← Book details Bakar Shuka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 56

Sashe 43

Bakar Shuka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ammi.....! ta fad'a da wani irin kuka me k'arfi dake fitowa daga can k'ark'ashin zuciyarta so take tayi magana amma kuka ya hanata, duk sunyi tsaye kanta cikin damuwa da tashin hankali, "kaita gida mayi magana daga baya, Abbi ya fad'a yana kallan Deen, kanshi ya d'aga alamar to kana ya sunkuya ya d'auke ta cak yabar wajen da ita, in banda kallanshi da kuka babu abinda take yi, saman gado ya shinfid'eta yaja mata bargo ya rufe ta zuwa k'irjinta ya juya zai fita caraf tayi ta rik'e hannunshi cikin sheshsheka tace " d....a...n A.....ll...ah kar...ka tafi.....ka zau....na dani na.....wa....ni, d'an....lo...ka...ci, guntun murmushi yayi mata tare da zame hannunshi daga cikin nata kana ya zauna saman sofar dake d'akin yana danna waya, idanuwanta kanshi ta kasa d'auke ido daga kanshi, yana sane da kallan da take yi mishi while yana jiyo sautin kukanta dake fita a hankali a haka bacci ya kashe shi, ita kam bata runtsa ba kwana tayi tana tunanin irin soyayyar da ahalinta keyi mata amma ta saka musu da bak'in batulci.

Wasa-wasa abu ya wace sekanni, awanni, satittika har aka kai wata d'aya, duk yadda Ajlaal ke tunanin abun ya wuce nan dan babu yadda bayyi da ita ba amma tak'i sake yarda dashi, ya rasa yadda zayyi da ita abun duniya ya tattaru yayi mishi yawa.

A b'angaren Deeyanah kuwa ta koma kamar tsohuwar data gaji da duniya, bata iya cin komai sai ruwan tea da drinks shima ba sosai ba, ta rame ta k'ek'ashe bata da aiki sai kuka, tun babu wanda ya sani har kowa ya sani, babu irin tambayar duniyar da ba'ayi mata ba akan meke damunta kullum amsarta d'aya ce babu komai, duk gida an tattara an zuba mata ido, ga bp d'inta da yayi mugun hawa.

Tana kwance saman gado, aka kira sallar la'asar ta mik'e da d'an hanzari jiri ya d'ebeta tayi baya ta fad'a saman gadon d'an shuuuuu taji cikin kanta da kunnenta, zama tayi saman gadon tana ganin komai bibbiyu yana juya mata, bango ta dafe ta mik'e tana bin bangon tana tafiya while tana gani dishi-dishi jiri na d'ibarta har takai k'ofar shiga bathroom d'in ta d'aga k'afarta zata shiga bathroom d'in jirin ya d'ebe ta, ta fad'i daga nan bata sake sanin inda kanta yake ba, babu wanda ya shigo har magariba, Deedee ne ya shigo wajenta, ganinta a kwance k'ofar bathroom yasa shi k'arasawa wajenta ya durk'usa gabanta yana girgizata tare da kiran sunanta, jin shiru yasa shi fita da gudu, d'akin Deen ya shiga yana haki, " Daddy kazo Momy ta fad'i tak'i tashi.

Jikinshi na rawa ya fito da d'an gudu, " Deeyanah ! ya fad'a yana jijjiga ta amma shiru, sai jini daya fara fitowa daga hancinta kad'an-kad'an, jikinshi na b'ari ya sumgume ta sai asibitin dake nan cikin estate d'insu, anyi mata gwaje-gwaje da aune-aune inda aka gano zuciyarta ta soma kumbura.

Gumi likitin ya goge kana ya soma magana yana kallan Abbi da Babah sa Deen da yayyan Deeyanah yace " wai meke damun yarinyar nan ne?

"Gaskiya ya kamata ku bincika kusan damuwarta da kuma matsalarta dan abun ya fara girma gaskiya, yarinya k'arama da k'ananun shekaru amma ace tana tattare da irin wannan damuwar dake neman haifar mata da bugawar zuciya, a zahirin gaskiya abun yafi k'arfi shekarunta dan haka ya kamata kusa ido akan wasu abubuwa fa, da fari bawan jini yanzu kuma kumburin zuciya?

Kallan da Abbi yayi mishi ne ya fahimtar dashi shi ake zargi akan damuwarta, dakyar ya iya had'iye yawun daya tsaya mishi tsakanin baki da mak'ogwaro, likitin ya d'ora da " a halin yanzu takai matakin da dole sai mun d'orata akan magani ta fara shan maganin, kuma koda ta fara shan maganin dole fa sai an saka ido kuma anyi mata maganin damuwarta in ba haka ba komai yana iya faruwa at any movement so take note please.

Ajiyar zuciya Abbi ya sauke a b'oye kana cikin nutsuwa yace " Allah ya tsare, in sha Allah zamu bincika da yardar Allah zamuyi maganin koma meye.

Tana kwance saman gadon luf tayi lamo yadda kasan babu rai a jikinta, fuskar nan tata tayi fayau sai uban haske, saboda kana ganin k'asusuwan fuskarta, jijiyoyin jikinta kam yadda kasan zana su akayi gasu nan rad'o-rad'o sun fito, hannunta dake june da ruwa ya kalla had'i da zuba mata ido yana mamaki abinda ke damunta da girma har haka, tunaninshi ya d'auko tun daga farko shekaru kusan uku baya, ta fara canjawa ne tun daga lokacin data suma ya kaita asibiti, a wancan lokacin ma haka ta shiga matsananciyar damuwa yayi juyin duniya ta fad'a mishi abinda ke damunta tak'i sanar dashi, tun daga lokacin bai sake gane kanta ba har yau.

"What is going on?

"Meke faruwa ne?

" Meke damunta?

"Meye damuwarta?

Yayiwa kanshi tambayar, kanshi ya kulle ya kasa gane ko fahimtar komai, ya rasa a ma'aunin da zai sanya abun, tunanin nika da yawa suka rink'a zuwa kanshi, ya sak'a wancan ya k'ulla wannan, " bakomai idan ta warke in sha Allah zan sake tambayar ta damuwarta duk da nayi alk'awarin bazan sake tambayar ta damuwarta ba, Babah ya dafa kafad'arshi tare da d'an matsa kafad'ar yana fad'in " karka ayi biyu, kabar tunanin nan, wani abu ya had'iye ya sake danne abun cikin ranshi, ya dad'e yana san ya tattauna matsalar dake tsakaninsu kodan asama musu masalaha, yana san yayi maganar da wani koba komai za'a bashi shawarar da zata kaisu da samun mafita, yana san yayi maganar da Babah tunda shi bashi da aboki balle suyi maganar to amma Babah mahaifinta ne, idan ya sanar dashi yana iya zama sanadiyyar samun matsala tsakaninta da iyayenta, dole babu yadda ya iya ya hak'ura ya danne komai cikin ranshi, shima abun na damunshi, shima yana cikin damuwar, shima da za'a gwada shi ya tabbatar sai an samu matsalar data fi tata a jikinshi.

"Badai zaka bar tunanin ba kenan?

Murmushin k'arfin hali yayi yana b'oye damuwarshi batare daya ce komai ba, kwananta hud'u a asibiti aka sallame ta, gata kam babu irin wanda bata gani ba, idan tace tana san abu kaza kafin ta gama rufe bakinta an kawo mata shi, kowa sai lallab'a yake yi kamar kwai, shima a fannin gogan babu yabo babu fallasa yana bata kulawa dai-dai iyawarshi, Ammi taso ta wuce part d'inta da ita amma Deeyanah tak'i binta dole Ammi ta hak'ura aka mayar da Deeyanah part d'insu, kwananta biyu da sallamota Abbi ya kira su ita da Deen a babban falonshi, Babah na gefe zaune suka shigo, bayan sun zauna a k'asan carpet suka gaida iyayen nasu, Abbi yayi gyaran murya kana ya soma magana.

" Deeyanah ya jikin naki?

"Alhamdulillah da sauk'i Abbi.

"Madalla haka ake so, an miki bayanin abinda yake damunki?

Sake sunkuyar da kanta tayi k'asa kana tace " eh!

"Kin san dalilan dake kawo irin wannan ciwon ko?

"Eh!, ta sake cewa cikin girmamawa, " kin san illolin ciwon?

"Eh! Abbi.

"To meyasa Deeyanah?

"Meyasa kika haifarwa kanki tunani da damuwar da zata iya zama silar rayuwarki?

"Kinyi tunanin halin da zamu shiga idan hakan ta faru?

"Ko sau d'aya kin duba mijinki da d'anki da zasuyi maraici?

Kanta k'asa hawaye ya soma d'iga daga idonta, " meke damunki?

"Meye damuwarki?

D'an shiru ne ya biyo baya sai sautin kukanta dake tashi k'asa-k'asa, "mu muka fi kowa cancanta damu san damuwarki, mu ya kamata mu san matsalarki dan mune iyayenki mu zamuyi miki maganinta, ko bamu da maganinta zamu baki shawara ta gaskiya tsakani da Allah wacce bazata cutar dake ba, kuma zamu tayaki da addu'a, ina tunanin kin san k'arfin da addu'ar iyaye take da ita ga d'ansu, dan Allah kiyi mana adalci ki yiwa kanki adalci, ki taimake mu ki taimaki kanki ki fad'a mana damuwarki tun kan ta girma tafi k'arfin mu.

Wannan karon sosai sautin kukan nata ya fito ya gauraye falon, bata so yin kukan gabansu ba, bata so ta basu alamar da zata basu tabbacin tana cikin matsala ba.

" Kodan matsalar daga gidan aurenki take?

"Kodai matsalar tana tattare da mijin aurenki?

"Dan muddin kaga mace cikin irin wannan mummunar matsala da tarin damuwa to imma daga mijinta ko 'ya'yanta ko kuma dai dangin mijinta da iyayen mijin, na tabbatar ke baki da matsalar 'ya'ya, dangin miji data iyayen miji sai dai kota mijin, ya k'arashe maganar idonshi kan Deen daya d'ago ya kalle shi.

"A'a, ba lalle matsalar daga gare shi take ba, Babah da tunda aka fara magana bai ce komai ba sai yanzu ya fad'a.

Cikin fad'a-fad'a Abbi yace " ai dama kai ka saba kare shi, duk abinda Deeni yayi kai a wajenka ba laifi bane, ya zaka ce matsalar ba daga shi bace idan ba daga wajen shi take ba daga ita take?

" Ya za'ayi ace yarinya kamar Deeyanah tana cikin irin wannan halin ace babu saka hannun mijinta kwata-kwata fisabilillahi?

Cikin sanyin murya Babah yace " kada kayi saurin yanke hukunci ka tsaya dai ayi bincike sosai, kallan mamakin anya kuwa kaika haife ta Abbi yayi mishi, kamar zayyi mishi magana sai kuma ya fasa, ya sake mayar da kallanshi gare su yace " kiyi mana bayani Deeyanah muji idan da cutarwa a zamantakewar taku sai mu duba masalahar kowa, idan ta kama ma dole sai a raba auren tunda aure ba wajibu bane Sunnah ce ba Farillah ba idan da cutarwa sai a hak'ura ba lalle ba dole.

"A raba auren fa kace?

Cewar Babah yana kallan Abbi cike da mamaki, shiru yayi baibi takan maganar Babah ba.

Saurin d'ago kanta tayi tana fitar da sautin kukanta sosai duk tabi ta rikice tana girgiza kanta tace " a'a Abbi dan Allah kar'a raba mu muna san junanmu, bashi da laifin komai, duk laifi na ne, nice na lalata komai Abbi, nice nake cutar dashi, dan Allah ku yafe min Abbi, ku taimaka ku yafe min, shima ku bashi hak'uri ya yafe min, tayi maganar cikin rikitaccen kuka tamkar ranta zai fita.

Cikin rashin fahimtar inda zancenta ya dosa gaba d'ayansu suke kallanta, " me kike nufi Deeyanah?
Chapter 43 · 0% Book details