← Book details Bakar Shuka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 55 OF 56

Sashe 55

Bakar Shuka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Abbah da kanshi ya kira Ajlaal ya sanar dashi batun sammacin da aka aiko, yayi dariya had'i da cewa " na sani ai tun kafin ma yakai kotun nasani, Allah ya kaimu ba damuwa, ashe ma iyakacin nan ya tsaya duk cika bakin nashi, Abbah yayi mamakin ganin ko a jikin Ajlaal dan haka yace " kaji tsoran Allah, kaji tsoran ranar had'uwarka da Allah, wallahi idan kaine wanda ka lalatawa yarinyar nan rayuwar to ka sani kaima Allah bazai barka ba, da sannu Ubangiji zai saka mata, ya mayar dakai abin kwatance, ya wulak'anta ka kafin mutuwarka ta riske ka.

"Na lalata mata rayuwa kodai muka lalatawa juna rayuwa?

Dan yaji maganar da Deeyanah ta fad'awa su Abbi sai a lokacin shi kanshi Ajlaal d'in yasan hak'ik'anin abinda ke faruwa, ya kuma alwashi akanta.

"Ina zaman zamana lafiya ta shigo rayuwata ta wargaza min duniya ta Abbah, duk abinda ya faru itace sanadi itace ta jawowa kanta, da kanta tayiwa kanta BAK'AR SHUKA....

Abbah zayyi magana Mamah tayi saurin tarar numfashin shi da fad'in " dan zatin Allah ka kyale yaron nan ka shafa mishi lafiya wannan wacce irin masifa ce ka saka yaro gaba ka tsare shi da maganganun banza, Ajlaal fa ba yaro bane ya girma ya isa ya yankewa kanshi hukuncin dayace da rayuwarshi.

"Yanzu maganar tawa ce ta zama maganganun banza?

Fuska ta yatsina had'i da tsare shi da ido tace " eh! koba hakan bane?

Abbah bayyi magana ba ya mik'e ya fice.

Ranar zaman kotu

Kotun ta cika mak'il da mutane da wad'anda suka zama dole da gayyar sod'i 'yan san ganin kwakwaf, masu san su gani da idonsu ba abasu labari ba, bak'ar mota Range Rover me bak'in tint da duk bin kwakkwafin mutum bazai ga wanda ke cikin motar ba, ta faka a harabar kotun ,daga ita sai Abbi ne suka zo kotun dan kowa k'in zuwa yayi, Babah ko cewa yayi bada shi za'a d'aurewa k'arya gindi ba shidai dayaga zai iya yaje can yayi tayi.

Doguwar rigar atamfa ce a jikinta sai hijab data sakko dashi fuskarshi ta rufe fuskarta ruf Abbi na binta a baya, ihuuuuu mutane suka soma yi mata had'i da jifanta da duwatsu, aiko kan kace me anyi mata jina-jina an fasa mata goshi da bakinta sai jini ke zuba, dakyar aka kwace ta a hannun mutane aka shigar da ita kotun, sai da rigar jikinta da hijab d'in suka yage, yana zaune a bancin farko kusa da Abbah da Mama, akanshi idonta ya fara sauka ya sakar mata shu'umin murmushi had'i da kashe mata ido d'aya, Abbah na d'ora idonshi akan yarinyar matsanancin tausayinta ya kamashi, ita kam Mama in banda uwar harara babu abinda take watsawa Deeyanah.

Tana cikin jikin Abbi yana ta kakkare ta suka zauna, bayan an natsa magatakardar kotu ya mik'e ya gabatar da k'ara, ya karanto k'orafi, Alk'ali yayi gyaran murya had'i da cewa " ina me k'ara?

Cikin nutsuwa Abbi ya mik'e da ita a jikinshi suka fita gaban kotu, Alk'ali ya sake cewa " ina wanda ake k'ara?

Cikin izza ta tak'ama ya fito ya tsaya daga d'aya b'angaren suna fuskantar juna, Alk'ali ya kalli Abbi yace " fad'awa wanda kake k’ara akan abinda kake k'ararshi, Abbi ya kalli Deeyanah yace " kada kiji tsoron komai da kowa ina tare dake, Allah zai tsaya mana, kiyiwa kotu bayanin komai bisa gaskiya da amana, bakinta na rawa, muryarta na shak'ewa while hijabinta na zamewa ya fad'i saboda yagar dake jikinshi, ta kwashe komai ta fad'awa kotu bata rage komai ba, nisawa Alk'ali yayi had'i mayar da kallanshi ga Ajlaal yace " to kaji abinda ake tuhumar ka dashi?

"Eh naji!.

"To me zaka cewa kotu!?

Gyaran muryar yayi kana cikin shariya yace " to ni dai gaskiya ban san komai akan wad'annan maganganun ba, yadda kowa yaga videon ta haka nima na gani, ni nama manta da ita, na dad'e da rufe babinta a rayuwata.

Alk'ali ya mayar da kallanshi gasu Deeyanah yace " to kunji, a hankali ta d'aga ido ta kalli Ajlaal ya d'auke idonshi gami da basarwa, Alk'ali yace " kuna da sheda ne?

Abbi ya kalli Deeyanah cike da tausayawa, itama shi ta kallan kana ta mayar ga kallanta ga Alk'ali tace " eh akwai shaidu.

D'an shiru Alk'alin yayi yana nazari kana yace " ku koma ku zauna, sai da yayi rubutu sannan ya sake d'agowa ya kalli inda lauyoyi suke yace " ina lauyan me k'ara?

Lokaci d'aya lauyoyi bakwai suka mik'e tsaye sosai mamaki ya fito k'arara saman fuskar Alk'alin cike da mamakin yace " dukkanku lauyoyin me k'ara ne?

Suka da eh cikin girmamawa, bayyi magana ba ya juya b'angaren Ajlaal yace " ina lauyanka?

Murmushin gefen baki yayi had'i da cewa " bani dako d'aya.

Jinjina kai Alk'alin yayi kana yace "lauyoyin me k'ara kuna da abin cewa?

D'aya daga cikinsu ya karkace ya soma magana, ya dad'e yana magana kana yayi shiru d'aya daga cikinsu shima ya fara maganar, sai da kuka gama kaf kana ya kalli Ajlaal yace " kana da abin cewa?

"A'a, Ajlaal yace fuskarshi d'auke da shu'umin murmushi, Alk'ali ya fara rubutu, ya d'an d'auki lokaci me tsayi yana rubuce-rubuce kana ya d'ago, "zamu cigaba da sauraren wannan shari'ar a ranar 30 ga wantan 6 na wannan shekarar inda masu k'ara zasu gabatar da shaidunsu a gaban kotu.

Da taimakon 'yan sandan kotun aka shigar da ita mota, koda suka koma gida babu wanda ya tambayesu yadda ta kasance a kotu, har shi kanshi Babah da Ammu, sosai ran Abbi ya b'aci da burus d'in da sukayi dasu, amma ya kanne bayyiwa kowa magana ba.

Tana shirin shigewa d'aki Abbi yace " kina da shaidun da zaki gabatar a kotu?

Cikin sanyinta da muryarta da bata fita sosai tace " eh! akwai text's d'in dayake turo min ta wayata da voice note ta WhatsApp kuma har yanzu suna nan a wayata.

"D'auko min wayar. Abbi ya fad'a yana zama.

Shigewa tayi cikin bedroom ta bud'e wardrobe ta zaro wayar tana fitowa ta kunna wayar dan ta manta rabanta da amfani da waya, yana zaune ta rusuna ta mik'a mishi wayar, ya karb'i wayar dai-dai lokacin data gama kunnuwa, mik'a mata wayar yayi yace " saka password d'in, ta karb'a ta cire password d'in ta sake mik'a mishi, yana k'ok'arin shiga WhatsApp wayar tayi hooking yayi-yayi wayar ta dannu tak'i dannuwa, sai kuma ta farfarfar, sai wayar ta kashe kanta, kallanta Abbi yayi yace " dama wayar nada matsala ne?

"A'a bata da matsalar komai, zayyi magana wayar ta kunna kanta, ta dad'e kafin ta zama normal bisa mamakin su komai na wayar ya sauka wayar ta dawo kamar sabuwa, babu abinda bai goge ba, murmushin takaici Abbi yayi yace " an datsi wayar (hacking) an goge komai dake kan wayar, cikin tashin hankali ta warce wayar daga hannun Abbi ta shiga duba wayar hannunta na rawa, amma yadda kasan yanzu ta bud'e wayar daga kwalinta, cikin tsoro idanuwanta waje tace " yanzu ya zamuyi a kotu bamu fa da wata shaidar bayan wannan?

Murmushin takaici ya sake yi a karo na biyu kana yace " sai dai mu jira ikon Allah.

Kotu Day2

Kotin tayi mak'il da jama'a, Alk'ali ya shigo kowa ya mik'e tsaye sai bayan ya zauna kana kowa ya zauna, bayan an natsa Alk'ali ya nemi lauyoyin me k'ara suka fito gaban kotu.

"Yana duba takardun gabanshi yace " ina shaidar da zaku gabatarwa da kotu?

Kallan juna lauyoyin sukayi kana d'aya daga cikinsu yace " babu wata shaida mun rasata, a fili Alk'ali ya fitar da nannauyan numfashi kana yace " zan sake baku dama ta biyu kuma ta k'arshe kuje ku sake binciko shaidar da zaku gabatar a gaban kotu, lauyoyin suka rusuna had'i da yin godiya suka koma suka zauna, d'an shiru ne ya ratsa kotun, Alk'ali yayi ta rubuta kana d'ago yace " an d'aga shari'ar zuwa nan da sati uku zai kama 20 ga watan gobe na wannan shekarar, kooootuuuu! ya mik'e ya fice kana kowa ya fice, fuskarshi d'auke da murmushi ya kalleta hannuwanshi hard'e a k'irjinshi yana tauna cingam, bayyi mata magana ba ya wuce ta gabansu yana fito.

Daga Deeyanah har Abbi jikinsu yayi mugun yin sanyi dan sun hango fad'uwa da rashin nasara k'arara, basu da wata makama ko mafita, jikinta a sanyaye ta wuce Abbi dake zaune a falo, d'an tari yayi yace " Deeyanah babu abinda za'a iya samu wanda zai tabbatar da laifin Ajlaal a kotu?

Jimmmmm tayi tana nazari kana ta d'ago kanta dake k'asa ta kalli Abbi tace " wallahi babu dama a waya ta ne kuma ya goge komai dake kan wayar, cikin jimami Abbi yace " bakomai akwai Allah, kuma yana bayan me gaskiya, muyi addu'a, ta d'aga mishi kanta had'i da wucewa bedroom d'inta.

Kotu Day3

Abbi da Deeyanah jiki ba kwari a sanyaye suka isa kotun cike da sanyin gwiwa, shiko yasha kwalliya da k'ananan kaya sai k'alli yake yana shek'i fuskarshi d'auke da wadataccen murmushi, ya kafe ta da ido baya ko blinking, tana jin yadda idonshi yake yawo a jikinta amma tak'i kallan inda yake, Alk'ali ya shigo kamar yadda aka saba kowa ya mik'e sai bayan ya zauna kowa ya zauna, magatakardar kotu ya mik'e ya karanto shari'ar da za'a saurara, bayan ya gama Alk'ali ya nemi ganin lauyoyin me k'ara.

"Kunzo da shaidar?

Kansu k'asa cikin rashin kwarin gwiwa suka amsa da a'a dan sunyi iya yinsu wajen neman hujjar da zasu gabatar a gaban kotu amma dayake Ajlaal shege ne baibar kafa ko d'aya ba yasa basu samu komai ba, sunyi duk wani bincike da bin kwakkwafi amma babu abinda suka samu.

Alk'ali ya d'auki lokaci me tsayi tana rubutu kana ya d'ago ya kalli Ajlaal yace " kana da abin cewa?

Baki ya d'an tab'e had'i da girgiza kanshi yace " a'a bani da wani abin cewa.
Chapter 55 · 0% Book details