← Book details Bakar Shuka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 56 OF 56

Sashe 56

Bakar Shuka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Sakamakon rashin hujja da shaidun da za'a gabatar a gaban kotu dan kotu ta samu gamsuwa yasa ni Alk'ali Bala Muhammad na yanke hukuncin korar k'arar had'i da rufe kundin shari'ar a ranar 20 ga watan 4 na wannan shekarar, ya buga stamp a jikin wata takarda ya mik'e, hannuwanta ta dunk'ule da k'arfi had'i da runtse idanuwanta.

"Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un! Abbi ya furta a zahiri cike da takaicin rashin nasarar da sukayi, jiki a sanyaye suka fito daga kotun suna shirin shiga mota ya k'araso inda suke yayi mata kallan cikin ido gami da tauna cingam, har ya juya zai tafi sai kuma ya dawo ya kalli cikin idonta yayi murmushi had'i da cewa " kina tunanin zakiyi nasara akaina ne!?

"Shifa Ubangiji ba azzalumin sarki bane, Ubangiji na kowa da kowa ne ko arne wanda ba musulmi ba ya rok'e shi zai amsa.

Hawayen data dad'e tana addu'a da fatan zubar su ne suka gangaro kan kuncinta, tasa yatsa ta d'auke hawaye had'i da kawar da kanta ta kalli gefe na tsayin seconds 2 kana ta mayar da kallanta gare shi tace " ka kuma yin nasara akaina, meyasa kake yin duk wad'annan abubuwan Ajlaal!?

"Meyasa kake san lallai dole saika lalata min rayuwata?

"Akan me wanne laifin nayi maka!?

Kallan rainin hankali ya watsa mata kana yayi murmushi yace " nima tambayar dana dad'e ina yiwa kaina kenan kafin na samu amsa ta a ranar da kike fad'awa mahaifinki da ahalinki sirikinki labarin silar faruwar komai, kuma ki daina cewa na lalata miki rayuwa, idan da wanda ya lalatawa wani rayuwa a tsakaninmu kece kika lalata min rayuwata, meyasa Deeyanah?

"Meyasa kika dagula komai keda k'awarki akan san zuciyarku?

" Meyasa ina zaman zamana lafiya da rayuwata a duniyata kuka shigo duniyata kuka tarwatsa min komai?

"Me nayi miki?

"Kin cuce ni! kin zalunce ni kin lalata komai Deeyanah, bamfa isa na canja kaina ba, ban isa na koma daddad'a kuma sauk'aka'k'iyar rayuwata kamar ta baya ba fa, ya k'arashe maganar hawaye nabin kuncinshi, ba k'aramin firgici ta shiga ba, tayi bala'in tsorata dan bata tab'a tsammanin yaji labarin ba, lalle akwai k'ura tunda har taga hawaye a idanun Ajlaal.

Cikin rawar murya tace " am....am... dan Allah kayi hak'uri wallahi ban san abun zai zama haka ba, nima shawarar k'awata nabi, na sani ni me laifi ce nice ummul aba'isin faruwar komai amma dan Allah kayi hak'uri ka kyale ni haka, idan ma fansa zaka d'auka akaina ka d'auki fiye da fansarka.

Yatsa yasa ya kawar da hawayenshi yayi murmushin da saida gabanta ya fad'i, lokaci d'aya taji yammmmm a cikin jinin jikinta.

"Gamuwar Gayya tafi ta gayya zafi Deeyanah! ada daban san silar faruwar komai bama banyi niyyar na kyale ki ba balle yanzu dana san kece kika zab'i hakan da kanki, wallahi bakiga komai ba yanzu ma aka fara wasan, sannan duk wanda yayi k’ok’arin shiga tsakanina dake saina ga bayanshi ko waye, haka duk wanda ya hanani aurenki a baya da kuma yanzu shima ya shirya ina nan zuwa gareshi, haka zalika duk duk wanda yayi k'ok'arin dakatar dani.... Lips d'inshi ya cije yana kallan Abbi, ya juya yabar wajen tabi bayanshi da kallo cike da matsanancin tsoro da fargabar da suka shige fiye dana koyaushe.

Ran Abbi a matuk'ar b'ace ya shiga gidan Ammu na zaune kan sofa tana sauraren karatun alkur'ani mai girma tana bi ya shigo, d'an kallansu tayi ta kawar da kanta gefe tana fad'in " sannu da zuwa!

Banza yayi da ita be amsa ba, dan yau haushin kowa yake ji kuma dai-dai yake da kowa, "saboda wulak'anci ace kana shari'a a kotu babu wanda zai tambaye halin da ake ciki, ko maganar babu wanda ya tab'a yi min, ta gane da ita yake dan haka ta mik'e zata bar wajen.

" Au wato ma dan wulak'anci shine ina magana zaki tashi kibar wajen?

"To Alhaji me kake nayi?

"Babu! nace babu! ya fad'a a harzuk'e, " Allah ya baka hak'uri bani nakar zoman ba, ta fad'a had'i da saurin barin wajen, nan Abbi ya zauna yana ta bambami babu wanda ya kula shi, Babah ma har yazo bakin k'ofa zai wuce zai shiga yaji bala'in yayan nashi, dan haka ya juya, sukayi kacib'us da Deen da shima part d'in zai shiga, " karka shiga neman wanda zai huce takaicin rashin nasararsu a kotu yake, aiko karaf a kunnen Abbi, nan fa ya k'ara harzuk'a ya zage yaita ruwan masifa kan me uwa da wabi har ma'aikatan gidan bai kyale ba, yayi iya yinshi babu wanda ya tanka mishi balle a samu wanda zai kula shi harya gaji dan kanshi ya bari.

K'arfe biyun dare tana zaune zaman dirshan a k'asan tile's a falo ba kuka take yi sai dai bala’in da take ji deep down gwara kukan sau dubu, ba zato ba tsammani sai ganinshi tayi a kanta tsaye, ta d'aga kai ta kalle shi batare da tayi magana ba, ta sunkuyar da kanta k’asa, “ Deeyanah!

Ya kira sunanta cikin taushin murya, kamar bazata d’ago ta kalleshi ba sai kuma ta d’ago, zubewa yayi gabanta bisa gwiwowinshi ya fakaici idonta cikin zafin nama Ajlaal ya shak'a mata wani abu a hancinta, a galabaice tana marisa ta kalle shi had'i da cewa " meee meee kaaaaa shak'aaa minnn!?

Baya tayi luuuuu zata fad'i ya tare ta, ta fad'a jikinshi ya sab'eta a kafad'a tare dayin waje da ita, d'an nesa da gidansu ya kaita inda zata iya hango gidansu tarwai ya ciro wata 'yar kwalba a aljihunshi ya shak'a mata a hancinata, batafi minti biyar da shak'a mata abun ba ta farfad'o, zambur tayi ta mik'e ta ja baya kanta ta kalla sosai kana ta fara waige-waige ta kasa fahimtar inda take ta dad'e kafin ta fahimci a inda take, ta juya ta fuskance shi maganarta na sark'ewa tace " meeeee neee neee kuma?

Murmushi ya sakar mata had'i da kallan cikin idonta ya d'age mata gira d'aya tare da nuna mata gidansu da idonshi, a d'an tsorace ta juya ta kalli gidan, ganin bataga komai ba, yasata sake kallanshi tace " me kake shirin aikatawa?

Bayyi magana ba illa murmushin daya sake yi mata had'i da sake nuna mata gidansu da idonshi, gidan ta zubawa ido na wajen minti biyar amma shiru, " wai me.......

Wata irin mahaukaciyar k'ara ce ta sakata yin shirun dole, saida k'asar wajen tayi girgiza ji kake durummmmmmmm! Dammmmmm! yadda kasan k'arar fashewar dutsen zuma rock ko gigitacciyar tsawar da akeyi lokacin damuna, durk'ushewa tayi a k'asa gami da sanya tafukan hannayenta ta toshe kunnuwanta.

Iface-ifacen mutane da salati ta fara jiyowa, a hankali ta zame hannayenta daga kan kunnuwanta, wani rikitaccen tsoro ne ya ziyarce ta lokaci d'aya, tana daga durk'ushen amma tana jin yadda k'afarta da jikinta ke rawa, dakyar ta tattaro d'an ragowar k'arfin daya rage mata ta mik'e, kallanshi take yi tana san tambayarshi k'arar meye amma ta kasa koda motsa bakinta balle ta iya furta koda kalma d'aya, fahimtar abinda take san tambaya yasa shi sake nuna mata gidansu da ido, tsoro, firgici da tashin hankali ne suka hanata juyawa ta kalli gidansu, hannunshi ya d'ora saman kafad'arta ya juyar da ita, idonta ne ya sauka akan gidansu dake ci da wata irin mahaukaciyar wuta, wata irin rawa k'afarta ta d'auka kafkafkaf jiri ya d'ebeta ya watsar gefe, kwakwalwarta ta tsaya cak, zuciyarta ta daina bugawa, komai nata ya tsaya cak ya daina aiki, yadda kasan mutum mutumin da aka dasa haka ta koma, tana ganin mutane nata ihuuuu ana tururuwar zuwa kai taimako amma ta kasa ko motsi, akan idanuwanta iyayenta, mijinta, yayyanta, 'yan uwanta da ahalinta gaba d'ayansu kaf suka k'one k'urmus tana jiyo salati da ihuuun azabar fitar ransu a cikin kunnenta amma babu yadda zatayi.

Duk iya k'ok'arin mutane sun kasa tunkarar gidan saboda tsananin k'arfin wutar daga nesa ma suna jiyo hucin wutar balle sunje kusa, ko mutum d'aya ba'a iya cetowa ba har ma'aikatan gidan sun k'one, jama'a sai tururuwa akeyi ana salati, bazata tab'a manta wannan bak'ar rana ba, ranar data rasa kowa nata a duniya, ta zama ita d'aya tilo tana reto a duniya, hoton wannan mummunar ranar bazai tab'a goguwa cikin kanta ba.

Babu abinda ke motsi a jikinta har idonta baya motsi yadai tsaya cak akan gidansu, murmushi yayi had'i da sunkuyawa ya kama hannunta yajata ba musu kamar rak'umi da akala tabi shi sukuku, duk inda ya cire k'afarshi nan zata d'ora tata kamar mutum mutumin da aka sassak'a da ice, babu abinda ta sani, ta manta komai da kowa, ita kanta ma ta manta wacece ita, babu abinda zata iya tunawa, yana rik'e da hannunta suka isa can nesa inda ya aje motarshi, ya bud'e mata gaban motar yace " shiga! amma ko gezau batayi ba, da kanshi ya saka ta cikin motar ya zaunar da ita, kana ya zagaya ya shiga yaja motar, bai tsaya ko'ina ba sai a harabar gidanshi, ya fito ya zagaya ya d'auke yayi cikin gidan da ita.

Saman bene ya hau da ita ya shiga d’aya daga cikin bedrooms ya shinfid’e ta saman gado, ya juya zuwa fridge ya bud’e ya d’auko kwalbar ruwan allura da saban sirinji yaja ruwan allurar ya kifa ta tare da mayar da gashin kanta gefe yayi mata allurar a k’eyarta, wata irin jijjiga jikinta ya d’auka lokaci d’aya hak’oranta suka rink’a kaf kaf kaf, bak’in cikin idanuwanta ya d’auke sai farin while idonta na far far far, ta dad’e haka kafin jikinta ya saki ta kwanta lakwas.

Kwashewa yayi da mahaukaciyar dariya tare da fad’in “ nayi miki allurar mantau na shafe miki duk abinda ke cikin kwakwalwarki kinyi loosing control sai abinda na sanar dake zaki yarda, ni kad’ai ne zab’inki kamar yadda na fad’a miki a baya, abinda naga dama dashi zaki yarda dole, nine dolenki sai yadda naga dama zanyi dake……
Chapter 56 · 0% Book details