← Book details Bakar Shuka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 56

Sashe 8

Bakar Shuka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kanta ta duk'ar cikin sanyi dukta dabarbarce ta rasa abinda zatace mishi, saboda yadda ya kafe ta da ido " fad'a min abinda yake tsakaninku?

Kanta k'asa ta kwashe komai ta fad'a mishi tun daga farkon zuwa k'arshe, Deeyanah bata tab'a sanin Deen yana da bak'ar zuciya ba, sai yau,
jikinshi har rawa yake, jijiyoyin kanshi sukayi rad'o-rad'o idonshi yayi jajir kamar gauta, " saboda ya mayar dake teddy kuma 'yar tsana wacce zai juya yadda yake so,
wacce zai d'auka sanda yaga dama ya aje lokacin dayaga dama bayan ya tozartaki cikin mutane sannan ya dawo yana miki kukan munafurci wai yana sanki saboda yafi kowa iya game?

" Ko an fad'a mishi kowa irinshi ne?

"An fad'a mishi kowa sakarai ne?

Yayi maganar a zafafe cikin b'acin rai, " wallahi saina nuna mishi yayi kuskure saina nuna mishi nafishi zafin kai, ya k'arasa maganar yana rik'o hannunta yana tafiya,
ganin yana nufar mota da ita yasata kalleshi tana fad'in " ina zamuje Yaya?

Maimakon ya bata amsa sayya bud'e gaban mota yace " shiga!, taso tayi mishi musu amma ta kasa saboda yanayin fuskarshi ya tsoratata,
yadda ya figi motar kad'ai ya isa ya tabbatar maka yana cikin b'acin rai, hannunta ta d'ora saman nashi cike da tsoro tace " Yaya ka kai gudun motar k'arshe fa,
ko kallanta bayyi ba ya cigaba da mugun gudu da motar, sosai gabanta ke fad'uwa, tashin hankali da fargaba ne suka shigeta lokaci d'aya dataga ya shiga get d'in makarantarsu,
sai yanzu ta fahimci abinda yake shirin yi, tasan halin Ajlaal sosai kamar yunwar cikinta haka tasan halin Deen, tasan ba k'aramar b'acacciya za'ayi ba muddin suka had'u,
a tsorace ta fara girgiza kanta kwalla na taruwa a idonta tana fad'in " a'a Yaya,
dan Allah karkayi haka wallahi Ajlaal yana da bak'ar zuciya shima,
idan kaje komai yana iya faruwa, birki ya taka k'uuuuuu, in banda dokawa babu abinda k'irjinshi keyi, ita kanta dake kusa dashi tana iya ganin yadda k'irjinshi ke sama da k'asa,
cike da tsoro ta d'ora hannunta saman nashi tace " please Yaya, kujera ya kwantar ya kwanta tare da lumshe idonshi,
tunda motar Deen ta faka a kan idon Ajlaal bai damu da yasan wanda ke cikin motar ba dan halinshi na shareya yana nan,
" kina sanshi ko?

Deen yayiwa Deeyanah tambayar, idonta dake cike da hawaye ta bud'e tarr ta kalleshi, yadda kasan bashi yayi maganar ba,
Ajlaal dake zaune ya mik'e ya nufi class da nufin dubawa ko Deeyanah ta k'araso, dan ya kirata yafi so ba adadi ba'a d'auka,
yana tafiya yana dialing number, bugun da zuciyarshi keyi da k'arfi ya tabbatar mishi Deeyanah na kusa, dafe k'irjinshi saitin zuciyarshi yayi,
yana murmushi had'i da kara wayar a kunne, dai-dai lokacin da zai wuce ta kusa da motar da Deeyanah ke ciki, wayarta ta soma ruri,
harya gota motar ya tsara cak danko a mafarki yaji k'anshinta da ringing wayarta zai gane, a hankali Deen ya bud'e idonshi ya zuba mata su,
wayar dake faman rori ya kalla kana yace " pick it, kanta ta girza mishi hawayen dake idonta suka samu damar gangarowa saman kuncinta,
"nace ki d'aga ko.....?

"Ko saina...! knocking window da akayi ya katse mishi maganarshi, yasan Ajlaal Basaan sama-sama a group d'insu,
shiyasa bayyi wani wahalar ganeshi ba, yadda yake kallan Deeyanah yana murmushi tana mayar mishi da martanin murmushi yasa wani k'ululun abu tokare mishi mak'ogwaronshi,
idanuwanshi suka sake rinewa ya rasa abinda keyi masa dad'i a duniya, can k'asan mak'oshinshi yace " nayi sake,
da yalwataccen murmushi a saman fuskarta ta kalli Deen tana fad'in " Yaya ga Ajlaal,
bayyi niyyar fita ba amma yadda Deeyanah tayi mishi da yadda Ajlaal ke buga masa glass d'in mota suka k'ara hasala shi,
bayyi magana ba ya bud'e motar ya fita, ya zagaya inda Ajlaal ke tsaye had'i da hard'e hannuwanshi a k'irji, yana k'are mishi kallo from head to toe yace " yadai Malam kake bugawa mutane mota?

Murmushi Ajlaal yayi yana mik'awa Deen hannu yace " ina yini?

"Alhamdulillah, cewar Deen batare daya mik'awa Ajlaal hannun ba, kallan Deeyanah yayi yana murmushi had'i da cewa " fito man....,
bai k'arasa maganar ba ganin hawaye a idonta da sauri ya zagaye Deen ya fara k'ok'arin bud'e motar, Deen na daga inda yake ya dannawa motar key,
ya tsaya yana kallan Ajlaal , " please ka bud'e ta kuka fa take, bai motsa ba balle yayi magana, cikin hargowa Ajlaal ya nufi Deen yana fad'in " nace ka bud'eta ko baka ji abinda nace ba?

Still shiru Deen yayi yana bin Ajlaal da ido, cikin matsanancin b'acin rai Ajlaal yaci kwalar Deen had'i da dunk'ule hannu zai kai mishi naushi,
" no! Ajlaal Yaya na ne, Deeyanah ta fad'a hankalinta a matuk'ar tashe, motar ya daka da k'arfi, har yaji ciwo, juyawa yayi yana shafa kanshi kafin ya dawo ya had'e hannunshi alamar rok'o yana fad'in " dan Allah!,
rigarshi ya gyara inda ya ci kwalarshi fuskarshi d'auke da murmushi yace " bata fad'a maka a kaf zuri'armu bamu auren bare ba?

" Sai dai idan Allah bai bawa mutum ba, amma idan Allah ya bashi babu mahaluk'in daya isa ya hana, hannu Deen ya d'aga mishi gami da cewa " ya isa, ni bana ja da hukuncin Allah,
bawai mace tana buk'atar namijin dazai mutu dominta bane kad'ai, a'a tana buk'atar namijin dazai rayu dominta ne,
wanda zai k'arfafi musuluncinta da imaninta wanda zai jagoranceta izuwa Aljanna cikin Aminci da yardar Allah,
haka mafi girman arziki mutum ya dace da abokin rayuwa, wanda ya damu da kyautatawa rayuwarshi na duniya da lahira,
ka sani kasa a ranka cewa nine mijin Deeyanah da izinin Allah, in sha Allah bata da mijin daya wuce ni Deen, kuma yau-yau d'innan ba sai gobe ba, za'a d'aura mana aure,
ta zama mallakina halaliyata, bai jira abinda zai ce ba ya wuce yabarshi nan tsaye,
da ido Ajlaal yabi Deen maganganunshi nayi mishi yawo aka, kafin Deen ya k'arasa ga motar Ajlaal ya rigashi hannunshi dake zubar jini wanda ya bugi motar dashi,
dashi ya naushi window'n glass d'in motar, ya rik'o Deeyanah, cak Deen ya tsaya yana bin hannun Ajlaal inda daya rik'e Deeyanah da kallo,
zuciya ta kawoshi har wuya kamar namijin zaki haka yayiyo kan Ajlaal,
cikin matsanancin kuka Deeyanah tace " a'a dan girman Allah karka tab'a shi please,
ido ya runtse da k'arfi kana ya bud'e su a lokaci zuciyarshi kamar zata tsage gida biyu, ji yake kamar ya cinnawa duniya wuta kowa ya huta, Ajlaal ya zagaye yq bud'e motar ya shiga had'i da figar motar yabar harabar makarantar,
Ajlaal yabi bayan motar da mugun gudu kamar zararre yana kiran sunanta, baya ya dawo da gudu ya nufi inda yayi parking motarshi ya shiga ya figeta ya rufa musu baya.

Ta window ta hango Ajlaal na binsu, jikinta ya d'auki rawa dan duk abinda ke faruwa tsakaninta da Ajlaal babu wanda ya sani a gida,
hannunta saman na Deen ta rik'eshi gam, cikin muryar kuka tace " karka kashe mu Yaya ka tafi a hankali please, kawar da kanshi yayi gefe aiko idonshi ya sauka akan wata mota dake biye dasu da gudu kamar hauka, ko ba'a fad'a mishi ba yasan Ajlaal ne, low yayi da motar sosai ya soma k'ok'arin gangarawa gefen titi, kuka ta saka mishi tana rok'onshi karya tsaya,
yaso ya tsaya amma yadda ta take rok'onshi yasashi ya taka motar, bai sausauta motar ba saida suka isa gida, mai gadinsu yayiwa kashedi da fad'in " karka sake ka bud'ewa kowa get duk wanda yazo karka sake ka barshi ya shiga matuk'ar ba d'an family bane,
cike da mamakin kashedin da Deen keyi mishi ya d'aga kanshi dan hakan bai tab'a faruwa a tsakaninsu ba, sama da shekaru 20 yana yi musu aikin gadi,
tsakanin Deen da ma'aikatan gidan sai kyautata da sam barka shi bai ma shiga harkar da bata tashi ba, ko a danginshi ne,
parking yayi a inda aka tanada dan aje motoci, ya kifa kanshi saman sitiyari yana sauke ajiyar zuciya, a sanyaye tace " kayi hak'uri please Yaya,
kanshi ya d'ago ya zuba mata ido na tsayin lokaci, " kayi hak'uri..... da sauri ya katseta da cewa ki rik'e hak'urinki bana so Deeyanah,
Tunda aka haife ki, kika bud'e ido kika ganni a rayuwarki Deeyanah, baki san yaushe ne ba, baki san ya akayi ba, kedai kawai kin bud'e idonki a duniya kin ganmu tare,
amma ban tab'a, tab'a koda d'an yatsanki bane balle jikinki ba, saboda bashi ne a gabana ba, ked'in ke kad'ai nake so Deeyanah,
saurin d'ago kanta tayi ta kalleshi yanayin kallan dayake yi mata yasata saurin duk'ar da kanta k'asa cike da kunya had'i da mamaki,
" eh Deeyanah ina sanki iya tsayin rayuwata na rayu ne da sanki, ban fad'a miki bane saboda ina tunanin bani da matsala da hakan,
cikin sanyi ya rik'o duka tafukan hannayenta cikin nashi tare da tausasa muryarshi yace " kece rayuwata,
ina da tabbacin babu wani haluk'in da zai miki irin san danake miki, a shekarunki bazaki tantance so, k'auna, soyayya ko sha'awa ba,
wad'annan k'ananan samarin da kike gani duk ba aure ne a gabansu ba, yaudara da lalata 'ya'yan mutane ne a ransu,
idan kin bani dama a yau a yanzu zan aureki, a yau zaki zama mallakina Deeyanah, amma idan baki yarda ba shikenan duk k'ok'arina ban isa na wuce iyakar abinda Allah ya rubuta zan samu ba,
hannunta ya saki ya juya da nufin fita daga cikin motar da sauri tace " dan Allah Yaya karka fad'i abinda ke faruwa a gida,
guntun murmushi yayi tare da k'arasa ficewa, wajen 11:30 na safe abun ya faru, dan haka yasan gaba d'aya iyayensu na gida, babban parlour'n gidan ya wuce,
ya tarar da kowa a ciki harda kakanninsu, cikin girmamawa ya duk'a ya gaidasu, cike da mamaki suka amsa mishi Babah ya d'ora da cewa " saukar yaushe Son?

Kanshi k'asa yace " yau Babah, " lafiya dai ko irin wannan zuwan bazata haka?

Murmushi yayi had'i da shafa kanshi yace " dama maganar auren mu ce ta taso, kafin Babah yayi magana mahaifinshi yayi saurin cewa " aurenku kuma?
Chapter 8 · 0% Book details