Sashe 34
Bakar Shuka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Wallahi d'ai-d'ai daga cikin 'yan siyar Nigeria ne bazasu ci wuta ba, kallan sosai yayi mata, kamar bazayyi magana ba sai kuma yace " ya akayi kika dawo gida, sai da ta juya idanuwanta kana tace " Napep nahau mana, " wannan lokacin da kika d'auka anan kawai kika tsaya?
Wata irin mummunar fad'uwa gabanta yayi, k'irjinta ya doka da tsananin k'arfi, ta tsaya cak tabar abinda take yi, a hankali ta juyo ta kalli cikin kwayar idonshi, shima tar yake kallan idonta, ganin irin kallan da yake yi mata yasata yin rau-rau da ido zatayi kuka tace " me kake nufi da wannan maganar taka Yaya?
Sosai take k'ok'arin k'ak'aro kuka tace " Yaya zargi na kake yi?
Tsoki ja mtswwww yace "idan ma zargi nake yi laifi ne?
"Ko ba kece kika jawa kanki zargin ba?
Ya fad'a idonshi tar cikin nata, abinda ta hango cikin kwayar idonshi ba k'aramin firgita ta yayi ba, wanda har ya hanata magana, tana kallanshi har ya fice bata iya furta koda kalma d'aya ba, ta dad'e tsaye nan inda ya barta a matuk'ar tsorace da abinda ta gani tattare dashi, cikin sanyin jiki ta juya ta cigaba da aikinta, kafin Magriba ta gama tuwon shinkafa da miyar Ogun leaf dayasha kifi sukunbiya da bushashshen kifi d'an Maiduguri, ga ganda da kwalla, ta zubawa Ammi nata a kula haka ma Ammu, da kanta ta mik'a musu, sama-sama ta tsaya suka gaisa saboda bata cikin nutsuwarta, taso ma tayi sob'o ko coconut drink amma ta kasa tuwon ma danta riga ta d'ora ne.
Bazata iya fassara abinda ta gani cikin idonshi ba amma koma meye abun tayi masifar tsorata dashi, har tayi wanka tayi sallah a firgice take, sai da tayi waya da Ajlaal kana yad'an kwantar mata da hankali.
Tana zaune kan sallaya bayan ta idar da sallar isha tana waya da Ajlaal kasancewar bluetooth d'inta babu caji yasata kara wayar a kunnenta fuskarta d'auke da murmushi, bata ji motsin shi ba sai kawai jin banko k'ofar bedroom d'inta taji, tayi saurin kifa wayar, tashin hankali, tsoro da firgici k'arara bayyane saman fuskarta, ga rashin gaskiya nan k'uru-k'uru yana gani a tattare da ita, yaso yayi magana amma ya fasa ya juya ya fice, yama fasa yin abinda ya kawo shi d'akin gaba d'aya dama raban daya shigo d'akinta har ya manta.
Jikinta na rawa ta kashe wayar batare da sunyi sallama ba ta mik'e tabi bayanshi duk ilahirin jikinta na tsuma, yana zaune saman dinning table yana daddana waya da alama ita yake jira ta bashi abinci, hakan ba k'aramin kwantar mata da hankali yayi ba dan tasan daya ji wayar da take yi da bai zauna zaman cin abinci ba, idanuwanta ta lumshe had'i da sauke ajiyar zuciya a hankali, duk abinda takeyi yana sane, ta k'araso ta zuba mishi abincin, ta d'auko mishi lemon Chiivita a fridge ta kawo mishi had'e da glass cup, itama ta zuba ta zauna tana ci sama-sama, gaba d'aya hankalinta yana kan wayarta, tana chart fuskarta d'auke da murmushi, duk wani motsinta yana sane dashi, shima murmushin yayi na gefen baki yana danne abinda ke taso mishi, tare dakai lomar tuwan, saboda b'acin rai ji yayi tamkar ya saka mad'aci a bakinshi, sai da yayi da gaske kafin ya iya daurewa ya had'iye tuwan bakinshi, kallanta ya sake yi yaga still she's on her phone, ya buga uban tsaki had'i da kwab'ar da plate d'in tuwan da k'arfi ya mik'e, firgigit tayi ta dawo cikin hayyacinta, ta kalleshi dai-dai lokacin da yake shigewa bedroom d'inshi kana ta dawo da kallanta kan tuwon, baki ta tab'e had'i da zagewa taci tuwon san ranta kana ta mik'e ta shige bedroom ta fad'a saman bed suka cigaba da wayarsu tana yi tana juyi cike da annashuwa.
Tayi nisa cikin wayar tana ta mirgine-mirgine ya shigo, tayi saurin tashi zaune saboda tsananin tsoro yadda kasan idanuwanta zaro fad'o, ido ya kafe ta dashi na tsayin lokaci, ta sunkuyar da kanta k'asa dan bazata iya jurewa irin kallan da yake yi mata ba, kamar daga sama taji yace " dawa kike waya?
A kid'ime ta d'ago ta kalle shi, kun san mutane masu manyan idanuwa basa iya b'uye tsoro, firgici da tashin hankali dan haka a idanuwanta ya hango zallar tashin hankalin data shiga, k'afarshi d'aya ya d'ora saman gadon yayinda d'aya k'afar tashi take taka k'asa, ya matso da fuskarshi gaf da tata ta yadda iskar numfashinshi take sauka cikin hancinta, ranshi a matuk'ar b'ace yace " dawa kike waya?
Yawu ta had'iye kwat ba shiri, take gumi ya soma tsatsafo mata a saman goshinta, in banda rawa babu abinda bakin keyi, bata ma da nutsuwar had'a kalamai balle ta iya yi mishi k'arya, " nace dawa kike waya?
Ya fad'a a tsawace, wata irin muguwar rawa da tsuma duk ilahirin jikinta ya d'auka lokaci d'aya ga matsanancin tsoronshi daya shigeta, idonshi dake kanta ya kai kan wayar, itama wayar ta kalla, ya kai hannu zai d'auki wayar tayi saurin d'auke wayar, wani irin kallo ya bita dashi me wuyar fassarawa, wani irin tuk'uk'i yaji yana taso mishi daga can k'asan k'irjinshi, idonshi yayi wani irin mugun ja, jijiyoyin kanshi sukayi rad'o-rad'o yadda kasan an zana su, da k'arfi ya finciko ta ya warb'ar da ita a k'asa, saboda tsabar soyar da zuciyarshi keyi mishi har bibbiyu yake gani, abinka dama dame zuciya, sake damk'o ta yayi ya d'agata sama, ya had'a ta da jikin bango ya mak'ure ta, ya shak'e mata wuya da iya k'arfinshi.
Tsabar azaba tasa idanuwanta yin jajir kamar gauta, duk sunyo waje k'uru-k'uru yadda kasan zasu fad'o k'asa, sosai ta soma kokawa da numfashinta dake neman kwace mata, d'aya hannun yakai ya d'auki wayar dake yashe a k'asa ya shiga dubawa, duk inda ya kamata ya duba ya duba amma baiga komai ba, har Chart d'inta ya duba, da Gallery, Message, Phonebook, received call, Missed called amma babu wani abu daya gani na zargi, hakan ya sashi sakinta ta zube k'asa tana tari da faman mayar da numfashi.
" Deeyanah karki bari na kama ki da wani abu daya danganci cin amana, butulci da yaudara, idan kika sake kika ci amanata zanyi nisa dake da duniyarki, zan yiwa rayuwarki nisan da har ki mutu bazaki sake gani na.
Yana gama fad'a ya nufi k'ofa zai fice har yakai bakin k'ofar ya juya ya kalle ta sosai yace " daga yau ni zan rink'a kaiki duk inda zaki, ban yarda ki fita ke kad'ai ba, bai jira amsarta ba ya fice, tabi bayanshi da kallo, har lokacin tana rik'e da wuyanta hawayen azaba nabin kuncinta, " Allah ya isa na mugu azzalumi kawai, ta fad'a a wahalce, dakyar ta mik'e ta d'auki wayarta ta koma saman gadon tana dialing number Ajlaal, number busy aka ce mata, tana niyyar sake kira wayarshi ta shigo.
Ranshi a matuk'ar b'ace yace " Deeyanah ki bari na kashe Deen please, wallahi badan ina tsoron b'acin ranki ba da yau bazai kwana duniya ba, " a tsawace tace " karka fara tunanin kashe min miji, shi d'in mijina ne, shine katangar dake tokare da bayana, ka kula, tsaki yayi had'i da kashe wayar ya jefata saman kujera, yana danasanin datsar wayar da yayi ya goge komai, " dama banyi hacking wayar nayi formatting ba, dana bari yaga abinda ya kamata ya gani komai yazo k'arshe, ya k'arashe maganar had'i da jan dogon tsaki.
Idanuwanshi ya lumshe had'i da tallafe kanshi yana jin zafin shak'ar da Deen yayiwa Deeyanah, wayarshi da tayi ringing yasa shi jan dogon tsaki mtswww had'i da bud'e idonshi ya d'auki wayar, batare daya duba sunan wanda ke jikin wayar ba ya kara a kunne yana fad'in " ki kyale ni please.
"Wacece zata kyale ka?
Jin muryar Mamanshi yasashi yin murmushi yana gyara zamanshi yace " Deeya.....!, saurin ankarewa yayi dan haka yace " wata ce, zatayi magana Abba ya warce wayar daga hannunta yana fad'in " kai yanzu Ajlaal kayi mana adalci kenan fisabilillahi?
Idanuwanshi ya lumshe ya sake bud'ewa a nutse dan ya riga yasan laifinshi, " akan mace ka sallama mu, tun daga ranar daka rasa Deeyanah shikenan muma ka yafe mu, ace muna gari d'aya amma sai muyi wata bamu saka ka a idonmu ba Ajlaal?
"Kayi hak'uri Abba in sha Allahu zan zo gobe.
Mama ta amshi wayar tana fad'in " me zaka ci na saka a dafa maka?
"Komai ma Mama! " kafa zo d'in please, mik'ewa yayi yana fad'in " zan zo in sha Allah Mama, wayar ya kashe ya saka a aljihun wondonshi ya zari key d'in mota ya fice.
Washe gari yana tashi yayi wanka ya shirya ya fice, minti 18 ne ya sada shi da gidansu, suna jin tsayawar mota suka fito harabar gidan, Mama nata rawar jikin ganinshi bakinta yak'i rufuwa, yayinda Abbah ke tsaye ya zuba mishi ido ganin yadda yayi wani fresh dashi, Mama na rik'e dashi har falo, kallanshi Abbah yayi sosai ya fitar da numfashi yace " Ajlaal!, yadda ya kira sunanshi ba k'aramin karya mishi zuciya yayi ba, a hankali ya d'ago ido ya zubawa Abbah ido.
"Ka sani babu da wani d'an sai kai, kai kad'ai Allah ya bamu balle idan babu kai muce akwai wani Wanda zai d'ebe mana kewa, gashi girma ya kamamu mu duka, lokacin da muka fi buk'atar ka a kusa damu, lokacin da muke buk'atar taimakonka, lokacin daya kamata ace ka karb'i ragamar dukiyata amma a lokacin ne zakayi nesa damu kayi watsi da al'amuranmu akan mace?
Kanshi k'asa yace " wallahi Abbah ba haka bane, " to yaya ne Ajlaal, ai ko babu amfanin da zakayi mana zamu so ganinka kusa damu.
" Kayi hak'uri in sha Allah zan gyara.
" Aikin kenan ayi hak'uri kullum abinda kake fad'a kenan.
" Wannan karon nayi maka alk'awarin zan rink'a zuwa kullum ina ganinku, " to mai zai hana ka dawo kusa damu gaba d'aya?