Sashe 50
Bakar Shuka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kowa dake wajen sandarewa yayi a tsaye yadda kasan gawar da aka dasa, babu wanda ya iya motsi balle magana, ya juya ya zai fice daga d'akin Abbi ya zaburo mishi Babah yayi saurin tare shi yana fad'in " aikin gama ya gama ka barshi ya samu nutsuwa kaji dai abinda likita yace, sai a lokacin ya kula da mutanen dake d'akin, cikin matsanancin b'acin rai da zafin zuciya Abbi ya bud'e baki zayyi magana Babah yayi saurin tarar numfashin shi da fad'in " dan Allah karka ce komai yanzu cikin fushi karka k'arasa dagula komai, nasan waye Deen fiye dakai duk da kai ka haife shi, nasan bazai tab'a aikata haka bashi da kwakkwaran dalili ba, tasan masifaffan son da yake yiwa Deeyanah, yasha fad'a min bazai iya rayuwa babu ita ba, yasha fad'a min itace rayuwa shi batare da yayi la'akari da cewar nina mahaifinta ba, ka kwantar da hankalinka abi komai a sannu kar muyi gaggawa.
Kanta ta kifa saman pillow ta fashe da wani irin rikitaccen kuka tana fad'in " na cuci kaina, na lalata komai nawa, babu wanda ya iya furta koda kalma d'aya balle a samu mai rarrashinta.
Saki! Kalmar da take jikinta a bakin wasu, kalmar dako kusa bata hasaso ta a kanta ba, kalmar da tayi yak'ini kan baza'a tab'a furta mata ba, kalmar da take tunanin tayiwa nisan nisa, yau ita aka furtawa kalmar saki!, jin abin take yi kamar almara, jin yanayin take yi, kamar a mafarki, ta kasa gaskata abin, duk da tasan ta cancanci fiye da haka.
A galabaice ya koma gida, part d'insu ya wuce ya shige bedroom d'inshi, babu abinda ya tab'a a gidan sai wasu daga cikin kayan sawarshi ya fice daga part d'in dakyar ya danni kanshi ya koma part d'in Babah, d'akinshi nada ya koma, yana shiga ya watsar da kayan a tsakar d'akin ya zauna ya had'a k'afafuwanshi ya cusa kanshi ciki.
A ranar a daddare aka sallamota daga asibiti, jikin kowa a sanyaye k'afa a sage suka dawo gidan, Ammi taso ta wuce part d'insu amma tak'i tace a part d'inta zata zauna dan tayi zaton Deen nacan, zatafi samun damar rarrashinshi su fahimci juna, da taimakon masu aiki aka gyara gidan tsaf, dakyar Ammi ta matsa mata tayi wanka, abinci kam babu yadda ba'ayi da ita ba amma tak'i cin ko kad'an, dan kar a dame ta, ta kwanta had'i da rufe idanuwanta kamar me bacci, ganin haka yasa kowa ya fice, suna ficewa ta tashi zauna ta fashe da kuka.
Tsakar dare da misalin k'arfe biyu da rabi tana tsaye k'ofar bedroom d'inshi tana shawarwari, tana san ta shiga suyi magana ta fahimta su fahimci juna, tana san ya bata dama ta fad'a mishi komai ta sanar dashi duk abinda ya faru, koda sun rabun tana san yasan ba amanar shi taci ba kamar yadda yake zato, bak'ar k'addara ce wacce mutum bai isa ya tsallakewa tashi ba, takai mintuna 30 tsaye ta kasa shiga, gabanta na fad'uwa ta d'ora hannunta akan handle d'in k'ofar, tana jin tsoronshi sosai amma tsoronshi na wannan lokacin yafi na koyaushe, kodan yanzu akwai kunyarshi da fargaba gami da tashin hankali oho, yawu ta had'iya had'i da runtse idonta da k'arfi ta bud'e k'ofar, wayam babu kowa, a sanyaye ta taka zuwa bathroom dan bata tsammanin zai bar mata gidan ba, nan ma baya nan, ta duba ko'ina baya nan, jikinta na tsuma ta duba wardrobe d'inshi taga ya kusa gwashe kayan sawarshi, sosai hankalinta ya tashi data tanbatar baya gidan, ita kam ta shiga uku yau ina zata saka kanta.
Ana idar da sallar asuba tayi waje dan a tsaye ta kwana Allah Allah ta rink'a yi ayi sallar asuba dan bama zata iya jira gari ya waye ba, tasan muddin yana garin nan bashi da inda zashi daya wuce part d'insu Babah, d'akinshi nada ta nufa, tana murd'a k'ofar tajita a rufe gam, a fili ta sauke ajiyar zuciya kana ta soma buga k'ofar tana kiran sunanshi, while tana kuka kamar ranta zai fita.
Tun tana buga k'ofar a hankali harta somayi da k'arfi tana fad'in " dan Allah Yaya ka saurare ni a karo na k'arshe dan Allah ka bud'e muyi magana ka bani wannan damar please Yaya, yadda take bugun k'ofar da k'arfi tana kuka da iya k'arfinta yasa kowa yasan abinda ke faruwa, dan sautin kukan nata har harabar gidan, Abbi da Babah da Yayyan Deeyanah da gudu suka shigo gidan dan sunyi zaton wani abu ne ya faru, durk'ushe suka sameta gaban k'ofa tana kuka wiwi tana k'oronshi kan ya saurare ta, sosai tausayinta ya kama Ammi da Abbi amma Ammu da Babah ko a jikinsu dan suna da tabbacin koma meye ya faru itace me laifi dari bisa dari, cikin sanyin jiki Ammi da Abbi suka k'arasa inda take, ta d'ago ta had'i da kwantar da kanta a k'irjinta tana shafa bayanta.
D'ago kanta tayi ta saukewa Ammi kumburarrun jajayen idanuwanta duk tabi ta birkice kamar zararriya " Ammi! Abbi dan Allah kusa baki ku rok'or min shi ya saurare ni a karo na k'arshe, ku rok'ar min shi albarmar yin magana dani, zan fad'a mishi komai, zan fad'a mishi gaskiya, dan Allah ya bani wannan damar dan girman Allah, nasan nayi mishi laifi mafi girman muni a duniya, nasani ni me laifi ce, "shhh shhh shh ya isa, ya isa haka, Ammi ta fad'a tana rungume ta dan samar mata nutsuwa.
Babu yadda ba'ayi da Deeyanah kan su tafi in ya huce zai saurare ta ba amma tak'i furrr, ganin haka yasa Abbi k'arasawa bakin k'ofar ya murd'a handle d'in yaji k'ofar a rufe, a hankali Abbi yayi knocking k'ofar yace " Deen bud'e k'ofar nan, shiru babu ko motsinshi, knocking Abbi ya sake yi had'i da kiran sunanshi amma still bai amsa ba, Babah da Ammu dake gefe suka had'a ido, Babah ya k'araso bakin k'ofar shima yayi knocking tare da yin magana amma Deen yak'i amsawa, sosai hankalinsu yayi masifar tashi dan sunyi zaton ba lafiya ba.
"Azan kaida Azran kuzo ku b'alle min k'ofar nan, jin abinda Babah yace yasa Deen yin gyaran murya alamar lafiyarshi lau, "au da kana jin mu amma kayi shiru?
Shiru ya sake yi bayyi magana ba, a hasale Abbi yace " Deen umarni na baka ka bud'e min k'ofar nan yanzu, Deen dake rakub'e can k'uryar d'aki ya d'ago runannun idanuwanshi kamar zayyi magana sai kuma ya fasa, baiko motsa ba balle yabi umarnin Abbi, abinka dama dame bak'ar zuciya, jin shiru ya k'ara hasala Abbi matuk'a ya bud'e baki zayyi magana Babah yayi saurin tarar numfashin shi da fad'in.
"Ka dai san yaron nan me biyayya ne matuk'a ko?
Abbi bayyi magana ba, dan bama shi da niyyar yin magana, Babah ya d'ora da cewa " kamar yadda dukkan mu muka san yana da biyayya sosai haka muka san yana da bak'ar zuciya, a halin yanzu ranshi a matuk'ar b'ace yake, ga zafin rabuwa da matarshi ga rad'ad'in sanadin rabuwar, duk da bamu san dalilin rabuwar tasu ba amma kai da ganin abinda ke faruwa kasan akwai lauje cikin nad'i, dan haka mafi masalaha a halin yanzu a kyale shi karka k'ara mishi wata damuwar kadai ji abinda likita yace ko?
Ajiyar zuciya Abbi ya sauke a fili kana yace " Allah ya kyauta, suka amsa da " Amin.
Dakyar Ammi taja Deeyanah suka bar part d'in, yadda kasan wacce ta haukace haka Deeyanah keyi, tsayin kwana uku kenan kullum sai tazo bakin k'ofar d'akinshi tayi kuka amma yak'i bud'ewa, yayinda shima tunda ya rufe kanshi a d'aki bai fito ba.
A wayewar kwana na hud'u anayin sallar isha tazo ta dasa kuka da magiya a k'ofar d'akin amma shiru, babu yadda ba'ayi da ita ta tashi ba amma ta kafe, dole tasa aka kyale ta a wajen, a k'ofar d'akin ta kwana har garin Allah ya waye tana nan zaune ko k'ifta idanuwanta batayi ba balle tayi bacci yadda taga rana haka taga dare, a bathroom d'in falo tayi alwala ta fito ta dawo k'ofar d'akinshi tayi sallah, haka da azahar tayi, duk abinda tayi idon kowa na kanta, tausayinsu ya kama kowa amma banda Babah dan ya tabbatar akwai wani gagarumin al amari a binne, sallah kad'ai ke tada Deeyanah daga k'ofar d'akinshi.
K'arfe uku na dare ruwan shan shi ya k'are ga matsananciyar k'ishir ruwa data adda be shi, cikin mutuwar jiki ya mik'e ya bud'e d'akin, yana fitowa yayi tuntub'e da ita, kallo d'aya yayi mata ya kauda kanshi babu d'igon tausayinta cikin ranshi saima zunzurutun k'iyayyarta dake ratsa shi, yi tayi kamar tana bacci, yasa k'afa ya tsallake ta, yana barin wajen tayi wuf ta mik'e ta shige bedroom d'in, store ya shiga ya d'ebo ruwa carton biyu da maltina carton biyu da carton d'in madara peak ta ruwa dan su kad'ai yake iya sha, ruwan da madara ya fara d'iba ya fito dasu, dayaga bata wajen bai d'auka ta shige bedroom d'in ba, yayi zaton gajiya tayi dan haka ta tafi, koda ya shiga d'akin ma bai ganta ba, ya ajiye ya koma ya d'auko sauran ya dawo, k'ofar ya mayar ya rufe da key hasken d'akin ya kashe ya koma saman bed ya kwanta idonshi yana kallan pop, dan rabanshi da bacci har ya manta tuni bacci ya k'auracewa idonshi.