Sashe 6
Bakar Shuka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sosai Ajlaal ya matsawa Deeyanah da rok'o akan ta kulashi ta taimaka ta so shi, duk inda tasa k'afa yana biye da ita ya zama tamkar inuwarta, ya susuce ya zare, gaban uban kowa durk'usawa yake yi a gabanta yana had'a ta da Allah,
yadda kasan mahaukaci haka Ajlaal ya koma, saida takai ga ta daina zuwa makaranta ita abimma har tsoro yake bata har gaban malamansu bai jin kunya balle tsoro kuka kam yayi shi har ya gaji, saboda Deeyanah yak'i zana jarabawarshi ta k'arshe wacce daga ita shikenan ya gama jami'a,
lokacin da labari ya iske Deeyanah sosai tayi mamakin abun, zuciyarta tayi rauni sosai, ta fara tausaya mishi, yayinda iyayenshi da Malamai sukayi tayi mishi fad'a,
amma ina wanda yayi nisa baya jin kira Ajlaal kam yayi nisan da bai jin kira, ko cikin bacci bashi da abin kira sai Deeyanah abun kamar hauka hauka ko wanda aka jefa haka ya koma,
tana zaune a cafeteria gaba d'aya hankalinta ya gama tafiya ga kallan wasu fararan tsuntsaye dake gabanta d'aya na bawa d'aya abinci ta bakinshi, firgigit tayi ta tsorata jin an rik'e k'afafuwanta,
" yi hak'uri na tsorataki ko?
Batayi mishi magana ba, sai k'ok'arin kwace k'afarta data shiga yi, gam ya rik'e k'afar da iya k'arfinshi yana rusa kuka tamkar wanda aka cewa uwarshi da ubanshi sun mutu,
abinka da makaranta kan kace me wajen ya cika makil Ajlaal kwance rub da ciki ya rik'e k'afafuwan Deeyanah,
wasu daga cikin d'aliban suka ciro waya suna d'aukar abinda ke faruwa, da ido Deeyanah tayi mishi alamar ya tashi amma yak'i,
" bazaki sani abu nak'i yi ba wannan ma dan dole ne, kiyi hak'uri bazan tashi ba har sai kin bani amsa ta, Malamai da dama sukayi mishi magana yak'i tashi,
akayi yin duniya yak'i tashi ya kafe sai Deeyanah ta bashi amsa zai tashi inba haka ba sai dai su kwana anan, Raleeya ta matsa kusa da Deeyanah tayi mata rad'a a kunne " ki amsa mishi kawai,
da sauri Deeyanah ta kalle ta tana zaro ido, k'asa Raleeya ta sakeyi da murya tace " wallahi baki da wata mafita wacce ta wuce wannan,
ki lallab'ashi ku rabu idan Allah ya had'aka da mahaukacin masoyi sai hak'uri, dakyar Raleeya ta shawo kan Deeyanah ta amince zata lallab'a Ajlaal,
kallanshi tayi fuskarta d'auke da murmushi tace " tashi mu tafi, ganin karon farko tayi mishi murmushi yasashi saurin mik'ewa, " daga yau ka zama aboki na,
kai ya girgiza yana fad'in " ba aboki nake san zama a wajenki ba, fiye da haka nake san zama, murmushinta ta k'ara fad'ad'awa tace " kayi hak'uri ka kwantar min da hankalinka,
duk wata soyayyar dakaga ta kafa tarihi a duniya daga abota ta samo asali, kayi hak'uri mubi komai a sannu daga abotar sai kayi k'ok'arin siye zuciya ta, kaji ko?
Tayi maganar cikin taushi cike da tausayawa, kamar k'aramin yaro ya mik'e yana d'aga mata kai, tun daga wannan rana Ajlaal da Deeyanah suka d'inke suka zama manyan abokanai,
tamkar gum haka ya zame mata, bacci kad'ai ke rabasu yayinda k'arfi da yaji Ajlaal ya dawo da kanshi level 1, tun abun na bawa mutane mamaki har ya dawo bawa kowa tsoro,
baijin maganar kowa sai tata, a hankali tausayin Ajlaal da Deeyanah keyi ya rikid'e ya fara zama SO, lokacin da mahaifinshi ya samu labari ba k'aramin tashi hankalinshi yayi ba, musamman da yaga videon Ajlaal durk'ushe gaban mace yana rok'on soyayyarta tamkar almajiri abin ba k'aramin b'ata ranshi yayi ba,
fisgo Ajlaal yayi cikin zafin rai ya yarfa mishi zafafan marika biyu, da sauri Mama (mahaifiyarshi) ta mik'e bakinta bud'e cike da mamaki kasancewar wannan ne karo na farko da hakan ya faru a iya tsayin rayuwarta, "lafiya Alhaji...?
Batare daya kalleta ba ya nuna mata yatsa, yana fad'in " karki soma tsumo bakinki cikin maganar nan, 'yan aikin tsaye sukayi suna kallan ikon Allah,
yau Alhaji Basaan ne da tab'uka abun arziki a gidanshi haka, mutumin dako kara Hajiya Halimatu ta aje baya iya k'etarawa yadda kasan k'aramin yaro haka yake a wajenta labari ya cika unguwa da duk mutanen da suka sansu cewar ta mallakeshi,
danko magana zayyi mata cikin girmamawa kanshi a duk'e yake mata, cikin hargowa Alhaji Basaan yace " kana da hankali kuwa Ajlaal ?
"Kasan me kakeyi?
"Kasan meka aikata kuwa?
Ajlaal dake rik'e da kuncinshi yace " kayi hak'uri Abba wallahi ina santa itace rayuwata, yayi maganar hawaye na gangaro mishi, cikin rashin fahimta Hajiya Halimatu tace " wai me ke faruwa ne Alhaji?
Wayar ya mik'a mata yana fad'in " kalli kiga abinda yayi kuma wannan bashi ne karo na farko ba, haka yarinyar tayi ta janshi a k'asa yana biye da ita kamar kare,
babban abin takaicinma wai ya koma level 1 saboda ita, saurin d'ago kanta tayi ta kalli Alhaji kana ta mayar da kallanta ga Ajlaal tana yi mishi kallan tuhuma,
kanshi ya sunyar k'asa hakan dayayi ya bata tabbacin abinda Alhaji ya fad'a gaskiya ne, hannun Alhaji ta kama ta zaunar dashi saman sofa,
"inaga mafita d'aya kawai muke da ita akan abun nan, " wacce mafita?
Cewar Alhaji Basaan yana binta da kallo, " a aura mishi ita, shiru Alhaji Basaan yayi na d'an wani lokaci kamar zai iya tab'uka wani abun kirki, " ya sunanta?
Ajlaal dake tsaye kamar an dasashi ya kasa motsawa saboda wani irin mugun dad'in da yake ji tun daga takun k'afarshi har tsakiyar kanshi,
ya rungume Hajiya Halimatu yana fad'in " nagode Mama nagode sosai,
"sunanta Deeyanah d'iyar Malam Abduljalal ce, da sauri Alhaji ya mik'e yana fad'in " wanne Abduljalal d'in?
A zabure Abba yace "Kar dai kace min Nakowa?
"Shi Abba cewar Ajlaal , "to ikon Allah wannan ba sai anyi wani bincike ko b'ata lokaci ba, zan nemi mutane sai muje, murmushi Ajlaal yayi yana shafa kanshi yace " nagode sosai amma dan Allah aje da wuri,
" zamuje da wuri amma sai kayi min alk'awarin zaka koma kamar da zaka koma Ajlaal Basaan d'in dana sani zaka koma level 4 d'inka,
" in sha Allah Abba, har Ajlaal yakai bakin k'ofa Alhaji Basaan ya kira sunanshi cikin taushin murya "Ajlaal..!,
jin yadda ya kira sunanshi yasashi juyawa cikin nutsuwa, " Lokaci da rayuwa suna da matuk'ar mahimmanci dan idan daya daga cikinsu ya kufce maka bazai taba dawo maka ba, kayi kokari ka amfanesu, ba shekara ba, ba wata ba, ba sati ba, ba kwana ko yini ba, ba awa ko minti ba dai-dai da dakika daya idan ta wuce daga rayuwarka bazata kara dawowa ba harka koma ga Allah, dan haka kasan me kayi a kowacce rana ta rayuwarka da zai amfane ka Duniya da Lahira,
fata, buri da mafarki duk abu d'aya ne, kuma kowa yana da nasa, yawan burikanka yawan jajircewarka, karka bari shirme da shiririta su cinye kaso mafi yawa a rayuwarka,
ya kamata kayi abinda zaka amfana kuma al'umma zasu amfaneshi, wanda zaka ci moyarshi duniya da lahira,
murmushi Ajlaal yayi tare da jinjina kanshi yace " nagode sosai Abba in sha Allah zanyi amfani da abinda ka fad'a min.
Daya shigo makaranta farkon abinda yake fara yi shine nemanta, in banda ma tayi mishi gargad'i da fad'in " karka soma gangancin zuwa gidan mu duk ranar daka sake kaje gidanmu nasan daga ranar bazaka sake ganina a rayuwarka ba dan cire ni za'ayi daga makaranta ayi min aure.
Murmushi yayi yace mata " dako saina addabi ahalinki da mijin daya aureki, da kice mace ta farko a duniyar musulunci da zata fara kasancewa matar maza biyu dan kuwa ko kinyi aure ke tawa ce ni kad'ai Deeyanah, tana d'aukar kalamanshi da wasa dan haka bata tab'a basu mahimmanci ba.
Yauma yana shigowa department d'insu ya wuce tana zaune cikin aji ana yi musu lecture's yayi sa'a tana dai-dai window dan haka yaje jikin windon ya tsaya yana kallanta, cikin sa'a ta d'ago ta kalli windon suka had'a ido, tayi mishi murmushi shima ya mayar mata da martanin murmushi, a hankali cikin rad'a-rad'a yace " yaushe zaku fito?
Itama cikin rad'a-rad'ar ta bashi amsa da " nan da minti 30, dayake dama ya saba idan zata kwana tana lectures sayya jirata duk dad'ewar da zatayi baya damuwa, ya koma gefe ya zauna yana jiranta.
"Deeyanah me nace?
Malaminsu ya tambaye ta saboda ya lura da abinda take yi, " na'am Malam! Ni?
"Eh! Ke me nake cewa yanzu?
Kame-kame ta soma yi, "fito nan, Malamin ya fad'a yana kafe ta da ido, cikin sanyin jiki ta fito gaban allo, alli ya mik'a mata yace " ungo maza k'arasa mana bayanin tunda naga kamar kin riga kin sani, bata karb'i allin dayake mik'o bata ba tace " kayi hak'uri dan Allah Malam.
"Dama soyayya da kula-kulan maza iyayanki suka turo ki yi makaranta?
"Arahar taki har takai haka?
"Gaskiya banyi zaton kina da sauk'in samu haka ba wall......
Tasssss! Tassssss! Ajlaal ya d'auke shi da gigitattun marika masu k'arfi, ya shak'i wuyanshi yana huci ya d'aga shi sama " idan mahaifiyarka ko matarka da 'yarka ta cikinka da k'anwarka aka fad'awa ya zaka ji?
" Suma fa 'ya'yan wasu ne, k'annan wasu sannan wata rana zasu zama matan wasu har su kai ga zama iyayen wasu, ya buga shi da k'asa zai rufe shi da duka Deeyanah tayi saurin shiga tsakiya tana zubar da hawaye tace " ka kyale shi dan Allah.
Hannunshi ya dunk'ule had'i da nausar iska kana ya rik'o hannunta suka fice daga ajin, ko ba'a fad'a mata ba tasan Ajlaal akwai bak'ar zuciya ji yadda jijiyoyin kanshi sukayi rad'o rad'o idanuwanshi sukayi jajir kamar gauta, bayyi mata magana ba ya bud'e mata gaban motar ba musu ta shiga ya mayar ya rufe ya zagaya ya shiga, ya figi motar da k'arfi ya tada k'ura.