Sashe 4
Bakar Shuka Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Nasmah ta shigo da sauri ta zauna kusa da ita tana sauke ajiyar zuciya tace " ina ta nemanki a waya na rasa ki, takaitaccen murmushi Manassah tayi mata batare da tayi magana ba, Nasmah zatayi magana wani ya shigo yace " Manassah kizo inji HOD,
kallan juna sukayi ita Nasmah kafin Nasmah ta kalli saurin tace " lafiya kuwa?
" Ban sani ba, abinda na sani shine yace na kira ki, murmushin yake tayi tana fad'in ina zuwa, tayi maganar tana mik'ewa.
Durkushe suke gaban HOD sai da ya dan dauki lokaci yana rubuce-rubuce a wasu file kafin ya rufe ya mayar da hankali kansu,
ya dade yana kallansu tare da nazartar yanayinsu kafin ya cire farin glass din dake manne a fuskarshi wanda kallo zakayi mishi ka gane Medical ne,
ajiyar zuciya ya sauke bayan ya gama kallansu yace " magana ta gaskiya kin bani mamaki Manassah, ban ji dadin abinda kika aikata ba,
magana tabi ta cika makaranta kamar iska, me yakaiki da aikata wannan aiki?
"Ba duka abinda muke so muke samu a rayuwarmu ba, abubuwa da dama muna hakura dasu saboda goben mu,
saboda bamu san me gobe zata haifar ba,
iya abinda ke rubuce a kaddarar rayuwarmu shine ya abinda zai same mu, masoyi ko makiya babu wanda ya isa iya sauya mana komai face abinda Ubangijin Sammai da Kassai ya zartar a rayuwarmu,
kamar ke kinga kin b'ata goma daya bata gyaru ba, kin kai mishi tallar kanki baki samu biyan bukata ba sai wulakanci da cin mutunci,
kodan darajar family ki da iyayenki bai kamata kiyi haka ba Manassah, hawayen da suka fara zubowa daga idonta tun daya magana ta goge tana fad'in " Malam kaima ka yarda zanyi hakan?
"Ka yarda da abinda kowa ya yarda dashi?
"Bayan babu wanda yake da tabbaci akan abinda ya faru, jita-jita da ji da jiyarwa ne irin ba mutanen wannan zamanin,
wanda babu wani abu da suka iya ko suka kware akwai face yada alfasha da sharri, kage da abinda baka ji ba baka gani ba,
sau da dama muna yin alkhairi da ayyukan kwarai amma ba'a fadarsu kadan kaddara zata sa kayi kuskure a soma yamadidi, wanda baiji ba, bai gani ba, baiga wanda yaji koya gani ba amma kaga ya zakalkale yana rantsuwa kamar agabanshi akayi,
wallahi Malam ba abinda ya faru kenan ba, daga nan ta kwashe duk abinda ya faru ta sanar dashi, numfashi ya fitar yace " to yanzu idan ni na yarda na kuma san bazaki aikata hakan ba sauran mutane fa?
Kanta ta dukar muryar na rawa tace " akwai Allah, sosai yayi musu nasiha mai ratsa jiki kana ya sallame su,
tafiya kawai take batare data san inda take jefa k'afarta ba, ta bayanta wani ya rabo ya d'aga murya yace " ashe bamu bane kadai 'yan iskan ba?
"Duk wanda ya samu dama zai dama, wani yayi caraf ya amshi " ah namu ne ya fito fili kuma gwara mu maza ne duk abinda zamuyi ado ne,
wata mace tace " muma da muke matan bamu taba kai tallar kanmu an dizgamu ba, wanda yace yanayi damu dashi muke yi,
" ana ganinsu kamammu na Allah ashe duk zamuce ta tadda muje mu, taku kawai aka fimu iyawa, da gudu tayi waje tana tare kukan daya ci k'arfinta da tafukan hannayenta,
anan tabar jakarta da sauran kayanta Nasmah ta nuna su da yatsa tare da cije lebenta na kasa tayi kwafa, tace " kuji tsoron Allah ku tuna akwai ranar da zakuyi bayani a bisa ayyukanku.
Napep ta shiga tare da bashi umarnin ya tafi, Nasmah ta k'araso wajen da sauri ta shiga cikin napep, sosai Manassah ke kuka wiwi tana fad'in,
" na hak'ura da karatun na hak'ura da makarantar nan, daga yau bazan sake zuwa ba, na bar makarantar har abada, Nasmah da ke girgiza kanta tunda Manassah ta soma magana tayi saurin cewa " a'a karkiyi haka please, K'uduri yafi rayuwa mahimmanci, Idan har wancan kudirin alkhairi ne ga alumma to lalle zai zama ukuba ga masu neman tauyeki, rayuwa zata iya canja miki a cikin mintuna kalilan abinda kika Saba dashi zai iya sauyawa zuwa Wanda baki taba tunani ba, bakin ciki ko farin ciki, rashi ko samu, Allah yana jarabtar bawa ta kowanne fanni,
ajiyar zuciya Manassah ta sauke tana cigaba da tsiyayar hawaye, Nasmah ta cigaba " akwai mafita idan har zakiyi, sai dai nasan ba lalle ki iya yi ba,
da sauri Manassah ta kalle ta tana fad'in " wacce irin mafita ce?
Kallan me napep din Nasmah tayi kana ta kalli Manassah tace " ki bari zanzo gida nayi miki bayani, sai dai akwai yiyuwar ba lalle ne ki iya aikatawa ba,
hakan kuma shi kad'ai ne mafita, then ina tsoron na bud'e miki SIRRIN RAYUWATA, ki k'i yi, daga karshe ma ki guje min ko ki rinka man wani mugun kallan,
har suka isa gida babu wanda yayi magana cikinsu, kowannensu da abinda yake sakawa cikin ranshi, ita Manassah tana mamakin kalaman Nasmah, cikin ranta tace " wacece Namsah?
" meye sirrin rayuwarta da take tsoron bayyana min?
Batare da tayi magana ba ta sauka daga napep din na shige gida Nasmah nayi mata magana bata juyo ba......!
*Cigaban Labari....*
Bata damu da yadda hawaye ya jik'a mata fuska ba, ta mik'e dakyar tana d'ingishi tabar cikin bolar, hanjin cikinta ya fara juyawa alamar yunwa take ji,
yadda kasan mahaukaciya haka Deeyanah ke tafiya ba takalmi, kafarta duk faso ta tsatstsage jini na bin k'afar, kayan jikinta sunyi fata-fata sun yage,
da bak'ar leda tayi dan kwali ta rufe gashin kanta, koda wasa batayi gangancin bi ta inda gawar mutanen daya kashe suke ba,
danta tabbatar zuwa yanzu mutane sun cika wajen, ta baya ta zagaye tayi ta tafiya ga yunwa da k'ishirwa na azalzalarta,
tayi tafiya takai ta awa biyu kafin takai bakin titi, jikinta na b'ari ta galabaita sosai harta manta da wacece ita, ta isa gaban wani shago muryarta sark'ewa tace " ru....ruwa
Bakinshi a sake yake binta da kallo tun daga sama har k'asa, tunanin daya fara zuwa ranshi ko mahaukaciya ce, bayyi magana ba ya mika mata pure water, jikinta na rawa ta wafta a hannunshi cikin abinda bai wuce dakika biyu zuwa uku ba ta zuke ruwan tas ta yadda ledar,
ta kara zuba mishi ido a karo na biyu, " baki k'oshi ba?
Da sauri ta daga mishi kanta alamar eh, bayyi magana ba ya mika mata wani ruwan, ta amsa ta shanye duka, cike da tausayawa yace " kin koshi?
"Kai ta daga mishi tana fad'in " Alhamdulillah, da sauri ya juyo ya kalleta yana mamaki dan har lokacin yayi tsammanin bata da hankali, " nagode tace tana barin wajen, yabi bayanta da kallo cikin ranshi yana mamaki mace har mace amma ta zata kamar tababbiya saboda yanayin rayuwa,
tsaye tayi gaban mai saida doya da kwai, ta k'urawa doyar ido bata ko kiftawa, jikinta har rawa yake saboda matsananciyar yunwar dake azalzalarta,
kallanta mai doyar yayi cike da k'ama yace " bar wajen nan, da ido kawai Deeyanah ta bishi batare dayi abinda yace ba, a tsawace yace " nace ki bar nan ko?
Deeyanah bata motsa ba ta cigaba da kallan doyar, zayyi magana wani dake zaune yana cin soyayyar doya da kwai yace bata ta biyu,
jin ace a bata yasata ta kalli Wanda yace abatan hawaye na gangaro mata tace " nagode sosai Bawan Allah, Ubangiji ya biyaka, ya amsa da Amin, me doyar ya d'ago kanshi ya kalleta yana fad'in " dama ba mahaukaciya bace ke?
Cikin sanyinta ta d'aga mishi kanta, faranti ya cika da doyar ya hada mata da soyayyar kwai da k'undu ya mik'a mata,
jikinta na rawa ta fisga ya kalleta cike da tausayawa, yadda take ci hannu baka hannu kwarya duk ilahirin jikinta na tsuma ya kara karya mishi zuciya,
tas ta cinye ta mik'e mishi faranti bakinta cike da doyar tace " nagode, ya amshi faranti tare da mika mata ruwa, ta amsa ta tabi, titi tabi taita tafiya saida ta fita daga cikin mutane sosai sannan ta samu gindin bishiya ta zauna,
ta sani duk rintsin da zata shiga bazata tab'a rasa mataimaka ba, saboda addu'ar da mahaifiyata tasha yi mata,
ta fashe da kuka data tuna yadda rayuwarta take a baya, yadda ta taso cikin babban dangi da suke santa, ta taso cikin gata da kulawar 'yan uwanta, balle uwa uba MIJINTA mai santa saboda Allah, wanda baya san ganin bacin ranta kona dakika daya, amma taci amanarshi tayi mishi butulci, duniyar tunani ta tsunduma tana tuno rayuwarta ta baya mai kunshi da haske da farin ciki.