← Book details Bakar Shuka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 56

Sashe 49

Bakar Shuka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya fad'a a haukace yana nufarta, baya tayi da sauri cike da tsoro, da iya k'arfinshi ya damk'i wuyanta ya gwara da mirror, mirror ya tsage kanta ya fashe, sai lokacin yaji kuka, aiko ya fashe da mahaukacin kukan mutuwa wiwi, kamar k'aramin yaro ya rink'a rusa kuka, ya zage iya k'arfin shi ya shiga dukanta kamar yadda zai daki namiji d'an uwanshi, yana dukan yana fad'in " me ya fini?

"Soyayya ya fini iyawa ko kuma sex d'in ya fini iyawa?

"Joy stick d'inshi tafi tawa girma kuwa dad'i ya fini?

"Dame na rage ki?

"Me na gaza mishi dashi?

"Nawa ne adadin kud'in da yake baki da ni bazan iya baki ba?

"Kika k'aurace min, kika haramta min abinda Allah ya halatta min kike je kina bawa wanda Allah ya haramta miki kanki, duk irin san da nake yi miki Deeyanah meyasa?

"Meyasa zakiyi min haka?

Ya fad'a yana kuka kamar ranshi zai fita, sosai yayi mata mahaukacin duka, bai daina dukanta ba saida ya tabbatar bata motsi sannan ya daina dukanta, k'asa ya zube yana mayar da numfashi, wani irin d'aci yake ji daga mak'ogwaranshi zuwa bakinshi, yasan yau kam komai nashi ya k'are, yasan yau duniyarshi ta k'are, yau al k'iyamarshi ta kama, har lokacin bai daina kukan ba.

Babah na dawowa daga sallah yaga wayam sai d'igon jini, da mamaki yake bin jinin da kallo, fita yayi ya tambayi wasu suka ce sunganshi ya hau napep, mota ya shiga yaja ya nufi gida ranshi cike da tarin tambayoyi fal, get d'in dake k'arye yabi da kallo mamakinshi na k'aruwa, cikin nutsuwa yayi parking ya fito dai-dai lokacin Abbi ya fito daga part d'insu da sauri ya nufi part d'insu Deeyanah, Babah yayi saurin cewa " wai lafiya?

"Meke faruwa ne?

Turus Abbi yayi yana kallan Babah yace " ban sani ba tun d'azu dai nake jiyo ihuu da kuka k'asa da k'arar fashe-fashe, " to ikon Allah, tare suka shiga cikin gidan, ya sata gaba ya kifa kanshi a tsakankanin cinyoyinshi yana sharb'ar kuka, a hankali suka turo k'ofar d'akin suka shigo dan sun jiyo sautin kukanshi, cikin tashin hankali suka nufe shi, " meke faruwa Deen?

Babah ya tambaya yana danne tsoronshi, jajayen idanuwanshi ya d'ago ya sauke su akansu, sai da gaban Abbai da Babah ya fad'i saboda kallan da yayi musu, " lafiya!?

"Meya faru dakai ne?

Babah ya sake tambayarshi yana bin d'akin da kallo, komai dake cikin bedroom ba a dai-dai yake ba an canjawa komai gurin zama, an fasa na fasawa, an lalata na lalatawa, yadda kasan filin wasan dambe na duniya, Abbi ya bud'e baki zayyi magana idonshi ya sauka akan Deeyanah dake kwance shame-shame cikin jini, " Subhanallahi!, yace yana nufarta sai lokacin Babah ya kula da ita, jijjiga ta Abbi ya shigayi yana kiran sunanta amma shiru bata motsa ba, jikinshi na rawa suka kamata shida Babah sukayi waje da ita, Deen na zaune yadda yake bai motsa ba, a kujerar baya suka kwantar da ita, Abbi ya zagaya da sauri ya shiga motar, Baba ya lek'a ta window yace " kaje da ita bari na taho dashi a dubashi kaga sai zubar da jini yake yi ba, Abbi bayyi magana ba yaja motar yabar harabar gidan.

Da hanzari Babah ya koma cikin gidan, maganar duniya yayiwa Deen amma bai tanka ba da ido kawai yake binsai yadda kasan me tab'in hankali, hannunshi Babah ya kama yaja shi ya biyo shi sakaka sai kace dolo, sanda suka isa asibitin har an shigar da Deeyanah Emergency room, da Doctor Babah ya had'a Deen, likitan yasa nurses sukayi mishi d'inku nan ciwukan dayaji a k'afa da hannu, akayi treatment d'inshi, likitan yaso ya bawa Deen gado saboda yadda jininshi yake a mugun haye, amma yak'i ya kafe kan shi bai kwanciya a asibiti, dole tasa ya k'ale shi.

Yana zaune kan kujera Abbi da Babah na tsaye suna magana a junansu, yayi kasak'e har lokacin bai furta koda kalma d'aya ba, bai ma san a duniyar da yake ba, har lokacin tantama yake shine Deen, shin da gaske abin yake faruwa ko kuwa dai mafarki yake yi.

Likitan ya fito daga Emergency room yana cire hand gloves, da sauri Abbi ya tare shi yana fad'in " ya jikin nata?

"Alhamdulillah da sauk'i amma dukan da akayi mata yayi yawa dan har ya jawo zubewar cikin dake jikinta na watanni hud'u, koma me tayi bai kamata ayi mata irin wannan mummunan dukan ba, babu kalmar dake kai komo cikin kanshi sai cikin jikinta, kalmar ta k'arasa birkita mishi komai, duk bayanin da likita yake yi babu abinda ya fahimta sai wannan kalmar, da gaske dai Deeyanah taci amanarshi, da gaske ta wargaza musu komai, ta riga ta tarwatsa ahalinsu, ta d'ai-d'aita farin ciki da kwanciyar hankakinsu, shekaru uku, shekaru uku tayi tana azabtar dashi ta hanyar k'aurace mishi, shekaru uku tayi basu had'a shinfid'a ba balle jiki, shekaru uku sukayi wata ma'amalar aure bata gifta ta tsakaninsu ba, amma itace d'auke da cikin wani, baya tunanin an tab'a cin amanar wani mahaluk'i a doron k'asa sama dashi, sosai zuciyarshi ke tafarfasa tana azalzalarshi, tabbas yau da ace shi ba musulmi bane da rufe kanshi zayyi a d'aki yasha giya yayi tatul kana ya kashe kanshi.

Komai ya d'auke mishi d'if duniya ta tsaya mishi cak, wannan wacce irin b'akar k'addara ce?

Ba Deeyanah ba kad'ai duk wata mace dake duniya sai da yaji ya tsane ta, a ranshi yake jin da za'a tattara mishi matan duniya gaba d'aya da sayya zazzaga musu fetur ya cinnna musu wuta, Cikin abinda bai wuce mintuna biyar ba yayi shawara tafi dubu, k'irjinshi ya dafe had'i da fashewa da rikitaccen kuka yana fad'in " mutuwa zanyi Abbi, Deeyanah ta lalata komai, ta gama tarwatsa min rayuwa da duniya ta, babu abinda yayi saura, komai ya k'are, wayyo Allah na, na shiga uku, inama mutuwa tazo ta d'auke ni, inama na mutu kafin ganin wannan bak'ar rana, inama ba'a halicce ni ba...

Saurin rufe mishi baki Babah yayi yana fad'in " haba Deeni sai kace ba musulmi ba, kana neman kaucewa hanya, me yayi zafi haka?

Bayyi musu magana ba ya mik'e yana dafe da kanshi ya soma k'ok'arin barin wajen, ya d'aga k'afarshi ya yanke jiki ya fad'i ji kake timmm, jiki na kerrrma Babah yayi kanshi, yayinda da Abbi ya tafi kiran Doctor.

"Sai da nace mishi zan bashi gado yak'i, likita ya fad'a yana saka mishi Cannula a hannu, ajiyar zuciya Babah ya sauke a hankali cike da damuwa yace " jinin nashi bai sauko bane har yanzu?

"Ina fa ya sakko, saima k'ara hawa da yayi sosai, kuyi addu'a dan komai yana iya faruwa dashi, ina jiye mishi tsoron paralyze ko heart attack.

"Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un, wai meke faruwa a tsakanin yaran nan?

Abbi ya fad'a yana kallan Babah da yayi suman tsaye kamar an dasa shi, ya kasa magana.

**************************

Yana zaune saman sofa ya d'ora k'afa d'aya kan d'aya akan dinning table hannunshi rik'e da gwangwanin lemo yana sha fuskarshi d'auke da makirin murmushi idanuwanshi akan laptop yana kallon abinda ke faruwa ta mini hiding camera daya baza ta ko'ina a gidan, zan iya cewa kusan kaf gidan ya b'oye 'yar k'aramar camera sirri wacce ta nan yake ganin duk wani motsinta.

Yaga duk abinda ya faru har makahon dukan da Deen yayi mata, yaji babu dad'i har cikin ranshi, ranshi ba k'aramin sosuwa yayi da dukan ba, amma tunda ita ta zab'arwa kanta hakan shikenan ya barta, da ace gari watsagal yayi mata wannan dukan da sayya tsinke mishi numfashi, mik'ewa yayi yana kurb'ar lemon yace " na fad'a miki duk duniya babu mai sanki sama dani.

Bayan kwanaki biyu....

Deeyanah ta farfad'o tun a daren da aka kawo ta, anyi mata tambayar duniya meke faruwa tsakanin su tak'i cewa komai bata da aiki sai kuka, ko kalma d'aya bata iya furtawa ba, hakan ya k'ara tabbatarwa da iyayen da akwai gagarumar matsala, a b'angaren Deen kuwa har lokacin bai farfad'o ba, hankalin kowa yakai mak'urar tashi damma likita ya tabbatar musu da babu matsala.

Washe gari da safe kusan gaba d'aya zuri'arsu suna d'akin Deeyanah, suna ta fama da ita kan taci abinci ko yaya yake amma fur tak'i, a d'akin Deen kuwa d'akin ba kowa dan likitoci sun hana kowa shiga a cewar su ciwonshi baya buk'atar hayaniya, idanuwanshi ya bud'e lokaci d'aya ya sauke su akan POP bai sha wahala wajen k'ok'arin tuna komai ba dan da komai ya farka tangaran babu abinda ya manta, k'arin ruwan da ake yi mishi ya fisge ya dafa bango ya mik'e yana bin bango ya fice daga d'akin yana layi da tangad'i ya nufi hanyar fita daga asibitin Abbi da Babah daya hango yasashi saurin rab'ewa dan a zatonshi wajen shi zasu, ganin sun shiga wani d'akin daban ba wanda ya fito ba ya sashi sake bin bango ya nufi d'akin, a hankali ya tura k'ofar, bayyi zaton tana asibitin ba, komawa yayi da baya.

"Dan Allah ara min paper da biro, ya fad'a da kyar, ba musu nurse d'in ta mik'a mishi, rubutu yayi a paper daya yaga kana ya mik'a mata biron ko godiya bai tsaya yi mata ba yabar wajen, d'akin da aka kwantar da Deeyanah ya koma ya tura k'ofar ya shiga, hankalin kowa yayi kanshi Ammi da Ammu dake gefe suka kalli juna kana Ammi tace " ka farka?

Saboda tsabar yadda idonshi ya gama rufewa bai kula da tarin jama'ar dake d'akin ba, ita kawai yake gani, gaban gadonta ya k'arasa ya mik'a mata takardar hannunshi yana fad'in " na sake ki saki uku, daga yau na datse igiyoyin da suka dabaibaye ni dake, daga yau na yanke duk wata alak'a dake tsakaninmu, bani bake har abada bana fatan sake ganinki a rayuwata.
Chapter 49 · 0% Book details