Sashe 36
Bakar Shuka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Ina san magana da Raleeya ne yau, ya k'arashe maganar had'i da sakin murmushin da bata isa ta iya fassarawa ba, yawun daya wuce mata ba shiri yasata kwarewa, sosai take tari while idonta kanshi tana kallanshi da idanuwanta da suka firfito kamar zasu fad'o k'asa, da k'arfi tsiya ta tsaida tarin, muryarta na shak'ewa tace " bari na shiga na kira ta, fuskarshi d'auke da murmushin har zuwa lokacin ya kafe ta da idanuwanshi dake k'ara firgita ta yace " nop! karki damu ba sai kin shiga ba, bari na samu yaro mu turo yayi yo mana sallama da mijinta in yazo shi sai yayi mana iso zuwa wajenta, " babu wanda fa ke shigar musu gida saboda tsaro, suna ma da k'attin k'arnuka, ta fad'a kamar me koyon magana, bai bi takanta ba ya bud'e motar ya fito, jikinta na rawa ta bud'e motar ta fito itama tana fad'in " ba saika aika yaro ba ka barni na shiga nayi mata magana mana.
Almajirin daya zo zai gifta shi ya kira tare da cewa " dan Allah shiga gidan nan kayi mana sallama dame gidan kome gadin gidan, Almajirin ya amsa da "to!, had'i da nufar gidan.
2
Hannuwanta ta dunk'ule waje d'aya had'i da d'aga kanta sama tana fad'in " Allah kada ka tozarta ni, Ubangiji kaji tausayi na kaji k'aina ka rufe min asiri nayau kad'ai, ta fad'a jikinta na wata irin muguwar kerrrrma, tare da wani kamilin mutum Almajirin ya fito, mutumin ya mik'awa Deen hannu suka gaisa fuskarshi d'auke da murmushi yace " bawan Allah ban gane ka ba?
Martanin murmushin shi Deen ya mayar mishi kana yace nine mijin Deeyanah, ya k'arashe maganar yana kallan Deeyanah, murmushin yak'e ta k'ak'aro ta shinfid'awa fuskarta, " ah Deeyanah ce wai, ni bamma kula dake ba ai, shine zaku tsaya anan, meyasa bazaku shiga ba?
Mamakin mutumin dabata tab'a ganinshi a duniya ba ya cika da yadda yake mata magana tamkar tsofaffin abokan da suka san juna sama da shekaru, " ina ya sanni?
"Ya akayi ya san sunana?
Kashe mata tunani yayi ta hanyar cewa " bakuyi waya da ita bane?
A dururuce cikin kame-kame duk ta gama rikicewa ta had'a uban gumi tace " wa?
Fakaitar idon Deen mutumin yayi ka kashewa Deeyanah ido d'aya, a fili ta sauke ajiyar zuciya had'i da sanya gefen mayafinta ta goge gumin dake tsatsafo mata, tasan wannan bakomai bane sai aikin Ajlaal, tana k'ok'arin saita kanta tace " anya bamuyi waya da ita ba, halan bata nan ta fita?
"Wallahi ta fita tun yamma bata dawo ba amma nasan yanzu zaku ganta, ku shiga ku jira ta, ido ta zaro had'i da cije leb'enta tana kallan mutumin ido ya lumshe mata tare da nuna mata hannu alamar bakomai ta kwantar da hankalinta, duk wata dak'ik'a ta duniya tare take bugawa da zuciyarta ta kafe Deen da ido tana jiran taji amsar da zai bayar yadda kasan k'irjinta zai fad'o k'asa haka take ji, " a'a bakomai ba sai mun jira ta ba, ma dawo wata rana, nannauyan numfashi ta fitar a fili gami da lumshe idanuwanta, Deen ya yiwa mutumin sallama ya shige mota dan gudun kar Deen ya zargi wani abu yasa tayi saurin bin bayanshi.
Tuk'in kawai yake yi amma hankalinshi baya jikinshi, motar tayi tsit sai sautin kukan Deeyanah dake tashi tana shashsheka, while tana d'an satar kallanshi, sai da sukayi d'an nisa kana ta d'ago ta kalleshi sosai tace " abun har ya kai haka Yaya?
"Har ya kai daka fara zargina kana kokwanto akan gaskiya da amanata?
"Ina dukkan yardar da kayi min?
"Ina tarin alk'awarirrikan da mukayiwa junan.....
Kallan daya jefa mata ne yasata had'iye sauran maganar, harya bud'e baki zayyi magana sai ya fasa, kuka ta fashe dashi wiwi kamar k'aramar yarinya, bayyi mata magana ba ya gangara gefen titi yayi parking, idanuwanshi ya runtse da k'arfi yana jin yadda kanshi ke barazanar tarwatsewa, a hankali ya bud'e idonshi da suka gama rinewa ya sauke su akanta, wani irin haushin ta yaji yana fisgarshi kamar ya rufe ta da duka, kwantar da kujerar motar yayi ya kwanta batare daya furta koda kalma d'aya ba.
Cike da mamaki ta kalleshi ta tuna a baya idan tanayi mishi kukan wasa danta tsokane shi kusan haukace mata yake yi, yayi ta rarrashinta yana lallab'a ta kamar kwai, amma yau itace take kuka a gabanshi ko kallo bata ishe shi ba, bak'in ciki yasata watsa mishi harara tare da goge hawayenta tace " ka kaini gida, ba musu ya d'ago had'i da yiwa motar key ya fad'a saman titi, har suka isa gida babu wanda ya sake yiwa wani magana a tsakaninsu, yana yin parking motar ya bud'e ya fice ya barta cikin motar tana bin bayanshi da kallo, cikin sanyin jiki da wani irin mugun tsoronshi ta mik'a hannu ta d'auki wayarta daya bar mata anan ta bud'e motar ta fita, koda ta shiga falon babu ko alamunshi cikin falon, kamar wacce kwai ya fashewa a ciki taja k'afa ta shige bedroom d'inta.
Tana shiga wayar hannunta ta soma haske alamar shigowar kira, sai da ta ja tsaki mtswwww kana tayi picking wayar, bata bari yayi magana ba tace " wai ya akayi kake sanin duk abinda zai faru ne tun kafin ya farun?
"Ya akayi ka san muna zuwa gidanka har kayi duk wannan shirin?
Dariya yayi sosai kana yace " shiyasa nace miki babu inda zaki shiga a duniya ki gujewa ganina da jina, bazaki tab'a iya b'oye min ba Deeyanah, duk inda kike ina tare dake, idanuwanta ta juya tace " kai ka sani, wannan mutumin waye shi?
"Ina zan san waye shi My Angel, idanuwanta waje tace " badai baka sanshi ba?
"Eh! ban sanshi ba, kanta ta dafe gami da runtse idanuwanta tace " ya Salam!
"Ya akayi ne?
Yace yana kai cokalin abinci bakinshi, " okay wato kai bama ka damu ba ko?
"Kaje ka d'auko mutumin da bamu sanshi ba ka saka shi cikin sabgar mu, baka tsoron wani abu ya biyo baya?
"Baka tsoron ya tona mana asiri?
"Rashin sanin nashi da bamuyi ba shiyasa babu abinda zai biyo baya, kuma shiyasa bazai tab'a tona mana asiri ba, dana ji kuna magana da Deen na tsaya tsai na fahimci nan gidan zaku zo, shine na fita waje can wata unguwa wacce kwata-kwata bata da had'aka da nan area na samo mutumin da zayyi presenting mijin Raleeya, bai san mu ba, bai san komai akan mu ba, bashi da wata makamar da zai tuna mana asiri tunda bai ma san asirin namu ba balle ya tone shi.
Sassanyan murmushi tayi me kyau ta kwanta kan gado cikin ranta tana jijjinawa kaifin kwakwalwa da basirar da Allah yayiwa Ajlaal, " naji kinyi murmushi, murmushin ta sake yi a karo na biyu, " yauwa kin sake yin wani, suka saka dariya a tare, " gobe zani wankin k'afa in sha Allahu, wata k'illa ma nayi jan lalle, "dan Allah kiyi min jan lalle yana bala'in yi miki kyau sosai, " in sha Allah zanyi maka, yana k'ok'arin kashe wayar tace " dama da maganar da nake sanyi dakai please.
"Okey Ina jinki!
Sai da tayi gyaran murya kana tace " kaga saboda rashin bawa Deen kaina da banayi ya fara zargin da akwai wani abu, kuma yana bala'in saka min ido yanzu sosai, d'an shiru tayi yace " uhunnn ina jinki cigaba da managarki, dan ya riga yasan k'arshen maganar, cikin in i na da rawar murya tace " shine dama nace idan ka bani izini ka yarda ka amince ka barni na rink'a bashi kaina ko sau d'aya a sati ne dan Allah, bayyi mata magana ba ya kashe wayarshi, wayar ya jefa saman gado had'i da jan tsoki "mstwwwww banza butulu kawai duk abinda nake yi mata, duk iya k'ok'arin da nake yi akanta amma a banza hankalinta yana kan mijinta sakarya mara wayo kawai.
A b'angaren ta kam wayar ta cire daga kunnenta tare da zubawa wayar ido, ta dad'e tana tunani, ta sak'a wancan ta kunce wancan har dare.
Da sassafe ta tashi ta gama duk abinda zatayi da wuri, tayi wanka ta shirya tsaf ta zauna tana zaman jiran fitowarshi a falon, ganin lokaci yana neman k'ure mata gashi tana san tayi har jan lallen yasata mik'ewa ta nufi hanyar bedroom d'inshi da raban data bi har ta manta, cikin d'an tsoro-tsoro tayi knocking, sai da ta d'auki lokaci tana kwankwasa k'ofar d'akin kana cikin isa ya bud'e baki dakyar kamar baya so yace " waye?
"D'an wulak'anci, in banda wulak'anci wa yake tsammanin zai buga mishi k'ofar d'aki?
Ta fad'a cikin ranta, a zahiri kuma cewa tayi " nice, a dak'ile yace " meye?
"Saloon nake san zuwa wankin k'afa da k'unshi, sai da ya d'auki lokaci bayyi magana ba, harta fidda rai daga samun amsar shi ta juya zata bar wajen taji yace " kije kawai, ina da abubuwan da zanyi masu mahimmaci, bata bashi amsa ba tabar wajen, jakarta da wayarta ta d'auka ta fice bayan ta zira hijab, bata jin zata iya tuk'i dan haka bata d'auki mukullin mota ba ta fice daga get d'in gidan, tana tafiya a k'afa yana biye da ita a baya a mota har ta fita bakin titi ta tare me Napep ta hau, yana biye da ita har shagon saloon d'in, me Napep d'in ya aje ta a wajen ta bud'e jakarta ta d'auko kud'i ta biyashi ta shige, nesa da wajen yayi parking yana jiran fitowarta, kanta da k'afarta aka fara wanke mata kana aka zana mata jan lalle me kyau yadda kasan d'orashi akayi a k'afar.
Bayan ta biya ta fito kunenta lik'e da waya tana murmushi tace " kaima kasan saika fara gani kafin shi, idan ma ya gani ai iyakacinshi ganin kawai, gani kuma ai ba tab'awa ba, ba ci ba, yana dariya sosai yace " nace ki bari nazo na d'aukeki amma kin k'i ko?