← Book details Bakar Shuka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 56

Sashe 32

Bakar Shuka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Dan bai yiwa ni ina d'a namiji da duk kalar iskancin da zanyi dan iya yinshi ba aure ne akaina ba ko duniyar ce akaina zan iya aikata koma meye amma na kame kai na, ke da kike mace a k'ark'ashin ikona sannan ke keyin abinda kike so, wallahi Wallahi tallahi na rantse miki da girman Allah kika sake na kamaki da cin amanata saina barki har abada koda kece autar matan duniya, koda hakan yana nufin bazan k'ara aure ba har a nad'e k'asa, k'asa-k'asa yayi da muryarshi yace " wallahi koda hakan yana nufin mutuwa ta, kuma zan tsane ki tsana ta har abada, Deeyanah bazaki sake gani na ba a iya tsayin rayuwar da zamuyi a duniya, yana kaiwa nan ya juya ya barta nan tsaye.

In banda rawa babu abinda jikinta keyi, duk da sanyin ac dake d'akin bai hanata yin gumi ba, mak'ogwaronta ya bushe har wani d'aci-d'aci yake mata yayinda da zuciyarta da k'irjinta ke luguden bugu, ji take yi kamar ana d'agata sama ana bugawa da k'asa, idonta yaji yake yi mata sosai saboda tsantsar tashin hankali, jikinta a sanyaye ta zame ta zauna kan kujerar dake bayanta had'i da cusa yatsunta duka goman cikin gashin kanta, bata san sanda ta saki kuka me k'una da soya zuciya ba, kukan dake fitowa daga can k'asan zuciyarta, ta rasa yadda zatayi, ta rasa mafita gaba d'aya kanta ya gama kullewa b'am, wannan wacce irin bak'ar rayuwa ce?

In banda na shiga uku, babu abinda take fad'a, ta durk'ushe nan wajen taita rusa kuka wiwi.

Shi kam a b'angaren shi yana shiga bedroom d'inshi ya zube saman bed rigingine idonshi kan roping, tunanin daya fara zuwa kanshi shine koyaje ya sanar da iyaynsu halin da ake ciki?

Kanshi ya girgiza had'i da furta " ni! nakai k'arar mace saboda sex Allah ya kiyaye?

Har yamma tayi yana nan kwance yama rasa tunanin da zayyi, ko sallar azahar bayyi ba, " kodai wani ta samu wanda ya fini iya sex?

Ya furta a hankali, da sauri yace " Astagfirullah, ya yana k'ok'arin cire zargin daga ranshi amma sai me daram zargin ya zauna mishi, yayi-yayi ya kawar da tunanin cikin kanshi amma ya kasa, " to idan ba wani ta samu ba ya akayi take iya controlling feelings d'inta?

"Me yasa tunda na tafi har na dawo bata neme ni ba?

"Meyasa bata yi min dirty talks kamar a baya when he's not at home?

Duk yadda Deen yaso kar ya zargi Deeyanah amma abun ya gagareshi, yayi iya yinshi yayi kokowa da zuciyarshi da tunaninshi amma abun yafi k'arfinshi, dole ya yarda ya amince da cewar akwai wani a rayuwar Deeyanah bayanshi, zambur ya mik'e zaune had'i da dafe kanshi dake barazanar tarwatsewa, a jikinshi yake jin duk wani noti dake jikinshi yana kuncewa, wani abu yaji yana fita daga zuciyarshi da wani irin k'arfi, take yaji ya fara tsanarta tsananin kyankyaminta na shigarshi, a hankali ya fara d'an marin kanshi yana fad'in " a'a Deen wannan tunanin banza ne da aikin shaid'an la'anannen Allah, wani irin k'aramin hoto zuciyarshi ta hango mishi na Deeyanah da wani, ai bai san sanda ya mik'e tsaye ba, kawai sai tsintar kanshi yayi yana tafiya.

"Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un, ya shiga maimaitawa deep down yana jin wani mugun tsoro na shigarshi, " dole na sakawa Deeyanah ido, dole na binciko abinda take b'oyewa, dole na rink'a bin diddiginta kodan karta kai ni wuta, ya fad'a a zahiri yana rik'e k'ugunshi, duk yadda yayi iya yinshi dan kar ya zargeta abun ya ci tura sai da zargin Deeyanah ya shiga ranshi.

*************************************

Yana zaune a falo ta fito hannunta rik'e da hand bag d'inta while kunnenta manne da bluetooth, tunda abun ya faru bata sake bari sun had'u da juna ba, bata san meyasa take mugun jin tsoranshi da kuma kunyarshi yanzu ba, ko ido bata san su had'a, kanta k'asa tace " ina kwana, an tashi lafiya?

"Sai da ya d'auki lokaci kamar bazai amsa ba, kana ya amsa da " Alhamdulillah, tana kallan gefe dan bata san su had'a ido tace " dama saloon zani.

"Da da kika shirya zaki tafi kin tambaye ni ? “ba gaban kanki kikayi ba?

"Ko kuma da can da kike fita yawonki da izini na kike fita?

"Ko sai yanzu dan kin ganni a zaune shine kika tambaye ni?

Kanta k'asa cikin sanyin murya tace " ba haka bane dama niya nayi idan na fito sai na tambayeka, da har zaice ta koma sai kuma wani tunani yazo kanshi, " sai kin dawo, ya fad'a tak'aice, kamar wacce aka hankad'a, tayi wuf tabar wajen.

"Kai gaskiya kina fama, dama har yanzu halin miskilancin Deen yana nan?

Ajlaal dake kan waya ya fad'a, " hmmmm haka yake har yanzu babu abinda ya canja ga bak'ar zuciya kamar ta fir'auna, wallahi zuciyar Deen da a kafiri yazo ban jin bai karb'i musulunci, ta fad'a tana yiwa motar key ta fice daga gidan, sosai Ajlal ya saka dariya har da neman gwarewa, " uhmmmm wato an tab'o maka inda yake maka ciwo an kushe mak'iyinka ko?

Yana k'ok'arin tsaida dariyar yace " a'a ba haka bane, gani nayi keda kanki kika fad'a, "yanzu dai duk ba wannan ba, meye first sex ko abinci ?

“Dan yunwa nake ji ban karya ba.

" Sex ne farko amma tunda kina jin yunwa bari na saka kuku ya dafa miki wani abun ko nayi miki order, dan idan kina jin yunwa bazan samu biyan buk'ata ba gwara na fara ciyar dake kici kiyi fam kafin a soma harka zaki fi bani joy ma.

Murmushi tayi me kama da dariya ta bud'e baki zatayi magana ya zabura had'i da cewa " what?

“Menene?

Ta tambaye shi, k’ara ware idonshi yayi sosai tare da cewa.

"Kin san me kuwa?

Hankalinta kwance tace "a'a, " wallahi Deen yana binki a baya, wani irin mahaukacin birki ta taka a tsakiyar titi k'uuuuuu saura kad'an ta had'a mummunan had'ari " me kace?

"Deen na bina ko me kace? Tayi maganar cikin tashin hankali.

"Wallahi yana binki gashi nan a bayanki yana bin motarki, in slowly ta lek'a ta windo, aiko ta hangoshi ya samu waje nesa da ita yayi parking saboda ta tsaya, wata irin muguwar tsuma jikinta ya d'auka har hak'oranta na had'uwa kafkafkaf, " na shiga uku Ajlaal, shikenan Deen ya fara zargina, ta fad'a out of control, sai a lokacin ta fahimci maganar daya fad'a mata yanzu da zata fito " da can da kike fita yawonki da izini na kike fita, wato yawon dayake nufi tana fita shine yawon banza na zuwa wajen maza, kukan bak'in ciki ne ya kufce mata.

"Kin ga ki nutsu yanzu kina yin wani motsi zai gane kin san yana binki, ki cigaba da tuk'inki kamar baki san yana binki ba, jikinta na rawa tayiwa motar key ta taka motar a hankali, " yauwa ina kika ce mishi zaki?

Bakinta na rawa tace "saloon, " to yi can d'in, tafi wajen saloon d'in, jikinta ba b’ari ta tuk'a motar bata zame ko'ina ba sai wajen saloon d'in, shiko Deen dake biye da ita ya samu waje yayi parking yana jiran fitowarta.

"Shit! wallahi yau naci burin samunki dan har zak'ami nasha zan moreki amma wannan jakin banzan ya b'ata min target, aiko ya faro wasan da bazai iya k'arashe shi ba, muddin yace duk inda zakije zai biki wallahi saina wahalar dashi, da daddare kuma naje gidanshi, d'akinshi kan gadonshi na mayar da mahaifa, na zazzagewa matarshi kwayena, dariya tayi tace " ni wallahi abun ma mamaki ya bani, bak'in munafuki dana barshi a gida kamar ba komai a ranshi, ashe shima nan wai yana da wayo, a haka kamar mutumin kirki ashe tsohon banza ne.Dariya Ajlaal yayi harda dukan table d'in dake gabanshi yace " ke dai kika fad'a ni ba ruwa na, baki na da goro, dogon tsoki mstwwwwww taja had'i da cewa " Allah kuwa sumi-sumi dashi kamar na Allah ashe mutumin banza ne d'an cikiyar sharri, inba cikiyar sharri ba meye nabin bayana fisabilillahi?

"Yanzu ya jawo min zuwa saloon d'in da banyi niyya ba, zayyi magana ta tsaya cak had'i da cewa " wai tsaya ma tayaya akayi kasan Deen yana bi na a baya?

"Wait! Wait! Karka ce min yadda kake bibiyata shima haka kake bibiyarshi?

Cikin basarwa yace " koma dai meye ba gashi yayi miki amfani ba, "ashe ma ni yayiwa amfani?

"Ah to wa yayiwa?

"Ni dai kin san babu uban da nake jin tsoro ko a gabanshi kika d'aga min cinya zan shiga wallahi, ido ta waro kamar tana gabanshi tace " a gabanshi fa.

"Wallahi am telling you, shi d'in banza ma, tun yi yana da sauk'i zan kwasheki tsaf, tab! ina ruwa na?

Ajiyar zuciya ta sauke had'i da cewa " ah lalle! suna waya har aka wanke mata k'afa da hannu aka gyara mata gashin kanta, yayinda har lokacin Deen na zaune cikin mota yana jiranta, bata bar wajen ba sai yamma lik'is.

Zaune ta iske shi saman sofa tayi mishi kallan gefen ido had'i da jan tsaki cikin ranta, ta wuce yabi bayanta da kallo.

Bayan sati d'aya, sosai rigima ta b'arke tsakanin Ajlaal da Deeyanah dan ya fututtuke idan bata zo ba shi zai zo dole, hannunta rik'e da tea cup ta fito daga kitchen "haba mana Ajlaal kana ganin fa halin da ake ciki, ko so kake a samu matsala asirinmu ya tonu?

"Asirin mu ya tonu ko kuma asirinki ya tonu?

"Naji koma meye ni dai kayi hak'uri ka d'an bari a alafa, " a lafi me?

"Wallahi hak'uri na ya k'are bazan iya ba, sati d'aya kenan fa bamuyi sex ba, zatayi magana ya katse ta da fad'in " kinga idan zaki zo ki zo idan kuma bazaki zo ba zaki ganni a gidan wallahi, bai bari tayi magana ba ya kashe wayar, wayar tabi da kallo cikin ranta tana tunanin mafita.
Chapter 32 · 0% Book details