← Book details Bakar Shuka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 56

Sashe 40

Bakar Shuka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bata kula wayar ba ta shige toilet, har ta fito daga toilet ba'a daina kiran wayar ba, amma ko'a jikinta yadda kasan ba wayarta ake kira ba, tana jan carbi ta isa inda wayar take ta d'auka da nufin kashe ta gaba d'aya, " 150 missed call, ta fad'a a zahiri cikin ranta tana jinjina daga jiya zuwa yau kawai yayi mata miss call d'ari da hamsin yaya kenan idan akayi sati, tana k'ok'arin kashe wayar kiranshi ya sake shigowa, wayar ta rik'e a hannunta tana jujjuyata tana tunanin ta d'aga ko karta d'aga " ki d'aga kiyi mishi kashedin karya sake kiranki, wata zuciyar ta bata amsa, yayinda wata zuciyar ke gargad'inta da " karki d'aga yana iya sake yaudararki.

Murmushi ta saki me ciwo tana furta " wallahi ko dad'in bakin duka mayaudaran mazan duniya za'a had'a mishi bazasu yi tasiri akaina ba wannan karon, cike da yak'ini ta d'aga wayar ta kara a kunnenta, cikin kunnenta ya sauke kasalalliyar ajiyar zuciya ya d'ora da fad'in.

"Karki fara Deeyanah, karki faro fad'an da bazaki iya kai k'arshen shi ba, karki d'aukowa kanki dala ba gammo, wallahi Deeyanah nafi hitila bala'i, dafin dake jikina yafi na bak'in maciji bazaki gaskata hakan ba sai lokacin da kikayi min taurin kai, idan kikace zaki bijirewa umarni na.....

Cikin masifa da taurin rai tace " umarninka umarnin Allah ne da idan nak'i binshi wani bala'in zai fad'a min?

"Waye kai Ajlaal?

"D'an iskan k'arshen zamani da sai da iskanci ya k'are babu komai sai kale kake yin naka?

"Banza wulak'anctacce tab'abbe halakkke d'an wuta, waye kai a duniyar iskanci da sunanka har yanzu ko unguwar da kake bai zagaye ba?

"Ina kaje ina aka sanka a duniyar shagalallu tab'abb'u da har yanzu babu wanda ya sanka a duniya?

"Duk iskancin ka ka kai Fir'auna?

"Ka kai d'an k'aruna?

"Ka kai Abu Jahil?

"Ka kai Barau kwallon Shege?

"Ko ka kai Musailamatus Kazzaba?

"Ko ka kai Abdullahi d'an Ubayyu d'an Salul?

"Ka kai Uddaru?

"Ka kai Lamaduru?

Kai da duk iskancinka baka kai Hamana ba, ko ka kai shaid'an da yayi fito na fito da Allah?

"Shi kanshi Hitilan da kake ikirarin kafi shi bala'i ko sawunshi baka taka ba.

Shiru yayi yana saurarenta har ta dasa aya kana yace " na baki na da kwana d'aya kizo idan baki zo ba.....

"Me zakayi idan ban zo d'in ba?

"Wallahi Tallahi Ajlaal ko shekara zaka bani bazan tab'a zuwa inda kake ba, an riga an gama, komai ya k'are Ajlaal an riga an buga kid'an tashi, zayyi magana ta kashe wayar had'i da jefa ta kan gado, rasa abinda zatayi yasata sulalewa k'asa had'i da sakin kuka.

Bayan sati d'aya...

Duk yadda kake zaton mutum zai shiga damuwa Deeyanah ta shiga fiye da haka, bata da aiki sai kuka, ko fita bata yi kullum tana d'aki tana aikin kuka da Istigfari, koyaushe tana kan sallaya dare da rana tana neman yafiyar Allah da karatun Al Qur'ani tana karatun hawaye na zuba, ko abinci bata iya ci iyaka ci tasha shayi, kasancewar ita da Deen tuni kusancin su ya tarwatse kowa rayuwarshi yake gudanarwa batare da d'an uwanshi ba, shiyasa Deen bai damu da rashin ganinta da bayayi kwana biyu ba, dan dama ba wani magana suke yi sosai ba sai idan ta kama.

Duk yadda Ajwaad ke tsammanin abun ya wuce nan dan shi a zatonshi da fari wasa take yi, sannu a hankali al amarin ya fara girmewa tunaninshi, duk sanda ya kira number ta bata shiga da alama ma a rufe wayar take ko kuma tayi blocking d'inshi dan ko text ya tura mata baya tafiya, iska ya kaiwa naushi tare da fad'in " shit!, me yarinyar nan ke nufi ne?

"Me take shirin aiwatarwa?

D'an shiru yayi yana tunani kana yace " wow! wai tana nufin the game is over?

"Kinyi kad'an Deeyanah, kinyi tsararo yarinya wallahi duk duniya babu wanda ya isa ya raba ni da ke, ko ke da kanki baki isa ki raba ni da kanki ba, zan iyayin komai zan iya kawar da kowa akanki, ya k'arashe maganar had'i da bushewa da mahaukaciyar dariya.

A b'angaren Deeyanah kuwa abun babu sauk'i sai azabtar da kanta da ruhinta take yi, agogo ta kalla k'arfe uku da minti 40, kanta dake barazanar tarwatsewa saboda azababban ciwon da yake yi mata ta dafe, saboda tsanin ciwon da kanta keyi har jiri ke d'ibarta, bango ta dafe da d'aya hannunta while d'aya hannun ta dafe kanta dashi, ta sunkuya zata kwanta a gado aka fisgota ta baya, sama aka d'aga ta da hannu d'aya kana aka matse ta da bango.

Wuyanta da aka shak'e ta soma kiciniyar kwacewa amma ta kasa, soma dukan hannun da aka shak'etan tayi amma a banza, sai da ya gaji dan kanshi kana ya sake ta, ta fad'i k'asa da rarrafe ta kama gado ta kifa tana tari, ta dad'e tana tarin hawaye da majina na zuba kana ta d'ago ta zuba mishi jajayen idanuwanta da hawaye ke zubawa dakyar muryarta bata fita sosai tace " kayi hauka ne?

"Ko kana so ka kashe ni ne?

Hannunshi ya sanya cikin wondon 3 quarter dayake sanye dashi.

"Me kike nufi Deeyanah?

Mik'ewa tayi ta nufi inda hijabinta ke aje ta d'auka ta saka cikin nutsuwa ta kallanshi ta nuna mishi k'ofa tace " fita!

"Wow! yace yana tafa hannu had'i da jijjiga kanshi, tun daga k'afarta ya d'auko kallo har izuwa fuskarta ya kwashe da dariya har da rik'e ciki yace " abun mamaki wonder shall never end!

"Ni! wai kike sakawa hijabi yau?

Ya fad'a still yana dariyar, zagaya ta ya soma yi tare da sanya hannu ya rik'e hijabin jikinta, " me yayi saura Deeyanah?

"Meye ban gani ba meye kuma ban tab'a ba, meye bak'ona a jikinki?

Ido ta runtse da k'arfi hawaye na gangarowa saman kuncinta, sai da ta cije lips d'inta kana ta bud'e idonta gami da nuna mishi k'ofa tace " fita!

Hijabin nata ya saki yaja baya yana kallanta yace " kuma fa sai naga kin k'ara kyau, kinyi fess dake kamar sabuwar budurwa dad'i na dake bakya tsufa ga kuma dad'i a gado, ya k'arashe maganar had'i da kashe mata ido d'aya, " ashhhhh yace yana mik'a, " dan Allah muje ki d'an lugwigwita ni a gado kamar yadda kika saba, kin gane ai, ido ta sake runtsewa da k'arfi kana ta bud'e su cikin d'an d'aga murya tace " nace ka fita ko?

Ta fad'a tana nuna mishi k'ofa, shu'umin murmushi ya saki yana d'aukar steps zuwa gare ta, hannunshi ya sanya ya zagayo da ita ta baya ya rik'o k'ugunta had'i da matso da ita daf dashi ta yadda suna iya jiyo fitar numfashin juna, ya sanya yatsunshi biyu yana shafa gefen kumatunta, muryarshi can k'asan mak'ogwaro yace " zan iyayin komai akan soyayya ta, ina sanki sama da komai da kowa Deeyan....

Hannayenta ta saka ta hankad'a shi baya da k'arfi ya sake yowa kanta zai rungume ta, kafin ya k'araso ta kifa mishi mari da iya k'arfinta ji kake tassss!, ta nuna shi da yatsa cikin bushewar zuciya da k'ek'ashewar rai, kallo d'aya zakayi mata kasan ta gama kaiwa k'arshe ta jefa idonta cikin nashi tana kallan cikin kwayar idonshi babu d'igon tsoranshi a cikin ranta, saboda tsabar b'acin rai jijiyoyin kanta sun fito sunyi rad'o-rad'o while duk ilahirin jikinta na tsuma.

"Karka kuskura ka sake matsowa kusa dani, ko taku d'aya ka k'ara sai na shayar dakai giyar mamaki Ajlaal, banza k'azami, wulak'antacce k'ask'antacce tab'abbe, wanda idan baka tuba ba sai kayi irin mutuwar karnuka, babu abinda ke damunka sai duhun jahilci na rashin ilimin addini, Basaan da Halimatu sun cuce ka da basu baka ingantacciyar tarbiyyar addinin Islama ba, na tsane ka Ajlaal na tsane ka fiye da mutuwa ta, idan da mutumin da nake san ganin mutuwarshi to kai ne, ban k'i naga gawarka kwance a gaba na ba, duk da zan so ace sai ka wulak'anta irin wulak'antar dako kafiri mak'iyin Allah yayi ta sai an tausaya mishi, ka cuce ni Ajlaal, ka lalata min gobe na, ka tarwatsa duniya ta da komai nawa, ka jefa ni cikin k'uncin da har in mutu haske bazai tab'a gauraye duhun ba, har in mutu bazan tab'a yafewa kaina ba, ni da farin ciki da walwala har izuwa fitar numfashi na na k'arshe.

"Allah ya isa Ajlaal, Allah ya isa na, Ubangiji ya saka min, sakayya cikin gaggawa, durk'ushewa tayi a k'asa had'i da sakin rikitaccen kuka tana fad'in " ka lalata min komai, babu abinda yayi saura komai ya lalace, Allah ya isa tsakani na dakai, Ubangiji yayi min sakayya.

"Ni kika mara Deeyanah?

Damk'o ta yayi ya d'ago ta sama cikin matsanancin b'acin rai ya kalle ta da jajayen idanuwanshi yana fad'in " ni kika mara?

Kakin majina tayi ta tofa mashi a fuskarshi ta d'ora da " an mare ka waye kai?

" Har yanzu da alama baki san waye ni ba.

"Kai ne a jikin dubu d'aya ko d'ari biyar da ya zama dole saina sanka.

Sakin ta yayi ta fad'a saman gado yasa yatsa ya dankwalo majinar data tofa mishi, ya kalli yatsan gami da yin murmushin gefen baki, sai kuma ya had'e fuskarshi yadda kasan bai tab'a yin dariya ba, ya durk'usa dai-dai fuskarta ya nuna mata yatsa yadda kasan zai tsone mata ido cikin matsanancin b'acin rai ya soma magana " baki isa ba Deeyanah, zan baki zab'i biyu kad'ai imma dai ki kashe aurenki kizo muyi aure mu rayu mu biyu a cikin duniyarmu daga mu sai 'ya'yanmu, ko kuma kizo mu cigaba da d'orawa daga inda muka tsaya, ina nufin kizo muci gaba da more rayuwarmu kamar yadda muke yi ko kuma..... ya cije leb'enshi.

Hankad'a shi baya tayi ta mik'e a haukace tace " ko kuma me?

"Ko kuma zan kashe Deen, ko kuma zan kashe gaba d'aya ahalinki, ko kuma zan k'arar da gaba d'aya danginki ko kuma na kashe tilon d'anki ko kuma zan saki videon ki ta fad'a a haukace, duk tabi ta haukace masa, " su kenan iya abinda kake tak'ama dasu?

" Shikenan iya barazanar taka kenan ko?
Chapter 40 · 0% Book details