Sashe 13
Bakar Shuka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Da hannunta ta nuna mishi mararta while tana jujjuya kanta saboda azaba, jallabiya ya zira da sauri, ya sunkuya da nufin d'aukarta,
da hannu tayi mishi alamar a'a, " please ki bari mu tafi asibiti, agogo ta kalla 2:30am na dare, shima agogon ya kalla danya gane nufinta,
" na sani dare yayi, amma bakomai, dakyar tayi k'arfin halin cewa " ka bari ya lafa, zanyi bacci gobe maje, " kin tabbatar LOML! kanta ta d'aga mishi alamar eh,
tallafe ta yayi ya kwantar da ita akan gado yaja mata bargo ya rufeta, cikin ikon Allah bacci me nauyi yayi gaba da ita,
da wuri ya tashi ya had'a mata ruwan wanka, ya dafa mata tea, dama Deedee yana part dinsu Babah, da salati a bakinta ta tashi, idonta ya sauka akanshi, suka sakarwa juna k'ayataccen murmushi,
" harka tashi?
Tayi maganar tana murza ido, " ba dole na tashi da wuri na shirya zuwa asibiti ba, " asibiti kuma?
Kallan da yayi mata yasata yin dariya tace " au ashe fa bani da lafiya ko?
Ta fad'a cike da tsokana, " au ashe ne ma ko?
" Kodan bake ke jin zafin ciwon ba?
" Oh! haka ne fa ko?
"Zafin a jikinka yake shiyasa bana ji, hancinta yaja yana dariya yace " tashi kiyi wanka muje kiga likita, " meeting d'inka fa?
Kanshi ya dafe yana koikwayon muryarta yace " au ashe fa ina da meeting ko?
Sosai ya bata dariya danta gane ramawa yayi, " Allah naji sauk'i kayi tafiyarka ba damuwa,
" kinga tashi ki shirya mu tafi, yayi maganar yana d'agota, cikin shagwab'a tace " Allah na samu sauk'i, kayi tafiyarka, turata yayi cikin ban d'aki yana dariya,
ta gama shiryawa tsaf, cikin shirinshi ya kalleta ya lumshe ido had'i da rausayar da kanshi, cikin sanyin murya yace " masha Allah, Ubangiji yayi halitta a wajen nan,
ta cikin mudubi ta kalleshi a nutse tace " Yaya kayi tafiyarka meeting d'inka wallahi jikina da sauk'i, idan ka matsa sai naje da kaina kai kayi tafiyarka,
ido ya zaro yana takowa gareta yace " na barki kiyi me?
"Allah Dee! da gaske nake, damma ka matsa ne zani, amma badan haka ba, da babu inda zani, dakyar ta shawo kanshi ya yarda zaje meeting ta tafi asibitin da kanta,
har bakin mota ta rakoshi tana d'auke da briefcase d'inshi, ya shiga ya zauna a mazaunin driver ya kalleta yana murmushi yace " kodai zakije ki d'auko hijab na kaiki da kaina inyaso saiki dawo,
motar ta rufe mishi tana dariya ta juya da gudu zata koma gida danta san idan ta biye mishi saisu kwana anan,
bayanta yabi da kallo yana murmushi, kanshi ya girgiza tare da yiwa motar key, harya kai bakin get zai fita ya tsaya had'i da kwala mata kira,
" Deeyanah!, ta juyo tana dariya, ya d'aga mata hannu yana murmushi yace " ki kula da kanki please, an na baki amanar kanki, dan haka nan yaji jikinshi wani iri shiyasa hankalinshi yak'i kwanciya,
tana dariya ta shige part d'insu.
Hijab ta saka ta zari handbag da key d'in mota ta fice, part d'in iyayensu ta shiga ta gaidasu, ta sanar dasu zata asibiti bata jin dad'i,
ganinta da Hijab yasa Deedee sanya kuka yana fad'in " Momy zan biki, kanshi ta shafa tana murmushi ta kasa cewa yazo su tafi tare, saboda kunyar iyayensu,
ganin basu ce ta tafi dashi ba, gashi yana kuka yasata zama, ta kasa tafiyar, " kikace asibiti zaki?
Cewar Babah, Ammi data gane meyasa tak'i tafiya tayi murmushi tana cewa " barta fasawa tayi saboda d'anta yana kuka bazata iya tafiya ta barshi ba, da sauri ta mik'e ta fice tana dariya cike da kunya, suma dariyar suke mata, Babah yace " rabu da ita zo ki d'auki d'anki,
tana cigaba da tafiya tace " a'a nifa ba haka nake nufi ba, ta k'arasa maganar tana shigewa mota, ta fice, tunda ta hau titi gabanta ke faman fad'uwa, a fili ta furta " innalillahi wa'inna ilaihir raji'un ,
" K'iiiiiiii motarta ta tsaya, tayi yin duniya amma tak'i tashi, ta fito daga cikin motar tana jan tsoki, jakarta ta bud'e ta fito da waya zata kira,
Yana tuk'i cikin kwanciyar hankali, wanda a zahiri hankalinshi ba'a kwancen yake ba, tun bayan rabuwarshi da ita ya rasa sukuni da walwala,
Shekaru biyar kenan rabunshi da ita, jin shekaru biyar d'inan yake kamar shekaru dubu biyar, yana rayuwa ne a tsaye amma ta ciki mutuwa yake yi a kowacce dak'ik'a, wayarshi dake ta faman ruri ya kalla kafin yaja d'an gajeren tsaki d'aga idon da zayyi idonshi ya sauka a kanta, kamar daga sama ya hangota tsaye jikin mota tana latsa waya, wucewa yayi had'i da girgiza kanshi dan idan da sabo ya saba da ganin gizonta, idanuwanshi sun dad'e da ribatuwa da ita, mudubi ya kalla yaga still tana tsaye, "kodai da gaske itan ce?
Ya tambayi kanshi, bai san sanda ya taka mahaukacin burki k'ukk'uuuuuuuuu ba saida gabanta yayi mummunar fad'uwa dataji k'arar burkin, jikinshi na rawa ya fito, bakinshi na rawa ya furta " Dee.....ya...nah!, yayi maganar a rarrabe kamar me koyan magana,
wata irin mahaukaciyar fad'uwa gabanta yayi, cikin kid'ima da tashin hankali taja baya tana fad'in " Aj....lal, kyakkyawan murmushinshi ya sakar mata yana fad'in " ashe zaki gane ni?
Cikin murmushin yak'e muryarta na rawa tace " so..sai ma, kawar da idonshi yayi daga kanta, dan jin wani irin mugun sonta da sha'awarta na taso mishi,
take yaji tamkar bai tab'a santa a duniya ba sai a wannan lokacin, wutar santa data lafa mishi ta taso mishi,
saboda ita yak'i aure, dan kullum gani yake zata dawo gare shi, ko sau d'aya bai tab'a cire rai da samunta ba, akanta yake kallan matan duniya tamkar maza ba mata ba,
motarta ya kalla yana fad'in " lafiya meya samu motar?
Yak'e ta kuma yi tace " tsayawa tayi, hannu ya mik'a mata yana fad'in " bani key d'in, ba musu ta bashi, dan kallo d'aya zakayi mata kasan a tsorace take,
yayi yin duniya motar tak'i tashi, ya fito yace " tak'i tashi ina zaki?
"Asibiti...
Sai a lokacin ya kula da cikin jikinta, wani abu yaji ya tokare mishi mak'oshi saboda bak'in ciki, murmushin dole ya k'ak'aro yace " muje na aje ki,
" a'a ka barshi zanyiwa k'aunata waya yazo yakaini,
ido ya runtse da k'arfi kana ya bud'e yana fad'in " ki tambaye shi idan ya yarda saina kaiki, tab! tashin hankali wanda ba'a saka maka rana,
Deen zatayiwa maganar Ajlaal, bayan tasan yafi san mutuwarshi akan Ajlaal,
"A'a zan hau napep kawai, yin duniya tahau ya kaita tak'i hawa, tsakiyar titi ya koma yayi zaman cin abinci ya tankwashe k'afafuwanshi,
cikin mamaki ta kalleshi kana ta mayar da kallanta kan uban go slow d'in daya had'a, mutane sai zagi suke yi, " ka tashi please, maimakon ya tashi sai yayi kneel down a gabanta,
yana fad'in " dan Allah ki hau na kaiki, yayi maganar hannunshi had'e alamar rok'o, batare daya damu da yadda mutane ke kallanshi ba, tasan halinshi da mugun taurin kan tsiya,
idan ya kafe akan abu ko za'a mutu bazai yanje ba, ganin mutane sun fara cire waya zasuyi musu video yasata cewa " tashi muje, da sauri ya mik'e duk ilahirin jikinshi na tsuma,
ya bud'e mata gaban mota, tak'i hawa ta bud'e baya ta shiga, mudubi ya saita yana kallanta, yana fad'in " shekaru biyar, watanni 60, sati 260, kwanaki 1800, awanni 43,200 ban ganki ba Deeyanah,
cikin matsanancin mamaki ta d'ago kanta dake duk'e ta kalleshi, "kina mamaki ko?
Guntun murmushi yayi yace " yau da gobe taba canja komai Deeyanah sai dai tana nuna mata hak'ik'anin mutane, shekaru, watanni, satittika basa iya canja hak'ik'anin abinda ke cikin zuciyar masoyi na gaskiya,
" niko kaga na dad'e da mantawa da rufe babinka a rayuwata, dan baka zame min dole saina rayu dakai a tunani ba, kamar yadda ban zame maka dole saika rayu dani a rayuwarka da zuciyarka ba,
ko dani ko bani, ko da kai ko ba kai kowa zai iya gudanar da rayuwarshi, danya kawar da maganar yace " yaranki nawa?
Banza tayi kamar bazatayi magana ba kafin tace " 1 DeeDee,
" DeeDee! Ya maimaita sunan kafin yace " Dee yana nufin Deeyanah ko?
Sosai yake bata mamaki amma data tuna yadda yake da kwakwalwa saita daina, murmushi tayi tace "eh! while d'aya Dee d'in kuma na nufin Deen, kai fa kana da aure?
"Hmmmmm ina ni ina aure bayan kina raye kina taka doran k'asa, koda bakya raye bazan tab'a yin aure ba, muddin bake ce matar ba,
yayi maganar cikin ranshi, a zahiri kuma yace " eh nayi aure harda yara biyu, Deeyanah da Ajlaal , sunan yarana, dayake 'yan biyu shine na saka musu sunan mu, idan tace bataji tausayin shi ba k'arya take take yi, "wannan wacce irin soyayya ce?
Ta fad'a cikin ranta, cikin sanyi tace " Allah ya raya su, ya amsa da " Amin ya Allah, kanta ta mayar kan wayarta ta cigaba da abinda take yi bata k'ara yi mishi magana ba.
*************************************
Farkawa tayi ta ganta a gidanta mijinta Deen zaune kusa da ita yana yi mata sannu, sosai kanta ya kulle bazata iya tuna komai ba, daga lokacin da take zaune a motar Ajlaal yana fad'a mata sunan yaranshi, kanta ta dafe tana san tuna wani abu amma ta kasa tuna komai,
jikinta tabi da kallo taga babu abinda ya canja, ta kalli Deen tace " Dee! ya akayi nazo nan?
"Waya akayi min, aka sanar dani nazo na d'aukeki an tsince ki cikin motarki a sume, ajiyar zuciya ta sauke still tana san tuna wani abu ta kasa, kanta take tambaya da " meya faru dani?
"Ya akayi haka ta faru?
"Ina Ajlaal?
"Meke faruwa ne?