Sashe 53
Bakar Shuka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Har haka kake santa?
"Fiye da haka ma, ina santa fiye da so, ina santa fiye da rayuwata, ina santa fiye da komai da kowa, zan iya rabuwa da kowa a kanta Babah, Deeyanah itace rayuwata, itace hasken duniya ta, itace haske a gare ni a duk yayin dana kasance a cikin duhu, itace duniya ta, itace ji na itace gani na itace komai nawa Babah, ina fatan na rayu da ita har rai da mutuwa, ina rok'on Allah yasa har a aljanna mu kasance tare...
Ajiyar zuciya Babah ya sauke bayan ya gama tunaninshi, cikin ranshi yana juya girman al amarin da zai juyar da irin wannan k'arfefaffiyar soyayyar zuwa cakud'add'iyar k'iyayya, ya tabbatarwa kanshi akwai gagarumar matsalar da saita shafi kowa.
**************************
Tana durk'ushe ta cusa kanta tsakankanin cinyoyinta ba kuka take yi ba, abin duniya ya ishe ta, kyalkyalewa yayi da mahaukaciyar dariya har da buga k'afa, tana jinshi amma ko gezau batayi ba, sai da yayi me isarshi kana ya durk'usa kusa da ita ya zuba mata ido yana kallanta yana dariya, ya d'an d'auki lokaci a haka kana yace " mijinki na farko ya kashewa mijinki na biyu d'a, shi kuma mijinki na biyu yaga bazai iya hak'uri ba shine ya rama ya kashewa mijinki na farko d'anshi shima, kinga mijinki na farko ya rasa d'a d'aya haka ma mijinki na biyu, sai dai ke 'ya'ya biyu kika rasa, ya kenan?
Zaman dirshan yayi a k'asa ya nutsu sosai kamar gaske yace " Deeyanah yanzu dai duk abinda zai faru ya riga ya faru sai dai a guji gaba laifi ne kunyi min keda mijinki amma ba komai na yafe muku, abinda nake so dake yanzu shine ki dawo mu cigaba dayin normal life d'inmu kamar da, mu cigaba da tsinkar korayen fure, sai lokacin ta d'ago da kanta ta sauke mishi ramammun jajayen idanuwanta akanshi, ko gezau bayyi ba saima cigaba da magana da yayi " mu cigaba da jin dad'in mu muna morar juna, amma fa sai inkin so zamu cigaba da aikata zina, muna iyayin auren mu, a wanke minke tass tass akai min gida na.
Bata san sanda k'untaccen murmushi ya kwace mata ba, lips ta cije da k'arfi har sai da hak'oranta suka fasa lips d'in, " me jiya tayi balle yau Ajlaal?
"Abinda jiyan batayi ba shine nake san yau d'in tayi ai.
Ya bata amsa yana gyara zamanshi, cikin kwayar idonshi ta kalla sosai kana tace " wallahi tallahi kasa a ranka nice ajalinka Ajlaal Basaan, a wad'annan tafukan hannun aka rubuta mutuwarka, ta fad'a tana nuna mishi tafin hannunta, "wow! wannan wanne irin daddad'an albishirin ne, aiko dana kasance mutumin dayafi kowa sa'a a duniya zan mutu a hannun abin k'aunata, itace abu na k'arshe da zan gani, akan tafukan hannayenta zan ja numfashi na na k'arshe, amma kafin nan kizo mu more rayuwarmu mana.
"Dan Allah me nayi maka a rayuwa?
"Wanne laifin na aikata maka da kake azabtar dani har haka?
"Guje min Deeyanah! guje min da kikayi shine kad'ai laifinki kuma ko yanzu kika ce zaki cigaba da guje min wllh bakiga komai ba.
"In dai k'auracewa sab'an Allah shine laifi na to kuwa yanzu na fara guje maka, kuma har abada zan kasance me guje maka me addu'ar neman tsari daga sharrinka.
Murmushin gefen baki yayi kana yace " wallahi tallahi idan baki dawo mun cigaba da rayuwarmu ba ko kizo muyi aure ba wallahil azim saina sakarwa duniya videonki dan bazai yiyu ki lasa min zuma a baki ba sannan kizo ki hana ni wallahi k'arya ne.
"Ba duniya ba ka sakarwa har lahira ka sakashi a majigi ka haska kowa ya gani koka harba shi duniyar mass yadda kowa zai gani bai dame ni ba, kuma ko'a jikina abinda na sani shine har abada bazan tab'a dawo maka ba, ko'a mafarki bazan tab'a aurenka ba, kai Allah ya tsinewa mafarkin da zai zo min dakai a cikinshi.
Tuntsurewa ya sake yi da mahaukaciyar dariya yana fad'in " to kuwa ki shirya dan daga yau komai yana iya faruwa, dan muddin bazan same ki ba sai dai ayi biyu babu kowa ma ya rasaki, mik'ewa yayi tsaye yana kallanta yace " zan baki lokaci kiyi tunani kafin ki yanke hukuncin da zai k'arasa wargaza miki d'an sauran farin cikin daya rage miki.
"Babu wani tunanin da zanyi indai akanka ne wallahi, nayi maka alk'awarin bazan tab'a dawo maka ba har abada.
"A'a fa Deeyanah!, kada kiyi wasa da wuta.
"Wasa da wuta kam aina gama yinshi harma ta k'ona ni, da tabanta zan mutu.
"To kuwa ina yi miki albishir d'in sakin videonki a social media wallahi tallahi.
Bakinta bud'e tace " da waya hanaka ka saki?
"Ka dad'e baka saki d'in ba sakarai shashasha kawai.
Dariya yayi ya juya ya taka zuwa k'ofa, har zai fita ya juya ya kalleta yace " ina yi miki albishirin duk duniya babu namijin daya isa ya mallake ki wannan alk'awarina ne, yasa kai ya fice, taso taje ta sanar da Deen halin da ake ciki amma tasan kota je bazai saurare ta ba dole tasa tayi hak'urin amma tasan tunda yace zai saki videon to kuwa tabbas ba makawa sayya saki d'in.
K'arfe goma sha biyu na dare ya saki video a Instagram, Twitter, Facebook, WhatsApp, TikTok, da Snap Chat, dayake sababbin account ya bud'e bada tsofaffin nashi yayi amfani ba yasa video bayyi saurin karad'e social media ba, sai da yayi rubutu a k'asa video kamar haka.
Wannan wata matar aure ce da take aikata zina da aurenta me suna Deeyanah Abduljalal matar Deen Abdulrasheed, aiko kafin asuba video ya gama karad'e duk wata kafar sada zumunta, aka rink'a forwarding groups to groups, cikin rashin sa'a aka tura videon group d'in da Azan Yayan Deeyanah ke ciki, yana zaune a falon Ammu tana kallan Tv shi kuma yana chart videon ya shigo shi bai ma kula da rubutun da akayi a k'asan videon ba kawai ya kunna videon kasancewar fuskarta ta fito tarwau sosai yasa ya gane ta, hannunshi na wata irin rawa ya koma group d'in sai a lokacin ya kula da rubutun ya maimaita sake karanta rubutun cikin kanshi yafi sau 100 kafin ya fahimci abinda aka rubuta.
Tashin hankali, bai san sanda wayar ta sub'uce daga hannunshi ba while videon yana yi, kamar ance Ammu ta kalla idonta ya sauka akan videon, taso ta kawar da kanta daga kan videon amma ina yadda kasan dansu kalli videon aka halicce su, kamar an dasa su akan videon Azan bayyi k'ok'arin hana Ammu kallan videon ba dan bai ma san inda kanshi yake ba, sai da videon ya gama ya kashe kanshi, wani irin abu Ammu take ji aduk sassan jikinta, dukkansu sun sandare a zaune, wata irin rawa da kerrrrma jikin Ammu ya d'auka lokaci.
"Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un dama abinda Deen ya gani kenan?
"Kenan wannan shine dalilin sakin da Deen yayi mata?
"Lalle Deen yayi namijin k'ok'arin daya iya daurewa ya jure ya rik'e wannan masifar shi kad'ai a cikin ranshi, zuciyarshi tayi dauriya da bata fashe ba Ammu, Azaan yayi maganar kamar zararre, suturai marasa kan gado ya rink’a zubawa Ammu, ya dad’e yana soki burutsun shi kafin ya fahimci shirun da falon ya d’auka,
kallan Ammu yayi tare dakai hannu jikinta ganin idanuwanta a bud’e amma basa motsi, duk jikinta ma babu inda yake motsi, yana tab’a ta tafi luuuuuu sai timmmm! Ammun ta kifa ta fad'i k'asa tana daga zaune, jikin Azaan na b'ari ya mik'e tsaye yana salati.
Hannun Ammu d'auke da towel ta fito daga kitchen tana amsa sallamar Abbi daya shigo, lokaci d'aya idanuwansu suka sauka akan akwatin tv, b'aro-b'aro hotan fuskarta ya fito sai dai an saka dishi-dishi an rufe tsiraicinsu, da dabara Abbi ya had'a kalmomin ya karanta headline d'in jikin labarin, cikin firgici Abbi da Ammi suka kalli juna kana sukayi saurin mayar da kallansu ga tv, da gudu su Azran suka shigo part d'in, turus sukayi gaba d'ayansu a falon Abbi ya kallesu suka kalle shi.
"Gaba d'aya social media da duniya ta d'auka Abbi babu wanda baiga videon nan ba, duk k'asar nan har k'asashen k'etare babu wanda bai san halin da ake ciki ba, abokanaina daga wajaje daban-daban sai kira na suke yi, Vakil ya fad'a cikin k'unci.
"Wai meke faruwa ne?
Azran dake tsaye k'afarshi na kasa d'aukar shi ya fad'a, "Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un, Abbi yace yana zama akan kujera had'i da cire hular kanshi, jiri ne ya d'ebi Ammi Azaan yayi saurin tare ta.
Fad'ar halin tashin hankalin da zuri'ar su Deeyanah suka shiga b'ata lokaci ne, duk yadda suke tunanin zasu shiga cikin k'unci da damuwa sun shiga fiye da haka, gidan ya koma tamkar mak'abarta babu walwala kai ko maganar kirki babu meyi sai in ta zama dole, Ammu kam sai da tayi sati d'aya a asibiti unconscious bata san inda kanta yake ba, jininta yayi masifar hawa, duk iya taimakon da likitoci zasu bata sun bata amma a banza, likitan yayiwa Babah bayani da fad'in " gaskiya komai yana iya faruwa dan tasamu mugun shock wanda ya haifar mata hawan jini sosai, sai dai muyi addu'ar Allah yasa idan ta farfad'o kada wata matsala ta biyo baya.
Kusan gaba d'ayansu suna a asibitin duk sunyi jigum-jigum Vakil ne ya fara lura da idon Ammu na motsi, cikin sanyin magana yace " Abbi tana motsi, gaba d'aya sukayo kanta, so take tayi magana amma ta kasa, tana ta k'ok'arin d'aga hannayenta ta kasa, Babah ne ya lura da hakan, da gudu ya tafi kiran likita, basu b'ata lokaci ba suka dawo tare da likitan, ya duddubata sosai, ya d'ago cikin jimami ya kalli Abbi da Babah a nutsu yace " sai dai kuyi hak'uri kamar yadda nayi muku bayani a baya, koda ta farka wata matsalar tana iya biyo baya, ta farka amma ta had'u da shanyewar b'arin jiki, kuma shima d’ayan b'arin jikin nata bamu da tabbacin zayyi aiki sosai kamar da.