Sashe 14
Bakar Shuka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ta jerawa kanta da kanta tambayoyin, tayi nisa cikin duniyar tunani ya katse mata tunani da fad'in " dama saida nace miki ki bari na kaiki kikace a'a, cikin mutuwar jiki ta kwantar da kanta saman k'irjinshi tana fad'in kayi hak'uri, ya shafa kanta yana murmushi, shiya taimaka mata tayi wanka ya shirya ta, hannunta cikin nashi suka fito falo ya zaunar da ita tare da bata abinci a baki, sukuku take Allah kad'ai yasan meke faruwa cikin ranta, haka nan hankalinta yak'i kwanciya, wani irin mugun tsoro da fargaba suka shige ta, in banda fad'uwa babu abinda gabanta keyi, tana san ta fad'awa Deen gaskiyar abinda ya faru tana jin tsoro.
Bayan kwana biyu Deeyanah zaune a falo tana kallon SunnaTv, ta shagala sosai da kallan saboda tarihin Sayyadina Umar ake yi, film d'in ya tafi da ita, shigowar sak'o cikin wayarta yasata d'auke idonta daga kan TV ta mayar kan wayarta,
sharewa tayi ta cigaba da kallanta, jim kad'an wayarta ta soma rori, saida taja tsoki saboda an katse mata kallanta kana tayi picking wayar batare data duba number ba,
" Assalamu Alaikum, Amin wa'alaikissalam, jin muryar Ajlaal yasata zaro ido sosai a tsorace, " lafiya?
"Ina ka samu number ta?
Cikin isa da tak'ama yace " zan turo miki address d'in gida na kizo yanzu ina san ganinki, wayar ta cire daga kunnenta ta duba a karo na biyu, kana ta mayar da wayar kunnenta tana fad'in " ka san wacce ka kira kuwa?
" Inaga baka san da wacce kake magana ba, dariya ya sanya sosai yana fad'in " da Mrs Deeyanah Deen nake magana na sani,
tsaki taja had'i da cewa " inaga dai ka samu tab'in hankali Ajlaal, tana k'ok'arin kashe wayar yayi saurin cewa " a'a kul karki soma kashe min waya, ga sak'o nan na turo miki ta WhatsApp ki duba saiki yanke hukuncin zaki zo ko a'a, yana gama magana ya kashe wayar,
jikinta na rawa ta duba WhatsApp d'in, video ta gani ya turo mata hannunta har rawa yake, tayi playing videon, itace kwance tsirara haihuwar uwarta da ubanta,
tana kwance wani namiji yazo shima jikinshi ba kaya amma ya rufe fuskarshi da mask, ita da kanta ta jawoshi jikinta ya fad'a kanta, suka shiga aiwatar da masha'a.
Bata san sanda ta buga wayar da bango ta tarwatse ba, kanta ya shiga juyawa ta soma ganin komai bibbiyu, k'ara tayi ta sulale k'asa a sume.Bata farka ba sai cikin dare, bakinta d'auke da salati ta dafe kanta tare da yamutsa fuskarta, a hankali ta bud'e idanuwanta da sukayi mata nauyi ta fara ganin komai dishi-dishi kafin a hankali idanta ya washe tarr,
k'ok'arin mik'ewa zaune ta soma hannunta dafe da kanta, " yi a hankali, taji an furta daga gefenta, idonta ta sake warewa sosai tana bin inda take da kallo, sai a lokacin ta kula da a asibiti take, hannunta jone da cannula ana k'ara mata ruwa.
"Sannu..! Deen! yace yana tallafe ta, juyawa tayi ta kalleshi, tana d'ora idonta akanshi komai ya shiga dawowa mata, tunaninta ya dawo, wata irin mahaukaciyar k'ara tayi tare da tushe kunnuwanta da hannayenta ta saki rikitaccen kuka tana fad'in.
"Na shiga uku!... na shiga uku na lalace.
"Subhanallah me yayi zafi haka Deeyanah?
Deen ya fad'a yana rik'e ta.
Ammi tace " kul karna sake jin kince kin shiga uku kinji ko?
A haukace kamar zararriya ta kalli Ammin tana girgiza kanta while tana kukan tace " idan da abinda yafi shiga uku ma na shiga, na shiga dubu ma ba uku ba, ina cikin bala'i da musiba Ammi,
wannan wacce irin bak'ar k'addara ce Allah ya d'ora min?
"Me yasa saini?
Rik'e mata hannu Ammi tayi tana fad'in " kowacce dak'ik'a data harba a agogo tana harbawa ne da rubutun wata k'addara a rayuwarmu,
K'addarar da zatana iya zama shafi cikin littafin rayuwarmu, fatanmu Allah ya gina mana katangar karfe da mummunar k'addara.
Cikin kuka Deeyanah tace " amma meyasa saini?
"Meyasa akaina kawai zata fad’a?
Idon Deen kanta yace " Deeyanah ki manta da abinda ya cutar dake amma karki sake ki manta da darasin daya koyar dake,
zatayi magana Deen yace " wai mema ya firgitaki haka?
D'an jimm tayi tana tunanin ta fad'a musu ko karta fad'a musu, "kiyi addu'a koma meye yazo miki da sauki saboda taka tsantsan baya hana afkuwar masifa, amma addu'a tana tasiri akan masifar data sauka dama wacce bata sauka ba, Masifa takan sakko sai addu'a ta tareta, suyita fafatawa har ranar tashin alkiyama, kinga masifar bazata cimma ma'abocin addu'a ba,
cikin mutuwar jiki tasa hannu ta goge hawayen dake ta faman zubowa saman fuskarta, " Ammi ki tayani addu'a mummunar k'addara ta afkawa min.
Kallon juna Ammi da Deen sukayi kafin suka mayar da kallonsu ga Deeyanah cikin rashin fahimta Ammi tace " kamar ya ban gane inda maganarki ta dosa ba!?
"Bazaki gane ba Ammi.
"Duk irin bayanin da zanyi miki bazaki fahimci komai cikin zance na ba, ni kaina na kasa fahimtar komai, ko kalma d'aya na kasa fahimta Ammi.
"Ki nutsu kiyi ki kwantar da hankalinki, kyayi mana bayani daga baya, Deen ya fad'a yana k'ok'arin had'a Ido da ita tak'i bashi dama, wani iri take ji cikin jikinta wai itace tayi video tsiraici na batsa?
Itace irin wannan bak'ar k'addarar ta fad'awa, komawa tayi ta kwanta had'i da lumshe idanuwanta hawaye na gangarowa ta gefen idanuwanta.
Ba bacci takeyi ba, tana jin hirar da Ammi da Deen keyi amma bata fahimci ko kalma d'aya cikin maganganun da sukeyi ba, hankalinta baya jikinta, k'ofar d'akin aka bud'e DeeDee ya shigo da gudu yana fad'in Momy, wani abu babba taji ya tokare mata mak'ogwaro ya soki Zuciyarta.
"Momy! Deedee ya fad'a yana fad'awa jikinta.
A fili ta sauke nannauyan ajiyar zuciya kafin ta d'agoshi tana k'ak'aro murmushin k'arfin hali ta lullub'awa fuskarta.
"Ki daina bari yana fad'a miki kinga ba ke kad'ai bace kar wani abu ya samu d'an cikinki, Ammi ta fad'a tana kallan yanayin Deeyanah, murmushi tayi batare da tace komai ba, su Babah suka shigo bakinsu d'auke da sallama, "au wai dama tare kuke dashi?
Eh! Mana ya gudo wajen iyayenshi yabarmu ba.
"Sannu Deeyanah ya jikin naki?
Cikin sanyin jiki da muryarta da bata fita sosai tace " da sauki?
"Wai meke damunta ne?
"Ince dai ba bari tayi ba ko?
Abbi yayi maganar a lokacin d'aya yana kallan Deen.
"Ga cikin ya d'an soma fitowa ma ba wani b'ari lafiyar cikin lau.
Cewar Ammi tana kallan cikin jikin Deeyanah.
Deen ya sauke ajiyar zuciya yace " nima dai ban san meke damunta ba Ina shiga gidan na ganta kwance k'asa a sume.
Ammi tace " To wai fad'uwa kikayi ne ko kokuwa dai wani abunne ya faru?
Deeyanah najinsu amma batayi magana ba.
"Deeyanah dake fa ake magana kinyi shiru kina jin mu, batare data d'ago kanta ba tace " bakomai Ammi, "to Allah ya kyauta.
Gaba d'ayansu suka amsa da "Amin.
Kwanakin Deeyanah uku a asibiti aka sallameta kowa ya fahimci akwai abinda ke damunta dan kallo d'aya zakayi mata kasan tana tattare da tarin damuwa.
Tun bayan komawarsu gida komai nata dana gidan ya canja ta zama wata sukuku ta daina magana sosai sai jefi-jefi ta koma shiru-shirun dole, duk suturun Deeyanah da faram-faram d'inta duk sun zamana babu duk lokacin dazaka ganta sai dai ka ganta zaune ta rafka uban tagumi hannu bibbiyu, dama wayar ta lalace layinta a kashe yake.
Tana zaune bakin gado ta rufe kanta a d'aki tana rusgar kuka wiki kamar ranta zai fita, idanuwanta har sun kumbura tana fad'in,
" wayyo Allah! na shiga uku!
" Ni Deeyanah na shiga uku rayuwata ta lalace tashin duniyata yazo, na jefa kaina da rayuwata a cikin masifa da babban k'alubalen da babu mai fitar dani sai Allah.
Zamewa tayi daga saman gadon ta durk'usa k'asa saman gwiwowinta ta d'aga hannayenta sama a fili ta soma addu'a.
"Ya Ubangijin Al'arshe ya Ubangijin sammai da k'assai ya gagara buwayi majib'ancin al amura me tausayi mai jin k'ai me yaye damuwa, ya Allah ya ka kawo min mafita, ka jib'anci ramura na, kayi min mafita ka kareni daga sharrin wannan bawa naka kayi min tsari daga kaidinshi, ta zame takai sujjada bata damu da cewar ko hijabi babu a jikinta ba while tana cigaba da rusa kuka.
Tsaye yayi cak yana kallanta cike matsanancin mamaki ya kasa fahimtar komai amma yaji komai, sai dai babu abinda ya iya ganewa kanshi ya juye a fili ya furta.
" Ka kareni daga sharrin wannan bawa naka, kayi min tsari daga kaidinshi?
"Waye wannan d'in da Deeyanah ke magana akanshi?
Yayi maganar kamar me koyan magana, cikin rashin gwarin jiki ya jawo k'afarshi ya k'araso kanta yayi tsaye yadda take rusa kuka sosai yake tab'a mishi zuciya.
" Deeyanah!
Ya kira sunanta a hankali cikin nutsuwa, bata shigowarshi ba balle motsinshi sai muryarshi dataji a kanta, da sauri ta d'ago daga sujjadar yana d'ora idonshi a kanta gabanshi ya fad'i saboda gaba d'aya kamaninta sun canja yadda kasan ba itace Deeyanah ba.
Itama a mugun tsorace take dan tana gudun koya fahinci maganganunta, a hankali yasa hannayenshi ya d'agota ya zaunar a gefen gado ya fita, bai dad'e ba ya dawo hannunshi d'auke da ruwa ya mik'a bata ta karb'a tashanye tas ta mik'a mishi kofin tana sauke ajiyar zuciya.
Ido ya zuba mata batare dayace mata komai ba har tsayin lokaci kafin yayi gyaran murya yace " meke faruwa dake ne Deeyanah?
Bata d'ago kai ta kallaeshi ba balle tayi magana.