Sashe 28
Bakar Shuka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kamar baya san yin magana yace " muna san junanmu mana, kina so na, kuma ke kanki shaida ce akan irin san da nake yi, so why not bazamu fito da soyayyarmu fili dan muci ribarta ba, meye amfanin soyayya idan babu aure?
"Gaskiya ni dai a'a, a nutse kamar yana kallanta yace " meye a'a d'in Deeyanah?
"Bakya so na ne, ko bazaki iya aure na ba?
"Tab tashin hankali, ta fad'a tana fitar da numfashi kafin ta d'ora da "Ka rufa min asiri karma ka soma tunanin fito da maganar nan yanzu.
"Hmmm naji to!, tace " yauwa, tana sauke numfashi, sai da ya gyara zama yace " yaushe zamuje gidan Aunty me kayan mata mu siyo ne, d'an shiru tayi kafin tace " ka bari sai nan da next week dan yanzu ma idan nace zan fita baza'a barni ba cewa za'ayi daga dawowata daga asibiti zan fara fita, " ok ba damuwa Allah ya kaimu.
Shi ko Deen da tunani Ammi ta barshi, ya rasa meyake damun Deeyanah ya rasa dalilin sauyawarta da yawa haka, wasu lokutan yasha tambayar kanshi ko shine ya sauya ba ita ba, ko shine keda matsalar data sanya ta sauyawa dole, yasha bincikar kanshi ta fannoni da dama, yasha tambayar kanshi menene gazawarshi a matsayin miji ko uba amma ya rasa yana san ya sameta suyi magana face to face ta fahimta amma tak'i bashi dama balle lokaci, so da dama yana fahimtar idan ya kirata a waya tana amsa mishi a dak'ile kamar ma ya matsa mata shiyasa ya daina sai lokaci zuwa lokaci, Families sun sha tambayarshi yaushe zai dawo har ta kai ga sun fara matsa mishi kan ya dawo kusan kullum sai sunyi mishi maganar dawowa dai-dai da Deedee duk sanda zasuyi magana dashi sayya cewa " Daddy ka dawo Ina san ganinka I missed you, amma banda Deeyanah ko sau d'aya bata tab'a cewa ya dawo ba, bata tab'a nemanshi ba, bata tab'a cewa tayi kewarshi ko kewar wani abu nashi ba, ai ko irin maganganun sex da irin yadda tayi kewar sex da sauran su tayi mishi amma shiru, ganin tunanin bazai kai mishi ba ya sashi mik'ewa ya shiga bathroom ya d'auro alwala ya tada sallar mafila kasancewar su can tsakar dare ne.
****************************************
Ajlaal da Deeyanah kam likkafa taci gaba dan har cikin Niger suke shiga neman maganin mata, sune Sokota, Zamfara, Katsina kai har Neja k'asar nufawa suke tsallakawa sai dai duk inda zasu je a jirgi suke zuwa dan basa kwana ranar suke zuwa su dawo ranar, babu abinda suka aje sai sex su dai ayi sex kawai aji dad'i, kullum suna manne da juna kamar cingam, sun yiwa junansu mummunan sabo da juna ta yadda ko bacci basa iyawa sai rungume da juna.
Wannan kenan.....
Cigaban Labari.....
Ihuuun yara da taji akanta suna fad'in " mahaukaciya 'yar macukule! mahaukaciya 'yar macukule!! ya dawo da ita cikin hayyacinta tayi firgigit ta dawo daga duniyar tunanin rayuwarta ta baya data tsunduma, kafin tayi wani yunk'uri dutsen da d'aya daga cikin yaran ya jeho ya sauka a saman goshinta, take goshin ya fashe jini ya soma zuba, ta sanya hannu ta dafe wajen had'i da mik'ewa ta soma tafiya danta bar wajen, ta yanki daji danta nisanta kanta daga duniyar mutane, gwara ta shiga daji wani naman dajin ya cinye ta data rink'a ganin wulak'anci da kyama wajen mutane bil Adama 'yan uwanta, babu irin tozarci da wulak'anci gami da cin mutuncin da bata gani ba a rayuwarta ta duniya ba, ana cewa Wata Shari'ar sai a lahira ita kam taga tata sakamakon shari'ar tun a duniya, yau ita Deeyanah Abduljalal ce ta k'are haka, lalle rayuwa tayi mata gwatson kenwa, duniya tayi mata atishawar tsaki, tasan har yau bata gama girbar bak'ar shuka data tayi ba, tasan da sauranta dan baici ace ta gama girbar abinda ta shuka ba.
Ta zama BAK'AR SHUKA... me fidda bak'in tsiro, bak'ar shuka d'an itaciyarta baya ciyuwa dan d'aci da bauri koka tauta saika furzar, ta zama bak'ar shuka da babu mahaluk'in da zai rab'e ta balle ya zauna a inuwarta, bak'ar shuka da babu me amfanarta, bak'ar shuka babu wanda zayyi marmarin irinta belle ya shuka....
Yuuuuu yaran suka bita suna yi mata ihuuun mahaukaciya 'yar macule wasu na jefanta da duwatsu wasu na d'ibar k'asa suna watsa mata, kwalla ta goge tana d'an gudu danta nisanta kanta da yaran, wani mutum dake tahowa ta hanyar data biyo ya k'araso wajen da hanzarinshi ya d'auki d'an icce ya kora yaran suka watse suna ihuuu, ya dawo inda take yace " sannu baiwar Allah, yayi maganar yana d'an ja baya cike da tsoron ko mahaukaciyar ce da gaske, yadda yayi yasata yin murmushi batare datace mishi komai ba ta wuce, wata irin dariya taji da gaba d'aya dajin sai da ya amsa kana aka ce " kin jawo mishi mutuwarshi Deeyanah, da sauri ta juyo sauke idon da zatayi taga mutum kwance shame-shame cikin jini, ta d'an ja baya hawaye na zubo mata tace " banyi mishi magana ba, murmushi kawai nayi mishi.
Dariyar aka sake yi a karo na biyu had'i cewa " murmushi fa kika ce Deeyanah?
"Ai gwamma kiyi mishi magana sau dubu da kiyi mishi murmushi, ki ta jawa mutane mutuwa ni kuma nayi miki alk'awarin zanta kashe su kamar kiyashi, bazan tab'a gajiya da kashe su ba, hawayenta ta goge tana fad'in " ka cigaba da tsinke numfashin bayin Allah, Ubangiji yana madakata yana jiranka, shikenan ace mutum ko taimako na yayi saika ga bayanshi?
"Ba dama a taimake ni ko a nuna tausayawa a gare ni?
"Ai baki cancanci taimakon kowa da tausayawa daga wajen kowa ba Deeyanah, gwara ki azabtu kamar yadda kika azabtar da wasu bayin Allah, gwara kema ki d'and'ani abinda suka d'and'ana, muguwa, azzaluma, macuciya, mayaudariya Allah ya isa tsakanina dake kan lalata min rayuwar da kikayi, kin tarwatsa gobe na, kin lalata duniya da lahira ta, tayaya kike tsammanin zan barki ki rayu cikin salama da kwanciyar hankali?
"Cikin matsanancin kuka tamkar ranta zai fita tace " naji nayi duk abinda ka fad'a, na aminta duk abinda ka fad'a gaskiya ne ban k'aryata ka ba, amma na baka hak'uri ai, na nemi yafiyarka, kuma kaima ai ka rama duk abinda nayi maka ka rama har ma ci riba sosai, dariya yayi yace " da saura dai yarinya ki jira duka-duka me akayi da maza?
Zatayi magana ya juya mata baya yabar wajen tana kallanshi har ya b'ace, yau kwananta biyu kenan ko ruwa bata sha ba, yunwa ta gama kwak'uleta takai k'arshe ta yadda dakyar take iya jan k'afarta ta galabaita sosai, fasa shiga dajin tayi danta san idan ta shiga babu inda zata samu abinci, ta biyo titi tana tafiya tana had'a hanya kamar wacce tasha kwaya, a haka ta isa shagon me siyar da abinci, ta d'an tsaya nesa da rumfar me abincin tasan idan ta matsa korota zasuyi saboda tsananin warin da take yi, mutane maak'il da wajen amma babu wanda ya kula dasu ita da tarin al'majiran data iske a wajen, tana nan tsaye wani yaci abincin ya rage fiye da rabi, da gudu suka zuba ita al'majiren suna rige-rigen d'auka Allah ya bata sa'a ta d'auka, ta dumama hannu ta cika bakinta fall ta k'ara cika hannu ta tura, ta shak'e sosai amma ba halin ta tsaya dan idan ta sake ta tsaya wawashewa zasuyi su barta, haushin ta wawashe abincin yasa wani almajiri kwana mata robarshi aka, sauran almajirin suka saka wawa, daga ita harsu duk wawar suke, dakyar ta samu tayi loma uku, dayake almajirai ne basu damu da warin da take yi ba, itama bata damu da k'arzuwar dake jikinsu ba.
Bata bar wajen ba sai dare aiko ta cika cikinta fall tasha ruwa ta juya zata bar wajen almajiran suka zagaye ta, dukkansu babu wanda ya haura shekaru goma sha uku zuwa sha hud'u, d'aya daga cikinsu ya d'aga robarshi ya sake kwad'a mata aka da k'arfi ya d'ora da " daga yau idan muka sake ganinki anan sai jikinki ya gaya miki, shegiya 'yar iska fice ki bamu waje kin zo duk kin wawashe mana abinci, ba musu ta juya tabar wajen batare data ce musu komai ba.
Cikin makarantar Primary ta lallab'a ta shiga batare dame gadin makarantar ya ganta ba, cikin sand'a ta isa bakin famfo, ta zagaya ta samu tsohun bokiti duk ya fashe sai data karkata shi gefe kana ta samu ruwa ya zauna ciki, waigawa gaba da bayanta tayi taga babu kowa dan haka ta cire kayanta ta diddirzasu haka babu sabulu ta wankesu, ta sake tarar ruwan ta watsawa jikinta, ta wanke bakin, tayi walwala ta d'an jira kayan suka bushe ta mayar jikinta, d'aya daga cikin ajujuwan makarantar ta shiga tayi sallah ta kwanta, bata dad'e ba wahalallan bacci yayi awon gaba da ita, sai firgita take yi cikin baccin tana sauke ajiyar zuciya.
Bata farka ba har garin Allah ya waye Allah ya taimaketa yau asabar da d'alibai sun cimmata, famfon ta koma tayi walwala tayi sallah kana ta sad'ad'a ta fice, hanya ta sake bi d'od'ar bata san inda take nufa ba, har azahar tayi, ta isa gefen wata me siyar da awara da dankalin hausa ta zauna daga d'an gefenta, har yamma tana zaune gefen me soya awarar, tausayinta ya kama yarinyar ta zuba awara biyar dankalin hausa biyar a leda da yaji da kabeji ta mik'a mata, jikin Deeyanah na rawa da tsuma ta mik'e ta amsa ta koma ta zauna ta cinye tas yarinyar ta sake mik'a mata ruwan sanyi ta amsa ta shanye ta yar da ledar tabar wajen tana tsoran tayi mata godiya ya kashe ta, yarinyar tabi bayanta da kallo cike da tausayawa, ganin yamma tayi kuma bata da wani wajen kwana yasa Deeyanah juyawa ta koma makarantar data kwana jiya.