← Book details Bakar Shuka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 56

Sashe 46

Bakar Shuka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tun daga wannan rana kullum Ajlaal sayya kira layinta ya tuna mata lissafin kwanaki, yauma tana tsaye a kitchen tana yankan albasa wayarta ta soma vibrating ko inda wayar take bata kalla ba ta cigaba da aikin gabanta, kira akayi tayi akai-akai, ta wawuri wayar a zuciye zata kashe ta, ganin ba number shi bace yasata sauke ajiyar zuciya a fili had'i da d'aga wayar, " ahhhhh! k'aunata yankan albasar ne ya hanaki d'aga wayata?

Wayar ta raba da kunnenta da niyyar kashe wayar yayi saurin fad'in " saura awanni 72 bi ma'ana kwanaki uku suka rage miki, na rantse miki da girmin Allah idan har baki yanke hukunci kafin wad'annan kwanakin ba saina sanar da mijinki duk abinda ke tsakaninmu na kuma bashi tabbaci ta hanyar tura mishi video.....

"Idan kuma ni na fad'a mishi da bakina fa?

D'auke wuta yayi d'if dan jin maganar yayi a bazata, d'auka yayi baiji abinda ta fad'a sosai ba, dan haka yace " eh!

"Eh!, nace idan kuma na riga ka na fad'a mishi komai da kaina fa shikenan barazana ta k'are?

Dariya yayi sosai me isar shi, dan dakyar ya iya tsayar da dariyar yace " wasa kake! wai irin ki bani mamakin nan, ko giya kike sha kya soma tunkarar Deen da wannan maganar?

"Zancen banza ma kenan, murmushi tayi me ciwo had'i da fitar da numfashi ta kashe wayar batare datace komai ba, gas d'in da take girkin ta kashe ta koma falo ta shiga safa da marwa tana tunani.

" Gwara kawai na fad'a mishi koba komai na huta da barazanar Ajlaal, kuma zan ji sauk'in nina fara fad'a mishi akan ace Ajlaal d'in ne ya fara sanar dashi, d'aki ta koma ta zauna saman gado, kamar an tsikare ta ta mik'e zambur ta shiga bathroom, babu abinda tayi a bathroom d'in ta fito ta sake komawa falo, ji tayi gaba d'aya gidan yayi mata zafi, tabbas da ba musulma bace ita da kirat d'in giya zata siyo ta shiga d'aki ta rufe kanta tayi tsirara ta sha giyar tayi mankas, wata k'ila idan ta bugu zata d'an manta damuwarta koda ta wucin dagi ce.

**********Idonta kan makekiyar tv bango tana kallan tashar sunna inda Malam Argugun yake wa'azi akan zaman takewar auratayya ji take tamkar sunanta yake kira yana wa'azin dan kusan gaba d'aya wa'azin ya shafi rayuwarta, da zamantakewar aurenta, wani hawayen bak'in ciki masu ciwo ne suka zubo mata, cikin kukan dake cinta tana danne shi tace " in sha Allah yau za'ayita ta k'are, bazan dauwamar da rayuwata cikin tsoro da firgicin tunuwar asirina ba, gwamma kawai na fad'a duk abinda zai faru ya faru.

Ta mik'e zata fita ya shigo sanye da jallabiya yatsanshi na latsa carbin tally counter, dakyar cikin dakewar zuciya ta runtse idonta da k'arfi muryarta na sark'ewa tace " in....ina....san....maga...na dakai, ta fad'a a rarrabe kamar me koyan magana.

"Nooooooo! Ajlaal yace da k'arfi had'i da wawurar computer gabanshi ya bugata da k'asa idanuwanshi sukayi jajir kamar wuta " a'a Deeyanah karkiyi min haka please, data ce zata fad'a mishi bai tab'a d'auka da gaske zata iya sanar dashi ba, bai d'auka tana da irin wannan k'arfin halin da dakewar zuciyar ba, yayi zaton shaci fad'i ne kawai ta fad'a ne danya kyale ta, dayasan da gaske take da yayi mata barazanar kashe shi idan ta sake ta fad'a mishi.

Ba musu ya k'araso ya zauna kan d'aya daga cikin kujerun har lokacin tana tsaye bata zauna ba, "ina jinki, yace yana bin jikinta dake rawa kamar mazari da kallo, kasa magana tayi ta kuma kasa zama, yakai mintuna goma a zaune yana jiranta, jin batace komai ba yasashi mik'ewa zai bar wajen, tayi saurin zubewa gabanshi had'i da rik'e k'afarshi gam ta saki rikitaccen kuka wiwi kamar wacce ake zarewa ranta.

Komawa yayi ya zauna ya zuba mata ido yana nazartar ta, an sake d'aukar lokaci batayi magana ba, bata kuma da niyyar yin magana, "Lafiya Deeyanah?

Ya fad'a a nutse, jajayen idanuwanta ta d'ago ta zuba mishi ta kalli cikin kwayar idanuwanshi, " bari na kalle ka Yaya wata k'ila bazan sake samun damar kallanka ina matsayin matarka ba, cikin rashin fahimta yace " ban gane ba?

Sake fashewa tayi da kuka tare da sake rik'e k'afafuwanshi gam, " na lalata komai Yaya, na wargaza komai, na cuci kaina, na lalata rayuwata nayiwa kaina babbar illa, na sari kaina da bak'in dafi, nayi BAK'AR SHUKAR da har in mutu bazata daina yad'o ba, Yaya BAK'AR SHUKAR danayi ce ta fara fidda bak'ak'en 'ya'ya, ka yafe idan zai yiyu Yaya.

"Wai meke faruwa ne?

Ya fad'a gabanshi na tsananta fad'uwa, sai da ta runtse idanuwanta da k'arfi dakyar ta motsa bakinta ta had'a kalaman " NA CUCE KA, NACI AMARKA Yaya, daga nan ta kwashe komai tasss tun daga farko har k'arshe ta fad'a mishi.

Ji yayi an fisgeshi an d'aga shi sama an buga shi da k'asa da k'arfi, kamar zararre ya kwashe da dariya yace " Deeyanah kenan a sani na baki da k'awaye balle ince sune suke zagaki ki rabu dani, idan har rabuwa kike san yi dani basai kin biyo ta wannan hanyar ba, dakin sanar dani da zan sawwak'e miki kuma na d'orawa kaina laifin idan ma iyayenmu kike ji, bazan bari kiyi laifi ba zan wanke ki a idonsu, cikin kuka ta kama kafad'unshi ta girgizashi tana fad'in " da gaske nake Yaya wallahil azim babu k'arya a magana ta.

Murmushi ya sake yi a karo na biyu yace " kice dai kawai kin daina so na Deeyanah ko kuma dama tun farko bani kike so ba matsa miki akayi batare da an tambaye ki ra'ayinki ba, zatayi magana ya dakatar da ita ta hanyar d'aga mata hannu ya mik'e yana fad'in " a gida d'aya aka haife mu muka girma, a d'aki d'aya aka rene mu, mutane d'aya ne sukayi mana tarbiyya Deeyanah idan har ke mace zaki iya aikata wad'annan abubuwan a tarbiyyar da aka bamu to ni namiji da yanzu ba'a san inda nake ba, ki rink'a tunani kafin ki zartar da abu ki tuna da mutuncin iyayenmu dana ahalimu dana gidanmu, koda ace kina san rabuwa dani bai kamata kiyiwa kanki irin wannan mummunan sharrin ba, zan baki kwanaki biyu kiyi tunani idan kinga kina san rabuwa dani shikenan, amma ki sani ina sanki, ina matuk'ar k'aunarki.

Tana gunjin kuka tana fad'in " na rantse maka da girman Allah da gaske nake, amma baiko juyo ba ya fice.

Bayanshi tabi da kallo cikin ranta tana jinjina girman yarda da amintar da yayi da ita, tabbas miji ne nagari, ya yarda da ita fiye da yadda ya yarda da kanshi, da kanta da bakinta ta sanar dashi komai amma duk da haka yak'i yarda ina kuma ga ace wani ne ya fad'a mishi, lalle Deen ya cika cikekken masoyin da za'ayi alfahari dashi a ko'ina a gaban kowa.

Tabbas yana zarginta amma ko kusa tunaninshi bai tab'a kaishi nan wajen ba, bai tab'a kai zarginshi ko kusa da nan ba, shi bama Deeyanah daya sani tun tana jaririya ba ko wata macen baya zaton zata aikata irin haka cikin hayyacinta sai dai idan an gusar mata da hankalinta, ya k'arashe tunanin yana gyara kwanciyarshi.

Kanshi ya d'aga sama yana kyalkyala dariya kamar kafuran farko, " duk da kin sanar dashi babu abinda zai canja yanzu ma aka fara wasan Deeyanah.

Yadda taga dare haka taga rana komai ya dawo mata sabo fil saboda kuka har muryarta ta dishe dakyar ta mik'e da lalube ta shiga bathroom dan bata gani sosai saboda kumburin da idanuwanta sukayi, turus tayi ganinshi zaune saman WC yana ganinta ya mik'e yana dariya " dama ke nake ta jira tun d'azu, hannuwanshi ya hard'e a k'irjinshi ya jingina bayanshi da bango, idonshi cikin nata fuskarshi d'auke da shu'umin murmushi.

"Malama Deeyanah kenan, kina ta cika bakin zaki fad'awa mijinki ki huta da barazana ta, banyi tsammanin da gaske zaki iya fad'a mishin ba, dan banyi tunanin kina da k'arfin hali har haka ba, amma bakomai tunda fad'a mishin bayyi amfanin komai ba, yak'i saurararki saima gwaleki da yayi yama d'auki maganar taki shirme, kuma shaci fad'i! ya k'arasa maganar had'i da tab'e baki ya d'aga gira d'aya irin I don't care d'innan, a hankali ya taka gabanta ya d'an sunkuya kad'an kasancewar ya fita tsayi, yakai bakinshi saitin kunnenta yace " karki damu har yanzu kina da sauran lokaci kuma ina nan ina jiranki, you're highly welcome k'ofa a bud'e take, ya k'arashe maganar had'i da hura mata iska a kunne ya kashe mata ido d'aya, ya rab'a ta gefenta zai wuce fuskarshi d'auke da murmushin cin nasara.

Har yakai bakin k'ofa zai fita ya jiyo muryarta tana fad'in " Yarda! aminta, yak'ini!

Juyowa tayi ta fuskance shi had'i da sakin hannunta data hard'e a k'irjinta ta furzar da iska daga bakinta tace " mema kace?

"Shirme! shaci fad'i! ya gwale ni, bai saurare ni ba ko?

Idonta ta bud'e tar cikin nashi tana kallanshi eyeball to eyeball tare da fad'in " duk ba su bane, Yarda! Amincewa da yak'ini ne, ya yarda dani fiye da yadda ya yarda da kowa da komai har da kanshi, ya aminta dani ya bani amana fiye da kowa, zuciyarshi nada yak'ini akaina shiyasa yak'i yarda da maganar duk da kasancewar ni da kaina da bakina na fad'a mishi, sai kayi tunani idan da wani ne ya fad'a mishi fa?

"Kwakwalwarka bazata iya hasaso abinda zai faru ba, so ka sani ba gwashale ni yayi ba, yarda dani da yayi yasa, bai zai tab'a tunanin irin wannan muguwar sakayyar daga gare ni ba.

Baki ya tab'e had'e da d'age gira d'aya irin bai dame ni ba, " duk da wannan tarin yarda da yayi dake kike san na wargazata ta hanyar nuna mishi videon blue film d'inki?

" Gaskiya bai kamata kiyi mishi wannan BAK'AR SHUKAR a zuciyarshi ba, dan bazata tab'a barin zuciyarshi ba, ina baki shawarar kibi shawarar daya baki ta sakinki kike son yayi, kice mishi eh kawai kinga asirinki bai tonu ba, ki dawo min mu dasa.
Chapter 46 · 0% Book details