← Book details Bakar Shuka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 51 OF 56

Sashe 51

Bakar Shuka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Fitowa tayi daga inda take labe ta zare key d'in kana ta kunna hasken d'akin, d'agowa yayi cike da mamaki, yana d'ora idonshi a kanta yaji wani k'ululun bak'in ciki ya tokare mishi mak'ogwaro, d'an sauk'in daya samu kwana biyu take ya gushe, fuskar nan kamar wanda aka saukarwa da sak'on mutuwa, babu d'igon annuri, tashi yayi zaune yana tsare ta da idanuwanshi jajaye, saban tashin hankali da tsoronshi ne suka saukar mata lokaci d'aya, tsare tan da yayi da ido yasa ta dabarbarcewa, jikinta na kerrrma ta nufe shi, kallan karki soma zuwa inda nake yayi mata, amma ta cigaba da nufarshi, gabanshi ta zube had'i da d'ora hannunta saman cinyarshi tana kuka wiwi, ai ji yayi kamar ta nana mishi k'arfen daya shekara a cikin wuta, zabura yayi ya mik'e had'i dasa k'afa yayi ball da ita yana huci yace " wallahi karki soma rab'a ta, bata damu da fashewar da bakinta yayi ba, kota kan jinin dake zuba bata bi, ta mik'e tana fad'in " dan Allah, dan Allah Yaya ka saurare ni.

"Bazan saurare ki ba, bazan tab'a saurarenki ba har a tashi duniya dan baki da abinda zaki fad'a min, baki da abin cewa, hawayen bak'in cikin suka taru a idonshi, bayyi k'auron hanasu zubowa ba.

"Kin san k'arfin sha'awata, kin fi kowa sanin yadda nake san sex, amma kika hanani kanki duk da haka na jure har tsayin shekaru uku ban fad'awa kowa ba, Allah shine shaida ko hannun mace ban tab'a rik'ewa ba, na kama miki kaina na killace da yak'inin kema zaki killace min kanki, a kullum zuciyata tana k'ok'arin zarginki amma ina dannewa ina baki uzirin akwai dalilin daya saki kike yin hakan, duk daren duniya k'ofar d'akina a bud'e take har garin Allah ya waye ina sa ran wata rana zaki zo, hawayenshi ya goge had'i da had'iye abinda ya tokare mishi mak'ogwaro.

Wallahi Yaya ba asan raina abin ya faru ba, kidnapping d'ina yayi, daga nan ta bashi labarin farkon sake fad'uwarsu lokacin da zata je asibiti da lokacin daya turo mata video, "idan zaka iya tunawa a lokacin har kwanciya nayi a asibita na shiga matsananciyar damuwa.

"Babu irin tambayar da ban yi miki akan ki sanar dani damuwarki ba amma kika k'i, har rok'onki nayi.

"Tsorata ni ya rink'a da video da kuma zai kashe kowa nawa yayi, ta fad'a cikin matsanancin kuka.

"Yaya cewa yayi idan na baka kaina sayya kashe ka, sayya k'arar da gaba d'aya zuri'armu, da nak'i jin kashedin shi na baka kaina shine fa ya caka mata wuk'a a zuciya.

"Wallahi Yaya nima ba'a san raina komai ya faru ba dole yayi min, "shiyasa har kika d'auki cikinshi?

"Jin tambayar tayi kamar daga sama dan bata san da maganar b'arin da tayi ba, cikin mamaki tace " ciki kuma?

Murmushi yayi me ciwo yace " likitan daya dubaki bai fad'a miki kinyi b'arin cikin wata hud'u sakamakon dukan danayi miki ba?

Cikinta ta shiga shafawa tamkar wacce ta zauce tana girgiza kanta ta kasa furta koda kalma d'aya.

"Kin kai mak'ura Deeyanah da aure a kanki kika d'auki cikin wani, mijinki na aure daban uban d'an cikinki daban.

Kanshi ya shafa yana tattare gaba d'aya damuwarshi a k'irjinshi, dakyar ya furta cikin Aj.... Sai ya d'anyi shiru kana yace " Ajlaal, bayan kin san irin tsanar danayi mishi, kin fi kowa sanin na tsane shi fiye da mutuwa ta, wallahi gwara ace min duka mazan Nigeria sun sanki a 'ya mace akanshi kad'ai ya sanki, nasha fad'a miki bana k'aunar ko sunanshi, amma duk da haka kika bashi kanki, zan iya yafe miki idan akace min mazan duka duniya sun kwanta dake amma bazan tab'a iya yafe miki ba idan Ajlaal ya rik'e hannunki balle ya sanki."Abin da ciwo! Deeyanah, da ace baki sani bane da sai nayi miki uziri to amma kin sani, kin san komai.

Cikin kukan mutuwa tace " idan nak'i yarda dashi zai kashe ka, zai kashe kowa...

Cikin hargowa yace " to sai me!?

"Meyasa baki bari ya kashe duk wanda zai kashe ba?

"Meyasa baki bari ya kashe ni ba?

"Wallahil azim na gwammaci mutuwa sau dubu idan anayi akan ganin wannan mummunan rana, amma kije bakomai burinki ya cika kin lalata min komai kin tarwatsa min rayuwa da farin ciki na, nida jin dad'in duniya har ranar da mutuwa ta zata riske ni, amma kafin nan zan tabbatar min da kalamaina na idan kika sake kika ci amanata zan rabu dake rabuwa ta har abada kuma har a tashi duniya baki sake ganina ba, zatayi magana yace " dan Allah karki sake nuna min wannan bak'ar fuskarta ki.

"Dan Allah ka fahimc.....

Wani k'ululun bak'in ciki ya had'iye hawaye nabin fuskarshi da wata irin murya me tsartsi yace " Deedee d'a na ne ko shi ma....?

Tun kafin ya gama maganar ta soma girgiza kanta while hawaye me k'una nabin kuncinta.

"Wallahi d'anka ne, Abduljalal d'anka ne halak malak Yaya.

"Abun harya kai haka Yaya?

"Har ya kai ka fara zargin Abduljalal ba d'anka bane?

"Dan Allah karkayi min haka Yaya, karfa ka manta kaine ka fara sani na 'ya mace, kaine kayi disvirgin d'ina.

"Bani da tabbaci akan budurcinki balle kasancewarshi d'a na.

Zatayi magana yace.

"Fita!

"Please Yaya!

"Out...!

Ya fad'a da k'arfi har saida d'akin ya amsa.

"Yaya kayi min uzuri please.

I said get out!

Ko gezauna batayi sai sautin kukanta data k'ara, hak'ark'arinta ya damk'a ya jata zuwa waje, k'ofar ya soma k'ok'arin bud'ewa yaji ta a rufe sai lokacin ya tuna da ya rufe k'ofar ta d'auke d'an mukullin hannunta ya murd'e da k'arfi ta saki k'arar azaba gami da sakin key d'in, ya d'auka ya bud'e d'akin ya hankad'a ta waje ya mayar da d'akinshi ya rufe.

************Sandarewa Ajlaal yayi a zaune cikin matsanancin mamaki kamar mutum mutumin da aka shuka, ya zubawa system d'in ido kamar yana jiran wani abu ya fito ta cikinta, cikin kame-kame ya furta " wait what!?

"Ciki!?

" Deeyanah ke d'auke da ciki na har na wata hud'u?

Jin abin yake kamar a mafarki, wani bak'on yanayi yake ji a jikinshi, ya kasa fahimtar komai, idan dai ba kuskuren fahimta yayi ba, Deeyanah ta samu ciki, amma sakamakon dukan da Deen yayi mata cikin ya zube, ihuuu ya saki da k'arfi ya d'auki laptop d'in ya buga da k'asa, ranshi yakai k'ololuwar b'aci, abinda fa ya dad'e yana nema ne, amma shine dan tsabar mugunta yayi sanadin fitar cikin?

Yadda kasan mayunwacin zaki haka yake nishi yana fitar da gurnani, sai huci yake kamar kububuwa, "no! tab! wallahi akwai bala'i tunda ya salwantar min da d'ana wallahi saina rama saina kashe tilon d'anshi ai d'a baifi d'a ba, ya fad'a out of control.

Mik'ewa tayi daga kan stool d'in daya jefa ta, ta bugu sosai, tana tafe tana tana tangal-tangal, Ammu da Babah suka sauke ajiyar zuciya a tare, cikin sanyi Ammu tace " ya kamata a kira yaran nan aji meke faruwa a tsakaninsu fa, " munyi magana da Abbi zamu kira su in sha Allah.

Tana dafe da k'irjinta while tana haki ta shiga part d'insu, a falo k'asan carpet ta zube tana mayar da numfashi, k'afarshi dake kan d'aya ya sauke yana kallanta deep down yana jin wani abu dabe san kome nene ba yana ratsa shi, a kasalance ya kira sunanta " Deeyanah!

Cak zuciyarta ta tsaya, wanda ita kanta bata san dalilin tsayawar zuciyarta ta ba, kodan batayi zaton yana wajen bane sai jin muryarshi tayi oho, zambur tayi ta mik'e, tana kallanshi, ta cikin kwayar idonta ya hango zallar k'iyayyarshi, guntun murmushi yayi yana fad'in " duk abinda nayi sanki ne sila Deeyanah, ya riga ya sake ki saki uku babu abinda yayi saura tsakaninku, please ki dawo min, kakin majina tayi ta kwamb'ala mishi a fuska, ta d'ora da " tur da kai da halinka, wallahi ko zan mutu bazan tab'a aurenka ba, koda kuwa hakan yana nufin mutuwa ta, Allah ya tsare ni wallahi, murmushi ya sake yi a karo na biyu kana yace " duk ba wannan ne ya kawo ni ba yanzu, nasan akwai lokacin da dole baki da zab'in daya wuce ni.

"Wallahi koda zan rasa kowa da komai, koda duniya da abinda ke cikinta zasu guje ni wallahi bazaka tab'a zama madogara ta ba, bazaka tab'a zama zab'i na, na k'arshe ba.

"Ashe duk wannan lokacin kina d'auke da gudan jina na ban sani ba, sai da ya cije lips d'inshi alamar zafin zuciya kana yace " shine wancan tsohon mijin naji bak'in mugu azzalumi munafuki yayi sanadiyyar salwantar min da d'ana na fari?

Sosai yadda yake magana da kwarin gwiwa ya bata mamaki, ya wani hak'ik'ance akan d'an shege, "akan d'an shege d'an zina kake jefar mijina da wad'annan maganganun?

"Out of correction, ba mijinki ba tsohon mijinki.

Kalmar tsohon mijinki ta dake ta sosai, ta maimaita kalmar cikin kanta yakai sau biyar, " bariki ji wallahi tallahi saina rama akan d'anshi yadda ya kashe min gudan jini na, sai na d'auki fansa akan Deedee wallahi, tashin hankali wanda ba'a saka maka rana, sai yanzu ta yarda da ake cewa tashin hankali ma hawan hawa ne, wani wan wani ne, dan sai da numfashinta yayi fitar bargu na wucin gadi, a haukace ta nufeshi tana girgiza kanta, " a'a dan Allah kome zakayi min kayi min amma karka tab'a min yaro dan Allah, karka saka shi cikin wannan abun ba ruwanshi please.

"To idan ban tab'a shi ba wa kike san na tab'a wanda ya kashe min nawa d'an?

Cak ta tsaida kuka danta fahimci Deen yake nufi.
Chapter 51 · 0% Book details