Sashe 54
Bakar Shuka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un Babah ya fad'a had'i da zama sakwaf ba kwari, nan damuwa da bak'in ciki suka k'aruwa sukayiwa zuri'ar yawa, mazansu da matansu manyansu da yaransu sai rusgar kuka sukeyi wiwi, zuciyoyinsu sunyi duhu dind'im babu d'igon haske a ciki, kwanan Ammu hud'u da farfad'owa zuciyarta ta buga ta samu heart attack, Allah ya karb'i rayuwarta, nan fa koke koke ya k'aru, duk abin nan da akeyi Deeyanah na gida kulle a d’aki sai da aka kai gawar Ammu kana ta fito tare da fad’awa kan gawar tana wani irin kuka tana fad'in " dan Allah Ammu ki tashi, ki tashi karki tafi ki barni a sanda nafi buk'atarki fiye da koyaushe, nice sanadiyyar mutuwarki ki yafe min dan Allah Ammu, karki mutu baki yafe min ba dan Allah, dakyar aka b'anb'areta daga jikin Ammu aka kaita makwancinta na gaskiya.
Tun bayan rasuwar Ammu komai ya k'arasa lalacewa Deeyanah dan babu me kulata balle ayi mata magana kaf gidan dan sun d'ora mata alhakin mutuwar Ammu akanta a cewarsu ita ta kashe musu uwa, rasuwar Ammu ta k'ara cunkusa k'iyayyar Deeyanah a zuciyar Deen dan ita ya d'auka uwa ba Ammi ba saboda ita ta reneshi, a d'aki ta keb'e kanta ta rufe babu abinda take yi sai kuka, har ta gaji da kukan hawayenta ya k'afe, komai na duniya ya fice mata daga rai, ta tsani kanta, in banda kashe kai babban laifi ne a addinin musulunci da tuni ta dad'e da kawo k'arshen numfashinta, ji tayi kamar taita tsigar gashin kanta d'aya bayan d'aya har su k'are, kanta ta shiga bugawa a bango tana fad'in " koban kashe kaina ba saina azabtar da kaina azabtarwa me tsananin gaske, duk da fashewar da kanta yayi jini yana zuba bai sa ta dena ba, har jinin ya rufe mata ido ruf bata ganin komai sai duhu, wata irin d'iba jini yayi mata ya kada ita gefe.
Cikin dare cincirundan zanga zangar suka taru a k'ofar get d'in su Deeyanah, suna ihuuuu suna jefa duwatsu gidan, kan kace kobo an farfashe musu windows da duk wasu glass dake gidan, har mutanen gidan da ma'aikatan gidan ba'a kyale ba, an fasawa da yawa daga cikinsu kai har Abbi da Babah saida aka ji musu ciwo, dakyar da taimakon jami'an tsaro aka kori mutanen, Commissioner of police ne ya basu wasu 'yan sanda dansu basu tsaro, ranar kam a tsorace suka kwana dan saida suka rurrufe ko'ina, washe gari asibitin dake cikin Estate d'in akayi musu treatment.
*********Bayan sati d'aya da lafawar 'yan zanga-zanga wasu mutane a manyan motoci suka zo gidan, Abbi da Babah sukayi musu iso har babban falo, bayan sun gaisa d'aya daga cikin mutanen yayi gyaran murya ya soma magana " daga k'ungiyar addinin musulunci ta k'asa muke, dama munzo kan maganar yarinyar nan da tayi wannan aika-aika, d'an shiru yayi ya kasa k'arasa maganar, Abbi yace " uhunnn muna jinka.
"An aiko mu ne kan muzo mu sanar daku cewar dole za'a JEFE! ta saboda tayi zina tana da aure kuma a koyarwar addininmu jefa shine hukuncin mutane irinta.
"Me?
"Ban fahimta ba!.
Abbi ya fad'a cikin zallar tashin hankali, "eh! kamar yadda kaji, an tsaida nan da sati biyu za'a jefe ta a gaban mutane dan hakan ya zama gargad'i da jan kunne ga 'yan baya.
Kasa magana Abbi da Babah sukayi har mutanen suka mik'e suka fita, yadda kasan iska haka maganar OIC tabi k'asa, nan fa k'ungiyo sukayo caa musamman Human Rights and Amnesty suka nemi ganin Babah mahaifin Deeyanah ba musu Babah ya amince, a office d'in Human Rights akayi zaman, inda daga k'arshe suka nemi ganin Deeyanah, dakyar ta amince ta zauna da Human rights d'in, ganin halin da take ciki yasa basu nemi jin komai daga bakinta ba, suka karb'i sa hannunta.
An d'ibi watanni ana fafata shari'a tsakanin OIC da Human Rights sai da aka kai ruwa rana kana Allah ya bawa Human Rights nasara kotu ta hana jefe Deeyanah, duk da ita Deeyanah da yayyanta sun so ace an bari an jefe tan, amma Abbi da Human Rights sukayi tsaye sukayi tsayyuwar tsayin daka, tasha bin dare tana addu'ar Allah yasa OIC suyi nasara a jefe ta, har a kotun sai da ta nemi kotu ta bada izinin a rataye ko a jefe ta amma Human Rights ta hana.
Har lokacin babu wanda yake yi mata magana a gidan, ita kad'ai take rayuwar ta, sai da Abbi yaga halin tsangwamar da take ciki kana ya nemi ganinta a falonshi, tun faruwar abun babu wanda ya nemi ganinta koya san halin da take ciki, kanta k'asa cike matsananciyar kunyarsu ta shiga falo, daga kallan farko da Abbin yayi mata bai sake sha'awar sake kallanta a karo na biyu ba, ta yankwane ta yamushe ta lalace abun dai ba'a cewa komai, da muryarta da tuni ta zama dashashshiya ta gaida su, ba yabo ba fallasa Abbi da Ammi suka amsa yayinda Babah da Deen ko kallan inda take basuyi ba, dan babu d'igon tausayinta a ransu.
" Deeyanah!, Abbi ya kira sunanta a nutse, kanta k'asa batare data d'ago ba ta amsa, " na kira ki ne dan ina san nasan ainahin hak'ik'anin abinda ke faruwa, kiji tsoran Allah ki fad'a min gaskiyar abinda ke faruwa dake.
A hankali ta d'ago kanta ta sauke idonta akanshi tana k'ara ganin girmanshi, tun da abin ya faru kowa gudunta yake yi, babu wanda ya tsaya ya saurare ta, ko sau d'aya tak babu wanda yaso jin ta bakinta ko abinda ya faru, a karon farko kuma mutum na farko daya saurare ta, ya kuma so jinta bakinta, kanta ta sunkuyar k'asa tana san hawaye su zubo mata amma babu ko d'igo, a fili ta sauke ajiyar zuciya tana sake d'agowa ta kalli Deen da Babah da kallo, duk da kallo d’aya tayi musu ta gane dolen da akayi musu shinfid'e akan fuskokinsu, kanta ta sunkuyar had'i da bud'e baki zata soma magana Deen yayi saurin mik'ewa ya kalli Babah yace " bari na amsa waya, Babah ya gane guduwa zayyi dan haka yayi saurin cewa " jeka!, dan kar Abbi ya hana shi, shima dole ce ta zaunar dashi.
Murmushin yak'e Deeyanah tayi kana ta soma bada labarin komai tun daga farkon had'uwarta da Ajlaal a makaranta har kawowa mafarin abun bata b'oye komai ba.
"Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un lalle Deeyanah kin tafka babban kuskure kece babbar me laifi duk abinda ke faruwa ke da kanki kika jawowa kanki, kin shuka BAK'AR SHUKA... shiyasa duk abinda Allah yace a bari barin nashi shine mafi alkhairi, shi kuma Ajlaal yayi amfani da k'uruciyarki yaci moriyar kwakwalwarki ta mace ya dasa miki tsoronshi da firgici cikin ranki da haka yayi amfani ya cimma burinshi a kanki, yayi wasa da kwakwalwarki, ina ita RALEEYA DATA JEFAKI CIKIN WANNAN MUMMUNAR K'ADDARAR?
"Tana ina?
"Ina labarinta yake?
"Sau Dama k'awaye suna da tasiri a rayuwar mutum, sukan kai mutum su baro shi, kamar yadda RALEEYA ta cuce ki ta jefa cikin gagarumar masifar da fitarki sai Allah yaso, ta zuga ki, ta baki shawara kin d'auka, meyasa data baki shawarar baki nemi shawarar kowa ba?
"Gashi nan ke abinda kuka aikata yake farauta ita tana can tana rayuwa cikin jin dad'i da walwala ta barki cikin danasani da nadama, shi kam Babah wani irin haushinta da tsanarta yaji sun k'ara ratsa shi da kafi, musamman ma da yaji sanadin abin ya d'auka k'addararta ce tazo mata a haka, amma yanzu daya ji ita ta jawowa kanta haushinta yake ji sosai, a fili yaja tsoki had'i da mik'ewa ya kalleta yayi kwafa, kamar bazayyi magana ba sai kuma yace.
"Kin cuci kanki kin cuci rayuwarki, kin jefa wad'anda basu ji ba basu gani ba cikin masifar da kika jefa kanki, d'an itaciyar BAK'AR SHUKAR... da kikayi ke kad'ai gashi nan kin raba mana muna cin shi tare dake, gangancinki yayi sanadiyyar mutuwar mahaifiyarki da d'anki, Allah ma kad'ai yasan iyakacin wad'anda zaki zama ajalinsu, nayi takaicin haihuwarki, nayi nadamar aurawa Deen ke, dama ban haifeki ba, ke inama ban auri uwarki ba balle na haife ki, da nasan bak'ar daga zaki zama dana sa an zubar da cikinki tun kafin ki zo duniya, kin b'atawa zuri'ar mu suna har a tashi duniya, kin jefa mu cikin kunyar duniya har mu mutu, kin zubar mana da k'ima da mutumcinmu dan yanzu bamu da wani sauran mutunci a idon Jama'a, muna sanye da tufafi amma ana kallan mu tsirara, matar da tayi dakon cikinki har tsayin watanni tara, tayi nak'udarki, kika tsaga tsatsanta kika fito, ta shayar dake daga jikinta, ta reneki amma ki rasa dame zaki biyata sai da mutuwa Deeyanah bayan ita ta baki rayuwa?
"Allah ya d'auki ranki kamar yadda kika zama sanadiyyar mutuwar Aina’u.
Da sauri ta amsa mishi da " Amin Babah, Amin ya Allah, Ubangiji ya amsa rok'onka ya karb'i raina na huta dan nima na gaji da wannan bak'ar rayuwar, zayyi magana Abbi yayi saurin mik'ewa ya jashi zuwa waje, bai jima ba ya dawo, sai da ya d'an saita kanshi kana yace " wallahi ko abinda na mallaka a duniya zai k'are saina ga bayan Ajlaal da duk wanda ya d'aure mishi gindi, yadda ya saki kuka saina zubar da hawayenshi, yadda ya saka mu cikin halin bak'in ciki da damuwa shima saina saka ahalinsu kaf a cikin kwatankwacin halin daya saka mu, saina tona mishi asiri duniya tasan waye shi.
********Cikin kwana d'aya Abbi ya gama duk wani shirye-shiryen da zayyi ya d'auki manyan kwararrun lawyers wad'anda zasu tsaya mishi a kotu, ranar litinin aka kaiwa iyayenshi sammacin kotu, babu yadda Babah bayyi da Abbi ba amma fur Abbi yak'i sauraranshi.