Sashe 10
Bakar Shuka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Matar tawa zaka tab'a a gaba na dan iskanci?
Jin Deen ya kira Deeyanah da matarshi yasa Ajlaal durk'ushewa k'asa ya kifa kanshi yana wani irin kuka mai gunji, Deen ya rik'o hannun Deeyanah suka bar parlour'n, Abbi da Babah da kowa suka fita suka bar Ajlaal , Alhaji Basaan da Hajiya Halimatu zaune.
" Saika tashi mu tafi asararre lusari wanda ya kasa nemarwa tilon d'ansa aure, dan mutuwar zuciya ka kasa cika masa buri da muradinshi, zungwi-zungwi sumi-sumi ya mik'e ya fita.
*****************************************
Zaune suke a gaban iyayensu anayi musu nasiha kasancewar yaune ranar tafiyarsu, Abbi yayi gyaran murya ya soma magana,
" magana ta farko kuyi rik'o dan Allah da Ma'aiki da addininku, kuji tsoron Allah a bisa dukkan mu'amulolinku,
Ubangijinmu me tausayi ne, idan kaga Allah yana hana maka jin dadin duniya, yana waita maka k'unci da bala'i to ka sani hakika kana da girma a wajen Allah kuma makusanci ne a gareshi,
kuma zai share maka hanya irin ta bayinsa cikakku, Allah baya kyautar duniya ga Annabawansa, ku sani babu wanda yake tausayin bawa sama da Ubangiji,
babu wanda yafi sanin bak'in cikin da kake ciki sama da Ubangijinka, kuma babu wanda yake da ikon yaye maka duk abinda ya dameka face Ubangiji, dan haka mu koma gareshi mu kasance masu neman taimako daga wajenshi a koyaushe,
ku kasance masu yafiya dan zuciyar data kasance mai yafiya mai ita zai kasance cikin salama,
sai hak'uri, hak'uri da juriya sune jigo kuma katangar da take tokare da igiyoyin aure, duk wanda yace bazayyi hak'uri a cikin zamantakewa ba yana tare da babban kalubalen rayuwa,
masu hak'uri kadai ake cikawa sakamakonsu ba tare da hisabi ba, hak'uri da Iyali kauna ce, hakuri da mak'ota dattaku ne, hakuri da jama'a mutunta kai ne, hak'uri da bin dokokin Allah dace imani ne,
duk mutumin daya rungumi d'abi'ar hak'uri to bazai tab'a rabuwa da samun nasara a rayuwa ba, duk da yake nasarar tana iya d'aukar lokaci,
idan kayi hakuri a rayuwa wata rana zaka zama madaukaki akan wadanda suka cutar dakai,
ita duniya gidan hak'uri ce, rayuwa kuma gidan juriya ne, haka duk girman bakin ciki baya tarwatsa zuciyar da akwai Allah a cikinta,
kyawawan dabi'u sune hak'ik'anin kyau ba kyawun fuska ba,
kowanne mutum yana da mabud'ai guda biyu a hannunshi na alkhairi dana sharri, shike zab'awa kanshi k'ofar dazai bud'e da mabud'inshi,
A wajen 'ya mace ba kudi ko tarin abin duniya ne arziki ba, sa'a da miji na gari shine babban arziki, sosai akayi musu nasiha me ratsa jiki, in banda kuka babu abinda Deeyanah keyi,
yayinda Deen kejin kukanta har k'ark'ashin zuciyarshi, har Airport 'yan gidansu suka raka su, dakyar Deeyanah ta rabu da 'yan uwanta.
A daddafe Ajlaal ya shiga gida ya kulle kanshi a d'aki yana rusgar kuka riris kamar mace, kwana biyu yayi a d'aki baci basha, baya magana da kowa,
Tsaye Alhaji Basaan yayi a k'ofar d'akin Ajlaal, sai da ya tattaro gaba d'aya k'arfin gwiwarshi kana yayi knocking,
tare da kiran sunanshi yana fad'in " Ajlaal ka bud'e min k'ofa in har na isa dakai, umarni na baka,
sai da akayi minti d'aya kana Alhaji Basaan yaji sautin key alamar an cire key, amma bai bud'e k'ofar ba, a hankali Alhaji Basaan ya tura k'ofar ya shiga,
halin dayaga Ajlaal a ciki yayi masifar d'aga mishi hankali ya kuma bashi mamaki, dan bayyi zaton yana san yarinyar har haka ba,
fita yayi ya had'owa Ajlaal tea ya dawo ya zauna kusa dashi tare da mik'a mishi kofin,
baya san magana dan haka ya karb'a ba musu, a hankali Alhaji Basaan ya dafashi yana fad'in " kana da hankali kuwa Ajlaal?
"Kana neman kashe kanka a banza a wofi akan mace, macen da tana can tare da mijinta........ bai k'arasa maganar ba yaji tasssssssss glass cup d'in hannun Ajlaal ya fashe,
saurin kallan hannun Ajlaal yayi yanata faman zubar da jini, " please Abba please, kayi shiru...' ya fad'a a galabaice,
Murmushin k'arfin hali Alhaji Basaan yayi yana kallan Ajwaad yace " Idan zuciya ta shiga cikin damuwa da bak'in ciki babu wani abu da zai zame mata nutsuwa da kwanciyar hankali face ambaton Allah
Dole muji babu dadi idan wanda muke so ya rabu damu, amma ba akan wanda ya yaudare mu ba,
rasa abinda muke so nuni ne na cewa rabonmu yana ta can wani wajen yana nemanmu, dan mun fad'i a soyayyar wani ba wai mun rasa soyayya ta har abada bane,
Ba asara bane danka rasa wanda kake so, arasa shine ka rasa kanka wajen kaunar wanda kai a wajensa ba komai bane,
sauk'i yana tare da tsanani, mai hak'uri yana cimma dad'i, mai kyauta baya rasawa, kowa yaji tsoron Allah, Ubangiji zayyi masa mafita, manta da damuwa ka fuskanci rayuwa, kowa ka gani a duniya akwai abinda ya dame shi, duk abinda ka rasa a rayuwa ba naka bane kuma ba alkhairinka bane, rabonka baya tab'a wuce ka.
idan Allah ya k'addara Deeyanah matarka ce ba aure tayi ba, ko mutuwa tayi saika aure ta, wani baya auren matar wani, kamar yadda wani baya haihuwar d'an wani,
sosai Alhaji Basaan yayi mishi nasiha ya kawo mishi misalai da dama, ya bashi shawara ya dage ya cimma muradanshi saboda bai san me gaba zata haifar ba.
***********************************
Tana ta faman sheshshekar kuka bacci ya d'auke ta bata sani, sanyin AC jirgin ya sata shigewa cikin jikinshi batare data sani ba, ta k'ank'ame shi sosai sai faman sauke ajiyar zuciya take yi, fuskarshi d'auke da siririn murmushi ya manna mata light kiss a goshi had'i da k'ara matseta a jikinshi.
K'arfe uku da kwata na dare na k'asar America jirginsu ya sauka a babban birninsu Washington, yaso ya sauko rungume da ita a jikinshi amma ganin ba fuska yasashi hak'ura, yana tafe tana biye dashi har suka fice daga airport, jerin gwanon taxi d'in dake gabansu yabi da kallo kafin ya zab'i d'aya cikinsu ya bud'e mata baya ta shiga kana shima ya shiga bayan me taxi driver ya saka musu kayansu a boot.
Gida ne d'an madaidaici me d'auke da d'akuna biyu kowanne da ban d'aki a cikinshi, sai babban falo da kitchen gidan ya tsaru sosai ga yasha home decor ga flowers kun dai san tsarin gidan turawa, tsaye tayi tana bin gidan da kallo har cikin ranta gidan ya burgeta gashi dai d'an k'arami d'an kijifjif gwanin ban sha'awa, babu abinda yafi d'aukar hankalinta sai barandar waje, d'aya daga cikin bedroom d'in ya nuna mata yana fad'in " ki d'auki wancan bedroom d'in, ni ga nawa can, batayi mishi magana ba ta shige bedroom d'in, d'akin a gyare tsaf kamar da wanda ke zaune gidan, hand bag d'inta ta aje saman wood bed ta zauna tana sauke ajiyar zuciya.
Cikin mutuwar jiki ta mik'e ta rage kayan jikinta ta fad'a ban d'aki, wanka tayi gami da d'auro alwala ta fito d'aure da towel d'in data gani aje a ban d'akin a wanke tsaf, k'ank'antar towel d'in tasa ko mazaunanta bai gama rufewa, gashi baima rutsa ta sosai ba, sai zamewa yake yi, d'an guntun tsaki taja had'i da rolling idanuwanta data tuno bata d'auko kayanta ba, juyawa tayi da nufin fita ya turo k'ofar ya shigo kai tsaye, idanuwanshi suka sauka akanta, yarrr yaji har cikin kanshi, yaso ya d'auke idonshi daga kanta amma ya kasa, itama duk tabi ta rikice tashin hankali bayyane saman fuskarta, sai kokawa take da towel yana zamewa, garin ta kaiwa hijab wawura towel d'in ya zame, naked body d'inta ya bayyana, ido ya runtse da k'arfi had'i da furta "ya Allah, sai da yayi da gaske kafin ya iya saita kanshi, jajayen idanuwanshi da suka rine cikin k'ank'anin lokaci ya bud'e ya sauke mata su a jikinta, wata irin tsuma jikinta ya d'auka saboda tsabar tsoratar da tayi na ganin yadda idanuwanshi suka canja kala, a hankali ya sunkuya ya d'auki towel d'in ya mik'a mata had'i da ficewa daga d'akin.
Bayan ta gama shiryawa, tayi sallah ta jera kayanta cikin wardrobe ta shirya gaban mudubinta ta saita komai, sai da ta samu nutsuwa kana taji yunwa, ga kewa da kad'aici gidansu babban gida ne, mai mutane da yawa nan ko daga ita sai shi, saita jita kamar cikin keji, bak'i ciki yasata fashewa da kuka.
Yana fita daga d'akin ya wuce bedroom d'inshi ya fad'a bathroom ya sakarwa kanshi shower ya dad'e ruwan na sauka kanshi sai faman sauke ajiyar zuciya yake yi, Deen ya kasancewa d'aya daga cikin maza masu matsananciyar sha'awa abu kad'an ke motsa mishi sha'awar shi, sai da d'auki lokaci cikin ban d'akin kana yayi wanka ya fito d'aure da towel a k'ugunshi, har lokacin yana cikin yanayi bawai sha'awar ta lafa bane, wondo ya saka 3 quarter dark blue da rigarshi ya fashe jikinshi da jerin turarurrukan dake kan mudubin shi wanda a k'alla sunyi goma kuma da gani designers ne,
fitowa yayi daga bedroom d'in zuwa falo ya kishingid'a saman sofa yana mayar da numfashi, sautin kukanta ya soma jiyowa kad'an-kad'an daga bedroom d'inta, cikin nutsuwa ya mik'e ya nufi bedroom d'in nata, har ya d'ora hannunshi akan handle d'in k'ofar sai kuma ya fasa shiga ya juya zuwa kitchen bai d'auki lokaci me tsayi ba ya had'a mata shayi me kauri, ya fito hannunshi d'auke da tea cup ya shiga d'akinta.
Tana zaune bakin gado tana ta faman kuka kamar ranta zai fita, ya mik'a mata kofin shayi, hannunshi daya mik'o mata kofin tabi da kallo,
had'i da kawar da kanta gefe tana cigaba da kukanta, akan bedside ya zauna bayan ya ajeyi kofin a gefe, ya rik'o hannayenta cikin nashi had'i da zuba mata ido,
ya dad'e yana kallanta kana ya sauke ajiyar zuciya yana fad'in " dama bakya so na Deeyanah?
" Wannan kuka duk na an aure miki ni ne?