Sashe 52
Bakar Shuka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
K'arasa zarewa tayi ta hukace tana fad'in "kome zakayi min ni kad'ai nina jawowa kaina amma banda su please, karka tab'a su dan Allah, dariya sosai yayi ya juya ya fice batare da yayi magana ba, tabi bayanshi da gudu, amma bisa mamakinta yana fita daga k'ofar data bishi ya b'ace babu ko alamunshi, a haukace ta nufi part d'in Babah babu ko d'an kwali balle takalmi, da k'arfi take bugun k'ofar d'akin Deen tana fad'in " ka fito zai kashe Deedee, dan Allah ka fito ka saurare ni da gaske nake yace sayya kashe Abduljalal, cike da mamaki Ammu ta k'araso inda take tana tambayarta waye " zai kashe Deedee d'in?
"Ajlaal ne Ammu, dan Allah ku taimake ni karya kashe min shi, Ammi da Abbi suka k'araso wajen dan Abbi yaga wucewar Deeyanah a haukace, da gudu ta nufi Ammi zaninta a hannu tana kuka wiwi " Ammi zai kashe min Deedee dan Allah ku fad'awa Yaya da gaske nake, kallan juna Ammi da Ammu sukayi cike da neman k'arin bayani,
ganin duk sun tsaya suna kallanta yasata komawa k'ofar d'akin Deen ta shiga bugun k'ofar a haukace tana ihuuu kamar zata b'alla k'ofar, da sauri Ammi ta k'arasa inda take ta rik'ota amma ta turje, " Ammi zai kashe shi da gaske yake, bashi da d'igon imani.
"Naji muje kiyi mana bayani a tsanake, Ammi ta fad'a tana jan hannunta, k'ara turjewa Deeyanah tayi, ganin abun nata kamar hauka yasa Abbi, Ammi da Ammu suka jata tana ihuu suka dannata a d'aki suka rufe dan sun lura tsoratarwa bazatayi mata aiki ba, bugun k'ofar d'akin da aka rufeta take yi a haukace tana fad'in " dan Allah Yaya ka fito ka ceci d'an mu.
Duk abinda ke faruwa Deen na ji, ya dayyi shiru ne kawai, abun kuma ya fara bawa iyayen tsoro duk sun dabarbarce kansu ya kulle babu abinda suka iya fahimta, tun Deeyanah na bugun da k'arfi harta gaji ta zube a k'asa tana sharb'ar kuka.
K'arfe shida na safe sautin kukan Ammi da salatinta ya cika gaba d'aya Estate d'in, kowa ya fito cikin tashin hankali ta fito harabar gidan d'auke da Deedee a hannunta, mazan gidan suna masallaci dan idan suka yi sallar asuba basa fitowa sai k'arfe shida, gaba d'aya suka fito har Babah da Abbi, Abbi ta nufa cikin tashin hankali ta mik'a mishi yaron tana fad'in " Alhaji na tashe shi zan shirya shi makaranta yak'i tashi babu irin tashin da banyi mishi ba yak'i tashi, tana kara kunnena a k'irjinshi banji komai ba, jikin Abbi na tsuma ya karb'i Deedee bai tsaya b'ata lokaci ba yayi asibiti dashi, su Babah suka bi bayanshi, gwajin farko likita ya gano yaron ya mutu a wanni biyu zuwa uku da suka wuce, sai dai sunyi duk wani binciken da zasuyi sun kasa gano dalilin mutuwar yaron.
Gaba d'ayansu jikinsu a sanyaye suka dawo gida d'auke da gawar Deedee, dakyar Babah yaje bakin k'ofar d'akin Deen, muryarshi bata fita sosai saboda yadda yake kokawa wajen danne abinda ke taso mishi, " Deen ka fito Allah yayiwa Deedee rasuwa, yakai ruku'un sallar azahar, jin abinda Babah ya fad'a ya sashi d'agowa had'i da cewa " Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un, mutuwa! Deedee ya mutu?
Ai ya manta da batun sallar da yake yi, jikinshi na b'ari yayinda da zuciyar ke tsalle kamar zata fad'o ta bakinshi ya bud'e k'ofar, Babah na tsaye yana jiranshi, hannunshi ya kama kamar k'aramin yaro ya fito dashi falo inda gawar Deedee ke kwance, gaban gawar ya zauna had'i da dunk'ule hannunshi ya saka a baki ya cija gami da fashewa da wani irin kuka me k'una, shi kad'ai ne abinda ya rage mishi shima gashi nan sun raba shi dashi, Deeyanah ta cuce shi mak'ura duk wani abu da yake so sai ta raba shi dasu, da gaske yake jin tsanarta har cikin jinin jikinshi, a sanadinta ya rabu da d'anshi, cikin k'araji ya rungume gawar Deedee yana kuka kamar ranshi zai fita, duk da yaji tana ihuun ya fito ya taimake ta zai kashe Deedee ko kusa bai tab'a tunanin da gaske take ba, bayyi zaton rashin imanin shi har ya kai haka ba.
Ammu na rik'e da hannun Deeyanah kamar daluwa take bin Ammi, cikin sanyi murya Ammi na share kwalla tace " mun rasa Deedee, bata fahimci inda zancen Ammi ya dosa ba dan haka ta zubawa Ammi ido, gane bata fahimci maganar ba yasa ta sake fad'in " Deedee ya rasu Deeyanah ga gawarshi nan.
"Wanne Deedee kuma?
"Waye Deedee?
Ta fad'a tana bin kowa dake falon da kallo dan kanta ya gama kullewa gaba d'aya.
Sai da su Ammi suka kalli juna cike da tsoron kota haukace kana cike da fargaba Ammi ta dafa ta tace " Deeyanah d'anku keda Deen.
Wani abu taji yana yawo saman kanta, lokaci d'aya taji duk ilahirin jikinta ya d'auki k'aik'aiyi.
Ji tayi kamar an kama jijiyoyin jikinta an tsinkasu lokaci d'aya, komai ya gama kunce mata, duniyar ta tsaya mata cak, babu abinda bai tsaya mata cikin kanta ba, a hankali ta zube bisa gwiwowinta so take tayi kuka amma ta kasa, magana take sanyi amma bakinta yayi mata mugun nauyi, cikin ranta take fad'in " dama dayace mata zai kashe d'ansu da gaske yake yi?
Duk da tasan zai iya aikata komai dan mafitar kanshi batayi zaton rashin imaninshi yakai mak'ura har haka ba, batayi zaton zai iya kashe yaro ba, rashin imanin yayi yawa, ita da kanta tayi sanadin d'anta, addu'a take san ta bud'i baki tayi amma yadda kasan an d'aure mata harshenta.
Cikin mutuwar jiki ta duk'a, cikin sand'a ta mik'a hannu zata tab'a gawar Deedee yayi saurin rik'e hannunta had'i da janye gawar Deedee d'in, idonshi cikin nata sun kad'a sunyi jajir, sai da k'irjinta ya kusa tsagewa saboda yadda ya doka da k'arfi, kanshi ya girgiza muryarshi na sark'ewa yace " karki soma tab'a min d'a dan bazan tab'a baki wannan damar ba, jikinta a sanyaye ta zame hannunta had'i da mik'ewa tabar falon, d'akinta ta koma ta jin gina bayanta da jikin k'ofar d'akin so take tayi kuka amma yadda kasan an shak'e ta haka take ji.
"Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un na kashe d'ana, na kashe shi da kaina, nice nayi sanadiyyar mutuwar tilon d'ana.
Ta fad'a a haukace kamar zararriya.
Deen da kanshi yayiwa Deedee wanka yayi mishi sutura kamar yadda musulunci ya koyar, aka kaishi gidan shi na gaskiya.
Tun bayan mutuwar Deedee abubuwa suka k'arasa jagulewa gaba d'aya family aka zama gidan zaman makoki babu me walwala ko fara'a, ganin halin da gaba d'aya family aka shiga yasa manyan family had'a family meeting, gaba d'aya an hallara a babban falon, gyaran murya Abbi yayi ya soma magana da fad'in " Alhamdulillah mun godewa Allah abisa jarabawar da yayi mana ta rashin d'a kuma jikan mu, sai dai dole tasa dole sai mun taru anan dan jin hak'ik'anin abinda ke faruwa tsakanin Deen da Deeyanah, gumin dake tsatstsafo mata a goshi ta goge deep down tana jin wani irin mugun tsoro na ratsata.
Abbi ya mayar da kallanshi ga Deen dake zaune d'osane kamar an dasa shi a wajen, cikin sanyin murya Abbi ya kira sunanshi " Deen..!
Cikin nutsuwa ya d'ago kanshi ya kalli Abbi batare daya amsa ba, " Deen meke faruwa tsakaninka da Deeyanah ne?
"Me yasa kayi mata saki har uku?
Ido ya runtse da k'arfi jijiyoyin kanshi sunyi rad'o-rad'o kamar an zana su, still bayyi magana ba, tausasa murya Babah yayi yace " kayi mana bayani mana Deen, idanuwanshi da suka gama rinewa zuwa asalin jajaye ya saukewa Babah su, a kasalance muryarshi na sark'ewa ya bud'e baki da niyyar yin magana amma ya kasa "Babah....Babah... kawai yake fad'a bayan sunan ya kasa fad'in komai, dunk'ulallan kukan daya cure mishi a mak'ogwaro ya kufce mishi, wani irin kuka yake yi me tuk'uk'i da k'una, a hankali Babah ya sauko daga kan kujerar da yake zaune yaje wajen Deen, kamar jira Deen yake ya fad'a jikinshi ya k'ank'ame shi sosai.
" Deeyanah ta cuce mu, ta lalata mana komai, na tsaneta fiye da tsana, na tsaneta fiye da komai da kowa. Ya fad'a kamar ranshi zai fita.
Kyale shi Babah yayi kukan me isarshi while yana bubbuga mishi bayanshi, ya dad'e yana kukan kana ya d'ago daga jikin Babah ya goge hawayenshi, "alfarma d'aya nake nema a wajenku please, da ido Babah yayi mishi alamar ya fad'a.
"D'an Allah ku barni na tafi, ku barni nayi nisa da wannan duniyar nayi nisan nisa da kowa da komai, d'an jimmmm Babah yayi kana ya juya ya kalli Abbi da Ammi, a kid'ime ta rarrafo inda yake ta rik'e k'afafuwanshi "A'a dan Allah karka tafi ka barni a wannan k'azantacciyar rayuwa, kai ya kamata ka tayani yak'in Yaya, dan Allah karka tafi ka barni ni kad'ai bazan iya ba, fad'an yafi k'arfi na Yaya, ta k'arashe maganar da wani irin kukan mutuwa.
K'afarshi data rik'e yasa ya hankad'a ta baya da k'arfi, bata damu da hankad'ata da yayi ba ta sake rarrafawa gaban Abbi " Abbi ku taimake ni dan girman Allah, na rasa Deedee shi kad'ai ya rage min Abbi, kada ku bari ya tsige kanshi daga gare ni, mik'ewa yayi ya fice tabi bayanshi da gudu har zaninta na fad'uwa, gabanshi tasha ta zube a k'asa ta rik'e k'afafuwanshi gam " dan Allah karka barni.
"Dana fad'a miki idan kika ci amanata zanyi miki nisan nisa baki yarda ba?
"Kamar ban tab'a fad'a miki ina sanki fiye da so ba amma muddin kika ci amanata zan barki har abada ba?
"Deedee shine 'yar zaren igiyar data alak'anta ni dake yanzu ko babu ita, babu wani abu dayayi saura a tsakani na dake, ko a lahira bana fatan sake ganinki, yasa k'afa ya tureta yayi gaba, Abbi zayyi magana Babah yayi saurin dakatar dashi yana tuna wani lokaci a baya....
Tunani....
Cikin shagwab'a Deen ya kwantar da kanshi a kafad'ar Babah had'i da sanya hannu ya dafe k'irjinshi saitin zuciyarshi yace " wash!
Babah yace " ya akayi ne namijin duniya?
"Deeyanah ce Babah, ya fad'a yana k'ara narkewa Babah, "me Deeyanah tayi maka?
"Zata kashe ni Babah, santa gaf yake da sa zuciyata tayi bindiga.