Sashe 41
Bakar Shuka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Sune abubuwan da kake amfani dasu wajen tsora ta ni kayi yadda kaso dani ko?
"Ko ba su ba ne?
"Idan sune na riga na sansu har ma na haddace su idan da wasu sabbabi ka fad'e su inji ina jira.
Hak'oranshi ya taune da k'arfi ya juya mata baya had'i da nausar bango da k'arfi ya tako ya dawo gabanta ya kalli cikin kwayar idonta yace " kina wasa da wuta yarinya, kina wasa da rayuwar ahalinki, tsaki taja had'i da jijjiga kanta tace " nace maka na riga na san wad'an nan ka samo wasu sababbi, cikin hargowa yace " baki san da wanda kike san yin wasan mutuwa ba, " waye kai?
"Ina san na san waye kai Ajlaal, uhunnn fad'a min ina jinka, " zan kashe kowa Deeyanah ina fad'a miki kina ganin kamar wasa ne ko?
Cikin masifa da hargowa tace " je ka! je ka kashe su d'in, maza jeka kashe su, ta fad'a tana yarfa mishi hannu, yatsa ya nuna ta dashi ya bud'e baki zayyi magana ta daka mishi tsawar da gaba d'aya d'akin sai da ya amsa " nace maka kaje ka kashe su, tunda rai da rayuwa a hannunka suke kana da iko da su, waye kai da kake tunk'aron datse numfashin wani?
"Kai d'igon maniyyi ne wanda aka halicce shi daga yunb'u (tab'o) wulak'antaccen bawa, wanda shi kanshi bashi da iko akan rayuwarshi balle ta wani, amma kana k'ababar zaka kashe, zaka kashe, to jeka kashe idan kana da iko da rayuwarsu, in banda kai sakarai ne shashasha har ana tunk'aho da kisan kai ne?
"Yadda kake yin tak'amar nan yana bani mamaki nakan ji kamar ka haukace a wasu lokutan, mutumin da bashi da tabbaci akan second d'aya na rayuwarshi, mutumin da bashi da tabbaci akan rayuwarshi, mutumin da bai san yaushe zai mutu ba, bai san a inane zai mutu ba, mutumin da idan Allah mai komai da kowa, wanda ke da ikon akan kowa da komai yaso yanzu anan take kana iya mutuwa amma shinke tak'amar kawo k'arshen rayuwar wasu, Ajlaal Basaan na k'alubance ka idan rai da rayuwar ahalina a hannunta take ina san ka kawo k'arshenta anan take yanzu-yanzu, haka idan rayuwar mijina tana k'ark'ashin ikonka da sarrafawarka ina san akawo min gawarshi yau d'in nan ba sai gobe ba, idan kana da iko da gobe da duniyar gaba d'aya ina san ka fad'a min abinda zai faru nan da awa d'aya a gaba.
Shiru sukayi gaba d'ayansu idanuwansu cikin na juna na wani d'an lokaci, murmushi tayi had'i da hard'e hannuwanta a k'irji tace " bazaka iya ba ko?
" Saboda baka sani ba?
"Bazaka iya ba, saboda baka da iko akan komai da kowa, kai kanka ikon rayuwarka da lafiyarka ake yi, a yanzu idan aka so ana iya kawo k'arshen su, oh! na tuna ashe fa baka da masaniya akan haka, ayya bashi da ilimin addini shiyasa, am pity you, banza wawa dabba d'an akuya fasik'i mazinaci wanda zai iyayin zina da mahaifiyarshi, zaka iya yin goho mahaifinka ya nemeka ta bayanka Ajlaal, tun da kake yin irin wad'annan mugayen kalaman zaka iyayin komai, zaka iya aikata duk wani sab'an Allah dake doron k'asa, banza jahili fajiri, gaka a tsaye haka kamar me hankali ashe banko ne, ina jiranka kaje ka kashe kowan kamar yadda kace Malam Me Rayuwa.
Matsowa yayi daf da ita ya nuna ta da yatsa zayyi magana tayi saurin tarar numfashi, ta nuna mishi yatsa har yana gogar fatar idonshi, idanuwanta sun firfito waje kamar zasu fad'o k'asa tana cije hak'ora ta soma magana cikin zafin rai " zuciya, gangar jiki na da ruhi na sun k'ek'ashe sun bushe k'ayau ta yadda babu wata firgitarwa, tsoratarwa da muzantawar ka da zasuyi tasiri akai na, ka sani duk abinda zakayi komeye shi wallahi tallahi bazai tab'a sawa na waiwayi gurb'atacciyar rayuwar da mukayi a baya ba, babu wani abu da zayyi tasiri akaina Ajlaal babu shi, koda duniya da abinda ke cikinta zaka cinnawa wuta kowa ya mutu.
" Kinyi ganganci Deeyanah, kin tafka babban kuskuren yin jayayya dani, cikin hargowa da d'aga murya tace " fita! yatsa ya nuna mata zayyi magana ta runtse idonta tare cewa " out! da k'arfi sai da d'akin ya amsa, yatsa ya k'ada mata a fuska gami da cije leb'enshi na k'asa yayi kwafa ya juya, har ya kai bakin k'ofa zai fice ya juyo tare da fad'in " na baki nan da kwana biyu zan jira jin abinda kika yanke, bai jira jin abinda zata ce ba ya fice.
Durk'ushewa tayi a k'asa hannunta d'aya saman gado ta saki rikitaccen kuka.
Yana ficewa daga d'akin ya haura katanga ya fice daga estate d'in gaba d'aya batare da wani ya ganshi ba, sai da yayi 'yar tafiya kana ya k'arasa inda ya aje motarshi, ya bud'e mazaunin driver ya shiga ya zauna, ajiyar zuciya ya sauke a fili tare da shafo kanshi tun daga k'eyarshi zuwa fuskarshi, tana neman saka mishi ciwon kai, ya rasa dalilin sauyawarta har haka, ya rasa meyasa take da taurin kai da kafiya, ya rasa me ya haifar da hakan, a yanayin yadda ya karance ta idan kashe ta zayyi ta hanyar yankar naman jikinta bazata tab'a yarda ta dawo mishi ba, daga maganganun bakinta ya samu tabbacin komai ya k'are ya san idan bai dage yayi da gaske ba yana iya rasata ma.
Sitiyari ya nausa da k'arfi har ya danne horn, horn d'in ya cika unguwar, tsaki yaja a fili tare da tallafe kanshi, ya dad'e a haka kafin yaja motar ya bar wajen.
Tana zaune a falo tana kallan wa'azin Sheik Isah Ali Pantami a sunna Tv kujerar dake gefe ya zauna Tv ya kalla ya d'an tab'e baki had'i da cewa " ba sauraron ba Allah yasa ayi aiki dashi, juyowa tayi ta d'an kalle shi kana ta mayar da idonta kan Tv, duk da bai san abinda ya faru ba amma wata irin muguwar kunyar shi da nauyinshi take ji, ko alamun shi taji sai gabanta ya yanke ya fad'i balle kuma ta ganshi, yanzu ma tunda ya zauna gabanta ke lugudan fad'uwa, idonta nakan TV amma bata iya fahimtar komai, batare daya kalle ta ba yace " idan kina da buk'atar wani abu kiyi min list idan kuma kud'in zan tura miki to!, shiru yayi yana jiran amsarta na wani d'an lokaci, jin batayi magana ba yasa shi mik'ewa yabar wajen tabi bayanshi da kallo kwalla na zuba.
"Haka na cuci kaina na lalata rayuwar gida na da ahalina?
"Haka na mayar da gidan aure na tamkar gidan zaman makoki?
"Ni da mijin aure na mun zama tamkar bak'in juna, kamar wad'anda akayiwa auren dole, sai kace ba auren soyayya mukayi ba, yana so na ina sanshi, sai kace wad'anda sukayi auren k'iyayya, na shiga uku, wayyo ni kaina na lalata komai, babu abinda zai gyaru, ta k'arashe maganar da firgitaccen kuka mai razana zuciya.
Ranar komai sabo ya dawo mata fil haka ta kwana cur saman sallaya tana sharb'ar kuka kamar wacce ake zarewa rai, ta manta yaushe raban da taga dariya da murmushi akan fuskar Deen, raban data ganshi cikin walwala da fara'a har ta manta, bazata iya tuna ranar k'arshe da sukayi hira cikin so irin na ma'aura ta ba, ta san yayi mata mugun hak'uri, yayi mata kara da kawaici, yayi juriya da kawar da kai, duk wani hak'uri da miji zayyiwa matarshi tasan yayi mata, duk uzurin daya kamata miji yayiwa matarshi yayi mata.
"Yayi k'ok'ari ma, yayi min duk abinda miji zayyiwa matarshi, yayi min abinda wa zai yiwa k'anwarshi kai har abinda ya kamata uba yayiwa 'yarshi Deen yayi min, ya rufa min asiri bai tab'a fad'awa iyayenmu halin da ake ciki ba, shekararmu biyu zuwa uku bama sex wanda shine gundarin auren, babu wata alak'a dake alak'anta ma'aura ta dake shiga tsakaninmu har tsayin kusan shekaru uku, amma duk da haka bai tab'a kai k'ara ta wajen iyayenmu ba, babu wanda zai so ni kamar ka, babu wata soyayya da zan samu dake saman taka a fad'in duniya, kai cikekken masoyi ne na gaskiya abin tunk'aho, kai miji nagari ne burin samun kowacce d'iya mace, ka cika masoyi, bani da abinda zan biyaka dashi bani da abinda zan saka maka dashi.
"Nayi maka butulci Deen, nayi maka muguwar sakayya, na cuce ka, naci amanarka har a gidanka a d'akinka akan gadonka na aure na kawo wani k'ato da bai biya sadaki na ba ya kwanta dani, na cuci rayuwa ta, nayiwa kai na babbar illa, idan baka yafe min ba hakk'inka zai ta bibiyata yana wahalar dani har zuwa k'arshen rayuwata, alhakinka ba bazai daina farautar farin ciki da walwala ta har izuwa fitar numfashi na na k'arshe ba, ka yafe min Deen, ka taimaka ka yafe min in baka yafe min ba nasan mummunan k'arshe zanyi da zai zamewa wasu Izzina, wani irin kuka take yi me gunji wanda ya cika gaba d'aya d'akin.
Kofin tangaran d'in hannunshi ya d'aga ya buga a window ji kake tasssss sun rotse gaba d'ayansu, baya yin shaye-shaye bai tab'a shan d'igon wani abu na maye ma, amma idan ka ganshi sai ka rantse babu abinda bai sha ba a halin da yake ciki ba, ya birkici ya haukace yadda kasan wanda ya gudo daga asibitin mahaukata, nishi yake yana haki kamar wanda ya kwana yana aikin k'arfi, wani iri yake ji a jikinshi zuciyarshi kam tamkar an zazzaga mata fetur an kesta ashana, gaba d'aya duniyar tayi mishi zafi, komai ya fice mishi a rai, haushin kowa yake ji, ji yake kamar ya zazzaga fetur ya k'ona kanshi ya huta da azabar da zuciyarshi keyi mishi, Bluetooth d'in dake kunnenshi ya zare yayi wurgi dashi, yaji duk abinta tace kaf.
"Ni ne k'aton banzan?
Ya fad'a kamar yana magana da wani, "ni Deeyanah ke jefa da wad'annan maganganun akan Deen?
"Wato yama fini sanki?
"Soyayyarshi itace abin kambamawa ba tawa ba, tawa ta zama ta banza?
"Soyayyarshi itace ta gaskiya tawa ta k'arya?
"Zan tabbatar miki da duk duniya nafi kowa sanki Deeyanah, zan tabbatar miki baki da masoyi kamar ni.