← Book details Bakar Shuka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 56

Sashe 42

Bakar Shuka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Zan d'auki duk abinda zakiyi min, zan jure duk wani zagi da cin mutuncin da zakiyi min amma bazan tab'a jure ki fifita wani gardi akaina ba, bazan jure jin tausasan kalamai akan Deen yayinda ni kuma kike kausasa min furuci ba, bazan lamunci wulak'anta min soyayya ta a gare ki kina kurara tashi ba, bazai yiyu ba Deeyanah, fad'awa saman sofa yayi yana dariya da iya k'arfinshi kamar zararre.

************************************

Nan kan sallayar wahalallan bacci ya kwashe ta tana kuka, sai sauke ajiyar zuciya take yi cikin bacci, sama-sama kamar a mafarki taji ana knocking k'ofar bedroom d'inta, sake bugun da akayi ya farkar da ita firgigit a d'an tsorace tana salati, idanuwanta ta lumshe had'i da goge gumin goshinta ta fitar da nannauyan numfashi, sake buga k'ofar d'akin akayi a karo na uku, hammar da take yi ta katse gami da cewa " shigo k'ofar a bud'e take, cikin nutsuwa ya nuro k'ofar ya shigo, daga tsaye ya tsaya kanta yana binta da kallan mamaki dan yaga alamar anan ta kwana, idanta da yayi ja kuma fuskarta a kumbure da alamar kuka ya kalla tare da fad'in " kina lafiya?

Ya fad'a cikin kulawa, kanta ta d'aga mishi alamar eh, kana cikin sanyin murya tace " ina kwana?

"Alhamdulillah, Ammu tace ta turo miki list zakiyi mata siyayya ko?

Kanta ta dafe tana rufe bakinta saboda hamma, d'an juyawa tayi ta kalli drawer dan ta dad'e da mantawa da wata waya, raban da tayi amfani da waya harta manta, mik'ewa tayi tana cewa " wallahi ban sani ba bari na duba, " idan kin shirya kiyi min magana na kaiki, idan kuma zakije da kanki to, ya fad'a idonshi kanta yana jiran amsarta, da sauri tace " a'a bari na shirya sai muje!, juyawa yayi ya fice batare daya ce komai ba, dayace idan zataje ta tafi har cikin zuciyarshi yayi maganar dan tuni ya tattara komai ya watsar ya samawa kanshi lafiya a cewarshi kowa yayi na gari dan kanshi, haka kowa ya gyara ya sani, bin diddigin da yayi mata da bai kamata da laifin komai ba ya k'ara mishi yak'ini da yarda akanta sosai, harga Allah yaji ya samu kwanciyar hankali fiye da baya, yakan ce " yasan Deeyanan shi bazata tab'a aikata abinda bai dace ba, yasan duk abinda zatayi akwai dalilinta nayin hakan, wata k'ila wani laifin yayi mata bisa rashin sani da yasata ta k'auce masa.

Wayar ta d'auko daga cikin drawer ta kunna, kamar jira yake yi ta kunna kiranshi ya shigo, tsaki taja ta zauna gefen gado tana jira kiran nashi ya katse ta duba sak'on Ammun, takai mintuna zaune tana san duba sak'on amma kiranshi dake shigowa akai akai ya hanata dubawa, a do not disturb ta saka wayar kana ta samu ta duba sak'on, sakonshi 453 ne suka shigo wayar, duk da IPhone bata hukin ranar sai da tata tayi, jira tayi wayar ta dawo dai-dai kana ta goge gaba d'aya sak'unan cikin wayar ta danna mishi blocking ta jefa wayar saman gado ta mik'e ta fad'a bathroom.

A d'an gaggauce tayi wanka ta fito ta shirya cikin kayan data san yafi san ya ga ta sanya, heavy make-up tayi tayi kyau sosai damma muguwar ramar da tayi ta rage mata kyau ga kumburin da fuskart tayi saboda kuka, kallan kanta tayi a mudubi tayi d'anyi gajeran murmushi ta fice hannunta rik'e da waya, dai-dai ya fito daga bedroom d'inshi yana d'aura agogo, tsayawa sukayi suna kallan juna shi ya fara d'auke idonshi daga kanta ya wuce, tabi bayanshi sumi-sumi kanta a k'asa.

Yana tuk'in a nutse tana ta faman janshi da hira, ya d'an yi mamaki duk da ya san dama tana da shegen surutu, jefa-jefi yakan bata amsa idan ta kama, a babban shagon siyayyar Sahad Store sukayi parking da sauri ta bud'e motar ta fito dan su jera amma yayi saurin yin gaba dan ya gane manufar ta, bata ji komai a ranta ba tabi bayanshi, tana duba list d'in tana d'ibar kayan harta gama, ta tura kwandon da kayan ke ciki gabanshi tana cewa " fara biyan wannan bari na duba abubuwan gida, bayyi magana ba ya karb'i keken kwandon ya tura zuwan wajen biya.

" Deeyanah! ya kira sunanta cike da kwarin gwiwa, saurin juyowa tayi ta zuba idanuwanta akanshi, yana tsaye hard'e da hannu a k'irjinshi fuskarshi d'auke da murmushi a d'an tsorace ta juya bayanta ta kalli Deen, ajiyar zuciya ta ganin yabar wajen tayi, murmushi yayi me kama da dariya yace " karki damu yabar wajen bazai tab'a sanin meke tsakaninmu ba sai idan kin so hakan.

Shiru tayi tana kallanshi batare datace komai ba, ya jijjiga kanshi had'i da cewa " eh sai inkin so zai sani, abinda nake nufi da sai kin so, sai idan kinyi taurin kai da kafiya kink'i dawo min, sai idan kin bujirewa umarni na, to anan fa zai san komai zai san duk abinda ke tsakaninmu kamar yadda kikaji nace komai to ina nufi zan sanar dashi duk wata badak'alar da mukayi zan tura mishi videon blue film d'in mu, ya k'ara shi maganar had'i da kashe mata ido d'aya, batayi magana ba ta girgiza kanta gami da juyawa zata bar wajen.

(Ku gane bambamcin dake tsakanin jijjiga kai da girgiza kai, jijjiga kai yana nufin d'aga kai sama da k'asa while girgiza kai daga b'arin hagu zuwa b'arin dama)

Fisgota yayi da k'arfi ta fad'a jikinshi ta bud'e baki zatayi magana ya yasa hannunshi ya rufe mata bakinta yasa k'arfi yaja ta, ta k'ofar baya, tana ta dukan shi amma a banza mota ya dannata ya zagaya ya shiga motar tana ta dukan glass tana ihuuu amma dayake motar tint ce babu wanda ya ganta, sai da yayi tafiya me nisa da ita kana yayi parking ya fito, ya zagaya b'arin da take ya bud'e ya finciko ta waje, baya ya juya tare da dafe kanshi, ihuuu yayi da k'arfi had'i da naushin iska ya juyo gareta yana kallanta sosai yace " ya kamata ki gane irin girman son da nake yi miki, ina sanki Deeyanah ina sanki fiye da so, ina sanki da duka zuciya ta, ya sunkuya inda take yade a k'asa yace " please ki so ni nima, ki soni koda kwatankwacin son da nake yi miki ne, ki kashe aurenki kizo muyi aure dan Allah.

"I love you try to understand my feelings please.

"I hate you Ajlaal, na tsane ka bana k'aunar ganinka ta fad'a cikin zafin rai had'i da tofa mishi yawo a fuska, a matuk'ar hasale ya damk'o gashin kanta ya kalli cikin kwayar idonta da idanuwanshi dake waje sunyi jajir yace " aiko kin taro fad'in da bazaki iya k'arasa shi ba, akan ki zan iya yiwa kowa komai Deeyanah, dana rayu babu ke gwara na mutu sau dubu.

"K'arya kake yi Ajlaal ba so na kake yi ba akwai dai abinda ke ranka game dani, dan idan har soyayyar da kake min gaskiya ce zaka so na rayu cikin farin ciki, zaka barni nayi rayuwata yadda naso, zakayi sadaukarwa irin sadaukarwa da jaruman masoyan farko sukeyi, ai akwai sadaukarwa a soyayya, zaka barni nayi rayuwa da wanda na zab'arwa kai na, zaka barni kuma kayi nesa dani nayi rayuwa tare da mijina da d'ana bawai kace na rabu dasu ba, wallahi tallahi Ajlaal ba soyayya bace abinda kake ikirarin kana yi min, a haukace yace " idan ba soyayya bace menene?

"Hauka, Hauka ne Ajlaal, abinda kake yi hauka ne amma ba soyayya ba, dan idan soyayya ce zaka barni nayi rayuwa ta cikin farin ciki koda hakan na nufin mutuwarka, kana da san kanka, san kanka yayi yawa Ajlaal har ya rufe maka ido kana neman halakar damu ka kaimu wuta, muzo duniya a banza mu koma a wofi.

" Danna so kaina laifi ne Deeyanah?

Hannunta ta had'e waje d'aya alamar rok'o tana kuka wiwi kamar ranta zai fita tace " dan Allah dan zatin Allah dan girman iyayenka ka fita daga cikin rayuwata ka barni nayi rayuwa cikin salama please.

"Bazan iya ba wallahi bazan iya ba Deeyanah, " to shikenan tunda bazaka iya ba kaje kayi duk abinda zakayi.

"Kina da sauran dama tun kan lokaci ya k'ure miki ki dawo min in ba haka ba zan lalata komai, " baka ji me nace ba kenan?

"Ai nace maka kaje kayi duk abinda zakayi.

"A'a fa karki kizo kina danasani da danama.

"Danasani da danama ai na gama yinsu koma ince cikin yinsu nake, nayi danasanin had'uwa dakai a rayuwata nayi danasanin saninka a rayuwata, kai bama saninka kad'ai ba harta jami'ar dana shiga na sanka sai da nayi danasanin karatun boko da tsanarshi gaba d'aya.

Dariya yayi sosai yace " shikenan tunda haka kika zab'arwa kanki amma ki sani baki fara danasani ba har yanzu zadai ki fara ranar tana nan zuwa ki shirya tarbarta, cikin matsanancin kuka ta d'aga hannayenta sama tana kallan sararin samaniya ta soma magana " Allah ya isa Ajlaal Allah ya isa na, Allah ya isar min, Ubangiji yayi min sakayya me tsanani a tsakani na da wannan bawa naka, Allah ya tsare ni daga sharrinka, Allah ya tsare ni daga mugayen alkaba'inka duk irin bala'i da masifar da kake nema na dasu ina rok'on Allah ya mayar maka abinka kanka.

Mik'ewa tayi ta juya zata bar wajen har tayi taku biyu zuwa uku ta juya ta kalli kwayar idonshi tace " kana yi min barazanar zaka sanar da Deen komai, murmushi tayi me ciwo had'i da cewa nayi maka alk'awarin kafin ka sanar dashi ni da kaina zan sanar dashi abinda ke tsakaninmu so ka kwantar da hankalinka ka kuma saka ranka a inuwa, na riga nakai matakin k'arshe nakai matakin da baka isa ka rikito dani k'asa ka dawo dani baya ba, kaima ina yi maka fatan shiriya idan kuma bazaka shiryu ba Allah yasan yanda zayyi dakai, ta juya tayi tafiyarta tana sharar kwalla da tunanin abinda zata cewa Deen.

Tsaye ta iske shi a harabar gida da sauran family duk anyi cirko-cirko ana tunnin sace ta akayi, tana shiga duk ayo kanta tana wani irin kuka ta fad'a jikin Ammi, " lafiya meya faru?

"Meya same ki?
Chapter 42 · 0% Book details