'e tana kukan.

"Meke damun Deeyanah haka?

" Me take b'oye mishi?

"Kika ce ba kuka kikeyi ba?

Murmushin yak'e ta k'ak'aro dole ta shinfid'awa fuskarta, tace " abu ne ya fad'a min a ido na.

Kamar zayyi magana sai kuma ya fasa, kayanshi ya cire ya k'arasa inda take, yana ganin canje-canje da dama a tattare da ita, da da ne da kanta zata kamo shi in saxy way suyi wankan tare, bayyi k'orafi ba ya rungumota a fili ya sauke ajiyar zuciya ,saurin sakinta yayi yaja baya " lafiyarki kuwa!?

Kallanshi tayi batare data ce mishi komai ba," ana wannan mugun sanyin kike wanka da ruwan sanyi?

Sake kallanshi tayi bata ce komai ba, dawowa yayi ya kunna hitar ruwan zafi, ruwan yayi d'an zafi, salaf sukayi wankan ya tuna lokutan da idan suna wanka tare suyi ta watse-watsan ruwa suna romancing juna daga nan sai sex, is so hardly suyi wanka tare basuyi sex ba.

Dole ta fito daga bathroom d'in batare da tayi wankan janaba ba (wankan tsarki) dan bazatayi a gabanshi ba, towel ya d'auko ya nufo ta dashi zai goge mata jikinta, tayi saurin barin jikin madubin ta nufi wardrobe, ta bud'a ta d'auko simple doguwar riga, ya nufo wardrobe d'in nan ma tayi saurin barin wajen, tsaye yayi rik'e da towel a hannunshi ya zuba mata ido, tasan kallanta yake yi dan haka tak'i kallanshi dan karsu had'a ido.

" Deeyanah! ya kira sunanta in a deeper voice.

Batare data kalleshi ba ta amsa, " na'am!

"Dan girman Allah dan zatin Allah ki daure ki sanar dani abinda yake damunki please.

Still bata kalleshi ba dan bata san su had'a ido tace " bakomai Yaya!

"Ko ban cancanci nasan damuwarki bane!?

Shiru tayi bata ce mishi komai ba, jin tayi shiru yasashi fara takowa yana nufarta, tana jin takun shi yana nufota tayi saurin juyawa zata bar wajen, yayi wuf ya rik'o ta ya d'aga ta sama ya zaunar da ita kan mirror yasa hannunshi a hab'arta ya d'ago kanta ya kira sunanta.

"Deeyanah!

Bata iya amsawa ba saboda yadda zuciyarta ke mugun bugu da k'arfi.

" Deeyanah! d'ago ki kalli cikin kwayar idona zaki ga tsantsar soyayyar danake yi miki, wallahi duk duniya nafi kowa sanki, nafi kowa sanin ciwonki da zafinki, nafi kowa kare miki mutuncinki, martabarki da k'imarki ke wallahi nafi Ammah da Babah sanki, dan haka ki fad'a min damuwarki please.

Cikin sanyin jikin daya fara zamar mata jiki cikin 'yan kwanakin nan ta d'ago aiko karaf idanuwansu suka sark'e cikin na juna, tayi saurin mayar da kanta k'asa.

"Please mana ki sanar dani, nayi miki alkawarin zan yak'i komeye koda zan rasa rayuwata kinji.

Cikin sanyin murya tace " bakomai!

Cikin b'acin rai da tafasar da zuciyarshi keyi ya daki mirror d'in bayanta da wani irin k'arfi mirror d'in ya tarwatse, wata irin muguwar tsorata tayi saura kad'an ta fad'o daga kan mirror d'in ta sanya hannunta ta toshe kunnuwanta, ya sake nausar mirror d'in a karo na biyu.

"Bakomai! Bakomai! abinda kike ta fad'a min kenan, baya ya juya mata had'i da cusa hannunshi cikin kwantacciyar suman kanshi while hannunshi na zubar da jini, ta durk'ushe a k'asa had'i sakin rikitaccen kuka, juyawa yayi ya nufota saboda tsabar tashin hankali babu inda baya rawa a jikinta,
ya sanya hannunshi ya d'agota ya matseta a jikinshi gam, idanuwanshi sunyi mugun ja kamar garwashi jijiyoyin kanshi sunyi rad'o-rad'o.

" Bakomai ko!?

" Ke da kanki kika ce min bakomai! ni kuma nayi miki alk'awarin har a tashi duniya bazan sake tambayarki damuwarki ba, ya saketa ya nufi k'ofa ya bud'e ya fice ya bango mata k'ofar d'akin da mugun k'arfi har sai da d'akin ya girgiza, ya fice daga shi sai towel d'aure a k'ugunshi, ta durk'ushe ta cigaba da kukanta, k'arar shigowar text taji ya shigo wayarta bata kula wayar ba ta mik'e ta koma bathroom tayi wankan tsarki ta fito, ko mai bata shafa ba ta zira doguwar riga ta tada sallah, ta dad'e zaune kan sallaya tana karatun Al-Quran kafin tayi addu'a ta shafa ta mik'e, tana ninke sallaya wayarta ta soma rori, wata irin muguwar fad'uwa gabanta yayi kamar munafuka ta isa gaban wayar cikin tashin hankali ta furta " shine!.

"Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un! ta sake furtawa cikin tsoro har wayar ta tsinke bata d'aga ba tana tsaye tana kallanta sake kiran wayar akayi a karo na biyu, cikin fargaba ta mik'a hannunta dake faman rawa ta d'auki wayar ta amsa tare da karawa a kunnenta.

"K'arya yake yi Deeyanah! Wallahi nafi kowa sanki bai kai ni sanki ba, ko rabin sanda nake yi miki bayayi miki shi, munafurci ne danya lallab'aki ki sanar dashi damuwarki ne, yayi maganar cikin hargowa.

"Wait tsaya Ajlaal wai ya akayi kasan duk wani motsina na gida dana waje!?

"Ya akayi kasan munyi wannan maganar da Deen!?

"Badai bi diddigi (tricker) ka saka min ba ko!?

Cikin dariya yace " har wankan da kukayi tare dashi na sani, ai na riga na fad'a miki duk inda kika shiga a fad'in duniya saina nemo ki Deeyanah, nayi sake kin kufce min a baya amma a wannan karon in duniya zata tashi babu wanda ya isa ya rabani dake duk wanda ya shiga gaba na zan kawar dashi a hanyata.

Cikin masifa tace " wai bi diddigi da d'au sauti ka saka min Ajlaal?

Wata irin dariya ya saki kana yace " fiya da nan yarinya! na fad'a miki zan iya yin komai akanki kamar yadda kikaji nace komai to Ina nufin komai, zatayi magana ya tari numfashinta da fad'in " idan kika sake kika sanar da Deen gaskiyar abinda ke faruwa tsakani na dake to ki tabbatar kin yankar mishi tikitin mutuwa, bai bari tayi magana ba ya kashe wayar.

Zama tayi bakin gado jiki ba kwari wani iri take ji a jikinta, tayi-tayi hawayenta su zubo amma sunk'i zubowa, cikin sanyin jiki ta kashe wayarta gaba d'aya ta jefa ta saman wardrobe ta fice daga d'akin, dayake bata iya cin komai sai ruwan tea yanzu kitchen ta shiga ta had'o ruwan black tea ta dawo Falo ta zauna tana kurb'a.

Bayan Kwana Biyu......
Chapter 17 · 0% Book details