Sashe 39
Bakar Shuka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Zina tana jawo masifu da bala'i wanda duk mai hankali idan yayi tunani bai kamata ya kai kansa cikin ta ba koda babu Shari'ar da zata hana yin taba. Illar da zina take jawowa yafi dukkan yadda mutum zayyi tunani.
Shiyasa cikin hikima da Buwaya irin ta Ubangiji yace kada a kusance tama balle a aikata ta saboda irin illar da take jawowa dan Adam.
Zina tana jawo fushin Ubangiji ya sauka ga bawa komai yaki da dadi, tana jawo tawayar arziki da rashin sanin manufa a rayuwa, tana saka kuncin zuciya da munana zato ga mutane, tana tafiyar da kwarjini da ƙima a idan mutane, illar zina yana shafar har zuria ta kuma jawo musu ƙasƙan ci, tana tafiyar da imani da kunya ga mutum, tana sa mutum ya rayu cikin nadama da wulakanci.
Illar zina da munin ta yafi karfin a rubuta su, ku nisan ci zina domin babu wani alheri dake tare da ita. Allah ya tsare mu ya kare mu. Aameen!.
Sosai Malamin ya zage yayi wa'azi akan zina ya fad'i azabobin da Allah ya tanadarwa masu aikata ta, da irin bak'ar masifar da zasu tsinta tun daga zarar ransu zuwa kwanciyar kabarinsu.
Rawar da jikinta keyi ce ta haifarwa da motar yin tangal- tangal a saman titi tana yawo daga wannan hannun zuwa wannan hannun dakyar ta samu ta iya tsaida motar a tsakiyar titi masu mashina da motoci da Napep sai zaginta suke amma bama tasan suna yi ba, jin babu iskar da zata shak'a kwata-kwata yasata bud'e motar da sauri jikinta na wani irin b'ari da kyarma, yadda kasan wacce ke shirin hawa iska, ko motar bata tsaya rufewa ba ta durk'ushe a k'asa tsakiyar titi tana mayar da numfashi kamar me Asthma, sosai take hakki while hannunta dafe da k'irjinta, wani abu take ji me zafi da k'arfi yana fita daga k'irjinta, yayinda da zuciyarta ke bud'ewa tana tarwatse, gaba d'aya tsikar jikinta a tashe take saboda tsabar tashin hankali, idanuwanta sukayi jajir kamar gauta, har wani yaji take ji kamar wacce aka shak'awa tiyagas.
Baki take san bud'ewa ta furta Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un amma abun ya gagara ko kalma d'aya ta gagara fitowa daga bakinta, a jikinta take jin yadda jijiyoyin jikinta ke tsinkewa jinin jikinta na tafasa, babu bata gab'a ta jikinta da bata karye ba, in banda rawa da kerrrrma babu abinda jikinta keyi, so take tayi kuka amma ta kasa, sosai take kokawa da numfashi, tayi iya bakin k'ok'arinta dan ta samu sassauci da sauk'i amma babu sauk'in.
Dakyar ta yunk'ura zata mik'e aiko sai amai ta shiga kelaya amai sosai, cikin aman ta durk'ushe ta saki wani irin mahaukacin kuka me rikitarwa yadda kasan ranta ake zarewa, kallo d'aya zakayi mata kasan da duka zuciyarta take kukan, cikin ihuuuu da hargowa take fad'in " Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un 'yar wuta ce ni.
"Wuta zan shiga! 'yar wuta ce, in na mutu a haka wallahi wuta zan shiga, na shiga uku! idan ban tuba ba wuta zan shiga, zanyi mummunan k'arshe, na shiga uku na lalace na cuci kaina da rayuwa ta, nayiwa kaina da kaina babbar illa, illar da har abada bazata dawo dai-dai ba, na tarwatsa komai, tarwatsawar da bazata tab'a dawowa dai-dai ba, na shiga uku, na jawowa kaina abin kunya, na jawowa iyaye na da ahalina abun fad'a, Allah ka yafe min, ta k'arasa maganar had'i da d'iban k'asa tana zubawa kanta tare da dukan kanta da hannu bibbiyu.
Kuka takeyi sosai dake fitowa daga can k'ark'ashin zuciyarta, tana ihuuu tana d'iban k'asa tana zubawa jikinta, in banda Allah ya taimake ta unguwar babu mutane da an taru ana kallanta, har masu yi mata video ma da an samu, ta dad'e cikin wannan mummunan yanayi kafin ta mik'e fuska kace-kace da majina da hawaye, dakyar take iya tuk'in tana tafe hawaye na zuba danta kasa tsaida hawayenta, bama tayi k'ok'arin tsayar dasu ba, dan ita zubar ma da sukeyi sauk'i ne a gare ta.
A bakin get tayi parking motar ta fito ko rufe motar batayi ba ta tura k'ofar shiga gidan wacce ba get ba ta shige, yadda take tafiya tana had'a hanya ga k'afarta babu takalmi yasa ma'aikatan kallanta baki bud'e, tana tafe tana tangad'i while hawaye na d'iga ta mik'awa d'aya daga cikin drivers d'in gidan key d'in motar batare data ce komai ba, hannu na rawa ya amsa, ta shige gida, dama can cikin motar tabar takalmin da jakarta da wayoyinta, duk abinda ke faruwa Ajlaal na jinta, shu'umin murmushi ya saki had'i da d'ora k'afa d'aya kan d'aya yace " kin makara Deeyanah, kin riga kin makara, wallahi baki isa ki raba kanki dani ba, dan zan iya yak'ar duniya na k'arar da kowa da komai daga doran k'asa, duk wanda yace zai shiga gaba na akanta ni kuma nayi alwashin kawar dashi daga hanya ta, zanyi komai danna mallakeki, ya k'arashe maganar yana fashewa da mahaukaciyar dariya.
Direct bedroom d'inta ta wuce ta shiga bathroom ta sakarwa kanta shower batare data cire kayan jikinta ba, har lokacin jikinta b'ari yake, ta dafa bango tana cigaba da kukan, takai awanni biyu ruwan shower na sauka kanta kana ta mik'e tsaye daga zaman dirshan d'in da tayi a k'asa, kayan jikinta ta cire tsaf ta zuba su a shara gaba d'aya kyankyamin kanta da jikinta da komai ma take yi, har kayan jikinta da bathroom d'in da gaba d'aya bata san ganin komai, dan duk abinda ta kalla hotan irin abinda sukayi da Ajlaal ke dawo mata cikin kanta, ido ta runtse da k'arfi hawaye na zubo mata, cikin zafin rai ta bud'e idanuwanta da suka gama rinewa zuwa ja, da wani irin zafin rai ta nufi inda take aje soson k'arfen wanke masai tasa hannu ta damk'e shi, da wani irin k'arfi ta soma dirzawa jikinta da iya k'arfinta.
Tana kuka tamkar ranta zai fita tana dirzar fatar jikinta jini na zuba da fushi take dirzar fatar kamar zata b'aye fatar jikinta, duk tabi taji ciwo amma hakan bai dame ta ba, ta dad'e tana wankan kana ta sulele tana kuka, tayi wankan tsarki yafi sau 20 gani take har zuwa lokacin daud'ar zina bata bar jikinta ba, gani take duk yawan wankan tsarkin da zatayi bazata tab'a samun tsarkin jiki dana ruhi ba, sai da ta gaji dan kanta kana ta hak'ura ta fito daga wankan, tana d'ora idonta akan gadon dake d'akin, ta ganta kwance Ajlaal na saman ruwan cikinta suna aikata zina, ido ta runtse da k'arfi had'i da kawar da kanta gefe tace " turrrr dani, kaico na, tun yanzu tun kan aje ko'ina mugun abinda na aikata ya fara farautar rayuwata, ya fara barazana ga farin ciki na.
Durk'ushewa tayi tana kuka wiwi tare da dukan k'irjinta tana fad'in " na tarwatsa gidana, na tarwatsa ahalina, na fasa gidana, na wargaza farin cikin mijina dana d'ana, na b'ata aure na, na b'ata sunan zuri'armu gaba d'aya, Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un na shiga uku na lalace, Allah na tuba ka yafe min, Astagfirullah Astagfirullah Astagfirullah, ta k'arashe maganar da wani irin kuka.
Ji tayi ta tsani gaba d'aya gidan komai ya fice mata a ranta ta tsani kanta, duk wata kusurwa ta gidan data kalla hoton ta da Ajlaal take gani suna aikata masha'a, har aka kira magriba tana nan zaune ta had'a kai da gwiwa tana ta faman risgar kuka wiwi tun muryarta na fita har yakai ya kawo muryarta ta dishashe idanuwanta sun kumbura suntum, dakyar ta rarrafa ta shiga ban d'aki ta d'auro alwala, ta fito ta shinfid'a sallaya ta zira doguwar riga ta tada sallah, tana tada sallar saban kuka ya kwace mata, dan sai yanzu taji tana jin kunyar Ubangiji, ta tayar da sallah yakai sau biyar kuka yana sata sallamewa sai haka ta hak'ura tayi sallar hawaye na zuba, da takai sujjada me memakon karatun sujjada sai Allah na tuba ka yafe min take maimaitawa.
D'ogowa tayi ta sake sabuwar sallah amma tana kai goshinta k'asa kuka ya kwace mata, dole tayi control kukan tayi sallar, data sallame sallar sake komawa tayi sujjada takai goshinta k'asa ta soma addu'a " Ya ALLAH! kasanya mu cikin bayinka tsarkaka masu dace da ni'imar ka, gafarar ka, rahamar ka, bud'i da wadatar zuci, da tsarkin zucciya, da shiriyar mu baki d'aya, ya Ubangijin talik'ai ya majib'ancin lamura, kai ne Afuwu me afuwa, kai ne Rahamanu me Rahama, kai ne mad'aukakin sarki wanda ba'a haifa ba kuma bai haifa ba, Allah ka yafe min, ka tsarkaken zuciya ta, kayi min afuwa da sassauci, kayiwa ruhina salama, ina jin kunyarka ya Ubangiji, ina jin kunyar girman laifi na, ina jin kunyar neman afuwa agare ka, Astagfirullah Astagfirullah! Astagfirullahna wa'atubi ilaik, ta k'arashe da wani irin kuka.
Ranar kam cur Deeyanah ta kwana saman sallaya tana neman yafiya da afuwar Ubangijinta, ko gyangyad'i batayi ba, duk iya satar bacci da ake fad'a yau kam ko kusa da ita bai zo ba balle ya sace ta, bayan ta idar da sallar asuba cigaba da zama tayi akan sallayar tana jan La'ilaha Illa antassubahanaka innikuntu minal zalimin har garin Allah ya waye.
Tana zaune kan sallayar taji ana kwankwasa k'ofar part d'insu agogon bango ta kalla taga k'arfe takwas da rabi, a fili ta sauke ajiyar zuciya kana ta mik'e ta fita hannunta rik'e da carbi, sai da ya rusuna kana ya gaida ita, bata iya amsawa kamar yadda ta saba ba, ya mik'a mata jakarta da takalmin da wayarta yace " jiya nazo har sau uku in kawo miki amma baki bud'e ba, da har zan sanar dasu Abba sai kuma na tuna Bature yana ciki ai, (Bature sunan da suke kiran Deen dashi kenan) murmushin yak'e tayi mishi ta karb'i kayan batare datayi magana ba ta juya ta koma cikin gidan, d'akinta ta sake komawa ta aje kayan tana shirin shiga ban d'aki wayarta ta soma rori, babu alamun tsoro ko firgici tattare da ita duk da ta riga tasan waye me kiran.