← Book details Bakar Shuka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 56

Sashe 3

Bakar Shuka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da wuri ta shiga makarantar direct class ta nufa har tana tuntube kasancewar wayar da Raleeya tayi mata ta sanar da ita, yau me English ke had'a Assignment dinshi,
tun farkon Semester Malamin ya bada Assignment din, ta rasa wanda zayyi mata, har caffe taje amma a banza,
ga Malamin yayi gargadin kar mutum biyu suyi iri daya, muddin yaga iri d'aya zayyi musu cancel gaba daya,
" kin san Allah haukana nayi mishi, tunda shi yace bai san copy copy ni na tab'a jin irin wannan kakalen,
Cewar Raleeya tana bata fuska, rolling ido Deeyanah tayi tana fad'in " ni haukan ma na kasa yi wallahi, na rasa ta in da zan fara abin duniya duk ya isheni,
shiru Raleeya tayi na d'an lokacin kafin ta sauke ajiyar zuciya tana fad'in " akwai mafita, cikin zakuwa Deeyanah tace " dan Allah?

" Eh, naji yawancin 'yan ajinmu na cewa wani d'an level 400 ne yayi musu, an ce duk makarantar nan ba mai k'ok'arin shi, wai sau kusan biyar yana samun scholarship yana k'in tafiya,
" me yasa?

Deeyanah tayi maganar cike da mamaki, " eh to wai shine bai sha'awar fita waje yayi karatu, inda yana da ra'ayi daya fita dan babanshi me mugun kudi ne,
naji ance shine sakataren governor fa, kuma shi kad'ai ya haifa, kuma mahaifinshi na mugun sonshi, kinga ra'ayin fita waje ne bayyi ba,
kamar dai ke da baki da ra'ayin fita waje karatu, Raleeya ta fad'a tana kai mata dukan wasa, baki ta tab'e tana fad'in " wallahi nima dai banga amfanin karatu waje ba,
sai b'ata tarbiyya da lalata d'abia a cirewa 'ya'ya mata kunya, su koma kamar tumakai, dariya Raleeya tayi tana fad'in " kedai kika sani, mudai samu ne da bamuyi ba, idan muka samu zamu,
" ke dai ban san surutun banza rakani wajen... wama yake...., " AJLAAL , sunanshi Ajlal.

"
Ajlal...! ta maimaita sunan saman lips d'inta, jin yadda ta Deeyanah ta maimaita sunan so calm yasa Raleeya kallanta tana murmushi tace " yayi masifar had'uwa,
ga kyau ga kudi, ga gayu da tsafta, ga Ilimi both boko da arabi ga kwakwalwa, gashi da aji wallahi,
cike da k'osawa Deeyanah ta juya idonta tana fad'in " kai nidai naga ta kaina, kodai kodai... ta k'arasa maganar tana d'age mata gira d'aya,
" wace ni kawata, wannan ai yafi k'arfin ajina,
" tab wallahi ki daina fadar haka kika san me Allah zayyi, " hmmm banda dai anan, dan bakin wuta ba wajen wasan makaho bane, guntun murmushi Deeyanah tayi hadi da gyara tsaiwarta tace " Raleeya Rayuwa kamar kwai take bata da gaba ko baya balle wani yasan alkiblarta, ba kuma asan fuskarta ko keyarta ba, ba wanda yake da tabbacin dan tsako zai zama ko ko wainar kwai zai zama, duniya kamar mace mai ciki ce babu wanda yasan abinda zata haifa,
Raleeya zata kuma magana Deeyanah tayi saurin cewa " dan Allah muje.

*AJLAL....!*

D'a d'aya tilo ga Alhaji Basaan da Hajiya Halimatu, Alhaji Basaan mutumin kirki ne ba laifi yana kwatantawa dai-dai gwargwado,
yayinda Haliya Halimatu ta kasance bak'ar muguwa kuma azzalumar mace marar imani, shi kanshi Alhaji Basaan d'in ba dad'inta yake ji ba dan tafi k'arfinshi sai abinda tace kuma take so shi yake yi, tana iya kunyata shi gaban kowa, idan tana yi mishi fad'a da tsawa saika rantse d'anta ne, daga shi har ma'aikatan gidan mugun tsoranta suke ji, ta zama mijin ya zama matar, ko kallanshi tayi yasan abinda take nufi, a b'angaren jama'a kuwa mutuniyar kirki ce ga faram-faram da mutane, sai d'an abinda ba'a rasa ba, tana zaune da kowa lafiya amma a gida yadda kasan boss haka take, taita muzurai ita kad'ai, yayinda Ajlaal ya kasancewa mutum mai saurin fushi da bakar zuciya,
idan ka b'ata mishi rai zayyi maka abinda shi da kanshi zai dawo yana nadama,
babbar matsalarshi saurin hannu yanzu zai kai duka, kodan ya taso a sangarce a kuma shagwabe ne oho, tunda Ajlaal yake bai tab'a wayar gari ya nemi wani abu ya rasa a rayuwarshi ba,
bayan wannan bashi da wani mugun hali, baya shaye-shaye, baya neman mata dan da d'an iska ne shi da an shiga uku yadda mata keyi mishi tururuwar kawo mishi tallar kansu,
amma ko kallo basu isheshi ba yanzu zai dizgaki a gaban kowa, ya sha wulakanta mata wasu ma harda mari.

Yauma kamar kullum tunda ya shigo makarantar mata ke kai mishi kokon bararsu akan soyayya, kusan mata uku ne suka tare shi suka sanar mishi suna sanshi,
babu wacce ya amsawa a cikinsu sai dai ya wuce su yayi kamar bai ji su ba, amma deep down ya kawo iya wuya, ji yake kamar zayyi bindiga saboda takaici da bakin ciki,
kwata-kwata baya san irin abun baya so, abun baya burgeshi, gani yake kamar rashin aji ne, rashin sanin darajar kai da karancin tarbiyya kesa mata su kawowa namiji tallar kansu.

Yana tafe yana mita a zuciyarshi ya gama k'uluwa sosai, ya k'uduri niyyar duk yarinyar data sake k'ok'arin tsayar dashi ko tayi mishi magana,
sayya kafa tarihi akanta wanda zai zamarwa wasu izzina, daga b'angare daya kaddara ta bud'e saban shafi a rayuwarsu ba tare da sun sani ba,
" minti d'aya please Ajlaal zamuyi magana dakai, Raleeya ta fad'i suna k'arasawa inda yake, tsayawa yayi cak tare da runtse idonshi yana jin yadda tuk'ukin bakin ciki ke tasowa tun daga kasan zuciyarshi,
"taimako nake nema daga gareka please ka taimaka man, Deeyanah ta fad'i cike da karaya,
bayyi magana ba bare ya juyo, bata damu da yadda yayi musu ba, tunda ta samu labarin yana da girman kai, da yanga, abun bai wani dame ta ba,
tunda ba alak'a take san k'ullawa dashi ba, assignment dinta kawai take san yayi mata, daga haka shikenan, k'ok'arin controlling kanshi yake san yi amma ya kasa, a tak'aice yace " a'a please, " dan Allah ka taimaka ka saurare ni,
ba wani abu bane INA SAN KA KO.....!,
loosing control yayi jin ta furta kalmar INA SANKA..., bai bari ta k'arasa fadar abinda take san fad'a ba ya d'auketa da marin daya sata kifawa,
a fusace ya juyo tare da d'aga murya yace " enough ya isa please! Am tired from all your drama, stop it please, yadda yayi maganar cikin hargowa ya jawo hankalin dalibai,
kan kace me an cika wajen makil, ya cigaba da cewa " bana sanku! ni kadai ne namiji a makarantar nan?

"Ni kadai ne keda abinda kuke so?

" Ni kadai ne nayi dai-dai da kalar namijin ra'ayinku?

" Ya isa please! stop it right now, bana sanku bani da ra'ayin soyayya daku, haba abun ya isheni haka kowacce mace ni, kowacce mace tana so na, koma zanyi soyayya bada irin ku ba, balgaza, jaka mara sanin daraja da k'imar kanta, ya k'arasa maganar yana nuna su a wulakance,
Raleeya dafe da kunci hawaye na gangaro mata ta kura mishi ido, bakin ciki ya hanata furta koda kalma daya,
takaici ya hana ta yi mishi bayanin ba cewa zatayi tana sanshi ba, so take tace mishi INA SAN KA KOYA MIN ASSIGNMENT,
amma ya datse maganarta ya tozartata ya wulakantata agaban dubban jama'a har da malamansu,
cikin fushi Raleeya tace " kai! ba abinda muke nufi kenan ba, assign..... " quite, I said ya isa haka ban san sake jin koda kalma daya tak,
yayi maganar yana nuna ta da yatsa while duk ilahirin jikinshi na kerrma,
baya Deeyanah taja saboda yadda Ajlaal ya matso gaf da ita har suna iya juyo fitar numfashin juna, a hankali ta d'ago kanta ta kalli mutanen dake wajen,
magana sukeyi sosai suna nunata harda masu zunbenta, da gudu ta juya tabar wajen had'i da fashewa da kuka, Raleeya ta nunashi da yatsa kamar zatayi magana sai kuma ta fasa tayi kwafa tabi bayan Deeyanah da sauri tana kwala mata kira, cike da halin ko in kula ya taka ya shige class babu damuwa balle nadamar abinda ya aikata a tattare dashi.

Bata tsaya ba duk da kiran da Raleeya keyi mata, ta fad'a napep tana fad'in " muje...,!
Napep din ya tada yana cewa " ina zan kaiki Hajiya?

Bata d'ago kai ba ta bashi amsa cikin murya kuka, " Magajin Rumfa, bai kuma magana ba yaja suka tafi, Raleeya ta k'araso wajen tana fad'in " wait... wait ku tsaya, amma ina sun riga sun tafi, kanta ta tana sharb'ar kukan takaicin yau ita namiji ya disga a gaban mutane, har bakin get ya kaita, tun kafin ya ida tsayawa ta bashi 1000 ta sauko, me napep d'in na kwala mata kira kan ta amshi canji, amma ko takan canjin bata bi ba,
da gudu ta shiga gida bata tsaya a parlour ba ta wuce bedroom dinta tare da rufe kofa ta fad'a saman bed ruf da cikin tare da saki saban kuka, saida tayi kwana uku bataje makaranta ba,
sai a rana ta uku ne ta shirya ta tafi, tunda ta shiga makarantar kanta ke duk'e k'asa, koda wasa batayi gangancin d'agawa ta kalli kowa ba,
duk inda ta wuce sai taga dalibai na nunata suna magana da dariya k'asa-k'asa, tafiya kawai take batare data san inda take jefa k'afarta ba,
jinta take kamar tana tafiya a saman kayoyi duk ta tsargu, kamar daga sama taga gungun dalibai sun kai goma sun sha gabanta,
cike da shakiyanci suna dariya guda daya daga cikinsu ya make murya yace " ina sanka.....!
sauran suka had'a murya wajen cewa " aaahhh bana sanki, sai kace dole, suka dau ihuuuu gaba d'ayansu,
batayi musu magana ba ta zagaye su ta raba ta wuce, suka bi bayanta suna ihuuuu, gabanta wani namiji yasha yana rangwada kamar mace ya yafa mayafi ya kalli wani dake gefenshi yace " ina sanka,
fuska dayan ya bata had'i da yiwa dayan marin karya yace " bana sanki, banza ballagaza kawai, daya namijin mai mayafi ya durkusa yana yarfa hannu yace " bafa haka nake nufi ba,
cewa zanyi ka koya man assignment, a tare sauran daliban suka dau ihuuu da shewa, batare da tayi musu magana ba ta wuce abinta ta shiga ta zauna a darare.
Chapter 3 · 0% Book details