← Book details Bakar Shuka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 48 OF 56

Sashe 48

Bakar Shuka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wani abu ya wulla mata a cikin kwali, kwalin na fad'uwa ya rabe biyu kan mutum ya mirgino zuwa gabanta kallan abun tayi taga kan wannan mutumin ne daya zuba mata ruwan tsami a jiki ya kuma tofa mata yawu, ko gezau Deeyanah batayi ba balle tsoro ko firgici ya bayyana a tattare da ita, kallan kan mutumin tayi had'i dayin tsaki tasa k'afa tayi ball da kan ta juya ta gyara kwanciyarta tana fad'in " ni ai yanzu naci dubu sai ceto babu wata gawar da zata razana ni, ta rufe idonta da nufin yin bacci amma sai me?

Ranar da komai ya k'are mata a rayuwarta, duniyarta ta tarwatse, farin ciki da walwala suka yanke mata ta shiga dawo mata cikin kwayar idanuwanta.

Waiwaye....

Wayar ta data dame ta da ringing ta d'aga kamar jira yake ta d'aga ya kwashe da mahaukaciyar dariya yana fad'in " tik tok tik tok rana bata k'arya sai dai uwar d'iya taji kunya, yau ne adadin kwanakin dana baki zasu cika cif-cif ina fatan kin shiryawa komai, kin shiryawa tarbar aradu daka?

Zatayi magana yayi saurin cewa har yanzu kina da sauran 10 second, so mu irga tare, amma ki sani idan har sakanni goman nan suka cika batare da kin d'auki zab'in daya danace ba har ki mutu kina danasani, so mu fara irgawa 10,9,8,7,6,5,4,3,2,1,0 ....., sai kawai ji tayi ya kashe wayar, wayar ta zame daga kunnenta ta zubawa ido kamar tana jiran wani abu ya fito ta cikin wayar.

Yana tsaye gaban mudubi ya fito daga wanka k'ugunshi d'aure da towel ya matsi lotion zai shafa a fuskarshi wayarshi ta d'an yi k'ara alamar shigowar sak'o kallan wayar yayi haka nan yaji gabanshi yayi muguwar fad'uwa, d'auke idonshi yayi daga kan wayar ya cigaba da abinda yake yi, har ya gama shiryawa bai sake bi takan wayar ba danshi yama manta da shigowar sak'on, jallabiya ya zira, har ya kai bakin k'ofa zai fita wayarshi ta sake yin k'ara a karo na biyu, sai lokacin ya tuna da wayar, komawa yayi ya d'auki wayar yana nufar k'ofar fita daga bedroom d'in yana duba sak'on daya shigo, video aka turo mishi ta WhatsApp da wata new number, video ya danna yayi playing, videon ya bud'e dai-dai lokacin daya d'ora hannunshi akan handle d'in k'ofa.

Tun daga kan k'afafuwanta aka soma hasko ta, hakan ya sashi tsayawa cak batare daya fita ba, macece kwance tsirara sanb'al akan gado, " subhanallah! yace yana kawar da idonshi, yana yawan jin labarin irin mutanan nan masu turawa mutane blue film ta WhatsApp bai tab'a yarda ba sai yau daya faru a kanshi, tsaki yaja yana fad'in " Allah ya kyauta, idonshi ya sauke akan wayar dai-dai sanda aka hasko fuskar Deeyanah kwance shame-shame tsirara haihuwar uwarta.

Wani irin mugun shock yaji tun daga kan babban d'an yatsanshi zuwa tsakiyar kanshi, ji yake kamar ana tsistsinka mishi jijiyoyin jikinshi, wayar yake so ya saki amma yadda kasan an saka gam an lik'e ta da jikinshi, kokawa ya shigayi da numfashin shi dake neman kwace mishi, batare daya sani ba wayar ta sub'uce daga hannunshi ta fad'i k'asa, baya yaja a mugun tsorace, idanuwanshi sunyi k'uru-k'uru tamkar wanda akayiwa turaren barkono, duk da wayar ta fad'i k'asa videon bai tsaya ba ya cigaba da yi, take komai nashi ya tsaya mishi cak, babu abinda ke aiki a jikinshi, bai san yadda akayi ba sai tsintar kanshi yayi zube k'asa wanwar a tsakiyar d'akin, saboda tsabar rud'ewa yana zaune a wajen amman ji yake kamar ruhin shi ya fita daga jikinshi shine ya koma gefe suna kallon videon tare.

Deeyanan shi matarshi ta sunna wacce ke d'auke da igiyoyin aurenshi itace wani k'ato da bai biya sadakinta ba yake sassak'a, tamkar wanda aka kafe idonshi akai, dakyar ya iya d'auke idonshi daga kan video, kaf-kaf jikinshi ya d'auki muguwar rawa kamar mazari, wani irin sanyi yake ji aduk wata k'ofar gashi dake jikinshi, tamkar yadda tangaran yake tarwatse haka wani abu me nauyin gaske ya tarwatse a zuciyarshi wanda yake da yak'inin har abada bazai tab'a dawowa dai-dai ba, ta cikin kunnenshi yake jiyo sautin tsistsinkewar jijiyoyin kanshi, kanshi dake barazanar tarwatsewa ya dafe da duka hannayenshi ya kurma firgitaccen ihuuu, jikinshi a sake ya mik'e sakaka, yadda kasan me koyan tafiya haka yake taka k'afufuwan ya isa gaban mudubi ta cikin mudubin yake kallan kanshi tamkar hannunshi ba'a jikinshi yake ba ya d'aga tare da nuna kanshi ta cikin mudubin muryarshi na sark'ewa yace " nine Deen kuwa?

" Anya nine dai?

Ya fad'a kamar zararre, hannunshi ya cusa cikin gashin kanshi ya runtse idanuwanshi da k'arfi ya shiga kurma ihuuun mutuwa, glass center table d'in dake tsakiyar d'akin ya d'auka ya jifi mudubi dashi gaba d'ayansu suka tarwatse, yana cigaba da kurrma ihuuu ya rink'a dukan mirror'n jikin wardrobe, duk da ciwon dayaji a hannunshi hakan bai sa ya daina ba, cikin k'ank'anin lokaci ya birkita gaba d'aya d'akin ya fashe komai dake cikin bedroom d'in, zamewa yayi ya durk'ushe akan gwiwowinshi, kuka yake san yayi koya samu sauk'i da sassaucin abinda yake ji amma yadda kasan an busar da idanuwanshi ko alamun kuka babu.

Gidan yayi mishi bak'ikk'irin komai yayi mishi duhu, ji yake an mak'ure shi, ji yake ta ko'ina a takure yake, Babah yake san gani, Baban kad'ai zai gani yaji 'yar dama-dama, kamar wanda aka tsikara da allura yayi zambur ya mik'e ta kan gilasan daya fasa yabi ya taka wuce yaji ciwo sosai amma bai damu ba, ya fice babu ko takalmi, jijiyoyin kanshi runyi rad'o-rad'o kamar an zana su, motar da yayi parking ya shiga ya figeta ko get d'in bai tsaya an bud'e mishi ba yayi ciki da get d'in ya fice, me gadi da sauran ma'aikatan sukayi cirko-cirko suna ganin ikon Allah ga get an b'alla.

Babu abinda yake gani a gabanshi sai duhu ikon Allah ne kad'ai yakai shi babban kamfaninsu, hand break yaja ya tsaida motar ya fito bai tsaya rufe ta ba yayi ciki, direct office d'in Babah ya wuce, yana zaune yana cike wasu takardu Deen ya shigo kamar an jeho shi, kallo d'aya yayi mishi ya san akwai gagarumar matsala, gabanshi na fad'uwa ya mik'e da sauri ya tako wajen Deen, zubewa Deen zayyi a k'asa Babah yayi saurin tallafe shi yana fad'in " Lafiya Deen?

Baki ya bud'e da nufin yin magana amma ya nemi muryarshi ya rasa, yayi-yayi yayi magana amma ya kasa, ji yayi an shak'e mishi mak'ogwaro, bakinshi ya k'afe, zuciyarshi ta soma bugawa da tsananin k'arfi kamar zata tsaga k'irjinshi ta fito, kanshi yayi mishi mugun nauyi kamar wanda aka d'orawa dakon duniya, jinshi yake kamar a saman iska a zaune, saboda tsabar tashin hankali har yaji-yaji yake ji a idanuwanshi, fatar jikinshi kam rad'ad'i take mishi kamar ya shafa attaruhu, bakinshi ya sake bud'ewa da nufin yayi magana amma yaji numfashinshi na neman d'aukewa nan fa ya shiga kokowa da numfashinshi, yasa hannayenshi duka ya rik'e wuyanshi, office d'in ya shiga juya mishi, yayinda da idanuwanshi suka zazzago sukayi jajir kamar gauta, d'if numfashinshi ya d'auke, kafin yaji an d'aga shi sama an fyad'a da k'asa, wata irin rawa duk ilahirin jikinshi ya d'auka idanuwanshi suka kakkafe kamar me farfad'iya.

Salati Babah yayi yana jijjiga shi gami da kiran sunanshi amma shiru, da sauri  ya fita ya nemo taimakon wasu daga cikin ma'aikatan kamfanin aka sakashi a mota sai asibiti, Emergency aka shigar dashi, sai da aka d'auki lokaci kafin likita ya fito.

" Mugun Shock ya samu wanda ya haifar mishi da hawan jini sosai lokaci d'aya amma yanzu komai yana under control in sha Allah.

" Shock?

Babah ya fad'a cikin matsanancin mamaki, " eh! amma an kaishi d'akin hutu muje na nuna maka d'akin, batare da ya sake cewa komai ba yabi bayan likitan, har k'ofar d'akin ya raka shi " yana ciki, idan ya farka ka kira ni, jikin Babah a sanyaye ya amsa da to, bai san dalilin dayasa gabanshi yake fad'uwa ba, zama yayi a akan sofa yana kallan Deen dake wahalallan baccin dole sai sauke ajiyar zuciya yake yi cikin baccin, kusan awa biyar Babah yakai yana jiran Deen ya farka amma har magariba bai farka ba, mik'ewa yayi dan yaje masallaci yayi sallah.

Yana fita Deen ya farka dishi-dishi yake ganin komai, a hankali ya dafa kanshi komai na dawo mishi, sai a lokacin ma ya tuna ainahin abinda ya gani a video, sai lokacin yake ganin komai tarrr, cikin kanshi yake hasko hotan Ajlaal kwance saman ruwan cikinta, k'arin ruwan ya fisge jini yayi tsartuwa daga jijiyar hannunshi, bai kula ba ya mik'e ya fita har lokacin dishi-dishin yake gani, yana tafe yana tangal-tangal kamar mashayi.

Me adai-daita sahu ya tare ya shiga, dakyar ya fad'a mishi inda zai kaishi, sauka yayi ya shiga gidan yana fad'awa me gadin " ka sallame shi, bibbiyu yake ganin komai, tana zaune bakin gado duniyar tayi mata zafi saboda ta jiyo ihuunshi kuma bayan fitarshi taje ta dubo dakin taga yadda ya tarwatsa komai, a d'osane take zaune a bakin gadon a matuk'ar tsorace take, banko k'ofar da yayi ne ya sata mik'ewa zumbur, had'i da fashewa da rikitaccen kuka tana fad'in " dama na fad'a maka Yaya, na fad'a maka da kaina da baki na amma kak'i yarda dani, ganin yadda ya koma cikin yini d'aya ba k'aramin firgita tayi ba, baya ta soma ja tana girgiza kanta.

Yana d'ora idonshi akanta yaji wata irin muguwar tsana da k'iyayyarta na ratsa shi, lokaci d'aya yaji babu abinda ya tsana a duniya sama da ita, duk wannan tarin soyayyar da yake yi mata babu d'igonshi, kallanta yakeyi kamar bak'in kumurcin daya kashe mishi iyaye.

Muryarshi na creaking yace " meyasa Deeyanah?

"Meyasa kika k'aurace min tsayin shekaru uku kika hana ni hakk'i na kika je kina bawa wani k'aton banza can?

"Why Deeyanah?
Chapter 48 · 0% Book details