Sashe 7
Bakar Shuka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A bak'in get d'in Estate d'insu yayi parking bayyi mata magana ba ya bud'e ya fita ya zagaya ya bud'e mata, cikin sanyi jiki ta fito, tayi tsaye tana kallanshi kamar zatayi magana sai kuma ta fasa tasa kai zata shige ciki "kiyi hak'uri please! ya fad'a cikin sanyin murya, cike da mamakin hak'urin da yake bata na miye ta juyo, murmushi ya sakar mata yaja motar ya tafi batare da yayi mata magana ba, tabi bayan motar da kallo tana murmushi tace " rigimamme!.
Washe gari kusan a tare suka shiga makaranta, suna wajen me siyar da gurasa ita da Raleeya ya k'araso wajen, kallo d'aya tayi mishi ta kawar da kanta tana fad'in " zaka ci gurasa band'ashe?
"Kin cika baki kina yi man tayin rowa wai zaka ci, to ban ci, dariya tayi gami da kallan me siyar da gurasar tace " ka had'a mishi special.
Ya soma cin gurasar kenan aka aiko kiransu shida Deeyanah, kallan juna sukayi kana ya mayar da kallanshi ga wanda aka turo yace " kace muna zuwa, hankalinshi kwance yadda kasan babu me jiranshi ya gama cin gurasar, "muje mana, a nutse ya mik'e suka jera har office d'in, Malamai suka gani birjik da gani meeting suke yi, da sallama a bakunansu suka shiga, ganin yadda Malaman suka tsatstsare su da ido yasa Ajlaal murtuke fuska murtuk kamar wanda akayiwa sammacin mutuwa, sai da ta d'an rusuna kana ta gaida Malaman suka amsa ba yabo ba fallasa, while shi yana daga tsaye yace " ina yini?
Daga haka bai k'ara ba, kad'an daga cikinsu ne suka amsa, HOD su yayi gyaran murya had'i da cewa " wai meke faruwa daku ne?
"Meke damunku?
"Meke yawo cikin kanku?
"Fisabilillahi abinda kayi ka kyauta kenan?
Cike da gwarin yace " me nayi Malam?
Cikin zafin rai ganin yana neman rena musu hankali d'aya daga cikin Malam yace " kai ka shiga taitayinka duk cikin mu nan babu sa'anka balle ka rena mana hankali, ido ya zubawa Malamin ya tsare shi da ido yana yi mishi kallan ka shiga hankalinka.
"Kasan wannan?
HOD ya fad'a yana nuna mishi Malamin su Deeyanah daya mara, "eh! yace kai tsaye cikin rashin tsoro.
"Meya had'aka dashi?
Tsayyuwarshi ya gyara kana cikin isa yace "Abun rashin kyautawa yayi ni kuma na gyara mishi, ya fad'awa 'yar wani, k'anwar wani, matar wani kuma mahaifiyar wani maganar da bata dace ba wacce idan aka fad'awa mahaifiyar shi ko k'anwarshi ko matarshi da 'yar shi sai inda k'arfinshi ya k'are, shiyasa nima na nuna mishi rashin dacewar hakan a aikace bada baki ba.
Kwafa d'aya daga cikin malaman yayi had'i da girgiza kanshi, Ajlaal yayi mishi kallan iyakacin nan amma bazan daku ba.
HOD yace " fad'a min abinda ya faru in details, tun daga farko har k'arshe ya komai ya fad'awa su HOD babu abinda ya b'oye har dukan da yayiwa Malamin sai da ya fad'a.
A zafafe d'aya daga cikin Malaman yace " kai ina ruwanka a cikin maganar?
"Meka had'a da ita k'anwarka kome?
A rene ya kalli Malamin yace " matata ce ko kai akwai wanda zayyi b'atanci ga matarka a gaban idonka kayi shiru?
"Lusarin namiji shashasha wanda bai san mutunci da k'imar kanshi ba shine wanda za'a ciwa matarshi mutunci a gaban idonshi tsoro yasa yayi shiru saboda tsabar rashin sanin ciwon kai......
Dakatar dashi HOD yayi ta hanyar d'aga mishi hannu kana yace " ka bashi hak'uri shikenan komai ya wuce dan kyautawa bai kyauta ba shima.
" In bashi hak'uri akan me?
"Me nayi na rashin dacewa da zan bashi hak'uri, shiya kamata ma ace ya bata hak'uri agaban mutunen daya muzanta ta, a d'an hasale HOD yace " nace ka bashi hak'uri ko?
"Kayi hak'uri Malaman ina ganin mutuncinka sosai amma gaskiya bazan iya bashi hak'uri ba, babu juyin duniyar da ba'ayi da Ajlaal ya bawa Malamin nan hak'uri ba amma ya lashi k'asa ya dire ya k'i fur.
"To shikenan tunda bazaka bashi hak'uri ba, kayi taurin kai kuma ka kafe duk da bamu ce saika koma cikin class gaban d'aliban daka mareshi a gabansu ba amma shine ka turje kak'i bin umarnin mu duk da munso muyi masalaha cikin salama dan haka mun yanke mu dakatar dakai har lokacin daka yanke ka bashi hak'uri, cikin tafasar zuciya ya bud'e baki zayyi magana tayi saurin rik'e hannunshi.
Hannunshi data rik'e ya kalla yana jin yadda bugun zuciyarshi ya k'aru da kaso 70 ido ya zuba mata batare daya iya furta komai ba, a hankali ta girgiza mishi kanta alamar a'a kana ta motsa labb'anta cikin sanyi tace " ka bashi hak'urin please.
Ido ya runtse da k'arfi, bashi da yadda zayyi bazai iya yi mata musu ba amma banda ita da idan duniya zata tashi bazai bashi hak'urin ba, idonshi a runtse yace " kayi hak'uri.
Ido ya k'ifta gami da cewa " eye! banji me kace ba fa, hannunshi dake cikin nata ta k'ara damk'ewa tana rad'a mishi please a kunne, idanuwanshi ya bud'e ya sauke su akansu sai da gabanta ya fad'i ganin yadda suka canja launi zuwa asalin jajaye, " kayi hak'uri.
"Nifa bana jinka, in zakayi magana kayi da sigar rok'o ba kana magana kamar kana bani umarni ba, kayi magiya Malam, ka rok’e ni, idonshi ya sake runtsewa da tsananin k'arfi kana ya d'an d'aga murya yace " kayi dan Allah, sai a lokacin Malamin ya sauke ajiyar zuciya kana ya d'ora da " bakomai dama ni ban k'ulla ce ka ba, HOD yayi musu 'yar nasiha akan rayuwa, tayi mishi godiya dan shi ko kalma d'aya bai tsinta ba cikin nasihar saboda tsabar zafin zuciya.
Suna fitowa su HOD suka rufarwa wannan Malamin da fad'a dan bayyi dai-dai ba.
Har bakin get ya kaita ta shige gida, shi kuma ya wuce bai nemeta sai dare ya kira wayarta tana zaune kan sallaya wayarta ta soma ringing bata amsa kiran ba sai ta shafa addu'ar, "an huce kenan?
"Au da fushi nayi?
"Sosai ma kuwa, wai dama haka kake da bak’ar zuciya?
“Anya zakayi saurin yafiya kuwa!?
Kwashewa yayi da dariya sosai yace “ me kike nufi?
“Ai gani nayi cikin d’an lokaci ka canja har kalar idonka ma saida ta canja kala anya da a zamanin su fir’auna da Abu Jahil kazo zaka karb’i musulunci kuwa?
Dariya ya kuma yi sosai har da buga k’afa had’i da cewa “ ai zuciyar bata kai nan ba, waya sukayi sosai kana sukayi sallama.
*America....*
Kwance yake saman kujera idanuwanshi lumshe dukda kasancewar ba bacci yake ba, abin duniya ya isheshi, tunda ya taho ko a waya baiji Deeyanah ko sau d'aya ba,
baiji halin da take ciki ba, muskutawa yayi ya gyara kwanciyarshi yana fad'in " gaskiya nayi k'ok'ari wata shida kenan fa ban ganta ba banji daga gareta ba,
k'arar shigowar sak'o dayaji a wayarshi yasashi jan d'an guntun tsaki yana d'aukar wayar, a Arewa Youth's Achievers group yaga alamar an turo sak'on,
group d'in daya had'a manyan matasan Arewa da suka zama wani abu a rayuwarsu, Ajlaal ne kad'ai wanda baya aiki, kuma d'alibi a group d'in,
shima dan ana saka ran gobenshi mai kyau ce, shiyasa aka saka shi, gashi da kwakwalwa da hazak'a gami da nacin karatu,
kuma yana bada gudunmawa sosai a group d'in dan sau da dama za'a bawa masu yin master Assignment su kasa sai Ajlaal ne zai koya musu,
sak'on da aka turo Deen ya karanta _" d'aya daga cikin Member d'inmu na wannan group Ajlaal Basaan wanda ba b'oyayye bane anan, kowa ya sanshi,_
_ya fad'a soyayya da wata yarinya, a makarantarsu bayan ya ci mutuncinta ya ci zarafinta ya muzantata ya tozartata ya wulakantata,_
_daga k'arshe Allah ya jarrabeshi da matsananciyar soyayyarta,_
kamar ya share sai kuma yayi playing videon da aka turo, baki ya tab'e had'i da cewa " sharmeee zambur ya mik'e tsaye kamar an tsikare shi, bakinshi bud'e cike da mamaki gami da tsoro ganin Deeyanah ce........Take jikinshi ya d'auki rawa da kerrrma yana tsuma, komawa yayi ya sake duba rubutun da akayi a k'asan videon, "meke faruwa ne?
"Meya had'a Ajlaal da Deeyanah?
"Me tayi mishi daya wulakantata yaci zarafinta?
"Ya akayi ni duk ban San wannan na faruwa ba?
"Ina nan ina zaton bani da matsala da ita, ina tunanin ina da yak'ini akanta, yayi maganar yana dafe da kanshi, kanshi ya d'aga alamar tunani ya dad'e a haka kafin ya sauke ajiyar zuciya a karo na ba adadi,
mik'ewa yayi ya shiga bedroom d'inshi da sauri, kayanshi ya shiga had'awa cikin gaggawa a trolley, ko wanka bayyi ba ya saka kayanshi ya jawo trolley,
ma'aikatan gidan yabarwa sallahun zaije ganin gida bazai dad'e ba zai dawo, su kula da gidan,
direct airport ya nufa, yasha wuya sosai kafin su bashi ticket, sai da yayi musu k'aryar mutuwa akayi mishi,
k'arfe 12:30 na dare ya sauka a Nigeria,
jirgin sama ya hau daga Abuja zuwa Kano, bai shiga gida ba sai 5:00 na safe, babu wanda ya gayawa yana tafe dan haka babu wanda yasan da zuwanshi,
d'akinshi ya wuce saboda damuwar dayake ciki bai ko cire kayan jikinshi ba ya kwanta, Allah Allah yake gari ya k'arasa wayewa.
Da sauri ta fito tana duba agogon hannunta, bata kula ba saiji tayi, tayi karo da abu, da sauri ta d'ago kanta tana ja baya cike da tsoro,
ganin Imran ba k'aramin mamaki ya bata ba, wanda ta kasa b'oye mamakinta ya fito ya bayyana k'arara saman fuskarta,
" mamakin na meye?
Ya fad'a yana k'are mata kallo, hannuwanshi sark'e a k'irjinshi, murmushinta ta fad'ad'a wanda ya bayyanar da kyawawan hak'oranta, " laaaa! Yaya yaushe kazo?
Tsaiwarshi ya gyara had'i da jefa idonshi cikin nata ya dad'e yana kallan kwayar idonta kafin ta sunkuyar da kanta k'asa, dan bazata iya jurewa kallan kwayar idonshi ba, kamar daga sama taji yace " waye Ajlaal?
"Meye alak'arku dashi?
Da sauri ta d'ago kanta ta kalle shi cike da tsoro da zallar tashin hankali, idonshi kanta ya tsuke fuska babu alamun wasa ko dariya yace " ya akayi?
"Kina mamakin yadda akayi na sani ne Deeyanah ?